BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

OK gani nan zuwa yace “yanufi wurin motarsa escort dinsa suka bud’e masa yashiga,
Suma suka shinshiga cikin nasu motocin suka nufi Asibityn.”


Kwance yake akan gadon Asibityn Sauk’i yasamu garesa Dan kuwa ba abinda yakeji yana masa ciwo a jikinsa,
Likita kawai yake jira yashigo ya sallame shi,

Gabansa yakeji yana fad’uwa akai akai,
Da zarar yaji hakan ba wacce take fad’o masa a rai sai Safna,
Tabbas yasan tana cikin mawuyacin hali,
Musamman rashin ganinsa da batayi ba, bataga yatura wurin maigariba domin a tsayar da ranar aurensu, dolene tashiga cikin damuwa.”

Runtse idonsa yayi yanajin wani abin yana bugar masa zuciya wanda yarasa ko meye shi,
Babu abinda yake gani sai Fuskar safna yake kallo a idonsa,
a lokacin da take ce masa , “Yarima inasonka zanyi biyayya a gareka, zan zama tamkar baiwa a gareka,
Kada kajuyamun baya idan katina DA ni shigeyace bana da iyaye.”

Hawaye suka shiga zuba a gefen idonsa,jikinsa yasoma rawa,
ji yakeyi kamar ya tashi ya tafi k’auyen a d’aura masu aure da ita ya d’aukota ya taho da ita domin yabata gata tabbatar da cewa MARAYU MA ‘YA’YA ne kamar kowa.,

Hajjah tana ganin zubar hawayensa wanda har tagaji da ganin suna fita a idonsa,
tin Tana Tausayinsa tana tambayarsa damuwarsa har ya Kai ta zuba masa ido tana kallonsa,
Dan tasan halin sauban sarai akwaishi da zurfin ciki, idan zai shekara dubu da abu a ransa yana damunsa baxai tab’a furtawa ba, hakan zai barshi a ransa yayita damunsa, yana ramewa sai dai idan kai ka fahimta da kanka snn ka magance masa matsalar cikin salama.”
Hakan yayi a lokacin Auren Saudat bai furta baya sonta ba,
Sai da akayi bikin yashiga cikin damuwa yana ramewa,
Tambayar duniya ba wacce ba’ayi masaba akan ramar da yakeyi kodai auren da akayi masa ne baya so,
Hakan zai girgiza kai alamar yanaso shi ba abinda yake damunsa,
Sai daga baya da hajjah ta saka masa ido anan ta fahimci baya son Saudat shine dalilin ramar tasa,
Hakan tayita kwantar masa da hankali akan ya rik’e matarsa hannu biyu tinda anriga da and’aura auren har ankawota gidansa,
Dole ne Ya koyawa zuciyarsa soyayyarta illaso daga baya idan yasami wacce yakeso sai ya aure ta.”

sai gashi shigowar Saudat gidan lokaci d’aya tashiga ran hajjah saboda tsananin son da takeyiwa sauban wanda bata iya b’oyeshi a duk inda take ko a gaban waye,
Snn shigowar saudat cikin gidan lokacin sauban yasami kwanciyar hankali da zama a lafiya a cikin masarautar dan kuwa gimbiya jamila tsoron mahaifiyar saudat takeyi.”

Maimartaba ya turo k’ofa yashigo da sallama,
Ganin hawaye suna zuba a idon yarima ya dakatar da fadawa akan kada sushigo su dakata waje ya mayar da k’ofa ya rufe.”

Cikin takon mulki yake takowa ya isa gaban gadon sauban ya sanya hannu ya dangwalo hawayen dake fita a gefen idonsa,
ya dubesu da kyau cike da mamaki ya tabbatar da tabbas hawaye ne ke zuba a idon magajin sarki,
Cikin gid’ima sarki yake kallonsa bakinsa yana rawa yace “magajin Sarki hawaye a idonka?” Ina raye a duniya?”
Meyafaru?”
Ina yake maka ciwo?”
Sam ba girma bane hawaye su dinga fita a idon gwarzon namiji kuma magajin Sarki, tashi zaune muyi magana.”

Jiki a sanyaye sauban ya tashi zaune yana kallon mahaifin nasa,
Hannu Sarki yasaka ya shafe masa hawayen fuskar tasa,
Yana kallonsa yace “bani labarin abinda yake damunka Wanda inada raina da lafiyata magajina yake zubar da hawayena akansa.”

Kallon mahaifinsa sauban yayi ya sunkuyar da kai yace “Abba damuwata safna ce.”

Sarki yasaki wani murmushin irin nasu na manya,
Hajjah taja dogon tsaki ta juyar da kai gefe, domin ita wlh ta d’auka wani abin can daban yake damunsa ko yake masa ciwo wanda yake sakashi yana zubar da hawaye.
Ita tarasa ko yaushe sauban ya susuce yazama raggo hakan DA. har yake zubar da hawayensa Mai tsada a kan macce.”

Sarki ya juya ya kalli hajjah yasaki murmushi snn ya nemi wuri ya zauna a gefen gado a kusa da sauban ya kallesa yana murmushi yace “fad’amun meyasami safna d’in?”

Kallonsa sauban yayi ya sunkuyar da Kai k’asa yace “inaji a jikina akwai wani mummunan abu da yasameta,
Abba Safna abar tausayice bata da iyaye bata da kowa sai Allah saini dana d’auki Alk’awari Zan taimaketa,
Abba bawai son safna nakeyiba kawai ina tausayin halin da take cikine,
DA kuma Wanda zata shiga idan tarasani,”
Abba Ina neman Alfarma a Karo na farko a wurinka itace katura fadawa yanzun nan sutafi k’auyen domin a tsayar da ranar aure na da Safna,
domin gudun kada asami Matsala a cikin Al’adarsu.”

Murmushi Sarki yasaki Wanda har sai da hakoransa suka fito,
Yana kallon sauban cike da wauta wai ba sonta yakeyi ba, bayan ga soyayyarta nan ya gani k’arara a cikin idonsa,
Murmushi Sarki ya kuma saki yana kallon sauban Yace “hakan kakeso a aiwatar yanzun magajin sarki?”

D’aga kai sauban yayi alamar eh.”

Sarki yace to “idan maigari yace a lokacin yake so d’aura
auren naku a tsaya a amso maka aurenta ko kuwa abarshi rana kawai kakeso asaka maka?”

Shuru sauban yayi ba amsa.
Sarki yasaki dariya wacce yasaka sauban shima ya d’an murmusa cike dajin kunya,
Sarki yace kabani amsa kai nake saurare domin da kaina zantafi ba aikeba “

Cikin jin kunya sauban ya sunkuyar da kai yace “duk yanda kace ranka ya dade a aiwatar da hakan.”

Sarki ya kuma sakin dariya yace “wnn amsar kai zaka bani ita,
Saboda a lokacin da kake zubar da hawayen k’auna baka nemi shawara daniba.”

Cike da jin kunya sauban ya kuma sunkuyar da kai sarki yana ganin hkn ya had’e fuska cike da zulaya yace “to shikenan Zan fasa tafiyar zan tura fadawa Zan ce masu da zarar suntafi akace za’a d’aura aure a lokacin zance kabada umurnin “kada a d’aura kai baka ra’ayin hakan, rana kawai kakeso asaka maka,
Idan sukace ba hakan sukeyiba,
Zance kace kabarwa duk Wanda yake sonta a d’aura dashi.”

Da sauri sauban ya d’aga Kai ya kalli Sarki yaga da gaske yake ba wani alamar wasa a tare dashi yace “ranka ya dad’e ba hakan nake nufiba, a d’aura auren dani, sutaho tare da ita.”

Dariya ta sub’ucewa sarki wacce tasaka sauban jin kunya,
Yayi saurin kwanciya tare da juya baya yana murmushi cike da jin kunya.”

Hajjah tana jin duk abinda sukeyi bata tanka masuba domin ta dade da sanin Sarkin Abdullah shi yake sakanta sauban yake yin duk abinda yaga dama.”

Sarki ya mik’e tsaye yana murmushi ya kalli hajjah yace “umma zamutafi karb’owa jikanki Aure a k’auyen gidan gonarsa, saiki shirya tarbon kishiya ta biyu.”

Mere baki hajjah tayi tace kafin a d’aura ayi binciken asalinta da abinda ya kashe iyayenta domin naji yana fad’in bata da iyaye,
Snn a tabbatar da asalinsu mai kyau ne tafito a cikin gidan asali, da daraja basa da wani abin fad’a,
kodan samun zuri’a mai tsafta,
Snn kada ka manta a cikin gidan sarauta zata shigo shi kuma gidan sarauta duk Wanda kagansa yashigo cikinsa a matsin matar Sarki KO d’an Sarki KO jikan Sarki dolene ya zamana yana da asuli Mai kyau.
Idan babu wnn to tabbas bata cancanta da zama matar saba dole ne ya barta duk son da yake mata.”

Gaban sauban ya fad’i dajin furuncin hajjah.”

Sarki yace “tabbas hakan ne umma,
Sai dai inaji a jikina kamar farin cikin da mahaifiyarsa take fad’ar masa zai samu a cikin gidan gonar sa,
Ina hasashen shine ya fara bayyana a garesa.” Domin samun macce ta gari babban farin cikin d’a namiji, yasami rabin duniyarsa domin kullum cikin farin ciki zaiyi ta zama har k’arshen rayuwarsa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button