BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL


Alhaji Habib Naira yana shiga cikin Asibityn gaba d’aya idon mutane sukayo kansa,
Anan take masu Neman taimako suka zagayeshi domin shi mutumin jama’a ne, mutum ne mai Alheri da tausayi
Dan hakan da zarar jama’a sukayi ido biyu dashi to kukansu ya kare domin Alhaji Habib Naira zaiyi masu kyautar girma da ban mmki.”

Hakan aka zagayeshi sai kud’i yake bawa mabumuk’ata, da gajiyayyu,
Da gyar escort nashi suka da katar da sauran jama’a snn yasami hanyar wucewa ya isa wurin matarsa Hajiya laila wacce take zaune a cikin mota tana kallonsa.”

Motar da take ciki escort nashi suka bud’e masa ya shiga,
Idansa akanta yana sakar mata murmushin so da k’auna a duniya bayan iyayensa babu abinda yakeso da ganin farin cikinsa kamar hajiya laila,
Janyota yayi zuwa jikinsa ya rungumeta yashiga share mata hawayen dake zuba a idonta, cikin sigar lallashi yake kwantar mata da hankali akan ta d’auki kaddara akan duk abinda ya faru ta daina sanyawa ranta damuwar b’atan suhailat.”

Doguwar ajiyar zuciya Hajiya laila taja snn tasakarwa mijinta murmushi tare da rik’o hannunsa duka biyu ta saka a cikin nata hannun ta d’an matse kad’an cike da shauk’i
tashiga fad’in na daina mijina ina Addu’a a koda yaushe Allah ya k’aramun dauriya da dangana a kan rashin tilon yata danayi.”

Dariya Alhaji yasaki yace “Ameen tare da kashe mata ido d’aya yana fad’in insha Allahu wnn dawowar danayi sainayi k’ok’ari nabaki wata Suhailat d’in kinga shikenan na kashe bakin magana.”

Dariya tasaki tana fad’in “kai Alhaji bakada dama mezan iya tsofai tsofai dani.”

Hararar wasa ya sakar mata yana fad’in “a Ina tsofan yake, a yanda nakejinki kinfi sabuwar budurwa dal a leda komai,
Dan kuwa duk Wanda ya kalleki yasan nayi dace nayi sa’a a cikin maza samun kyakkyawar macce mai tsafta da iya ado uwa uba ga k’amshi, ni kuwa me zanyi da wata macce a duniya idan kina tare dani.”

Murmushin farin ciki take saki domin tana yawan jin wnn yabon a bakin gwarzon mijin nata,
.”nagode mijina Allah yaci gaba da faranta maka kamar yanda kake farantamun.”

Ameen yace tare da cire hannunsa cikin nata yana fad’in “mutafi naga marar lafiyar Allah yasa ta farfad’o.”

Hakan suka bud’e k’ofa suka fita fuskokinsu cike da farin ciki escort suka take masu baya suka nufi d’akinda Safna take ciki a kwance cikin mawuyacin hali.”

Wurin gadonta suka nufa inda Alhaji Habib naira yana yin ido biyu da fuskarta sai da gabansa ya fad’i, yayi saurin k’arasawa wurin gadonta yana kallonta,
Hajiya laila kuma ta juya tana bawa escort umurni akan su dakata a waje kafin sufito,
Snn ta juya ta cewa Alhaji mutafi, ganin baya kusa da ita, yasa
Cikin sauri d’aga kai ta hangosa a bakin gadon safna yana k’are mata kallo cike tausayi,
Wurin ta nufa taja ta tsaya a kusa dashi tana fad’in Alhaji kaga yarinyar ko gwanin ban tausayi,
Dam gabanta ya fad’i da tayi ido biyu da safna wacce a lokacin ta farfad’o daga allurar baccin da akayi mata.”

Cikin sauri hajiya Laila tanufi wurin safna tana kallonta ido ciki ido Wanda itama safna kallonta takeyi hawaye suna mata zuba a gefen idonta,

Sannu yaya jikin naki Hajiya laila tace.”
D’aga Kai safna tayi alamar da sauk’i,
Hawaye kawai kezuba a idonta ga wani irin fad’uwar gaba da takeji tarasa sanin kona meye.”

Suna tsaitsaye akan gadon safna ba Wanda ya kuma yin magana dukansu su uku gabansu sai fad’uwa yakeyi bakinsu ya rufe ba Wanda ya kuma furta kalma d’aya,
Likita ya turo k’ofa yashigo tare da sallama.”

Gaida Alhaji yyi snn yanufi wurin safna,
yacire mata ruwan da ya k’are ya kuma juna Mata masu,
Ido kawai safna take bin koya dashi tana kallo hawaye suna Mata zuba,
Gyaran murya likita yayi ya kalli hajiya yace “Alhmdulillah ba wata matsala a tare da ita,
Duk iya gwaje gwajen da mukayi mungano buguwa ce kawai tayi a kanta Wanda insha Allah nan da kwana biyu zata sami lafiya.”

Alhaji yace Allah ya k’ara bata lafiya.”

Suka amsa da “Ameen.”

Muryar safna ta tsinke masu magana da take kallon Hajiya laila tace “umma zan sha ruwa, yunwa nakeji.”

Dam gaban Hajiya laila ya fad’i, dajin yarinyar takirata da suna umma sai taji sunan ya dace da ita, karon farko Taji wani girma ya darar mata taji k’aunar yarinyar ta shigeta a lokaci d’aya, idonta ya cika da hawaye tayi saurin sanya hannu ta share ta matsa a kusa da Safna ta d’ora Hannu a saman goshinta tana gyara Mata gashin kanta daya kusan lullub’e mata fuska tace “yata yunwa kikeji?”

Safna ta d’aga Kai, alamar eh.”

Hajiya laila tasaki murmushi tace “kada kidamu yanzun za’a kawo mki abinci kinji.”

Safna ta d’aga kai alamar “to.”

Hajiya Laila ta janyo kujera ta zauna tana murmushi tana kallon fuskar safna, domin lokaci d’aya ta tsinci kanta cikin farin ciki da k’aunar wnn yarinyar sai takeji kamar ‘yarta ce Suhailat ta dawo gareta.”

Alhaji Habib naira yana tsaye a kansu yana kallonsu cike da farin ciki Dan kuwa shima a lokaci d’aya soyayyar yarinyar tashiga ransa.”

Hajiya laila ta kamo hannun safna ta rik’e tace “meye sunanki ‘yata.”

“d’an murmushi safna tasaki domin kalmar da hajiya laila takirata da ita ta ‘yata tayi matukar yimata dad’i
domin tinda tayi wayo ta girma idan aka cire Baba ba Wanda ya tab’a kiranta da wnn kalmar ta ‘yata, azahiri wasu har kyamatarta sukeyi basa son tarab’esu, saboda tana shegiya bata da asali,

Hawaye suka wanke mata fuska da ta tuno da Baba,
Ta kalli hajiya cikin muryar kuka tace “sunana Safna.”

Hannu Hajiya laila tasaka tana share mata hawaye dake zuba a idonta tana fad’in daina kuka ‘yata daga yau kukanki ya k’are,
Wanne gari kike suwaye mahaifanki domin Zan tura a sanar dasu halin da kike ciki don gudun kada ayi ta nemanki.”

Bana da kowa ni kad’ai nake rayuwata, kowa kyamata yakeyi, mahaifina kuma ya rasu
Ta fashe da kuka mai sauti gwanin ban tausayi.”

MRS ANAS BAWA

REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

Page 31

Runtse ido hajiya Laila tayi domin tanajin Sautin kukan Safna yana ratse KO wanne lungu da sak’o na jikinta,
Hannunta tasaka tarik’o hannun safna cike da tausayi, ta tashi daga kan kujerar da take a zaune ta hau kan gadon da Safna take a kwance ta janyota zuwa jikinta ta tsura Mata ido sosai tana kallonta snn tayi k’arfin halin yin magana tace “daina kuka Safna,
Allah ya jikan mahaifinki da rahama,
Ki kwantar da hankalinki daga yau kukanki ya k’are bak’in cikinki ya k’are idan duk duniya kowa yana kyamarki mu bama kyamarki domin zamu taimakeki zamu taimaki rayuwarki.”

Girgiza kai likita yayi cike da tausayi, Wanda yake tsaye a wuri d’aya yana jin duk abinda yake faruwa,
Hanyar fita yanufa yana mai tausayin rayuwar safna,
yarinya k’arama mai k’ananun shekaru kyakkyawa amma bata da gata, tabbas rayuwarta abar tausayice .”

Bayan fitar likita daga d’akin, direban Alhaji Habib ya turo k’ofa yashigo yana rik’e da ledodin abinci Wanda Alhaji yabashi umurnin ya sawo,
A gaban Hajiya laila ya durkusa ya ajiye snn ya juya ya fita.”

Hajiya Laila ta tayar da Safna zaune cikin dabara da kwantar da hankali tashiga bata abinci da kanta tana kumajin k’aunarta da tausayinta suna ratsata, hakan shima Alhaji Habib shi yake tsiyaya mata ruwa a kofi yana bata tare da yimata nasiha akan ta d’auki kaddara a duk yanda tazo mata a matsayinta na musulma.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button