BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Inna Furai ta jingina da ƙarfen gado sai kawai ta fashe da matsanancin kuka, tana yi tana fatar majina. Abin duniya goma da ashirin ne damu su Auwalu, don haka kowa ya yi jim! Babu wanda ya iya tofa magana ɗaya sai gani suka yi Inna Furai ta fara haɗa ƴan kayayyakinta na sawa da ke kan gado. Sabi’u ya ce: “Inna lafiya kuwa wai me yake faruwa ne kike haɗa kaya?”

Inna Furai ta juyo a fusace ta ce, “Zaman ku a nan bai amfane ni da komai ba. Kuna gani ta gama zazzage mini rashin mutumci a ka babu wanda ya tanka mata. Wallahi ko ku bi mini haƙƙin zazzagar albarkar da ta yi mini a ka ko kuma yanzu na fice na baku wuri ku yi yanda kuke so. Gara ni tawagar Malam da ƴan sama jannati ta zo ta ɗauke ni ko kowa ya huta, dama na kiraku ne domin mu kashe mu binne amma da alama ku dai ba ƴan goyo ba ne, don na lura za ku iya zazzage mini sauran albarka da ta rage mini a kaina.

Gabaɗaya shiru suka yi suna nazarin abin da yake damun Mahaifiyarsu, don rikici sun san Mahaifiyarsu mace ce mai matuƙar rikici amma wannan karon gani suke har da mutuwar mahaifinsu da ta taɓa ta.

Lantan na gama sauraron Inna Furai ta miƙe tsaye tana shartar ƙwalla, ɗan ƙullin kayanta da ke ƙarƙarashin gado ta janyo ta fara kiciniyar ɗorawa a ka tana matsalar hawaye. Da sauri Auwalu ya miƙe ya riƙe kayan yana cewa, “Inna Lantana don Allah ina za ki a tsohon daren nan?” Lantan ta kunto mayafinta ta yafa a kanta ta ce, “Auwalu don Allah karka kawo mini maganar da za ta tunzurani har ta kai ga na nemi shaƙe wannan tsohuwar har lahira. Duk irin cin mutumcin da ta yi mini a gabanku baku gani ba za ka taso tsalo-tsalo kana tambayata ka bar ni yau ko ƙasa da sama za ta haɗe ba zan kwana a gidan nan ba.”

Nan fa hayaniya ta fara ta shi a cikin gidan, Inna Furai na gama saurarar maganar Lantan ta sa hannu bibbiyu ta dafe ƙirji a razane tana zare idanu kamar wacce ta yi tozali da kumurcin maciji. Bata tanka musu komai ba sai gani suka yi ta sauko ƙasa daidai wurin da Lantan take tsaye ta fashe da kuka haɗe ta rungumo ƙafafuwan Lantan tsam a jikinta. Tana cikin kuka ta ɗaga kai ta dubi Lantan tana cewa, “Wallahi ba za ki bar ɗaƙin nan ba sai kin zazzage ragowar numfashin da nake shaƙa, Lantan yau ni kike muradin kashewa a gaban ƴaƴana. Ai kuwa ko ba yanzu na mutu ba na rataya a wuyanki Kai Auwalu ku shaida haka.”

Inna Furai ta juya ga su Auwalu tana musu mugun kallo ta ce, “Allah na tuba wacce uwar na haɗa da su bayan alaƙar haihuwa? Da su Auwalu da Sabi’u kuma ni kam gara ma a ce ban da kowa tun da babu mai tare mini faɗa a gidan nan. Har ana niyyar halakani da sauran rayuwa kai jama’a Lantan an ya kina tsoron Allah kuwa? Duk wanda ya kashe wani dai wuta za shi.”

Lantan ta yi tsalle can gefe abin ka da da marar jiki, can gefen babban gado ta matsa tana cewa, “Laƙadi ja’akum… Tuf! Aniyarki ta faɗa kanki karki ja mini masifa ki maƙala mini sharrin kisan kai ina zaune ƙalau.” A wannan karon Inna Furai bata tanka mata ba sai gani suka yi zaraf ta fice daga ɗakin, da sauri iyalanta suka bi bayanta suna roƙon ta dawo ɗaki saboda dare.

Tana fita ita ma Lantan ta sa ƙafa ta fito ganin haka ba ƙaramin ɗaga hankalin su Auwalu ya yi ba, musamman shi da yana tsaye a nan ne amma zuciyarsa na wurin Yahanasu yana tunanin halin da take ciki. Inna Furai na ganin Lantan ta fito ta bita jiki a sanyaye kamar kazar da ake jefa da gishiri ta ruƙo hannunta sannan ta fashe da kuka. Ita ma Lantan zuciyarta ce ta karye sai kawai ta fashe da kuka, sai da suka yi mai isarsu sannan Inna Furai ta ce, “Yanzu Lantan da na barki tafiya za ki yi a daren nan?” Lantan ta fyace majina a haɓar zaninta ta ce, “Ina zan iya tafiya na barki Furai kina cikin jimamin rashin miji, Furaira rashin miji tashin hankali ne har kin tuno mini da rasuwar Mahaifinsu Ɗan’iya kai rayuwa babu tabbas Allah ya jiƙanka Malam Mudassiru.” Lantan ta rushe da matsanancin kuka. Rabe ya matso da niyyar rarrashinsu Inna Furai ta doke hannunsa tana cewa, “Allah wadaran naka ya lalace. Wallahi kaf gidan nan banga wanda zai hanani zazzage muku albarka ba. Wai kamar yanda Lantan take a wurina ta tashi za ta tafi cikin dare amma babu mutum ɗaya da zai hanata tafiya kaico! Wallahi kun ji jiki ƴan bakinciki bantaɓa sanin bakwa ƙaunar aminiyata ba kuma ƙanwar Mahaifinku ba sai yau.”Inna Furai na gama maganar ta ja hannun Lantan suka bar su Auwalu a tsaye sake da baki.

Ba su da zaɓi haka suma suka bi su Inna Furai ciki, cikin ƙaguwa Auwalu ya ce, “Inna za mu iya tafiya yanzu?”

Inna Furai ta saki salati ta na kallon Auwalu da wani yanayi har sai da ya tsargu ya ɗan fara sosa ƙeya sannan Inna Furai ta ce, “Wallahi kai dai Auwalu na riga da na san matsayina a wurinka. Tun mahaifinka na raye har ya mutu ban taɓa musa wa maganarsa ba, sai yau don ƙasa ta rufe masa ido?” Ta fashe da kuka tana ci-gaba da cewa, “Ban shirya mutuwa da shiga jahanna ba. Sharaɗi fatalwar mahaifinku ta bani sai na shayar da ku mama kamar yanda na shayar da ku kuna yara, kuma ban ga wanda zai hanani bin umarninsa ba.”

Lokaci ɗaya suka ɗauki salati gabaɗaya saboda ta’ajibin jin maganar Mahaifiyarsu, Larai cikin matsananciyar damuwa ta ce, “Inna kin san me kike faɗa kuwa? Yanzu kina nufin Baba ne ya yi miki fatalwa? Inna don Allah kar wani abu ya ruɗe ki ko ya tsorata ki saboda wanda ya mutu ya mutu kenan ba zai ƙara dawowa ba. Sai dai idan shaiɗan ne yake son razanar…”

A hassale Inna Furai ta katse Larai da cewar, “A’uzubillahi minasshaɗanirrajim. Ba zan ga shaiɗan da idona ba Larai kafirta ni kike son yi da za ki haɗa ni da Shaiɗan la’anannan Allah?” Larai rasa hanyar da za ta ɓullowa Mahaifiyarta ta yi don gabaɗaya sun rasa gane kanta. Lantan da ke gefe ta kalli Larai ta ce, “Wallahi ki tubar wa Allah idan ba haka ba, azabar Allah tuni za ta yi fata-fata da ke. Kuma ni gani nake maganar Furaira tana kan hanya don ni kaina lokacin da Malam Mudassiru ya rasu har gizo ya riƙa yi mini a tsakar ɗaki. Don haka ku yi biyayya idan ba haka ba duk cikinku babu mai kaucewa azabar Ubangiji, musamman kai Rabe da ka fi tsoka wallahi tuni wuta za ta tsotse namanka ka lalace a jahannama.”

Ganin wannan lamarin yana ƙoƙarin zama babba ya sa Auwalu ya zame jikinsa ya je Shagon Soro ya taso Yayan mahaifinsu ya sanar da shi halin da ake ciki. Har ɗakin Inna Furai ya shiga yana shiga ya same ta, ta yashe riga a sama tana kumfar bakin Larai ta tsugunna ta fara karɓa tun da sauran mazan taurin kai za su nuna mata. Da sauri ya ɗauke kansa gefe don bai yi tsammanin abin da suka faɗa da gaske ba ne. Nan take ya shiga yi mata nasiha amma duk da haka Inna Furai ta shafawa idonta toka ganin haka ya sa ya fara lallashin ta bari zuwa safiya sai a san abin yi. Da ƙyar da suɗin goshi aka samu shawo kan Inna Furai ta haƙura zuwa safiya sannan kowa ya kama gabansa. Bayan tafiyarsu Lantan ta zabga uban tagumi sannan ta ce, “Yanzu Furaira da idanunki biyu kika yi tozali da Yaya Mamman ni fa ɗazu ƙarya na kirfo da na ce ina ganin Fatalwar Mudassiru, saboda yaran nan sai su raina mu ni kuma a duniya babu abin da na ƙi jini irin raini.”

Inna Furai ta miƙawa Lantan hannu ta ce, “Lantan taɓa ni na ji.” Da sauri Lantan ta kai hannu tana shafa hannunta. Inna Furai ta mirtsika ido ta ce, “Billahilazi idan har wannan taɓawar da kika yi mini mafarki ce to a mafarki na ga Malam. Wallahi da idanuna na ganshi a wurin zaman alwalarsa amma tun da baku yadda ba nan gaba na kuma ganinsa nasa ya fitowa kowa a zahiri.” Kamar wacce aka tsamo daga ruwan sanyi haka jikin Lantan ya yi sanyi ta rasa abin faɗa don hantar cikinta ta fara kaɗawa musamman da ta san Inna Furai ba ta yin rantsuwa sai da ƙwaƙƙwaran dalili. Kwanciya suka yi sai dai kowa da abin da yake wassafawa a cikin zuciyarsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button