DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL
Bintu taji dad’in kyautar gidan gonar da mahaifinta ya Mata tashiga yi Masa Addu’ar samun rahamar ubangiji,
Domin itama tana tinanin gidan gonar a ranta tana Addu’ar Allah yasa idan za’ayi rabon gado ya fad’a a cikin gadonta Domin tana tsananin son wurin tin tana k’ara hakan wani lokacin sarki zai d’auketa sushiga jirgi ya kaita gidan gonar domin kawai farin cikinta,
Har zuwa girmanta Wanda ta mayar da zuwa gidan gonar duk k’arshen wata take zuwa tana kwana biyu a cikinsa tare da kuyangi tana nishad’i da farin ciki domin duk lokacin da tsinci kanta a cikinsa tana jinta cikin wani farin ciki marar misaltuwa hakan zata dinga murmushi da annashawa a cikinsa tanaji a jikinta akwai wani farin ciki babba Wanda ya danganci rayuwarta a cikin gidan gonar, Wanda Yake Cikin k’auyen Lissa a k’ark’ashin k’aramar hukumar mulkin Adamawa State.”
Bayan an kammala rabon gado,
Bintu ta dawo gida tare da Abdullah da Sauban,
Hakan Abdullah yaci gaba da kular mata da gidan gonar tamkar mahaifinta Yana Raye.”
duk k’arshen wata suke zuwa ziyara gidan gonar kamar yanda takeyi a can baya,
tare da shi da ita da Sauban a lokacin Yana da shekara uku a duniya,
Hakan Yana matuk’ar sanyata farin ciki, Yana cire Mata damuwar rashin mahaifinta da tayi.”
Ana hakan Bintu ta Fara laulayin samun wani cikin,
Wanda Abdullah ya fahimci cikine da ita ya shiga farin ciki,
Anan take gidan sarautar kowa ya d’auka Bintu ciki ke gareta duk kowa yashiga murna da farin ciki duk Wanda ka kalli fuskarsa a lokacin Yana cikin murna da farin cikin samun cikin bintu.”
Amma Banda Jamila domin k’ura takai Banga tsakaninta da Bintu duk abinda za’ayi sai dai ayi saboda bazai yuwo ta Kuma haihuwa a gidan Nan ba.”
Ana hakan cikin Bintu ya Kai wata hud’u,
Tafiya ta Kama Abdullah zuwa Bauchi wurin nad’in sarautar babban Abokinsa Kuma Amininsa wato Yarima Hayat Wanda mahaifinsa sarkin Bauchi ya mutu, za’ayi bikin d’ora d’ansa Hayat akan kujerar sarauta.”
Yaso yatafi da Bintu sai dai yanayin jikin nata ne batajin dad’in sa,
Kuma yasan zainab bazata bishiba saboda Bata k’aunar d’agawa daga gidan tayi ko tafiyar wuni d’ayace saboda kada tabar kujerar mulkinta.”
Hakan ya shirya yayi tafiyarsa shi kad’ai cike da kewar matansa musamman Bintu wacce take cikin lalurar laulayi.”
Tafiyarsa tayi matuk’ar yiwa Jamila dad’i,
Dama ta shirya ai watar da komai na mutuwar Bintu tare da d’anta Sauban tako wacce hanya tinda maganin boka baya tasiri a kanta, idan tasan wata ai Bata San wataba.”
Hakan yasa tayo hayar manyan ‘yan ta’adda domin su kashe Bintu da d’anta Sauban,
Anan tabasu Kayan bayin gidan suka saka a jikinsu Dan gudun kada a ganesu,
Kasan cewar gidan cike Yake da bayi da kunyangi suna shawagi Rana da dare.”
Wani dare Bintu tana kwance ita kad’ai, a lokacin Sauban Yana tare da sarki,
Domin tinda ta Fara ciwo Yake kwana a wurin maimartaba,
Acan cikin baccinta taji sautin muryar gardawa a kanta cikin sauri ta bud’e idonta,
Ai Kuwa tayi arba da gardawa sanye da kayan bayi,
Wanda da zarar ka gansu kasan ba bayi bane,
Addu’a tashigayi d’aya daga ciki ya Sanya hannu ya make Mata Baki a anan take jini ya cika Mata bakin gaba d’aya.”
Yunkurin tashi takeyi d’aya cikinsu yabita ya haye kanta ya sanya filo ya danne kanta,
Sai da yaga Bata motsi alamar ta mutu snn ya dagata suka gyara Mata kwanciya kamar wacce take bacci snn suka fita suka bar d’akin.”
Basuyi tinanin Ina d’anta Yake ba,
Sukayi ficewarsu.
Suna fita sukaci karo da Jamila, sukayi Mata nuni da aiki yayi kyau, ta mik’a masu jakar kud’insu suka fita ta hanyar baya.”
Safiya tana wayewa a gidan sarautar hankalin kowa a tashe cewar ankwanta da Bintu ba’a tashi da itaba,
Mutuwar da tafirgita kowa a gidan duk Wanda kagani cike Yake da bak’in ciki fuskar kowa sai zubar da hawaye takeyi.”????
REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S✍
???? D’AN SARKI SAUBAN????
Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)
DIDECTED TO Fateemah M Uthman
Page 8
Abdullah Yana cikin jama’a ana hidimar bikin nad’in sarautar Abokinsa Hayat gabansa sai fad’uwa ykeyi yarasa dalili, anan take jikinsa ya soma rawa yaji a duniya ba Wacce yakeso yagani sai Bintu, anan take ya Tina halin da ya barta na tsananin laulayi,
Hakan ya fito daga cikin taron mutanen batare da anlura dashiba ya shiga motarsa tare da fadawansa suka d’auki hanyar komawa gida baiyi sallama da kowa ba.”
Saukarsu kenan bai wani jira aka bud’e Masa murfin motarba ya bud’e da kansa gabansa Yana fad’uwa,
Kai tsaye b’angaren Bintu yanufa jikinsa sai rawa yakeyi ji Yake akwai abinda ya Sami Bintu
Tafiya yakeyi kamar zai tashi sama burinsa ya gansa a b’angaren Bintu Wanda duk inda ya gifta fadawa da bayi sai kallonsa sukeyi cike da tausayi wasu suna sharar hawaye.’
Bai lura da kowa ba domin idonsa a rufe yake hakan yasa bai fahimci kallon da ake masaba bai Kuma fahimci kukan da bayi da kuyangi sukeyi ba, hakan yasanya gaba cikin sauri ya Isa b’angaren Bintu, Wanda tin a k’ofar b’angaren nata ya ganshi cike da mutune sai a lokacin ya lura da yanayin fuskokin mutanen dake wurin zaune ko wanne ya rafka tagumi,
ko wanne cike yake da damuwa wasu suna matsar hawaye.”
Gabansa ya fad’i cikin Azama ya tinkari d’akin Bintu Wacce aka kammala shiryata cikin sitirarta tana sanye da linkafani fari fes Wanda yayi Mata kyau fuskarta sai wani Annuri take fitarwa ga murmushinta Mai sanyi a kan fuskarta,
Kai tsaye ido rufe yazo wurinta ya durk’usa Yana fad’in Bintu tashi nadawo Yaya jikin naki, ko mutafi asibity ne,? Bintu kitashi Mana Yana girgizata?”
Ji yayi andafashi ta bayansa yayi saurin juyawa yaga Hajjah ce tana matsar hawaye abinda tin tashinsa bai tab’a gani a idon Hajjah mahaifiyarsa ba, ya Kuma rud’ewa,
Hajjah ta d’agoshi ya mik’e tsaye ta rungume shi tana fad’in Abdullah sai dai kayi hakuri domin Bintu ta rigamu gidan gaskiya ankwanta da ita ba’a tashi da itaba.”
Wani irin razana yayi yasaki jikin Hajjah yanufi wurin gawar Bintu yashiga girgiza Yana fad’in kitashi Bintu Baki mutuba kitashi.” Ina shuru ba motsi Bintu ta mutu,
Wani irin kuka yasaki Mai tsoma zuciya Yana rungume da gawarta.”
Tausayi ya Bawa duk mutanen dake wurin suma sukashiga zubar da hawaye Mai k’arfi.”
Ana hakan sarki ya shigo tare da sarkin zamfara dama su ake jira ayi Mata sallah akaita gidanta na gaskiya,
Ganin kukan da Abdullah yakeyi yabawa sarki tausayi ya d’agoshi ya rungumeshi Yana fadin daina kuka Yarima Addu’a ya kamata kayiwa Bintu adai adai wnn lokacin Addu’arka take buk’ata, in har kacika masoyinta,
Kasani ko wanne Mai Rai zai mutu muyiwa kanmu fatan cikawa da imani Bintu lokacinta ne yayi.”
Hakan sarki yayi ta kwantarwa Abdullah da hankali har yayi shuru ya daina kuka ya koma Kukan zuci wanda yafi komai zafi,
Hakan aka d’auki Bintu akayi Mata sallah snn aka kaita gidanta na gaskiya.”
Sai da aka Kai Bintu aka dawo snn Jamila tafito daga b’angarenta tana kukan munafurci tana fad’in bintu da Sauban Allah ya jik’anku hak’ik’a munyi Rashi babba a gidan nan”
Kyara kalamanki Sauban Yana raye bai mutuba,
Sautin muryar Hajjah taji ya dura a kan dodon kunnenta,
Wanda yasa tayi saurin d’aga Kai a zabure ta kalli Hajjah da Anna sai Kuma Sauban dake kusa da Anna Yayi shuru Yana kallon kowa d’aya bayan d’aya bini bini sai ajiyar zuciya Yake saukewa
jama’a duk sun zagayesu ana amsar gaisuwa.”