BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Daga ɗaki mai kallon gabas Baba Auwalu ne ya ɗaga labule yana haskowa da fitila zaraf matarsa Yahanasu ta miƙe tana tambayarsa da yake su sabbabun amare ne. Daga can nesa suka hango Inna a yashe tana ko numfashi bata yi. Gabansa ne ya faɗi yace, “Wa nake gani kamar Inna a ƙasa.” Sahura ta dafa kafaɗarsa ta ce, “Auwaluna ni ban yarda ita bace kawai magauta ne suka yi maka ture.”

Duk duniya babu abin da Auwalu ya tsana sama da a ɓata ran Yahanasu amma tabbas wannan karon ba zai iya haƙura ya bar Mahaifiyarsa a wannan yanayin ba. Kasancewar dare ne amma bai hana sakar mata murmushi ba ya ce, "Allah shi zai kare ni amma bana tunanin wani zai yi mini ture cikin dare." Kafin ta yi magana tuni Auwalu ya yi gaba, ganin haka ya sa ta ja tinga ta tsaya don har ga Allah a tsorace take musamman da ya kasance ranar ne aka yi rasuwa.

Hankali a tashe ya fara yayyafawa Inna ruwa ganin ta fara motsi ya sa ya kamata yana bubbuga ƙofar Baba Sule, Baba Sule na ji ya yi fakare kamar mai bacci don gabaɗaya ya gama rikicewa. Sama-sama Sahura ta fara jin bugun ƙofa firgigit ta miƙe sai ji ta yi Sule ya riƙe hannunta gam, tana shirin yin magana Baba Sule ya janyota cikin raɗa ya fara cewa, “Kada ki yi magana za su yi sama da ke” Waigawa Sahura ta yi tana kallon ƙofa don ita a tunaninta masu buga ƙofar ne za su yi sama da ita. Suka ƙarajin bugun ƙofa Auwalu yana cewa, “Yaya Sule fito ka taimaka mini jikin Inna ya yi tsanani ina jin makewayi za ta ta faɗi.” Sahura ta ja guntun tsaki ta ce,

“To! Sai ka tashi tun da ta ka ji muryar Auwalu.” Baba sule ya sake ƙasa da murya yanda daga shi sai Sahura ne za su ji abin da yake faɗa ya ce, “Ki koma ki kwanta kawai ina ji a jikina waɗannan ƴan sama jannati ne suka rikiɗa. Takaici ya kama Sahura yanda ta ga Maigidanta yana rawar ɗari ga shi ba lokacin zafi ba, ta miƙe tana fusgar hannu ta ce, “Sakarni ko ƴan ƙasa jannati ne babu abin da zai hanani fita.”Tana jan hannu Baba sule yana ja don a tunaninsa muddin ta saki hannunsa shi kenan za su yi sama da shi.

Sororo Sahura ta yi tana kallon ikon Allah, don ita a iya saninta da Sule ba su taɓa irin wannan wasan da shi, don haka ta sake ɓata fusaka ta ce, “Sule wai wani abu ne yake damunka ko gamo ka yi cikin dare n sani ba?” Baba Sule ya yi wura-wura yana kallon hagu da dama ya sake ƙanƙance murya ya ce, “Sahura a kowanne lokaci za a iya yin sama da ni.” Wani takaicin ne ya sake rufe ta, ta miƙe tana ƙoƙarin fisge hanunta amma abin ya ci tura don ƙarfin mace dana namiji ba ɗaya.

Auwalu da ke jin ƙusur-ƙusur a ɗaki sai ya sungumi Inna don a ganinsa bai kamata ya sake buga ƙofar ɗakin ma’aurata cikin dare ba. Can sashen su Inna Furai ya nufa Yahanasu ta ƙwalla masa kira tana cewa, “Auwaluna ina za ka ni dai tsoro nake ji.” Auwalu ya waigo ya ce, “Shiga ɗaki Inna zan kai na dawo.”

Dubu na daga ɗaki tana jin duk abin da yake faruwa, tana jin Baba Auwalu ya tafi ta yi zaraf ta fito cikin sanɗa sai da ta zo daga bakin ƙofar Yahanasu ta yi gyaran murya ta sake kausashe murya irin ta Marigayi mai carbi ta ce, “Wato ita rayuwar barzahu daɗi gare ta ni Mamman. Yanzu tun da na zagayo rayuwata ta baya dole na ɗauki mai ɗakin nan.” Cikin Yahanasu ne ya kaɗa nan take jikinta ya hau karkarawa kamar mazari. Dubu ta yi irin tarin tsofaffin ta sake cewa, “Amma ita Yahanasu za mu ɗaga mata ƙafa sai dole ta bi sharaɗinmu ko ba haka ba ƴan sama jannati?” Dubu ta sake sauya murya ta ce, “Ai dole ma ta bi umarninmu ko yanzu mu faɗa ɗakin.” Yahanasu bata san lokacin da ta yi farat ta ce, “Wallahi ku faɗa ko meye zan bi.”

Dubu ta maƙale murya ta ce, “Dole ki zama makauniyar ƙarfi da ya ji muddin kika buɗe idonki sai dai ki wayi gari a ƙiyama.” Tun Dubu bata rufe baki ba Yahanasu ta runtse ido biyu ta ce, “Wallahi na rufe har abada ba zan sake buɗe su ba amma don Allah karku cutar da ni.”

Dubu har da ƴar tsawarta ta ce, “Kin tabbata kin rufe ko na aiko da Ƴan sama jannati su shigo?” Yahanasu ta sake runtse idonta tana cewa, “Na rufe wallahi na rufe.” Dubu ta saki murmushin mugunta a ƙasan zuciyarta tana cewa, “Yau zan ga ƙaryar soyayya kullin a ishe mu da Auwaluna.” A fili Dubu ta ce mata, “Maza tashi tsaye ki rungume bango.” Da sauri Yahanasu ta fara lalaube-lalube har ta taɓo bango.

A hankali Dubu ta zura kai ta leƙa ta hango Yahanasu na rungumar bango, zuruf ta faɗa ɗakin cikin sanɗa. Sai da ta je daidai wurin Yahanasu sannan ta ɗaga zabgegen Carbin Marigayi ta zabgawa Yahanasu a ƙeya, sai ta fara wani gunji tana cewa, “Gargaɗin yan sama jannati kenan.” Tana faɗar haka har ta fice daga cikin ɗakin.

Yahanasu tun da ta gantsare take hawaye a tsaye sai dai ta kasa buɗe idonta saboda tsoron abin da kaje ya zo.

Duk abin da yake faruwa a kunnen Sahura da Baba Sule, cikin Baba sule ne ya sake ɗurar ruwa. Sahura ita kanta jikinta ya fara sanyi musamman da ta jiyo Ihun Yahanasu, shiru ta yi kamar ruwa ya cinye ta duk masifar da take yi ta daina. Domin da alama zancen Sule ya tabbata.

Lokacin da Auwalu ya ƙarasa ɗakin Inna Furai, har lokacin bata dawo hayyacinta ba. Yana shiga ya kwantar da ita akan ƙaramin gado, sannan ya fara tashin ƙanwar Mahaifinsu Lantan da ta zo daga garin Zariya. Ganin halin da Inna Furai take ciki ba ƙaramin ɗaga hankulan mutanen ɗakin ya yi ba. Auwalu ya juya zai fita Inna Furai ta riƙo hannunsa ta ce, “Auwalu! Yau na haɗu da zazzagar rayuwa. Don haka ka haɗo mini kawunan ƴan uwanka mazan su da matan su a yanzun nan. Idan ba haka ba wallahi sai na zazzagar da albarkasu kowa ya lalace.”

Auwalu da sauran mutanen ɗakin sun yi tsammanin zafin ciwo ne ya sa Inna Furai take sumbatu. Lantan ta ƙara matsawa kusa da Inna Furai ta ce, “Furaira sanu kin ji Allah sa dai ba akan makarai kika faɗi ba.” Wannan magana ba ƙaramin fusata Inna Furai ta yi ba, a zafafe ta ɗago ta ce, “A kan bulikiya na faɗi! Lantan bana son zazzagar wulaƙanci. Kai Auwalu ka tara mini ƴan uwanka a daren wallahi tun ban zazzage albarkar da ke kanka ba.” Kamar sabon munafiki haka Auwalu ya fice sum sum sum daga ɗakin. Haka ya rinƙa bi ɗaya bayan ɗaya yana taso su. Wannan tashin da Auwalu yake yi wa ƴan uwansa ne ya sa kusan rabin mutanen gidan suka tashi daɗin daɗawa idan kowa ya ji ance Inna Furai ta faɗi a hanyar banɗaki sai ya wartsake masu tafiya ɗakinta na yi masu jaje suma suna yi.

Kafin wani lokaci tuni ɗakin Inna Furai ya cika da ƴaƴanta su rai takwas maza biyar mata uku. Sai da ta kalle su ɗaya bayan ɗaya sai kawai suka ga ta ɗaga riga ta ce, “Larai bisimillah” Larai zuciyar ta ɗaya ta ɗauka Inna Furai so take a ƙarasa cire mata riga, nan take ta fara cikiniyar tuɓe mata riga. Cikin ƙaraji Inna Furai ta fisge tana cewa, “Larai yanzu bijirewa umarnina za ki yi? Ni za ki zazzagewa albarka a ka” Sai ji suka yi Inna Furai ta fashe da matsanancin kuka. Lokaci ɗaya suka kalli juna domin ba su ga abin da zai sa Inna Furai kuka ba. Auwalu ya sunkuyo ya ce, “Inna ki yi hakuri me kike so?”

Inna Furai ta ɗago mamanta ɗaya ta ce, “Mahaifinku ya zazzage mini albarka ɗazu nan domin daga zuwansa lahira har ya haɗa kai da ƴan sama jannati. Ba zan zazzage maka bayani gabaɗaya ba amma Auwalu ungo sha ka ji.”
[7/1, 6:02 PM] My Data sim number: DUBU JIKAR MAI CARBI

        ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

FREE PAGE 2

      Auwalu sam bai fahimci inda maganar Inna Furai ta dosa ba, don tun da ya ji ta ambaci Mahaifinsu ya tabbatar da zafin ciwo ne yake damunta da kiɗimewar rashin da aka yi musu. Saboda gudun faɗanta ya sa ya wayance da cewa, "Inna ban fahimci abin da kike faɗa ba. Amma kuma duk wanda ya mutu kin san sai dai mu bishi da addu'a ita ce mafita." Inna ta yi ƙuri tana kallonsa sai zuwan can kawai ta fashe da kuka. Lantan da ke gefe takaici da baƙin ciki gabaɗaya suka turniƙe ta, don gani take kamar har da biyu Inna Furai take lanjarewa. Kasa haƙuri ta yi ta ce: "Furaira don Allah ki shafa mana lafiya ki bar mu, mu ji da abin da yake damunmu. Haka kawai ki tayar mana da balli a tsakiyar dare akanki aka fara mutuwar miji? Ko kuma ke kaɗai kika san zafin miji muna zaune ki ishe mu da zancen fatalwa. Ki barni na kwanta na yi baccin da ban samu na yi shi jiya ba." 

Inna Furai ta fyace majina da gefen zaninta ta waiga ta ce, “Wallahi babu ƙatuwar Matar da za ta zo mini ɗaki ta nemi kawo mini zazzagar albarka ido biyu. Idan ba za ki iya ba ki tashi ki fice dama ni bana gayyar tsintsinya da bulugari, bare kuma mafici abin banza.” Lantan jin maganar Inna Furai ta yi kamar ta watsa mata ruwan zafi, don haka ta zaburo a hasaale ta ce, “Ban da ƙaddara da rashin ɗan’uwana da na yi, me zai kawo ni ɗakinki kaico Allah ya jiƙanka Yaya Mamman. Wai yau jininka ake wulaƙantawa saboda ƙasa ta rufe mata ido, kai jama’a ɗan’adam butulu. Wanne irin karamci ne Ɗan’uwana bai yi miki ba?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button