DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Bak’in ciki duk ya gama lullub’e gimbiya Jamila sai zufa take fitarwa gaba d’aya a jikinta kamar wacce tafito daga wanka,
tarasa mafita, anan take tashiga tunanin,
ita Abdullah zai yaudara,ita Abdullah zai zalinta ace saura sati d’aya d’aurin aurensa Amma bai fad’a mataba meta mashi a rayuwa?”
Takai zaune dafe da Kanta hawayen bakin ciki suka Fara wanke Mata fuska.”
Shuru tayi tashiga tunanin yaushe rabonta da Abdullah,
Yaushe rabon da su tsaya suyi magana Kota minti talatin ne,
Baza Manta Yana yawan aiko kuyangi kiranta mantawa takeyi Bata zuwa har ya gama jiranta yayi tafiyarsa,
hakan ko a wurin kwanciya,
Tana d’akinta Yana d’akinsa Bata zuwa wurinsa Domin jitakeyi tayi aiki ta gaji hutu take buk’ata,
Shi Kuma Abdullah namijine Wanda baya bin macce d’akinta duk yanda yakejin buk’ata idan Bata kawo kantaba sai dai ya hakura.”
Wani kuka yazo Mata Mai k’arfi tayi saurin rufe bakinta dan kada kuyanginta sujita Su fahimci halin da take ciki,
ta shiga fad’in nashiga uku “
Ko saboda hakan zai k’ara Aure?”
Wlh na daina Abdullah kazo kace mun kafasa Auren Nan zan gyara duka kuskurena.”
Mik’ewa tayi ta shiga toilet ta wanke idonta tafito ta Fara shirya tarbon mijinta, Domin yau ta shirya bashi hakuri idan wani laifi tayi Masa ko wani kuskure Wanda zai Sanya ya k’ara Aure yayi hakuri ta daina zata tarairayeshi fiye ma da da,
Abinda Bata saniba Abdullah ya tsufa a zamfara bazai dawoba sai da matarsa.”
Shuru ba Abdullah ba labarinsa har zuwa k’arfe goma na dare Wanda a iya saninta dashi baya kai k’arfe goma batare da yadawo gida ba.”
Wasa Wasa har safiya ta waye ba Abdullah, hakan yasa ta yanke hukuncin zuwa sashen Sarauniya Hajjah Domin ta tambayeta ina Abdullah ya tafi duk da dai har da sa hannunta Abdullah zaiyi Mata kishiya.”
Zuwanta wurin Hajjah anan Hajjah take fad’a Mata ai Abdullah Yana zamfara bazai dawoba sai angama d’aurin aure sa.”
Wani bak’in cikin da takaici Mai had’e da zazzafan kishi ya rufe idon jamila Anan take tashiga fad’awa Hajjah maganar da duk tafito a bakinta taciwa hajjah mutumci
Daga k’arshe tace ita meyasa sarki baiyi mata kishiyar bane.”
Ido kawai Hajjah tabi Jamila dashi cike da mamaki da Al’ajabi Domin a duniya babu Wanda ya tab’a ci Mata mutumci ido cikin Ido kamar Jamila surukarta matar d’anta.”
Sai da Jamila ta gama cin mutumcinta snn tafito daga b’angaren Hajjah a fusace tanufi sashenta zuciyarta na k’una da rad’ad’i.”
Bayan d’aurin auren Bintu da Abdullah, aka d’auko Amarya daga masarautar zamfara zuwa masarautar Adamawa, wani sabon bikin ne aka had’a a gidan Ango tare da wasanni irin na gidan sarauta, Wanda hakan ya K’ara kunawa Jamila rai ganin ita a lokacin da aka auro ta ba ayi hakan ba, ta Kuma d’aukar wani Alwashi a ranta, tare da Jin tsanar Bintu Mai tsanani ta d’arsu a zuciyarta.”
Shigowar Bintu a cikin gidan sarautar canji ya Fara samuwa a cikin gidan, Domin duk wani k’unci da ake Sanyawa fadawa da bayi tare da kuyangu duk ya kau, Domin Bintu macce ce wacce ta tashi a gidan sarauta tasan yanda ake gudanar da mulki cikin Adalci snn gata da tausayi Bata kaskantar da talaka da bayinta ta d’auka da ita dasu duk d’aya na wurin ubangiji bawani babbanci snn Bata d’aukar kanta ita wata ce, kamar Jamila.”
Hakan yayiwa Hajjah dad’i ganin. Halayya Bintu Mai kyauce sai yanzun take farin ciki da dariya ganin tilon d’ansu ya dace da macce ta gari wacce take dai dai da rayuwarsa.”
Hajjah taja Bintu a jikinta tashiga fad’a Mata duk wani sirrin masarautar Wanda Bata tab’a yarda Jamila ta sandasuba domin tin farko ta fahimci rayuwarta maccece Mai son kanta ga kuma mugunta.”
Kowa a gidan idan kaji ya bud’e Baki ba Wanda zai ambata sai Bintu Alherinta ake fad’i tare da Adalcinta, snn Bintu kaifi d’ayace ba tsoro ko shakka a tare da ita Dan hakan suke fito na fito da Jamila, Dan Bata tsoronta ko kad’an musamman da ta fahimci halayanta ba masu kyau bane, hakan yasa Sam basa Zama a inuwa d’aya Jamila tanaso ta Fara tin karar Bintu Amma kwarjininta yake hanata aikata Mata komai,
Snn a duk lokacin da take yunkurin ai watar da wani zalinci a gidan,
Bintu takan dakatar da ita ba tsoro ko shakka, zata shiga karanto Mata k’undun tarihin mulki.ba hakan yace ayiba.”
Dole Jamila takeja baya Domin tasan kowa Yana bayan Bintu a gidan daga ciki kuwa har da maimartaba sarki,
Tabbas maganar bokanya tafito cewa Bintu zatazo da wani haske a gidan, to gashi ta Fara gani tanaji tana gani komai ya tsaya Mata cak.”
Abdullah Yana tsananin son Bintu Wanda son da Yake Mata yasa yakasa b’uyeshi a duk inda yake a duk yanayin da ya tsinci kansa,
Hakan Jamila ta Kuma Jin haushi da takaici tashiga tunanin Ina wuta tajefa Bintu,
Ana hakan Bintu ta Fara laulayin ciki, irin laulayin Nan Mai sakarwa mutum kasala da yawan amai anan take komai yayi sanyi a tare da ita.”
Kwajin farko aka tabbatar da cewa tana d’auke da ciki d’an wata d’aya.
Murna a cikin masarautar abin ba’a magana har da d’an kwarya kwaryar biki aka shirya,
Anan take sarki yayi Mata kyauta taban mamaki, hakan Hajjah wacce lafiya ta Kiya mata yau ciwo gobe lafiya, itama tayi murna sosai dama babban burinta kenan taga jikokinta.”
Jin labarin bintu tana da ciki ya k’ara d’aga hankalin Jamila ganin daga zuwanta daga baya har tasamu ciki dama tasan za’ayi hakan Kuma tasan ba Dan komai akayi Auren ba sai Dan ta shigo gidan ta haihu domin ta gaji sarautar masarautar tinda sun saba da mulki sunsan da d’insa,
Ynzun ana nufin idan ta haihu d’anta kenan zai hau kujerar mulki, Ina bazai yuwoba,
Anan take tabawa jakadiya kud’i masu yawa tace “taje wurin bokanya duk yanda za’ayi ayi a zubar da cikin dake tare da Bintu kada asake a barta ta haifeshi Kai idan da Halima har itama Bintu tabi cikin nata zuwa lahira.”
“Angama ya uwargiyata wnn shi dai dai kinyi tunani Mai kyau Allah ya k’ara maki kaifin basira snn jakadiya ta tashi tafita tanufi k’auyen bokanya k’araba.”
Karon farko bokanya da tayi diba tace “Ina ciki bazai zubeba sabida yarinyar da abinda ke cikinta haske ne dasu, tin farko nariga da ta fad’a Maku cewa tauraruwar yarinyar haske gareta,
Jakadiya tace “Allah ya k’ara maki lafiya ya bokanya k’araba ba wani abu da za’ayi akan sai cikin da ita kanta idan da Hali akasheta tamutu ta tafi da cikin can lahira.”
Bokanya k’araba ta d’aga murya cikin wani sauti Mai firgitarwa tace bai yuwoba,zai yiwo a kashetaba domin idan akayi yunkurin kasheta komai zai iya faruwa dagani har ku,
Sai dai ayi asirin da zata haifin abinda ke cikinta yafito duniya ba rai.”
Jakadiya tace “wnn ma yayi.”
Aka Bata wani turaren Wanda zasu dinga turarawa a lokacin da sukasan Bintu zata shak’i warin turaren a ko wacce Rana har tsawon wata bakwai,
Wanda da zarar tana shak’ar warin turaren ako da yaushe to abinda ke cikinta bazai tab’a fitowa da raiba sai a macce.”
Hakan akayi kullum safiyar Allah sai sunyi turaren wnn maganin a k’ofar b’angaren Bintu a inda aka San Bata gani.”
Bintu baiwar Allah tana ciki a kwance tana fama da laulayin cikinta kuyangi sai hidima sukeyi da ita,
dazarar sunyi turaren tashak’i warinsa, zata dingaji tamkar an k’ara mata wani wutar azabar ciwo a tare da ita.”
Wasa Wasa Bintu duk ta rame ta fita a hayyacinta ga azabar laulayi ga a azabar turaren da Jamila take turara Mata, Abdullah ya Kuma tud’ewa Yana tausayinta sai kula yakeyi da ita fiye da tunanin Mai karatu, wani lokacin yakanji warin turaren Amma baya kawo komai a ransa.”