DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL
A k’auyen lassa maigari da fadawansa tare da mutanen gari dake zaune suna zaman makoki akan yan uwansu da sukayi rashi, mutanen k’auyuka na kusa da garin sai ketarowa sukeyi suna masu jaje tare da gaisuwa, KO wanne yana zaune a fadar maigari maza da mata sai jimami akeyi,
Suna hakan zazzaune jigum jigum sukajiyo jiniyi tare da manyan motoci suna shigowa cikin garin.”
hankalin kowa ya tafi zuwa wurin domin KO ba’a fad’a masuba tabbas sun tabbata wnn jiniyar da yawan motocin wnnan tafiyar Sarki ne da kansa ba yarima.”
A gaban fadar maigari sukayi parking din motocinsu a jere, inda maigari ya mik’e tsaye tare da mak’arabbansa suka nufi wurin motor Sarki domin tarbonsa,
Manyan Fadawan sarki suna Rik’e da manyan buloli, suka zagaye motar Sarki KO wanne ya bud’e babban rigarsa suka kare bakin motar Sarki zaifito daga mota.
Saida yafito aka kuma gyara masa rigarsa snn suka janye domin bawa Sarki hanya ya wuce.”
Taku yakeyi cike da k’asaita fadawa suna zuba masa kirari yanufi wurin maigari dake tsaye wuri d’aya tare da hakin mansa cike da farin ciki,
Babbar kujera aka d’orawa sarki ya zauna, snn mutanen gari suka shiga kawo gaisuwa d’aya bayan d’aya,
Sarki yana murmushi yana amsawa fadawa suma suna amsawa, yana k’arewa garin kallo da mutanen dake cikinsa ganin duk mutanen dake cikinsa a hargitse suke,
Bayan an kammala gaisuwa,
kowa ya nemi wuri ya zauna, ana zaman sauraren abinda sarki yazo dashi domin duk a tunaninsu jaje yataho yamasu.”
Gyaran murya sarki yayi yafara da cewa, “Alhmdulillah Ina matuk’ar godiya da wnn tarba da nasamu a gareku hakika na dade da sanin mutanen garin nan masu karamci ne da karrama bak’o,
sai dai wannan zuwan da nayi na fahimci gaba d’aya a halin garin dama garin baki d’aya suna cikin damuwa da firgici meyake faruwa?”
Kallon juna suka shigayi ganin a she Sarki baisan abinda yake faruwa ba,
Cikin girmamawa maigari ya sunkuyar da Kai yashiga bawa Sarki labarin duk abinda ya faru ya rufe daga k’arshe ya rufe maganar da b’atan Safna wacce yarima yayi shad’i akanta, tare da mahaifinta har yanxun ba’a gansuba, ba’a sami labarinsu ba.”
wasu suna fad’in sun mutu, mafi inganci Labari Wanda mukaji a bakin matar mahaifinta gata can a zaune cewar guduwa sukayi basu mutuba.”
“Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un sarki yake fad’i cike da jimami da tausayawa,
Maigari ya kalli inno yace matso kiyi masa bayani yanda abin yafaru,
tana rawar jiki ta matso ta Kai durk’ushe a gaban Sarki tare da sunkuyar da kai tana fad’in ranka ya dad’e ba mutuwa sukayiba guduwa sukayi, nima naso nabisu mugudu a tare, fad’uwa nayi sakamakon k’usa da nataka a k’afata,
Ranka ya dad’e Allah kawai ya k’addari zan rayu da a kwai kwana na gaba,
saboda a lokacin da nafad’i sai da wani k’aton garde yabi takaina ya wuce yana fad’in zamu dawo mu iyar da kaiki lahira, Inajin hakan na d’aga kaina naga sun dafawa su Malam da safna wad’anda suke rik’e da hannun juna suna gudu,
Ina ganin g
Hakan Nashiga jan ciki har nasamu nakawo kaina bayan gida a k’ark’ashin wani iccen mangwaro a nan na b’uya har suka dawo sunata nemana basu ganniba.”
Ta fashe da kuka tana fad’in ranka ya dad’e “Safna Annobace rayuwarmu tunda malam ya tsintota a kan hanya ya kawota cikin gidanmu muke had’uwa da bala’i iri iri, Allah kad’ai yasan irin zuri’ar su.”
Fadawa suka daka mata tsawa, ganin nan take fuskar Sarki ta canza alamar b’acin rai, suka shiga fad’in “gyara kalamanki sarki ya gaji da saurarenki kina iya tashi kitafi.”
Tana gogar hawaye hannunta d’aya rik’e da zanenta, tanufi wurin zamanta,
Snn Sarki yayi gyaran murya ya kalli maigari yace “gaskiya ne abinda wnn matar tafad’a akan yarinyar da yarima yayi shad’i akanta?”
“Gaskiya ne ranka ya dad’e bamusan asalinta ba a gefen gari malam Audu ya tsinto ta ya kawomun ita, daga k’arshe yanuna yanason ya taimaketa zai rik’eta domin bai tab’a haihuwa ba.”
Girgiza Kai Sarki yayi domin duk inda ransa yake ya b’aci,
Wato Sauban yana nufin shegiya ‘yar tsintowa zai aura ya shigo da ita cikin gidan sarauta mai cike da asali kyakkyawan tarihi,
Murmushi Sarki yasaki ya danne b’acin ransa yace “hak’ik’a nayi bak’in ciki da tausayin abinda yasami ahalin garin nan Wanda har yayi sanadin mutuwar wasu rayunka daga cikinku,
Kuyi hakuri Ku d’auki kaddara Zan taimakeku Zan tsaya tsayin daka domin ganin ko suwaye suka aikata maku hakan.”
Had’a baki sukayi suna godiya,
Snn Sarki yabada ‘umurni a bud’e but a d’auko kud’i abawa duk Wanda yake wurin dubu ashirin kafin yayo masu aike.”
Hakan aka shiga rabamasu kud’in suna godiya cike da farin ciki tare da yiwa Sarki fatan Alheri,
Snn Sarki yamik’e yashiga mota fadawa suka maramasa baya yafita daga k’auyen KO gidan gona baiyi tunanin zaigashiba domin duk inda ransa yake a b’ace yake.”
Sauban kwance a cikin lambun dake part d’insa inda yake yawan zama yana shan iska, Safwan zaune a gefensa yana bashi labarin yanda ginin kamfaninsa ya wakana bayan kwanciyarsa a asibity, irin cigaban da aka samu, a kamfanin wurin ganin ginin ya fito yayi kyau,
Kasan cewar Safwan yaci gaba da gudanar da komai har komai ya kammala a yanda yasan sauban yakeso.”
Fad’a masa yakeyi irin kud’in da aka zubawa wurin gaskiya maimartaba ya taka rawar gani domin ganin komai ya maka a yanda kakeso,
Banza dashi sauban yayi sai dannar wayarsa yakeyi yana kuma kallon kan screen din wayar,
Ba komai yake kalloba sai hotunan Safna wad’anda suka zamar masa madubin dubawarsa akoda yaushe.”
A zahirance Kuma duk abinda Safwan yake fad’i yana jinsa yana kuma saurarensa sosai yakejin dadin maganar da yake masa akan kamfaninsa Wanda shine cikar burinsa.”
Safwan baidamu da rashin kulawar da sauban baiyi masaba domin idan da sabo ya isa ace yasaba da wnn murd’and’en halin nasa, Wanda duk yanda kake dashi baka isa ka gane farin cikinsa ko Akasin hakan ba,
Yaci gaba da cewa “a gaskiya Abba yana sonka duk a cikin ‘yayansa ba wanda yake son yadinga ganin farin cikinsa kamarka,
Shawarata anan abokina itace kaci gaba da yiwa Abba biyayya ka faran tamasa kamar yanda akoda yaushe yake k’ok’arin yaga ya faranta maka,
Allah ya k’ara masa lafiya da nisan kwana.”
Sai a lokacin sauban ya d’aga Kai ya kalli Safwan yasakar masa murmushi yace “Ameen.”
Tare da d’aukar lemu dake cikin cup yakai bakinsa ya d’an kurb’a snn ya ajiye,
Ya kalli Safwan yace “wani lokacin kana magana cikin natsuwa da hankali tare da fahimta, wani lokacin idan kayi wata maganar nakanji kamar na rufeka da duka.”
Dariya Safwan yasaki yana fad’in Allah yabaka hakuri Dan nasan ka kusan sanya fadawa su dakeni,
Murmushi Kawai sauban yasaki,
Safwan ya kallesa yace Abokina nafa manta ban fad’a makaba,
Na kusan zama Daddy Dan kuwa Allah yayi najefa kwallo a cikin raga,
Saura Kai, a gaskiya ya kamata kayi k’ok’ari daren yau kada kayi bacci har sai kasamu kajefa kwallonka a cikin raga.”
Had’e fuska sauban yayi ba alamar dariya a tare dashi yaci gaba da dannar wayar hannunsa,
Jiniyar motocin sarki sukaji hakan ya tabbatarwa sauban Abba yadawo kenan.”
Shima Safwan yanajin hakan ya mik’e yace “Abokina nizan tafi domin kuwa kasan banason Ina Jan dogon shak’o bana kusa ga love d’ita bare Kasan yanzun laulayi mukeyi,
Ya d’an sunkuya gefen kunnen sauban kamar zai fad’a masa wata magana Wacce bayason kowa yaji,
cike da tsoKana yace “wai kasan wani abu kuwa gani nakeyi kamar ‘yan uku ne na zuba Mata a mahaifa.”
Yana kaiwa nan yasaki dariya yayi tafiyarsa.”