BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

A karo na biyu Baba Abubakar ya sake kiran sunansa, “Aseem.” A marairaice ya ɗago ya amsa sannan Mahaifinsa ya ci gaba da cewa, “Inno fa mahaifiyata ce kana ganin zan iya kaucewa umarninta, idan har ina neman albarka duniya da lahira? Su fa iyaye biyayya ake musu akan duk abin da suka buƙata matsawar bai saɓawa mahallici ba, ko da kuwa baka ƙaunar abin sai ka ga wata rana abin ya zame maka alkairi.” Murya a raunane Aseem ya ce, “Daddy nima ban taɓa saɓa umarninka ba, amma maganar gaskiya idan aka tilasta ni na auri Dubu sai dai na barta a gidan nan, na yi tafiya ta.”

“Da ka wulaƙanta ƴar ɗan’uwa bayan ka aureta; ai gara ka ce mini ban isa na saka ko na hanaka ba. Zan yi ƙoƙarin ganin na shawo kan Inno idan ta amince shi kenan, idan bata amince ba, ka yi haƙuri ka amshi ƙadaddararka hannu bibbiyu, ka san kowanne bawa baya kaucewa ƙaddararsa, ta yiwu alkairin na gaba kai da kanka za ka ji daɗin haka. Saboda sautari muna ƙin abin da shi ne alkairi a tattare da mu sai daga baya mu fahimci haka.” Shiru ne ya ratsa Aseem ya kasa furta komai, zuciyarsa ban da zafi babu abin da take yi masa. Jiki a sanyaye ya tuƙa mota suka wuce gida, kowa na saka da warwara a cikin zuciyarsa.

Tun shigar su cikin gidan Hajiya Nafisa ta fahimci gabaɗaya babu mai cikakkiyar walwala a tattare da su, har ta fi damuwa da damuwar Aseem saboda Baba Abubakar ba wani zaman daɗi suke yi ba, duk akan maganar komawarsu Ɗangwauro. Aseem na shiga ɗaki ta bi bayansa, a ɗaki ta same shi yana kaiwa da kawowa haɗe da kaiwa bango naushi. A ɗan tsorace ta fara watsa masa tambayoyi:

“Lafiya Asem? Wani abin ne ya faru da ku daga kai har Daddynku na ga baku da walwala?” Murya a can ƙasa ya ce, “Mommy babu komai, kawai wurin aiki ne suka kira ni akan wani issue ɗin.” Kallon tsaf ta yi masa tana son gano gaskiyar abin da ya faɗa sannan ta ce, “An ya ba wani abin ne yake faruwa a Ɗangwaro ba?”

Da sauri ya kalle ta sai kuma ya ɗauke kai gefe saboda ambatar sunan garin, ba ƙaramin dawo masa da ɓacin rai ya yi ba, ya zauna a gefen katifarsa ya dafe kansa da hannu bibbiyu ya ce, “A’a Mommy.” Taɓe baki ta yi ta ce, “Idan ma wani abin kuke ɓoyewa indai Hajiya babba ta kafe kai da fata na san ko ba daɗe ko ba jima zai fito fili.” Tana gama maganar ta fice daga ɗakin.

Aseem ya ƙi sanar da Mahaifiyarsa ne saboda ya san Daddynsu ba zai taɓa sanar mata a wannan ranar ba, duba da yanayin zaman da suke a wannan lokacin. Uwa-uba kuma ya san idan ya gaya mata kamar ya ƙara hura wutar tashin hankali a tsakanin iyayen nasu ne. Lokaci ɗaya tsanar Dubu ta mamaye zuciyarsa don duk ita ce silar komai, dukda hali irin na mahaifiyarsa tun da ya taso bai taɓa jin suna sa’insa ita da Mahaifinsa ba. Amma lokaci ɗaya ta tarwatsa farincikinsu ga auren iyayensu, da yake tangal-tangal tun da har lokacin Hajiya Nafisa na kan bakarta da ta koma ƙauyen nan, gara ya sallameta ta kwashi ƴaƴanta, ta riƙe a wurinta ko sa samu irin mijin da take buri da fatan su samu. Kamar yanda ta gama yi wa Aseem tanadin ƴar ƙawarta, saboda komai ta fi so su yi cikin bajinta da harkar girma.

A daren ranar ya haɗa kayansa tsaf a cikin jaka, washegari da sassafe ya wuce Lagos da yake acen yake aikinsa. Wannan ya ƙara tabbatarwa da Hajiya Nafisa tabbas akwai wata a ƙasa, amma zafin zuciya irin nata ya sa ba za ta iya tambayar mahaifinsa don jin abin da yake faruwa ba. Kuma ta lura shi kansa har lokacin baya cikin walwala, ga yawan waya da ta ga yana yi da ƴan’uwansa. Ga shi ba wata kyakkyawar alaƙa gare ta da facalolinta ba, bare ta kira ɗaya daga ciki don ta ji halin da ake ciki ba.

BAYAN SATI BIYU

Duk wani daɗin baki da dabara irin ta tsofaffi Yaya babba ta yi wa Dubu, kuma tuni ta ji ta aminta da Aseem a matsayin mijin aure. Don ba ƙaramin ƙawatawa Yaya babba ta riƙa yi mata ba, tana nuna mata irin rayuwar jin daɗin da za ta yi matuƙar da auri Aseem, hatta wanki ta daina sai dai ya ɗauko mai yi mata. Kan Dubu ba ƙaramin girma ya ƙara ba don ji ta yi duk faɗin garinsu babu wacce ta yi dacen mijin aure sama da ita.

Tuni maganar auren Aseem da Dubu ta karaɗe cikin ƙauyen Ɗangwauro, mutane da yawa mamakin wannan haɗin suke yi ganin Aseem cikakken ɗan gayu amma ya ƙare a auren Dubu. Cikin dangi sai tsegungumi ake da wannan maganar, lokacin da labarin auren Aseem da Dubu ya isa kunnen Hafsa ƴar wurin Hajiya Fauziyya, zama ta yi dirshen tana kuka don duk duniya babu wanda take so da ƙauna sama da Aseem, amma rana tsaka a ce wai Dubu ita ce za ta aure shi. Tun daga ranar ta bar walwala bata da aiki sai zaman ɗaki, ga shi an yi tambayar duniya ta ƙi faɗa, sai dai ta ce bata jin daɗi.

A wannan lokacin saura kwana uku tariyarsu a Ɗangwaro, sun gyara sashensu da sauran ɓangarorin gidan, gidan ya fito kamar a birni. Har fasalin ƙofar gida suka sauya suka rushe gaban gidan, suka saka ƙaton gate wanda mota za ta iya shiga har harabar wurin da suka zagaye da ya zama wurin parking space. Haka bikin su Dubu a lokacin saura sati biyu cif, su Yaya babba har an fara gyaran Amare. Aseem da Dubu a gefen sashen su Yaya babba aka gyara musu, gini ne mai ɗaki uku sai kitchen da banɗaki. Sai Salisu da Zulfa suna maƙota da su Dubu, Bilalu da Murja suna maƙotaka da Baba Auwalu sai kuma Bashari da Maryama a suke maƙotaka da su Baba Adamu. Duk gyaran da ake wa amaren Yaya babba da Inna Furai sune jigo da ragamar komai.

Sai dai duk wannan budurin da ake yi mai gayya mai aiki, Mahaifiyar Aseem bata san wainar da ake toyawa ba har sai ana gobe tariyarsu, a lokacin da suke tsaka da hatsaniya ita da mijinta. Suma ganin Manyan akwatuna ta yi a ɗakinsa kishi ya rufe mata ido don a tsammaninta idan sun koma Ɗangwaro aure zai ƙara. Bayan ya gama sauraronta ya saki murmushin ƙeta don ya san muddin ya sanar da ita abin da yake faruwa ba lallai ta samu damar runtsawa a ranar ba. Saboda yana da tabbacin Aseem bai sanar mata da abin da yake faruwa ba, saboda har lokacin shi ma ɗaukan maganar yake kamar almara. Kafin lokacin akwai lokacin da Baba Abubakar ya kira a kan maganar kayan lefe, amma babu wata tsayayyiyar amsa da Aseem ya bashi. Hakan ne ya sa ya bugi ƙirji ya yi masa komai, saboda idan ya biye ta tashi ya san babu abin da Aseem zai yi.

Shi kuwa Aseem har kullin sai ya yi yunƙurun sanar wa mahaifiyarsa halin da ake ciki, amma fargabar tashin hankalin da za a shiga sai ta hana shi, don haka ya danne a bari Mahaifinsa ya sanar mata da kansa. Kuma dama sun riga da sun yi maganar shi da Mahaifinsa ya ce masa kada ya gaya mata har sai shi ya tunkareta ya gaya mata.

Bakinsa ɗauke da murmushi ya ce, ‘Kanyan ɗanki Aseem ne za a kai masa na aure, yanzu haka saura sati biyu bikin dama ko baki tambaya ba yau na yi niyyar sanar da ke.” Ku san suman tsaye ta yi jikinta har rawa yake ta ce, “Idan ma wasa kake min don Allah ka fito ka gaya mini gaskiya, idan aure za ka ƙara ba sai ka ɓillo min ta wannan sigar ba.” Bai tanka mata ba ya buɗe durowar kayansa ya zaro katin ɗaurin aure ya miƙa mata. Hannu na rawa ya karɓa ta fara karantawa da yake ɗaurin auren mutane da yawa ne, sai ba za ido take don ta ga sunan Aseem da sunan Amaryar da za a aura mata ba tare da ta santa ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button