BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Ɗan’iya ya zayyanewa Mahaifiyarsa abin da ya faru. Hansatu na jin ƙarashen labarin ta shuri takalma garin ɗaukan takalmi ƙafarta, ta shuri bokitin Ɗan’iya da ke cike da yashi. Hansatu ta nuna Bokitin tana faɗin, “Ɗan’iya ba wannan ba ne bakitin da ka fita da shi?” Nan take mamaki ya cika su. Hansatu ta suri bokitin ragadadar da ke cike da yashi, ko ta kan Balarabe bata bi ba ta wuce gidansu Dubu tana kumafar baki.

Lokacin da Yaya babba ta gama jin jawabinta, kallon sheƙeƙe ta yi wa Hansatu sannan ta ce, “Hansatu kura ko mayya kika mayar mini da Dubu da za ta iya cinye bokitin ragadada guda? Allah na tuba me ye ragadada abin da duk yaɗi da jijiya ne, me ye Dubu bata ci a gidan nan?” Takaici ya kama Hansatu ta yi ƙwafa sannan ta ce, “Dama ai sake ta samu shi ya sa take shuka tsiyar da take so, to wallahi daga kaina ba za ta sake yi wa wani haka ba.” Tana gama masifar ta fice, Inna furai ta bita har soro tana mayar mata da martani.

“Aniyarki ta faɗa kanki, azzulama mai baƙin baki. Bayan zazzagar iya shegen da kika yi mata shi ne bai ishe ki ba za ki biyota har gida kenan.” Sai da ta ga ficewar Hansatu ta juya ta samu Yaya tana faɗin, “Yaya an ya maganar yarinyar nan bata kan hanya, na san halin Dubu sarai za ta iya tare yaron nan ta karɓe bokitin ragadadar fa.” Yaya babba ta yi ƙwafa cike da takaici ta ce, “Ai kuwa wallahi da na ɗebe mata falsafar albarka alƙur’an da babu ni babu ita.”

Hansatu kai tsaye wurin mai unguwa ta wuce bayan ta kwashi gaisuwa ta zayyane masa abin da yake faruwa, ba shiri ya aika da kiran gaggawa gidan Marigayi mai carbi. Zuwan dogarawan ya yi daidai da zuwan Baba Abubakar shi da Aseem, wannan sammaci ba ƙaramin ɓata ran Baba Abubakar ya yi ba. Ya ci alwashin idan kuwa haka ta tabbata Dubu ce ta cinye ragadadar, tabbas ba ƙaramin hukunci zai ɗauka akanta ba don duk abin da Yaya babba za ta faɗa sai dai ya toshe kunnuwansa. Shi da Aseem suka wuce wurin mai unguwa ba tare da sun shiga cikin gidan ba. Suna zuwa aka aika kiran Dubu, tare da Dogarawan suka taho tana zuwa ta yi turus! Jiki a sanyaye ta zauna ta hangi Aseem na wurga mata harara sai Ɗan’iya da idanunsa suka yi wuri-wuri, saboda kukan da ya sha. Hansatu lokaci-lokaci take kallon Dubu tana ƙwafa cike da jin haushi.

Shiru wurin ya ɗauka Mai gari ya ƙurawa Dubu ido yana son gano gaskiyar lamari, don ya san sarai Dubu za ta yi abin da ya fi haka, bayan an gabatar da abin da ya tara su a wurin, Mai unguwa ya kalli Ɗan’iya ya ce, “Ɗan’iya ko za ka gaya mana yanda abin da ya kasance.” Ɗan’iya ya fyace majina sannan ya zayyane duk abin da ya faru tsakaninsa da Dubu. Tun bai rufe baki ba Dubu ta yi caraf ta fara magana, “Alƙur’an ƙarya yake yi mini haka kawai zai yi mini sharri saboda ba ƙaunata ake…” Da sauri Baba Abubakar ya katse ta yana yi mata daƙuwa Hansatu ta tura ɗankwali gaba tana faɗin, “Allah ya taimakeka ka yi mini tsakani da Dubu wallahi muddin ta sake shiga gonata sai na yi ƙasa-ƙasa da ita. Ƙwaranƙwatsa kuma sai an biya ni kuɗin ragadadata.” Mai unguwa zai yi magana Aseem ya zaro dubu biyar ya miƙawa Hansatu yana faɗin, “Shi kenan magana ta wuce.” Dubu na gefe da ta ga maƙudan kuɗin da aka bawa Hansatu ta yi zaraf ta ce, “Wallahi ragadadarta bata kai da kuɗin nan bayan kafin na karɓi bokitin Ɗan’iya ya ce mini ta dubu ɗaya ce.” Ta ƙarasa maganar za ta warci kuɗin da sauri Hansatu ta maƙe su tana cewa, “Ai irin wannan asara kullin ma Allah ya kawo ta.” Baba Garba saboda ɓacin rai sallama ya yi wa Mai gari ya tafi ya tafi, shi kuwa Aseem hannun Dubu ya fisga suna tafe yana haɗa hannunsa da nashi yana murzawa. Ban da wash! Babu abin da take yi saboda yanda hannunta yake yi mata raɗaɗi.

Suna shiga cikin gidan suka wuce sashen su Yaya babba har lokacin hannun Aseem na riƙe da Dubu. Tun da Yaya babba ta hango su take sakin murmushi, don shi kansa Aseem har sai da ya saki murmushi saboda yanda ya ga kakar ta shi cikin farinciki. Tun kafin su zauna ta sake washe baki tana faɗin, “Allah ƙadiran alamanyasha’u. Ikon Allah! Allah mai sanin abin da yake cikin zuciya.” Gabaɗaya ba su kawo komai a ransu ba sai ɗan murmushi da suka yi. Bayan sun gaisa cikin ɓacin rai Baba Abubakar ya fara yi wa Dubu faɗa, kasancewar mutum ne ba mai zafi ba ya sa bai cika faɗa ba, amma Dubu ba ƙaramin tsora ta yi ba. Saboda dama mai haƙuri bai iya faɗa ba. Yana gamawa Yaya babba ta dasa nata faɗan.

“Maganar gaskiya Dubu kin wulaƙanta ni ki rasa me za ki karɓarwa yaro sai ragadada?” Inna Furai ce ta shiga ɗakin tana girgiza kai ta ce, “Don Allah Garba ka ji wata muguwar ɗabi’a, ka gaya mana meye Dubu bata ci a gidan nan?” Yaya babba ta yi ƙwafa ta ce, “Gane mini hanya Furaira neman maganar fa. Garba ka rabani da Dubu tun takaicinta bai kashe ni ba, ba zan iya ba gaskiya ba za ta ƙara kwanar mini a ɗaki ba. Ina dalili ta kashe ni ta cuci iyalaina, ko da dai kun girama shi fa Maraici ba daɗi gare shi. Don Allah Garba idan babu ni ba kun zama marayu gaba da baya ba? Na gaji gaskiya, ka sa Dubu a gaba ka tafi da ita na bar maka ita halak malak.”

Baba Abubakar ba ƙaramin daɗi ya ji ba, don dama ya jima yana san ɗaukan Dubu Yaya babba ce take hanawa. Ya gyara zama ya ce, “Dama Inno na daɗe ina yi miki maganar amma yanzu tun da kin amince zan tafi da ita.” Madadin Yaya babba ta yi magana sai ta yi jim sannan ta ce, “Ni fa Garba ba raba ni da Dubu ne bana so ka yi ba, gaskiya a riƙa zalintar marainiyar Allah ne bana so. Wannan matar taka ba ƙaunar Dubu take ba, sai ta zo ta yi ta gallazawa marainiyar Allah, ina nan ban san halin da ake ciki ba. Kai kuma mutuwar sonta kake ballantana ka tsawatar mata. Gidan Ado kuma Fauziyya sai jaraba mace sai masifa ko ƴaƴan cikinta ba ƙaunarsu take ba bare kuma Dubu, raba ni da bawa Ado Dubu ana zaune ƙalau. Ita kuma waccan mai tausayin ƙasar komai nata ba kuzari ina dalili inkai Dubu ta riƙa barinta da yunwa? Ni inbawa Rahama Dubu ta kashe ta da yunwa Allah ya tsare ni. Don Allah Garba wacce riba suke ci wai Rahama basa karyawa sai goman safe, mu da anan ƙarfe goma an fara haramar na rana. A’a gara Dubu ta yi zamanta a nan ina ganinta ina jin daɗi.” Baba Abubakar ya girgiza kai don dama sai da ya ayyana haka amma ya ci alwashin ko da dabara sai ya karɓi Dubu muddin ya dawo gidan da zama, don barinta a haka har girmanta akwai gagarumar matsala.

Yaya Babba ta kalli Inna Furai ta ce, “Furaira ki gaya masa mana ai kyayi mini kara dai ko?” Inna Furai ta washe baki ta ce, “Garba wani abin alkhairi muka hango kuma mun san da kai da kaya duk mallakar wuya ne. Mun yanke shawara ni da Yaya ya kamata a ci gaba da yaɗa zumunci.” Gaban Baba Abubakar sai da ya faɗi don ya san wataƙila wani abin za su ɓallo masa.

Inna Furai ta karɓe zan cen da cewa, “Ka san dai bikin su Salisu da su Zulfa bayan babbar sallar nan ne kuma dududu bikin saura wata guda ina jin.” Baba Abubakar ya gyaɗa kai ya ce, “Ai ina jin lokacinma mun dawo nan.” Inna Furai ta yi dariya ta ce, “Ai za ku sha hidima tun da auren ƴaƴa shida ba wasa ba.” Baba Abubakar ya yi murmushi don shi kansa idan ya tuna bikin har daɗi yake ji ace cikin gidansu za su aurar da ƴaƴa shida maza da mata kuma duk auren gida abin akwai farinciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button