DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL
Yanufi k’ofar fita yace “muntafi,
Hajjah tace “adawo lafiya.”
Snn Sarki yafita ya bawa fadawa umurnin sushiga mota,
ya fad’a masu inda za’a tafi,
Suka d’auki hanyar k’auyen Lassa.”
Suna fita daga asibityn Anawa Sarki jiniya,
Alhaji Habib Naira shima yashigo da tawagarsa sarki yabada umurni a tsaya,
hakan shima Alhaji Habib yaba da umurni a tsaya, anan suka fito daga motar suna dariya suka shiga gaisawa da juma cike da farin ciki da kewar juna,
Tare da tambayar yaushe rabo,
Domin Alhaji Habib business dinsa baya barinsa zama yau yana wannan k’asa gobe yana wancan k’asa jibi yana wancan k’asa.”
Anan Alhaji Habib yake tambayar Yaya Sauban?” Ai yanzun
Yasan yaron ya girma sosai.”
.dariya sarki yasaki yana fad’in sosai kuwa har yayi aure,
Yanzun hakan k’arb’o masa auren mata ta biyu zamu tafi muyi.”
Kuma tab’awa sukayi suna dariya Alhaji Habib yace “yaro yayi gadon ajiye mata da yawa,
kaine baya ko ni.”
Sarki yasaki dariya yana fad’in lafiyar kenan, ai duk Wanda ya ganmu yasan ba rangwanci a tare damu.”
Suna dariya tare da zolayar juna sukayi sallama ko wanne yashiga motarsa Alhaji Habib yana fad’in abokina kafin natafi zan shigo fada domin asakamun Albarka,
Sarki yana dariya yace “badamuwa sai ka shigo,
Sukaja mota suka tafi cike da farin cikin ganin juna domin abokanaine sosai kasuwanci ne yarabasu da junansu.”
Sarki yana fita daga asibityn likita yashigo ya k’ara duba jikin sauban yaga yasami lafiya,
Anan take ya sallamesu direba tare da fadawa suka d’aukesu a mota suka nufi gida su.”
Dawowar dakaru da labarin da sukaje dashi na tarwatsa k’auyen su safna ba k’aramun farin ciki yasaka Saudat da mahaifiyar taba,
Musamman dasukaji cewar Safna ta mutu domin,
Sunce dajin da tabi da gudu anan ne maciji ya kashe biyu daga cikin mutanensu, suma dakyar suka sha,
Suna da yak’inin ko gaggar jikin safna baza’a gani bare gawarta shikenan ta mutu sai dai wata ba itaba”
Wayyo dad’i a ranar Saudat kid’a tasaka a b’angarenta saboda farin ciki sai cashewa takeyi tana rawa, tana juyawa Yau duniya tamata dad’i, gaba d’aya ta manta da mijinta dake kwance akan gadon asibity.”
Har sauban yadawo gida batasaniba,
Hakan ya nufi part d’insa ya shiga toilet yayi wanka yafito, yasaka k’ananun kayansa marasa nauyi farin wando riga bak’a,
Yunwa yakeji amma babu abinci a b’angaren nasa,
Hakan ya janyo ‘ya’yan itatuwa ya soma ci,
Ciyakeyi yana lumshe ido
Babu abinda yake masa yawo a kai sai magagganun da hajjah tayi akan Safna, sune suke masa yawo sunaso su birgita masa,
kwakwalwa,
Wad’anda take cewa dole ne a binciko asalinta atabbatar da suna da kyakkyawan asali basa da wani abi fad’i, domin duk wacce taza shigo gidan sarauta dolene sai in tana da cikakken asali mai kyau
To yanzun idan sarki ya shiga bin ciken asalinta yasami cewar tsintar ta akayi a gefen hanya,
ana nufin bata da asali shegiyace Shikenan.”
Rasa zaiyi bazai taimaki rayuwarta ba?”
Runtse idonsa yayi yanajin zuciyarsa tana k’una,
Jiyakeyi duk abinda zai faru sai dai yafaru amma bazai tab’a barin rayuwar safna ta sallawanta ba, akan wani dalili can nasu na masarauta.”
sautin kid’a yakeji yana tashi a part d’inta Wanda duk ya damesa ya hanashi sukuni bare yayi tunanin mafitar abinda yake damunsa, kwakwalwarsa da kansa duk sun har gitse,
Cikin zafin rai yafita yanufi part dinta,
Har ya tura k’ofa yashiga batasaniba abinda baitab’ayiba shiga d’akinta.”
Manyan mata yagani su hud’u kwance a kan gadonta KO wacce ba kayan kirki a jikinta,
Tana tsaye a tsakiyar d’aki sai rawa takeyi tana juyawa, irin rawar da turawa sukeyi idan suna cikin farin ciki.”
Wani bak’in ciki ya kamasa ya kashe soket d’in,
Jin shurun da tayi ba sauti t
Yasa ta juya a fusace domin ganin Wanda ya kashe mata sauti.”
Ido biyu tayi dashi tsaye a bayanta,
Anan take gabanta ya fad’i,
Ta juya da sauri ta kalli matan da ta ajiye a kan gadonta.”
ajiyar zuciya ta sauke ganin ba abinda suke aikatawa a kwance kawai suke,
Kallonta yakeyi cike da tsana da takaici da ace shi ma’abucin dukan macce ne da yau babu abinda zai gana ya daki saudat yayi mata duka irin na mutuwa.”
REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S✍
???? D’AN SARKI SAUBAN????
Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)
Page 30
ALHAMDULILLAH ALLAH NAGODE MAKA DOMIN KAINE ABIN GODIYA,
INA KUKE MASOYA DA ABOKANAN ARZIKI INA GODIYA A GAREKU DOMIN KUN NUNAMUN KULAWA BABU ABINDA ZANCE SAI DAI NAYI MAKU FATAN ALHERI A DUK INDA KUKE, DA MASU KIRAN WAYANA DA MASU TUROMUN MASSAGE DUKA NAGODE ALLAHU YA BAR K’AUNA NAJI SAUKI SOSAI ALLAH YABANI IKON FARANTA MAKU NAGODE NAGODE NAGODE????????????????
* kallon tsana Sauban yaci gaba da wurgawa Saudat, cike da jin haushi da tak’aicinta,
yaja dogon tsaki ya juya ya bar wurin yanufi d’akinsa,
Kan gado ya kwanta rigingine ya rufe ido yana tunanin mugun hali irin na Saudat.”
Saudat kuma tana ganin ya yafita,
A fusace ta juya ta kalli ‘yan matan dake kwance a kan gadonta ta sakar masu harara cike da bak’in cikin ganin da mijinta yamasu a hakan, wani irin kishin mijinta taji ya taso mata, taja da baya ta jingina a bango tana sauke numfashi da sauri da sauri kamar wacce tayi gudu, hawayen bak’in ciki suka shiga kwarara a idonta, bakad’an taji zafin ganin da sauban ya masu cikin tsinanun kayan dake sanye a jikinsu ba,
Bud’e idonta tayi wad’anda suka rine zuwa launin ja, ta d’orasu akansu, ta warga masu kallon tsana,
A fusace ta daka masu tsawa tace “kutashi kufita na tsaneku, bana son nasake ganin fuskokinku,
Kuma kusani sai kun d’and’ani azabata mai tsanani sakamakon ganin tsaraicin da mijina yayi maku
Tin yanzun kuzab’awa kanku horo mafi tsanani kafin na zab’a maku da kaina.”
Gabanta suka kai durk’ushe tare da had’e hannayensu wuri d’aya alamar ban hak’uri,
Suna fad’in ranki ya dad’e tuba mukeyi,
Ki gafarcemu bazamu sake ba, bamusan yarima zai shigoba ayi hakuri ya uwargijiya mai Adalci,
“Kufita nace tare da nuna masu k’ofa waje,
Cikin sauri suka fita suka bar d’akin.”
Juyawa tayi tafita tanufi d’akin yarima,
tura k’ofar d’akinsa tayi sannu a hankali da sallama a bakinta,
Jin shuru ba’a amsa bata ba yasa taja ta tsaya tana kale kale a ina zata ganshi
A can kan gado ta hangosa kwance yayi rigingine idonsa a rufe tamkar Wanda yakeyin bacci,
Ajiyar zuciya ta sauke tashiga takawa sannu a hankali ta nufi wurinsa,
A gefen gadon taja ta tsaya a dai dai saiti kansa ta d’an sunkuyar da kanta tana kallon kyakkyawan gashin kansa wanda yake kwance a kansa tamkar gashin kan jariri,
Hakan ya kuma sanya fuskarsa tayi kyau da adon,
sajensa Wanda yake zagaye da fuskarsa har zuwa bakinsa, tashiga kallo anan take tsikar jikinta ta tashi tafarajin wata irin matsananciyar sha’awarsa tana dirar Mata,
Tana’ tsananin son gashin bakinsa, tana son tayita kallon kyakyawar fuskarsa mai cike da Annuri,
A hankali ta sanya hannu ta shiga shafa masa gashin bakinsa tana fad’in “Sadaukina kayi hakuri idan na b’ata maka rai.”
Idonsa ya bud’e ya d’orasu a kanta ya wurga mata wani irin kallon tsana snn ya mayar da idonsa ya rufe.”
Firgicewa tayi da kallon da ya Mata,
Ta kuma narkewa tana basa hakuri,
Shuru yayi bai tanka Mata ba,
sai da tayi magiya ta gaji, ganin baya da niyar tanka mata yasa ta tashi nufi kicin domin shirya masa abinci wata k’ila yunwa yakeji, ko ganin hakan zai sanya zuciyarsa tayi sanyi.”