BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Gabaɗaya waɗannan ƴaƴayen kowanne yana da tashi zuri’ar, daga cikin waɗanda ba sa cikin gidan gandun, akwai Baba Abubakar Mazaunin unguwar Na’ibawa, kuma lakcara (Lectural) ne kwalejin Sa’adatu rimi. Sai Baba Adamu.

Baba Abubakar yana da mace ɗaya Hajiya Nafisa da yara Huɗu: Aseem, Nabila, Husna da Humaira. Aseem da Humaira sunan Mai carbi da Yaya babba suka ci amma ana kiran Humaira da Ummi. Baba Adamu yana zaune a unguwar Gyaɗi-gyaɗi likitane yana aiki a asibitin Aminu Kano. Yana da mata biyu Hajiya Rahama ita ce Uwar gida tana da ƴaƴa biyu Fahad da Fatima sai Hajiya Fauziyya mai ƴaƴa uku Halifa mai sunan Marigayi Mai carbi, Zainab sai Hafsa. Sai Hadiza da Larai da suke aure a wasu gidajen.

Tsayawa zayyano wannan ahalin Marugayi mai carbi ba ƙaramin ɓata lokacin mai karatu bane.

Dawowa Labari.

Kimanin sha biyun rana da ƴan mintuna, zaune yake a cikin motarsa yana ƴan danne-dannensa. Ya kai kimanin mintuna ashirin da faka motar amma yana ciki bai fito ba. Ɗaiɗaikun yara ne suka fara zagaye motar suna kallo wasu daga cikinsu har da masu shafawa. Tsirarin ƴan mata sa’annin Dubu har da masu kallon fuskarsu a jikin mudubin motar, ganin suna niyyar yi masa ɓarna ya sa ya zuge galashin motar. Wani sihirtaccen ƙamshi ne ya fito daga cikin motar nai sanyin ƙamshi. Ƙamshinsa ne ya ankarar da su akwai mutumin da ke cikin motar. Kallon su ya fara yi kowa ya shiga taitayinsa sakamakon ganin fuskarsa ko ɗigon murmushi babu. Mugun kallon da ya wurga musu ne ya sa kowacce daga cikinsu ta kama kanta, sum sum sum suka wuce. Gajiya ya fara yi da zaman motar sannu a hankali ya zuro ƙafarsa waje tare da fitowa ya jingina da jikin motar yana ƴan danne-danne a wayarsa. Kakin sojan ba ƙaramin ƙarɓarsa ya yi ba, ya yi kyau matuƙa ga wani kwarjini da yake da shi.

Kasancear mutanen ƙofar gidan sun watse sakamakon ruɗanin da yake faruwa wasu daga ciki kuma sun tafi asibiti wurin Inna Furai.

Lambar mahaifiyarsa ya kira sai da ta kusa katsewa sannan ta ɗauka. Kamar zai yi kuka ya fara yi mata magana: “Momma don Allah ki zo ki shigo da ni banga su Daddy ba kuma na san gidan cike yake da mutane…” Bai ƙarasa magana ba Baba Munkaila ya ƙarasa wurinsa yana washe baki ya ce, “Wa nake gani kamar Soja? Soja mazan fama saukar yaushe.” Zame wayar ya yi yana sosa kai ya ce, “Yanzu na ƙaraso Baba.”

“Bismillah mu je ciki mana” Baba Munkaila ya nuna masa hanya. Sai da ya kulle motar sannan suka ƙarasa cikin gida.

Dubu tun a hanya su Kaltume suka tare ta da zancen baƙon da suka yi. Hura hanci ta yi kanta na ƙara girma sannan ta ce, “Wani dogo mai mota baƙa? Yau ma da kayan sojoji yazo ko?” Har rige-rigen bata amsa suke sannan ta tallaɓi ƙwaryar tsakin da ta karɓo ta fara buɗa kafaɗa tana cewa, “Ai shi ya sa nake gaya muku duk shegen da ya kawo raini wallahi haɗa shi da Yaya Aseem zan yi ya ci ubansa. ” Tana gama maganar ta yi gaba. Su kuwa kowa ya yi zuru-zuru don basa manta ranar da suka taɓa ganinsa da bindiga.

Dubu cike da ɗoki ta shiga gidan don ko ba komai so take ta riƙa ƙare masa kallo tana ayyana wai shi ma ɗan uwanta ne a matsayinsa na soja. Ita ba shi yake birgeta ba illa kakinsa na soja da sautari idan zai zo garin da su yake zuwa.

Kamar wacce aka wurga tana shiga gidan ta yi ciki da Nabila ai kuwa suka fara faɗa, juyawar da Dubu za ta yi a zafafe ta sheƙawa Aseem garin tsakin da ta karɓo daga injin niƙa. Sai ga Aseem da ke cikin unifom ɗin sojoji har da hankicin ɗin goge-goge ya fito furu-furu kamar wanda ya yi wanka da toka. Gashin kansa har wani tsinin farin garin masara ya yi.

Ummou Aslam Bint Adam????
[7/1, 5:59 PM] My Data sim number: DUBU JIKAR MAI CARBI

        ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.

FREE PAGE 6
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan???????????????????????????????????????? subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

Duk wannan abin da ya faru sam Dubu bata lura ba, masifa na cin ta bata san da ta sheƙa wa Aseem garin masara a jiki ba, sai ma uban tsalle da ta buga ta cukumi wuyan Nabila tana kai duka tana cewa: “Wallahi ba za ki daki banza, kwarankwasa dubu sai na koya miki hankali, hegiya tsigi-tsila da ƙafa kamar ta tsinken tsintsiya” Ganin ɗankwalin da ke kanta na niyyar kawo mata cikas ya sa ta fisge shi wurga shi ta baya sai kuwa ya sauka a kan fuskar Aseem, ban da tsami da bashi babu abin da yake tashi a cikinsa. Sai ga kitson kanta ya fito duk ya tuje hatta da tsagar kitson ta haɗe sai furu-furun amosani a saman kan.

Warin ɗankwalin ne ya doki fuskar Aseem har ya shaƙa da ƙofofin hancinsa ya sa shi farkowa daga suman tsayen da ya yi na wucin gadi. Aseem tun da ya zo duniya ba a taɓa yi masa abin da ya fusata shi lokaci ɗaya kamar abin da Dubu ta yi masa, dom shi abin daga haushi ma sai ya koma ba shi mamaki. Bakinciki da ganin yadda mutane suka zura masa ido ne ya ɓata masa rai har ya gagara sanin abin da zai aiwatar don ya wanke masa zuciya. Amma tabbas sai ya koya mata hankali don ya lura har lokacin Yaya babba ba ta ɗora ta a hanyar arziƙi ba.

Duk yanda Dubu ta so nunawa Nabila ƙarshen iyawarta abin ya ci tura don a girme Nabila ta girme ta da kusan shekara huɗu. Gudun kar a kunyatata cikin jama’a ya sa Dubu ta tattara ƙarfinta ta fara wani fisge-fisge kamar mai aljanu tana kai duka ta ko’ina, ai kuwa ta ɗaga ƙafa bisa taautsayi ta harbawa Aseem da ke saƙa da warwara akan irin abin da ya dace ya yi mata. A hassale ya ƙarasa wurinta cikin zafin nama ya fisgi hannunta. Cikin tsiwa da rashin sanin wa ya riƙe ta Dubu ta ce, “Wallahi duk wanda ya riƙe ni sai na yi masa jini da majina dalla ku sake ni wallahi ba za ta daki banza ba.” Ai kuwa ya sauke mata mari a fuska, kafin wancen marin ya gama ratsa fuskarta ya sake kifa mata wani marin har sa da ta ga wasu irin taurari na gilma mata. A gigice Dubu ta buga tsalle cikin fitar hayyaci ta ce, “Innalillahi wayyo Baba Munkaila zai kashe ni wayyo! Inno fuskata.”

Sauke hannun Aseem ya yi daidai da fitowar Yaya Babba za ta zagaya banɗaki. Da sauri ta saki butar hannunta ta fashe da kuka ta ƙarasa wurinsu, tana shirin riƙe hannun Dubu; Aseem ya sake fisgar Dubu ya nufi hanyar fita da ita. Duk irin kiran da Yaya Babba take yi masa ko waiwayenta bai yi ba bare ta saka ran zai tanka mata.

Duk yanda zuciyar Dubu take a bushe wannan karon sai da hanjin cikin ya kaɗa, tsoro ya mamaye ta musamman ta lura da irin ɓarin makauniyar da ta yi masa da garin masara. Suna zuwa soron ƙarshe ta yi ta maza ta fara ƙoƙarin fisge hannunta tana faɗin:

“Wai ina za ka kaini? Ka sakar mini hannu malam.” Idanunsa sun kaɗa jawur saboda ɓacin rai don haka tambayar Dubu ba ƙaramin baƙanta masa rai ta ƙara yi ba. Bai tanka mata ba ya sake fusgarta da ƙarfin tsiya ya buɗe mota ya wurga ta sannan ya buɗe mazaunin direba ya zauna.

Ganin ya tuƙa mota da ya fice da gudun tsiya ya ƙara hargitsa hanjin ciki Dubu, don wannan karon har ta fara bubbuga gilashin motar tana ihu. Can gefen titi ya gangar ya faka motar sai dai uffan bai ce ba. Sai da ya share minti biyar a haka yana jin kukan da Dubu take yi da ɗan ƙarfinta, ya zaro ƴar ƙaramar bindiga ya juya yana ce mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button