BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Hajiya Nafisa da ta cika fam har wani ɗaci take ji a zuciyarta ta ce, “Inno yanzu shawarar Dubu za a ɗauka? Dubu har wata mutum ce da za a saurari shawara daga bakinta. Maganar gaskiya wannan ci baya ne ace shekara sama da ashirin da bakwai muna zaune a cikin birni rana tsaka a ce mu dawo ƙau…” A hanzarce Baba Abubakar ya ce: “Nafisa! Bana son jin bakinki!”

“A’a ka barta Garba idan bata tsefe ni ba ai ba za ta nuna mini ta isa ba. Don Allah ka gaya mini lokacin da ka auro Nafisa a ina ka aurota da ya wuce ƙauye. Ka tuna lokacin da kuka je ƙauyensu ɗaurin aure Labaran ƙanina cewa ya yi ruwan garinsu kamar turɓaya haka yake. Nan dai gidan gado ne ko ana so ko ba’a so dole mutum ya dawo.” Rai a matuƙar ɓace Aseem ya ɗago yana kallon Yaya babba, da Dubu da ke gefe. Furzar da iska ya yi ya sunkuyar da kai yana danne-danne da waya, sai dai ba zai ce ga takamaimai abin da yake latsawa ba. Baba Adamu ya russuna ya ce, “Inno a duba lamarin dai saboda yanayin aikinmu ga makarantar yara. Idan sha’awar zama kike kusa da mu ni ko Yaya Abubakar wani sai ya ɗauke ki, koma can da zama.”

“Haram giya a gidan liman! Ba da ni ba. Ba zan taɓa bijirewa umarnin Mahaifinku ba, na gama magana idan za ku dawo nan kowa ya gyara wurinsa ya dawo, idan ba za ku dawo ba shi kenan” Tana gama maganar ta rushe da matsanancin kuka.

Zuciyar Baba Munkaila fes don ya san ko ba komai ya san idan suka dawo cikin gidan za su iya ɗauke masa cefanen gidansa. Baba Abubakar yanayinsa sam babu walwala ya dubi Mahaifiyarsa ya ce:

“Inno wannan kawai kike buƙata?” Da sauri Hajiya Nafisa ta hangame baki. Hajiya Fauziya ma ta cika fam tana watsawa Yaya babba harara ƙasa-ƙasa.

Yaya babba ta share hawaye ta ce, “Garba idan kuka yi mini wannan duniya da lahira kun biya ni haƙƙin mahaifiya. Ni dai Allah ne gatana kuma da shi na dogara, ko na dogara da ɗaya daga cikinku?” Baba Munkaila ya ce, “Inno mu kuma fa?”

“Munkaila a gidan duniya ka gaya mini wane abu ka taɓa yi mini.” Baba Munkaila zai yi magana, Baba Abubakar ya katse shi da cewar, “Shi kenan zamu dawo Inno amma ki ɗan bamu lokaci tun da kin ga tashin namu babu shiri dole akwai abubuwan da za mu gudanar.”

“Allah dai ya yi muku albarka Garba, ku yi komai a nutse wallahi. Me ake da gaggawa aikin shaiɗan. Me ye haɗinmu da shaiɗan muna masoya Mazon Allah (S.A.W). Allah ya yi mana tsari da shaiɗan, ku bi komai a sannu ko nan da sati biyu ne.” Cikin haɗin baki suka ce, “Sati biyu Inno?”

“Ko ya yi yawa?”

Baba Adamu ya ce, “Inno Sati biyu ai ya yi kaɗan ina laifin nan da wata guda kinsan ko a gun aiki sai mun ɗauki uzuri.” Ya gaya mata haka ne don ya san yanda take bawa aikinsu muhimmanci. Sai da ta yi jim sannan ta ce.

“Eh ka fi ni gaskiya Ado maza ku je ku yi komai a nutse kar wurin aikin su ji haushi su sallame ku ko?” Hajiya Nafisa kamar za ta yi kuka ta ce, “Yanzu Alhaji shi kenan ka amince nan ɗin za mu dawo?” Aseem ya sa hannunsa ya damƙi hannun mahaifiyarsa don ba ya son ace ita ta fara ɓullo da wata maganar. Fisgewa ta yi ta ci gaba da cewa, “Maganar gaskiya ba a yi mana adalci ba, sai da aka ga ƴaƴanmu sun zama ƴanmata za a ce mu dawo ƙauye wallahi da sake…” Cikin tsawa Baba Abubakar ya ce:

“Nafisa ya isa haka! Tashi ku fice an sallame ku.” Rai a ɓace gabaɗaya matan nasu suka fice daga ɗakin. Baba Abubakar ya russuna ya ce, “Na barki lafiya Inno.” Yana fita Baba Adamu da tsirarun ƴan uwansu suka bi bayansa. Ɗakin ya rage daga Baba Munkaila, Aseem, Dubu, Yaya babba sai Hadiza.

Jiki a sanyaye Yaya babba ta kalli Baba Munkaila ta ce, “Munkaila an ya yaran nan ba haushina suka ji ba kuwa? Na ga kamar a fusace suka fita. Don Allah meye laifina don na nemi haɗa kan zuri’ata?” Baba Munkaila ya washe baki ya ce, “Babu Inno kawai dai haka kika gani amma babu abin da suka ji, ya za a yi su ji haushinki.” Yaya babba ta yi murmushi cikin jin daɗi.

Hadiza da ke gefe ta ce, “Gaskiya Inna bai kamata ace kowacce shawara Dubu ta gaya miki ki ɗauka ki yi amfani da ita ba. Mu fa mune ƴaƴanki mu ya kamata ki kira mu ji shirinki amma nawa Dubu take da za ta baki shawara.” Yaya babba ta yi shiru kamar mai nazari sannan ta ce, “Kuma maganarki fa haka take don kin manta shawarar da Dubu ta bani akan sayar da ƙaton ragona ta ce na siyo ƴan tsaki, me ake yi da kiwon kaji idan ba asara ba? A rana ɗaya sai a fitar mini da mushen biyar suka lalace a banza bai fi ƙwara goma muka mora ba cikin Sittin. Kai amma Dubu an yi shakiyyiyar yarinyar, da ta ga kaza ta fara rufa sai dai na ji ta wasa wuƙa ta yanka, ni an ya ba da biyu ma Dubu ta riƙa yanka kajin nan ana soyawa ba?” Hadiza ta taɓe baki ta ce, “Ai koma meye Inno kun fi kusa. Amma kiwon kaji ana samu da shi wacce kika ɗora akai ce dai sai a hankali. Yanzu mu koma maganar su Yaya Adamu maganar gaskiya Inno ba za su ji daɗin zaman gidan nan ba, tun da sun saba da zaman cikin gari kina gani tun a gabanki me Nafisa take faɗa. Kina ganin zamansu a kusa da ke babu wata matsala?” Yaya Babba ta saci kallon Aseem sannan ta ce, “Ni fa Nafisa ta birgeni, sabo fa aka ce miki Hadiza. Sabo turken wawa, kuma ko ke ce haka za ki faɗa. Gaskiya ki daina cin naman mutane a ɗakina karki haramta mini mala’ikun rahama shigowa ɗakina ina zaune ƙalau. Yanzu ga Soja a zaune idan ya ji kina aibata mahaifiyarsa ba sai ya ɗauki gaba da ke.”

Aseem bai tanka musu ba Hadiza ta ce, “Inno gaskiya fa na faɗa ko a gaban Nafisa zan faɗa ba wai Aseem ba. Ina guje miki abin da za a zo ana yin babu daɗi Amma tun da haka kike so shi kenan Allah ya dawo da su lafiya.” Hadiza na gamaƙ maganar ta tashi ta fice, Baba Munkaila ya rufa mata baya.

Aka bar Yaya babba da riƙe haɓa, Aseem na shirin ta shi ta ce masa, “Soja don Allah ka bar ni na kwashewa yaran nan albarka, kana ganin abin da duk suka yi mini wai haɗe mini kai za su yi su ware ni daga cikinsu. Cikin halin ko’inkula Aseem ya ɗaga kafaɗa ya ce: “Ki kwashe musu mana, idan kin ga dama ki tsine musu ƴaƴana ko naki. Wallahi akwai abubawan da dama da idan muka dawo zan saita muku zama ke da sheɗaniyar jikar taki mutum ya kawo mini wargi na sa bakin bindiga na harbe shi.” Yana gama maganar ya fice a fusace. Da sauri Yaya babba ta dafe ƙirji a firgice da jin maganar da Aseem ya faɗa.

Ummou Aslam Bint Adam????
DUBU JIKAR MAI CARBI

        ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.

FREE PAGE 8
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan???????????????????????????????????????? subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

 Aseem haka ya tafi ya bar Yaya babba hangame da baki, ta yi ƙasa da murya ta ce, "Dubu kin ji abin da Soja ya ce mini kuwa?" Dubu ta bushe da dariyar ƙeta don duk wanda ya ga yanda Yaya babba ta tsure sai ya fahimcin irin fargabar da ta shiga. Dubu ta ja hijabinta ta rufe kanta ta ce, "Ai wallahi Inno tsaf zai harbe ki don ba imani gare shi ba. Ni fa wallahi ina jin ma da ƙyar idan kafiran nan ba su fara koya masa kafirci ba." Da sauri Yaya Babba ta dafa cinyar Dubu ta ce, "Ke Dubu raba ni da jin wannan maganar, Mai sunan Malam ne zai amshi addinin kafirai?" Dubu ta ɗauke kai gefe ta ce, "Yoo musulmin ƙwarai za a haɗa shi da Allah da manzonsa ya ƙi ji ne?"

“A’a! Amma ki ji tsoron Allah Dubu kar ki sa na tuhumi Garba ya sake ɗaukan gaba da ni.” Dubu ta ɓata fuska ta ce, “Ai dama ke ba a magana da ke sai kin kwashe kin gaya musu, haka kika gama ci mini mutumci a gabansu kina kirana da ƙazama.” Yaya babba ta janyo Dubu cinyarta ta ce, “Ina sane na gaya musu haka idan ba haka ba wallahi Soja gaba zai ɗauka da ni amma ki bar ni da su idan suka dawo gidan nan duk za mu saita musu zama.” Dubu na jin haka ta bushe da dariya don har ta gama tamawa yanda za ta yi wasan kura da Nabila don da alama ta lura ita ce hoton Hajiya Nafisa da duk wasu halayenta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button