BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

          FREE PAGE 5


 Fuskar Mama Uwani ce ta rune saboda ɓacin rai nan take ta fara fesar da numfashi mai ɗauke da turirin hayaƙi mai zafi, sannu a hankali Hannuwanta suka fara fidda wasu irin baƙaƙen farata masu matuƙar kaifin gaske, harshenta ne ya fara zazzagowa haɗe da fidda waɗansu irin jeluna masu tsawo da santsi tamkar ƴaƴan maciji, fatar jikinta ce ta fara sauya launi zuwa kalar ja haɗe da wani gashi da ya fara tsattsafo mata. Cikin wata irin murya mara daɗin sauraro ta fara magana.

“Wace ce ke?” Intisar ta saki malalacin murmushi ta fara zagaye ɗakin tana ƙarewa Mama Uwani da ke ɗauke da mummunar siffa ta ce, “Menene damuwarka har kake son sanin ni wacece? Dama ka yi abin da yake gabanka don sanin wacece ni ba zai amfane ka da komai ba.” A haukace Mama Uwani ta buga uban tsalle da waɗansu manyan fuka-fukai da suka fito daga ƙasan hammarta, ta dira a gaban Intisar haɗe da karta mata faratanta bisa tsautsayi farcen ɗan yatsanta ɗaya ya karci gefen fuskarta. A zafafe ta matsa baya cikin huci, nan take fatar jikinta ta fara darewa tsokar namanta ta fara bayyana a fili, kanta ya fara rabewa gida biyu wani dogon ƙaho ta fara tsorowa daga tsakiyar kanta. Tana shirin mayar da martani daga can bakin ƙofa suka ji maganar Mommy na ƙwalawa Mama Uwani kira, kamar ƙiftawar ido tuni suka koma hallitarsu ta ainihi. Mama Uwani ta zubawa Intisar wani mugun kallo cike da takaici ta furta, “Idan kere na yawo zabo na yawo watarana za a haɗu.”

Intisar ta ɗaga kafaɗa cikin rashin nuna damuwa ta ce, “Kamar yadda Ungozoma ke jiran mai naƙuda haka koyaushe nake dakon haɗuwarmu domin nasan ba a dauwama da kashi a ciki.” Dire zancen Intisar ya yi daidai da shigowar Mommy cikin ɗakin wasu baƙin mata na biye da ita, kallon Mama Uwani ta yi a ɗan faɗace ta fara faɗin, “Mama Uwani kina ji ina ta magana lafiyarki kuwa?” Kamar yadda ta saba ladabi a gaban su Mommy haka Mama Uwani ta dausashe murya ta ce, “Hajiya a yi haƙuri yanzu na zo wuce wa na hangi wannan baƙuwar ta shigo ɗakin nan shi ne na shigo don na sanar mata cikin gida ake zaman makokin, wallahi na sha’afa ban ji ki ba.” Mommy ta faɗaɗa murmushi tana kallon Intisar ta ce, “Ƴanmata sannu da zuwa.” A kunyace Intisar ta sunne kai haɗe da tsugunnawa har ƙasa tana faɗin, “Mommy ina kwana?” Mommy ta dafa kafaɗarta tana ɗago ta, ta c: “Lafita ƙalau ‘yata tashi tsaye.” Intisar ta amsa da, “Mommy ina Raihan?” A firgice Mama Uwani ta ɗago cikin suɓutar baki ta furta, “Me Raihan za ta yi miki?”

Da sauri Mommy ta kalli Mama Uwani fuska babu walwala ta ce, “Mama Uwani ya haka ne?” Mama Uwani ranta ya sake ɓaci, ta russunar da kai tana faɗin, “Ayi haƙuri Hajiya.” Mommy bata tanka mata ba, ta juya wurin baƙin da take tafe da su ta ce, “Ga baƙi nan ki wuce da su sashenku.” Ta juya wurin Intisar ta ce, “Ni kamar Intisar nake gani.” Intisar ta sosa kai a kunyace ta ce, “Ni ce Mommy, dama na ji abin da ya faru ne na zo in yi mata gaisuwa.” Mommy ta sake goge hawayen fuskarta da yake zuba, don mutuwar Mama Hasiya ba ƙaramin dukanta ta yi ba, ta riƙo hannun Intisar don dama tun da ta ganta take yi mata kallon sani, abin da ya hanata gane ta sau ɗaya ta taɓa ganin wani zuwa da suka yi da Raihan. Intisar ta sake lafewa a jikin Mommy suka nufi hanyar fita, Mommy tana faɗin, “Allah sarki Intisar, ya su mommynku.” Intisar ta ce, “Duk lafiya ƙalau ta ce a yi muku gaisuwa kafin ta shigo.” Mama Uwani jiki a saluɓe ta ja baƙin suka nufi sashensu, Intisar tana tafe tana sakin wani shu’umin murmushi haɗe da bankawa Mommy harara a fakaice.

Wuce mutane suka rinƙa yi duk in da ta keta sai gaisuwa ake yi mata, mommy har lokacin hawaye ne ɗauke a fuskarta. Suna zuwa ta wuce da ita sashen Raihan, Raihan na zaune da su Batula ƴaƴan ƙanne da yayyan mommy, suma ƴan mata ne kuma ta su ta zo ɗaya da Raihan.

Intisar na shiga Raihan ta faɗaɗa fara’arta tana miƙa mata hannu daga zaune, da sauri Intisar ta rungumeta tana faɗin; “Besti ya ƙarin haƙuri.” Idanun Raihan ya ciko da ƙwallah, sai da ta sa hannu ta goge hawaye cikin shassheƙar kuka ta ce, “Besti wai Mama Hasiya ce ta mutu, idan kin tuna hirarmu da ke last ba nace miki ni na ɗauki alƙawarin Baby shower ba idan ta samu Ciki?” Intisar ta matso hawaye cikin sigar tausayi ta furta, “Kayya Besti ya za a yi na manta da hirar Mama Hasiya.” Raihan ta ci gaba da kuka tana faɗin, “Intisar Mama Hasiya na sona kamar ita ta haife ni, wai ita ce ta mutu shi kenan mun rasata.” Kamar haɗin baki lokaci ɗaya suka fashe da kuka mai ban tausayi, sai da ƙyar aka lallashe su musamman Raihan.

Bayan wani lokaci suna zaune tuni an sallaci Mama Hasiya an kaita makancinta, Mama Uwani ce ta turo ƙofar ta shiga saboda gabaɗaya zuciyarta ba ta aminta da Intisar ba, don tun ranar da ta fara ɗora ido a kanta ta fahimci ita ba alheri bace a rayuwar Raihan. Sai dai duk yadda ta so bin diddigin gano wacece ita abin ya faskara, don haka ko da ta shiga ɗakin sai ta hau goge-goge don ganin abin da yake faruwa. Intisar na ganin haka ta saki murmushi a fakaice don ta san tsiyar da za ta shukawa Mama Uwani, yamutsa fuska Intisar ta yi ta ce, “Besti pls ki ce Mama Uwani ba ni ruwa and takalmana suna waje ta kwasominsu.” A hargitse Mama Uwani ta wurgawa Intisar mugun kallo saboda ɓacin rai har sai da ta so bayyana fushinta a fili, kai tsaye Raihan ta dubi Mama Uwani ta ce, “Mama Uwani ki ɗaukowa Intisar ruwa a falo na firij ɗina ya ƙare.” Ganin rainin hankalin Intisar ya yi wa Mama Uwani yawa ya sa bata tanka wa Raihan ba ta kalli Intisar, ta fara wani huci idanunta suka fara sauya lauyi ba tare da Raihan da sauran mutanen ɗakin sun lura ba.

Kofar toilet ɗin Raihan ta kalla lokaci ɗaya kofar ta buɗe da ƙarfi, wani tafkeken maciji ne ya fara silalowa bakinsa na fidda baƙin hayaƙi. Wata uwar ƙara suka ƙwalla a firgice kowa ya fara neman hanyar fita, kafin wani lokaci tuni duk sun fice daga ɗakin har Intisar don ko kaɗan bata yinƙurin yin wani abu a gaban Raihan da zai bayyana ita ainihin wacece.

Mama Uwani nan take ta ɓace a wurin, macijin ra rabu gida biyu ɗaya ya rikiɗa zuwa siffar Raihan ɗaya kuma yana nan a siffarsa ta farko,  ita kuma Mama Uwani ta ɓace tare da Raihan ɗin ainihi. Kamar ƙiftawar ido haka Mama Uwani ta ɗira a wani tsibiri mai ɗauke da dogayen bishiyu masu duhun gaske, sai wasu korayen tsuntsaye masu yawan da wasu hallitu masu siffar ƙadangaru sai dai jelunar su gashi gare ta kamar jelar tunkiya. Raihan da take sume ta shimfiɗar, Mama Uwani ta zauna ta zura mata ido, nan take  ta rikiɗa zuwa surarta ta ainihi wato HUZAIFA. Miƙewa ya yi da surar wata ƙatuwar hallita mai matuƙar tsawo, fatar jikinsa kamar bayan kada ga wata zabgegiyar jela a bayansa mai ɗauke da kawunan macizai masu fidda aman wuta. Hannuwansa ɗauke suke da manyan farata sai harshensa da suke dalalar da wani baƙin ruwa mai yauƙi.

Kamar wancen karan da ya kaita daularsa ta ƙarƙashin ƙasa, a yanzu ma zuwa ya yi daidai wurin da take kwance ya zuba mata ido wata matsananciyar sha’awar Raihan na sake fisgarsa. A hankali Raihan ta sauke ajiyar zuciya sanyin shukokin wurin ya fara dukan gangar jikinta, motsi ta fara yi alamar za ta farfaɗo. Ruwan bakinsa ya ɗiga mata a saitin goshinta, a cen gefe ya je ya ɗauko wannan ƙaramar hallitar mai siffar kunkuru ya ɗagata da hannuwa biyu yana kallo yana jin daɗi, domin babu abin da ya fi saurin faranta ransa sama da ya ga ya haɗa Raihan da abin da ta haifa masa. Mayar da jaririn hallitar ya yi sannan ya dawo kan Raihan da ke kwance, a hankali ya fara mu’amala da ita yana sarrafa sassan jikinta ga wata irin kewarta da ya yi don ya jima bai kusance ta ba, tun ranar da ta haifi wannan mumummunar hallitar tun da ba ya iya ɗaukan kwana biyu cir ba tare da ya kusance ta har ya yi mu’amala da sassan jikinta ba.

Yana tsaka da mu’amala da ita ya ji wata iska ta fara, kaɗawa mai tafe da sarewa. A hankali ya ɗago kansa yana kallon abin da yake faruwa don ko ba a faɗa ba, ya san Mugaza ce za ta dira a wurinsu. Tun bai gama tunaninta ba ya ji kecewar dariyarta a tsakar kansa, miƙewa ya yi daga kan Raihan a lokacin ya bayan ya samu nutsuwa da ita, ya taka wurin Mugaza fuska a haɗe cikin wata irin murya ya furta, “Me ya kawo ki Turakata bayan kinsan hutawa nake yi?” Haushi ne ya sake rufe Mugaza da ke ɗauke da surar wani ƙaton tsuntsu mai kan angulu. Sai da ta yi tsalle-tsallenta sannan ta dira a gabansa rai a ɓace ta mayar masa da martani, “Akwai wani hutu da ya dace ka yi bayan bana kusa da kai?” Huzaifa ya ƙare mata kallo yana shirin magana ta ci gaba da cewa, “Sau nawa zan gaya maka ka fita daga rayuwar yarinyar nan, idan ba haka ba wallahi sai na halakata ta hanyar kisa mai muni.” Wani uban tsalle ya buga haɗe da girgiza sannan ya rikiɗa zuwa surar matashin saurayin bil’adam, ya kalli matarsa Mugaza tare da sakin wani shu’umin murmushi ya ce, “Wannan yarinyar da kike gani na fansar da raina a gareta idan kin ga ban tsayawa rayuwarta ba sai dai bana numfashi, ita ɗin ta zama jinin jikina ko iyayen da suka haifeta idan suka nemi raba ni da ita sai na tarwatsa rayuwarsu.” Jinjina kai Mugaza ta yi haɗe da sakin wata irin shu’umar dariya sannan ta ce, “Wannan shi ne gargaɗi na ƙarshe da na yi maka a kanta, tun da baka ji ba za ka ga ni a gaba kuma idan kwaɓarka ta yi ruwa karka yi kuka da ni. Sai dai zan ci gaba da baka kulawa a matsayina na matarka mai ƙaunarka, amma a kan wannan yarinyar babu wata kalma da za ta sake shiga tsakaninmu. Sai na ladaftar da ruhinta ta yadda za ta yi danasani, sai na azabtar da gangar jikinta domin sai na shayar da ita azaba mai raɗadi” Tana gama maganar ta tashi daga cikin tsibirin ta fice, ko a jikin Huzaifa ya ƙarasa wurin da Raihan take kwance ya sake rikiɗa zuwa siffar marigayya Mama Hasiya haɗe da sauya fasalin wurin, a hankali ya sa hannu ya fara tashinta tare da faɗin sunanta. Ahankali ta buɗe idonta tana kallon wurin da take da Mama Hasiya da take kanta a tsaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button