BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Ɗaukan gawar jaririn ta yi ta miƙawa sauran mutanen wurin, da sauri suka caɓe shi suka buɗe wani ƙaramin ɗaki mai ja da baƙin labule suka wurga ciki.

Raihan na zuwa gida a hankali ta fara zaga bangon da ke cikin ɗakunansu, ga mamakinta tana bi ta cikin ɗakinta ta hangi mai siffarta kwance a kan makwancinta a gefe ɗaya ga Mama Uwani tana zaune tana gadinta. Amma ga mamakinta sai gani ta yi ta gifta ta gabanta ba tare da ta lura da ita ba. Hasalima ratsawa take yi ta ko’ina ba tare da gini ko ƙofa sun yi mata shamaki ba, a hankali ta ci gaba da tafiya kamar mai tafiya a sararin samaniya har ta dira a ɗakin Mahaifiyarta sai da ta ƙare mata kallo sannan ta wuce ɗakin da Mama Hasiya take kwance tana bacci. Kamar yadda Hatsabibiya ta umarceta haka ta tsaya a saitin kanta, ƙashin hannunta ta kai saitin fuskar Mama Hasiya lokaci ɗaya ta buɗe idonta firgigit ta sauke su a kan Raihan, sai dai a cikin idanunta gani ta yi Raihan ta siffanta da wata mummunar hallita, cikin rashin tausayi Raihan ta ƙarasa gabanta ta damƙo maƙogaronta, nan take Mama Hasiya ta fara kakari idanunta suka firfito waje.

Da murya mai wahalarwa Mama Hasiya ta fara karanta kalmar shahada, tana yi tana ambaton sunan Maigidanta da duk sunan wanda ya zo bakinta.

Ana cikin haka wasu tafka-tafkan kunamu suka fara ratsowa ta jikin bango girman kowacce ɗaya ya fi girman kan jariri, da gudu suka fara rarrafowa suka haye gadon sun kai kusan goma suka maƙale a jikin Mama Hatsiya kowacce ta kafa bakinta suka fara zuƙar jini.

Cikin tsananin azaba Mama Hasiya ta fara wani irin ƙaraji da gurnani, tun tana cikin hayyacinta har ta fara fita daga haka idanunta suka kafe rai ya yi halinsa. Raihan na ganin haka ta saki wuyan gawar Mama Hasiya ta faɗa kan gado yaraf ta ja mayafi ta rufeta sannan ta miƙawa kunamin nan hannu lokaci ɗaya suka maƙaleta, ta ɗago da su saitin fuskarta. Haƙoranta ne suka fara girma ga wata fiƙa irin ta karnuka da ta fito mata, bakinta ya fara zubda wani baƙin jini mai yauƙi. Ƙwayar idanunta zazzago suna wani irin juyi, a hankali ta fara takawa ta fice daga ɗakin ta koma ta sashen ɗakin Mahaifiyarta, ta jima a bakin window sai da ta yi ƙwafa sannan ta ratsa ta jikin bango ta fice daga gidan.

Bayan sun wurga Jaririn cikin wannan ɗakin wata irin tsawa aka yi mai haɗe da walƙiya, a hankali hatsabibiya ta shiga ɗakin tuni wata mummunar hallita mai ɗauke da kawuna har guda goma a jikinta, a kowanne baki akwai aikin da yake aiwatarwa. A ɗaya daga cikin kan mummunar hallitar ta cafke jaririn tana laƙumewa, wani kan kuma ya fara amayo da kuɗaɗe kala-kala har da na ƙasashen waje, ya yin da wani kan ya fara tatsar da wani ruwa mai yauƙi yana zuba watsu ƙananan ƙwari suna zuwa suna tsotsa.

Suna nan tsaya Raihan ta diro cikin gidan, hannuwanta biyu saƙale da kunamu tana tafe cikin takun ƙasaita dauke mummunar hallita. Tana zuwa Hatsabibiya ta fito fuskarta ɗauke da murmushi, shigar Raihan wurin ya sa jikin wannan dattijon ya fara ɓamɓarowa daskararran jikinsa ya fara rozayewa a hankali har ya rozaye gabaɗaya. Wata irin girgiza ya yi nan take ya fara kallon mutanen wurin ɗaya bayan ɗaya, Hatsabibiya ta tako a hankali fuskarta ɗauke da annuri ta ce, “Barka da dawowa cikin rayuwarka ta ainihini Ya masoyina.” Hannuwanta ya riƙo yana bin ta da kallo lokaci ɗaya ya rungume ta yana shafa bayanta sannan ya ce, “Ina godiya da sadaukarwarki, amma ya aka yi kika samu tsarkakken jini alhalin an ce sai ta silar Muraza shin kun samota ne?” Hannunsa ta ja bakin wata tsohuwar rijiya da ke cikin ɗakin tana faɗin, “Mu je turaka zan baka labari.” Tana rufe baki suka faɗa cikin rijiyar shigewarsu keda wuya wurin ya shafe tamkar ba a taɓa hallitar wani abu a wurin ba.

Wani tutturnan mutum da suke kira da Mataimaki shi ya ƙarasa wurin Raihan ya karɓi kunamin hannunta, ya zuba su a cikin wani ƙoƙon kai sannan ya dubi Raihan ya ce, “An gaishe ki Jaruma, Shugaba mai cikakken iko sai ke gagabadau. Za ki iya tafiya sai ranar taro na gaba amma a ranar muna buƙatar tukwicin sabuwar gawar mace mai ƙarancin shekaru kar su yi ƙasa da talati kar kuma ta haura shekara arba’in.” Raihan ban da jinjina kai babu abin da take yi, tana gama sauraronsa ta dubi Intisar alamar su tafi. Intisar ta nuna mata wata ƙoriyar ƙwarya mai cike da wani ruwa mai ɗauke da launin jini kamar anwanke nama, sannan ta ce: “Ki kuskure bakinki da ruwan tsarki domin samun albarka.” Ba musu Raihan ta ƙarasa ta ɗauki ƙwaryar ta kafa kanta, tana kafa kai ta ji kanta ya sake yin nauyi dumm! A hankali ta iya kai ƙwaryar bakinta ta kuskure wata irin kasala ta mamaye jikinta, ga wani irin addababban bacci da ya lulluɓe idanunta. Tana ajiye ƙwaryar ta tafi luuuu za ta faɗi da sauri Intisar ta taro ta jikinta, sannan ta saɓa ta a kafaɗa ta fice daga cikin kogon dutsen kai tsaye ta wuce gidan su Raihan.

Intisar bata tsaya a ko'ina ba sai a tsakiyar ɗakin Raihan, tana kallon Mama Uwani ta saki wani malalacin murmushi. Kwantar da Raihan ta yi sannan ta fara zagaye ɗakin ba tare da idanun Mama Uwani sun gane mata Intisar ba, lokaci ɗaya ta saki wata mahaukaciyar dariya. Tun tana dariya a tsaye har ta durƙushe a wurin sannan ta ratse ta ƙarƙashin ƙasa ta fice daga ɗakin.

WASHEGARI

Da Asuba bayan su Inno sun gabatar da sallah suna zaune kowacce a sallayarta suna jan carbi, Goggo ta dubi Inno ta ce: "Wai ni kuwa yarinyar ta tashi sallah kuwa don ko motsinta ban ji ba, saboda Allah neman haihuwa ya fi bautar Ubaniji. Jiya na ga saboda neman haihuwa raba dare suka yi a wurin wancen Kafiriin, gaskiya a tambayi Malamai an ya; ya hallata neman haihuwa wurin kafiri." Inno takaici ya fara rufeta, ta dubi Goggo ta ce, "Zinaru ki yi ta kanki idan kika kafirta min yarinya a yau ba sai gobe wallahi sai Audullahi ya mayar da ke Albasu. Kafira ce da har yanzu za ta zauna babu sallah babu salati?" Goggo cikin nuna rashin damuwa ta wara hannuwa tana faɗin, "Allah shi ne masanin daidai, ba zan amsa ba ki sa na yi wa ƴar mutane ƙazafi akan abin da ban ji ba ban gani ba, ni dai na san da Hasiya ta tashi za ta leƙo wurinmu. Bari ki ga na je na tashe ta ko na samu lada mai tsoka, bar zancen Albasu tun da ko jini baki taɓa zubarwa a cen balle a binne mabiyyarki." Goggo na ƙarasa maganar ta fice daga ɗakin, tana tafe tana mita har ta ƙarasa bakin ƙofa tana ƙoƙarin buɗe ƙofar sai ga Inno ta rufo mata baya ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Saboda Allah Zinaru in haifi abartawa a ciki amma ki nemi ki yi mana farraƙu da ita, Allah ya sani idan Hasiya ta ga ban tashe ba na ɓalɓalce don ɗauka za ta yi baƙin cikin shiga aljanna nake yi mata." Goggo bata bi ta kan Inno ba ta tura ƙofar tana rangaɗa sallama, kamar haɗin baki suka shiga ambatar sunan Hasiya amma shiru suka ji kamar an shuka dusa. Inno ce ta yaye zanin rufar jikinta nan take suka yi tozali da gawarta, kusan suman tsaye suka yi aka rasa mai furta koda kalma ɗaya ne.  Nan take Inno ta yanke jiki ta faɗi, Goggo jiki na tsuma ta juye hanyar waje tana ƙwalawa Mommy kira. Can sashenta ta wuce saboda fargaba tini ta zubar da carbi don lokaci ɗaya ya tsinke ya tarwatse, da kusan rarrafe Goggo ta hau sama tun bata ƙarasa ba suka ci karo da Mommy shi kansa Daddy kiran Goggo ne ya sa shi fitowa daga ɗakinsa a lokacin yana zaune yana cike-ciken takardu.Hankali a tashe  suka shiga jera mata tambayoyi ban da nuna musu ƙofa babu abin da take yi, sai da ƙyar suka samu ta iya furta, "Hasiya babu ta riga mu gidan gaskiya." Cikin rashin fahimta suka ce, "Wace Hasiya?" Saboda ko a kaɗan basu kawo Hasiya a ransu ba. Goggo cike da jin haushi ta ce, "Hasiya dai ƙanwarka Audullahi ko kana da wata Hasiyan ne." Kusan tare suka nufi hanyar sauka don zuwa su ganowa idanunsu.

Kamar masu rige-rige haka suka shiga ɗakin da Hasiya ke yashe a kan gado, Daddy ne ya fara zuwa kan Inno Mommy ta ƙarasa wurin gawar Hasiya ta fara tattaɓata tana ambatar sunanta amma shiru tafiya ta miƙa. Da hanzari Mommy ta wuce firji ta ɗebo ruwa ta fara yayyafawa Inno sannan ta yayyafawa Hasiya, nan take Inno ta fara motsawa saidai da alama bata cikin hayyacinta amma Hasiya ko alamar motsi bata yi. Daddy ne ya rungumo Inno ya fita a guje yana ƙalawa maigadi waya, kusan gware suka yi a hanya Daddy ya nufi wurin motoci yana faɗin, “Maza-maza buɗe min gate.” Tun bai rufe baki ba Driver ya fara kiciniyar buɗe ƙofa nan take bawa motarsa wuta ya fice daga gidan, Mommy jiki a sanyaye ta bi bayan motar da kallo fuska ɗauke da hawaye. Ɗakin ta koma ta janyo hannun Goggo ta rufe ɗakin, kan kujera ta zauna ta rafka tagumi ban da hawaye babu abin da take yi, saboda ba ƙaramin shaƙuwa suka yi da Hasiya ba. Goggo ban da sintiri babu abin da take yi tana nan tsaye suka ga Mama Uwani ta fita, cikin rashin sani ta fara tambaya, Goggo da sai a lokacin kuka ya kubce mata cikin shassheka ta ce, “Bari Uwani yau mun wayi gari da tashin hankali Hasiya babu, yarinyar nan jiya-jiya muka gama hira da ita amma yau sai labari.” A tsorace Mama Uwani ta nufi ɗakin don ganewa idonta, tana shiga ta samu gawar a kan gado cikin hanzari ta buɗe ta tana ƙarewa gawar kallo.

Ido ta zurawa gawar tana jinjina kai a hankali ya furta, “Tabbas akwai lauje ciki naɗi amma akwai ɓoyayyan al’amari a dangane da gawar nan.” Tana gama maganar ta fice daga ɗakin zuwa falo, ba a ɗauki lokaci ba sai ga Daddy ya dawo. Dawowarsa babu wuya mommy ta tashi Raihan ta sanar da ita halin da ake ciki, murtsuke ido ta yi tana yamutsa fuska ta ce, “Mommy waye ya mutu?” Mommy ta sake maimaita mata, “Mamanki Hasiya yanzu haka gawarta na ɗaki mutane sun fara taruwa.” Lokaci ɗaya ta ji kanta ya yi mata nauyi dum! Har sai da ta runtse idonta ta buɗe ta dafa kanta da hannu biyu ta ce, “Mommy me ya sameta ta mutu?” Da sauri Mommy ta rufe mata baki tana faɗin, “Raihan wa yace miki sai an yi ciwo ake yin mutuwa?” Jikin Raihan ba ƙaramin mutuwa ya yi ba, a hanakali ta tashi tana haɗa hanya jikinta sanye da rigar bacci shara-shara babu abin da ta ɓoye na surarta. Ɗakin da Mama Hasiya take ta tunkara Mama Uwani na hangota da sauri ta nufi wurinta ta rungomata tsam a jikinta tana faɗin, “Uwar ɗakina sai haƙuri.” Wani iri Raihan ta ji a jikinta yarr a lokaci ɗaya kanta ya yi mata yaaaam! Tsigar jikinta ce ta ci gaba da tashi, a hankali ta saki hannunta tana bin Raihan da wani mayatattacen kallo.

Kafin wani lokaci tuni gidan ya cika da mutane ban da koke-koke babu abin da ake yi, Raihan can gefe ta raɓe ta fashe da wani irin matsanancin kuka. Mai gidanta da aka gaya masa da farko ƙaryatawa ya yi sai da ya zo ya ganta, zama ya yi kamar mace ya yi ta kuka sai da ƙyar ya yi shiru. Kimanin ƙarfe goma aka gama wanke gawarta aka shiryata, ana gabda za a fita da ita sai ga Intisar ta turo ƙofa ta shiga gidan tana kallon mutanen gidan ɗaiɗai tana shigowa ana ɗaukan gawar, tana kalle-kalle Mama Uwani ta fisgi hannun Intisar ta ja ta ɗakin baya wanda baƙi suke sauka a ciki. Rai a matuƙar ɓace ta dubi Intisar ta ce, “Me ya kawo ki gidan nan?” Intisar dariya ta yi ta fara takawa a hankali sai da ta yi taku uku sannan ta juya ta kalli Mama Uwani ta ce, “Abin da ka ke yi cikin suffar tsofaffi shi ne ya kawo ni a wannan suffar.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button