BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Ana hakan cikin Bintu ya tsufa ya Kai wata Tara ya girma sosai a lokacin lafiya ta Fara samuwa da ita duk wani laulayi ya Kau haihuwa ake jira, da zarar jamila tayi Ido biyu da cikin ji takeyi kamar ta kurma ihu ko tasanya bindiga ta harbeta daga ita har cikin su mutu kowa ya huta.”

Wani Lokacin takan Kira jakadiya ta dinga ce Mata Anya kuwa abin dake cikin Bintu ya mutuwa kowa?”
Jakadiya zatace ki daina ko kwanto a Kai yamutu ranki ya dad’e domin bokanya Bata k’arya da zarar tafad”i magana to sai ya faru.”
Snn hankalin Jamila ya kwanta ta d’an saki murmushi, tace na tsani Bintu kamar yanda na tsani mutuwa ta.”

Wani dare da k’arfe uku Bintu ta tashi da nak’uda a lokacin tana tare da Abdullah ganin yanayin da take ciki yasa yafita yaje yakira jakadiyar Hajjah Domin yasan Hajjah kawaici ne da ita ko ya fad’a Mata bazuwa zatayiba
Jakadiyar Hajjah danjijuwace wacce zata iya Kai shekara 45 Amintacciyace a wurin Hajjah Domin Yardar da Hajjah tamata itace ta raini Abdullah tin Yana k’araminsa tsakaninsa da mahaifiyarsa hajjah sai dai yasha nono ya tafi wurin jakadiyar Mai suna ANNA.”

Suna zuwa tare da Anna cikin sauri sai dai sukaji kukan jariri Wanda kukansa ya k’arad’e b’angaren Yarima Abdullah duk wani mutum Wanda yake rayuwa a cikin sashen gaba d’aya yaji kukan jaririn,
zubbur Jamila tayi tafito daga d’akinta Jin kukan jariri da tayi,
Dama wani bacci kirki takeyiba domin tinda taga cikin Bintu ya tsufa ya Isa haihuwa ta daina kwana da Ido biyu sai da da Ido d’aya Domin tana sauraron taji bintu ta haihu,
babban burinta shine taji ance Bintu ta haihu abin da ta haifa ya mutu, idan da Hali tafison tabi d’anta su mutu a tare.”

Jin kukan jaririn da tayi yasa tafito da sauri ba ko mayafi a kanta,
tana zarar Ido tanufi b’angaren Bintu tana fad’in a Ina nakejin kukan jariri.”

kitibis tayi da santalelen d’a namiji sak mahaifinsa wani b’angare ya d’ebo mahaifiyarsa Yana hannun Anna ta gyarashi cikin kayan sanyinsa ruwan Madara masu tsananin kyau.”

Ido biyu sukayi da Anna suka kalli juna,
Jamila tayi saurin sakin murmushi tare da mik’a hannu zata k’arb’e jaririn tana fad’in “ya akayi hakan, taga yaro Yana motsi cikin k’oshin lafiya, gabanta ya fad’i ta mere Baki tace Amma dai
macce ce aka haifa ba namijiba,
Anna tace namiji ne magajin sarki insha Allah had’ida mik’awa yarima Abdullah jaririn,
Wanda hankalinsa Yana kan Bintu wacce take kwance a kan gado tana kallon kowa d’aya bayan d’aya tana murmushi.”

Jamila na ganin Anna ta hana Mata jaririn yasa taja da baya ta juya tafita daga d’akin Bata Kuma furta komai ba zuciyarta tana tafarfasa,

tsakanin Anna da Jamila Kar Tasan Karne domin Anna tasha Kama Jamila a bayan gida tana bine wani abin ko tasamesu suna magana tare da jakadiyarta,
Wnn dalilin yasa Jamila take shakka Anna domin rufuwar asirinta domin tasan Anna jardadiyar sarki ce sosai komai tafad’a Masa baya musu zai yarda”

A Ranar kasa Zama Jamila tayi sai hawayen bak’in ciki yake Mata Ambaliya a fuska ganin tanaji tana gani wata tazo daga baya ta haihu kuma d’a namiji ita Kuma ko b’atan wata bata tab’ayiba tabbas dole ne ta Hana wnn yaron Zaman duniya dole ne ta salwantar da rayuwarsa Kai har ma da rayuwar mahaifiyarsa.”

Washe gari gaba d’aya gidan sarautar ya karad’e da murna bintu matar Yarima Abdullah ta haifi d’a namiji,
Maimartaba sai da yayi sujjada ga mahaliccinsa domin Jin dad’i Wanda Kuma yazo Masa da Albishir ya Masa kyauta ta ban girma, hakan Hajjah sai da ta zubar da hawaye Dan murna,
A ranar gidan kowa cike yake da murna da farin ciki sai hada hada akeyi fuskokin kowa cike suke da murna Amma Banda Jamila da jakadiyarta.”

A ranar suna yaro yaci sunan SAUBAN, Wanda maimartaba sarki yasaka Masa sunan da kansa sabida Yana tsananin son sunan domin ya Sha Alwashi da zarar anyi haihuwa a gidan indai namiji aka haifa to baya da wani suna da za’a saka Masa bayan SAUBAN.”

Bikin sunan Sauban bikin sunane Wanda ba’a tab’ayin irinsa ba a gidan sarautar domin bikine na masarauta biyu masarautar zamfara da masarautar Adamawa ko wanne yanaji da kud’i da mulki kuma ko wanne Yana nuna farin cikinsa da tashi bajinta domin Sauban shine jika na farko a masarautar biyu.”

Farin ciki a wurin Abdullah Abin ba’a magana domin duk inda yake Yana tare da matarsa da d’ansa Wanda hakan ya Kuma k’onawa Jamila rai k’ara d’auki Alwashin sai ta salwantar da rayuwar Bintu da d’anta Sauban.”

REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

DIDECTED TO Fateemah M Uthman

Page 7

Bayan bikin sunan SAUBAN Anna ta dawo da Zama gaba d’aya a b’angaren Bintu domin kula da ita da jaririnta, bisaga umurnin Hajjah domin tasan Jamila zata iya aikata masu komai idan taga ba kowa a kusa dasu tinda ba mutumci da imani ne da itaba.”

Sauban da mahaifiyarsa sun Sami kulawa ta musamman.a wurin Anna domin gasasu takeyi da ruwan zafi yanda ya kamata.”

Wanda hakan yayi matuk’ar k’ona ran Jamila,
domin bataso Anna ta dawo b’angaren Bintu da zamaba,
burinta shine ta fakaici idon mutane tashiga d’akin ta Sanya hannu ta shak’e wuyan Sauban ta kasheshi da hannunta kowa ya huta, Amma Ina ba Hali Anna ta saka Mata Ido sosai.”

Hakan suka kammala jegonsu cike da kulawa tare da tarairaya a wurin Anna da Abdullah.”

Sauban ya girma yayi wayo ya taso cikin farin jinin Al’umma gashi kyakkyawa ya d’ebo kyawon mamansa da babanshi duk Wanda yaga Sauban sai yaji yaron yashiga ransa, Wanda Jamila da zarar tayi Ido biyu dashi takejin tsananin tsanarsa a ranta Bata k’aunar ta gansa Dan hakan duk wata hanya da zaisaka ta tayi Ido biyu da Sauban Bata bi,
A kullum safiyar Allah tunaninta d’aya ta wacce hanya zatabi ta kawar da sauban da mahaifiyarsa a doron k’asa.”

Ana hakan Sauban sai Kuma girma yakeyi Yana wayo Wanda a yanzun shekararsa biyu baya da wurin Zama sai fada kusa da sarki, wani lokacin tare da sarki suke kwana a d’aki d’aya saboda k’aunar da sarki yake Masa,
Sauban jarumine tin Yana k’aramunsa ba k’aramun Abu ne yake sakashi kukaba, ko fad’uwa yayi hakan zai tashi da kansa batare da an tayar dashiba, Kuma
ba alamar kuka ko Jin ciwo a tare dashi, snn baya da yawan magana tin Yana k’aramunsa domin ko magana ake Masa idan ba yaga damar amsawa ba baya amsawa shuru yakeyi tamkar bayaji, wani lokacin Kuma sai dai ya d’aga hannu alamar ya amsa.
Wnn halin nasa yasaka sarki yake matuk’ar son shi domin jinin sarauta ne Yake yawo a jikinsa,
hakan Yana nuni da cewa jarumin maza ne, za’ayi fafatawa dashi a fagen fama,
Dan hakan sarki ya d’auki harmar bashi wani magani Mai saka jarumta da kaifin basira tare da kuzari.”

Shekarar Sauban biyu da rabi mahaifin Bintu ya rasu wato sarkin zamfara,”
Mutuwar da tarazana Bintu tare da sarki da Abdullah da Kuma Hajjah.”

Bintu tayi bak’in cikin mutuwar mahaifinta sosai,
Wanda kuka da kewarsa ya kasa tsaya Mata a fuska,
Abdullah sai aikin lallashinta kawai yakeyi.”

Bayan wata d’aya aka nad’a babban d’an sarkin zamfara wato yayan Bintu a kan kujerar mulkin.”

Bayan an nad’a sabon sarkin zamfara, akazo wurin rabon gado anan ake fad’a Mata tin kafin mahaifinsu ya rasu ya bar wasiyar cewa gidan gonarsa dake Adamawa a can cikin wani k’auye Mai suna lissa, ya bawa Bintu gidan gonar kada a sakashi a cikin rabon gado saboda tin Bintu tana k’arama take matuk’ar son gidan gonar Dan haka natane ya Bata, a fad’a Mata hakan a Kuma dank’a Mata ta kardunsa a hannunta.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button