BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Inna Furai tun da suka dawo daga asibiti take ta bacci ba ita ta farka ba sai bayan magriba, tana farkawa ta hangi Larai a gefenta. Da murnarta ta tarbe ta da sannu sai dai ta lura da yanda Mahaifiyar tata take ƙarewa ɗakin kallo, matsawa kusa da ita ta yi ta ce, “Sannu Inna ya jikin?” Inna Furai ta yunƙura za ta tashi, Larai ta taimaika mata tashi sannan ta ce, “Larai ina su Lantan suke?” Larai ta yi murmushi ta ce, “Inna su Lantan ai sun wuce tun safe yanzu dai bari ki yi alwala ki yi sallah sai ki ciki abinci, ko sai kin fara cin abincin?” Inna Furai ta girgiza kai tana faɗin, “Wane mutum sallah ai ita ce gaba da komai, bare yanzu da Fatale suke kawo mana farmaki. Amma ya maganar tawagar fatwar da ƴan sama jannati?” Larai ta ce, “Inna don Allah ki bar maganar nan wannan fa duk ya wuce komai ya daidaita yanzu bari na kawo miki ruwa ki yi alwala.” Tun daga lokacin Inna furai ta ɗan saki jikinta ta fara harkokinta.

Kafin wani lokaci tuni maganar dawowar su Baba Abubakar ta karaɗe cikin gidan, wasu daga cikin facalolin ban da murna babu abin da suke yi don dama ba ƙaramin haushi suke ji ba, a duk lokacin da suka ga su Hajiya Rahama sun zo garin fes kowacce ta ƴaƴanta cikin gayu. Wasu daga ciki kuma suna jin haushi don gani suke matuƙar matansu Baba Abubakar suka dawo gidan sun koma bola a wurin Yaya babba, don a haka ma ya suka iya da tsiyar da Dubu take shuka musu amma basu da abin faɗa? Wasu kuma murna ɗaya suke ta dawowar tasu don suma su dangwali abin arziƙi saboda ko banza za su ci gaba da cin mai kyau saɓanin da, da sai dai su ga an direwa Yaya babba kayan alatu na more rayuwa sai dai idan ƴaƴansu sun je ta zaunar da su ta ba su, su ci su yi ƙat su suna daga gefe suna lasar baki.

Kamar haɗin baka duka matan Baba Abubakar da Baba Adamu suka haɗa kai kowacce ta kwashi ƴaƴanta suka yi tafiyarsu. Shi kansa Aseem yana fita ya shiga motarsa ya yi gaba, Hajiya Nafisa ta tasa ƴaƴanta suka wuce bakin titi suka tari abin hawa suka tafi don saboda ɓacin rai ko ta kan Maigidanta bata bi ba. Hajiya Rahama da Hajiya Fauziyya ma tafiya suka yi, a hanya babu mai tankawa kowa saboda takaici har suka ƙarasa gida.

Suna zuwa gida kowacce ta yi sashenta da iyalanta saboda ko da cen ma dama ba wani cikakken zaman lafiya suke yi ba. A ranar ma abin da ya sa wani abu bai haɗo su ba saboda ba daɗi ya sa su tafiyar ba kowacce zuciyarta cunkushe take da baƙin ciki.

Gidan Baba Abubakar.

Hajiya Nafisa na zuwa gida ta ɗau waya ta kira ƙawarta Hajiya Ikilima, bata jima da shiga ba aka ɗauka da sallam. Ko ƙwaƙƙwarar gaisuwa ba su yi ba Hajiya Nafisa ta fara da cewa, “Ƙawata don Allah kina ina? Ina son ganinki cikin gaggawa!” Daga can ɓangaren ta bata amsa, “Lafiya kuwa Ƙawas ko tsohuwar ita ma ta sheƙa ne?”

Hajiya Nafisa ta yi murmushin takaici ta ce, “Wallahi da za ta sheƙa da na fi kowa murna a rayuwar duniyar nan. Kai ni tun da nake na taɓa ganin ƙaddararriyar tsohuwa kamarta kuwa, yanzu kina ina kizo na dawo gida don Allah maganar gaggawa ce ina son ganinki.” Hajiya Ikilima ta sauke ajiyar zuciya ta ce, “Gani nan zuwa yanzu kuwa amma ince dai mijinki baya nan ko? Don kinsan gani yake kamar ni nake zuga ki shi ya sa ma bana son zuwa idan yana nan.” A ƙagauce Hajiya Nafisa ta ce, “Ba fa ya nan ya can ƙauyensu ni dai sai kin ƙaraso.” Daga haka suka yi sallama, Hajiya Nafisa ta fara sintiri a cikin ɗaki.

Tana nan tsaye ta ji sallamar Aseem, tun bai tufe baki ba ta fita falon idanu a ƙanƙance ta fara magana: “Aseem yanzu saboda Allah wannan tsohuwar ta yi mana adalci kenan? Saboda Allah a ce duk abin da waccen ƴar iskar yarinyar, mai zubin sheɗanun ta gaya mata da shi za ta yi amfani. Wacce rayuwar za mu tsinta a zaman ƙauye? Tun da ba ta ce mu koma ba sai da ta ga yaranmu sun zama ƴanmata wato yanda waccen za ta zauna a ƙauye tana baƙincikin su Nabila su sami miji a birni. Da sake wallahi, Allah sai dai Mahaifinka ya zama ko zaman ƙauyen ko kuma mu raba gari.”

Dama ya san za a rina don haka ya shiga sashen mahaifiyar tashi don ya samu ya taushe ta. Amma maganarta ta ƙarshe ta fi firgita hanjin cikinsa, saboda tun da yake bai taɓa jin makamanciyar wannan maganar daga bakin Mahaifiyarsa ba. Shi kansa sheda ne duk irin ɗabi’un Mahaifiyarsa na rashin haƙuri amma mace ce mai kyawawan ɗabi’u. Matsalarta ɗaya rashin haƙuri da kawar da kai sai kuma son kanta da saurin ɗaukar zuga, amma bayan wanna baya jin tana da wasu halaye marasa kyau.

Cikin sigar lallashi ya kalli mahaifiyarsa ya ce, “Don Allah mommy zauna mu yi magana.” Bata musa ba ta zauna a kan kujera tana kallonsa. Aseem ya ci gaba da cewa, “Mommy don Allah ki kwantar da hankalinki wannan fa ba abin tashin hankali bane. Kamata ya yi a ajiye maganar nan agefe har zuwan bayan sadakar bakwai, amma Mommy kun taho gida ke da su Nabila da Aunty kina ganin Daddy zai ji daɗi?”

“Dama ban aikata haka don jin daɗinsa ba, Aseem idan kana da wata maganar bayan wannan ka yi amma magana ɗaya za a gaya mini na saurara cewar mun fasa komawa ƙauye. Ina nan wallahi mahaifinku zai dawo ya same ni.” Tashin hankali wanda ba a sa masa rana. Miƙewa Aseem ya yi ya ce, “Allah ya huci zuciyarki Mommy amma hakan sam bai dace ba yanzu idan Iya ce (Mahaifiyar Hajiya Nafisa) ta ɓata miki rai na san ba za ki yi haka ba, kin ga Daddy shi ma gani zai yi don ba mahaifiyarki ba…”

“Fita ka bani wuri” Hajiya Nafisa ta faɗa tana nunawa Aseem ƙofa azafafe. Sum sum sum ya miƙe zai fita ta ci gaba da faɗa, “Ai wallahi dama na sani wannan zaman daɓaron da tsohuwar nan take zuwa duk lokacin dana haihu ba banza ba, ta gama asirce mini ƴaƴa fa magane-maganen da take basu tun jarirantaka. Ban da lalacewa kai ba me shigar mana ba ne sai inda ƙarfinka ya ƙare, a’a kai gudun ɓacin ran mahaifinka kake yi.” Aseem ya fice daga falon ya bar Mhaifiyarsa tana da sababi.

Gidan Baba Adamu.

Hajiya Rahama ita kaɗai ta ƙule a ɗaki tana nazari, lokaci ɗaya ta ji kamar ba su kyauta da abin da suka yi ba domin suma idan mahaifansu ne dole su yi musu biyayya. Tashi ta yi jiki a sanyaye ta nufi sashen Kishiyarta Hajiya Fauziya, a falo ta same ta tana waya, tana ganin Hajiya Rahama ta ce, “Ok, ba damuwa za mu yi waya an jima.” Hajiya Rahama ta kalli Hajiya Fauziya ta ce, “Mamin yara na zo mu yi magan.” Kujera ta nuna mata fuska ba walwala ta ce, “Zauna ina jin ki.”

“Gani nake kamar ba mu kyatawa Alhaji ba, saboda Mahaifiyarsa tamkar mahaifiyarmu ce idan ta mu mahaifiyar ce muma babu yanda muka iya dole mu yi mata biyayya. Kina gani ko sadakar uku ba a yi mun taho gani nake gaskiya akwai…” Tun bata ƙarasa ba Hajiya Fauziyya ta katse ta da cewar,

“Don Allah idan wannan ne ya kawo ki kwashi tsummokaran ƙafafuwanki ki ƙara gaba, bana son kutungwila da shegen iyayi kamar ta macen kyankyaso. Kin san da haka kika ɗebo ƙafa kika taho ai sai ki tashi ki koma ba sai kin zo min ba.” Hajiya Rahama ta miƙe tana cewa, “Ni na kawo kaina duk abin da kika faɗa, nina ja wa kaina.”

“Oho fice ki bani wuri tun da ban gayyatoki ba, kinibabbiya kawai.” Hajiya Fauziyya ta faɗa tana huci kamar wacce ta yi tseren gudu.”

Hajiya Rahama na komawa sashenta ta samu ana kiran wayarta, tana dubawa ta ga lambar maigidansu har sai da hanjin cikinta ya kaɗa, da ƙyar ta yi ta maza ta ɗauki wayar da sallam. Bai amsa mata ya fara da cewa, “Rahama ina yi miki kallon mai hankali ashe ba haka ba ne. Kun nuna mini Mahaifiyata bata isa da ku ba, kun kama hanya kun taho ba tare da izinina ba. Na gode kun nuna min ni kaina ba wata tsiya bace a wurinku.” Jiki a sanyaye Hajiya Rahama ta ce, “Don Allah ka yi haƙuri Alhaji wallahi nima na yi nadama amma yanzu zan taho insha…”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button