BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Ƙauyen Ɗangwauro.

“Inno kullin haka kike faɗa amma fa har yau ko kirana a wayarki bai taɓa yi ba, kina ganin su Zulfa kullin cikin waya suke.” Dubu ta faɗa tana kwaɓe fuska. Yaya babba ta washe baki ta ce, “Kin san Soja da kunya, tun yana yaro duk cikinku babu mai kunyarsa. Allah na tuba wacce kunya gare ku rannan ina jin Zulfa tana waya akan gadona, munafukar yarinyar ta ɗauka bacci nake har cewa take ko Lobin-lobin ko I Lobiyu. Wai har da cewa tana kewarsa. Don Allah Dubu ki ji mini falsafar rashin kunya ta dubi gardi kamar Salisu ta ce, tana kewarsa wannan bata cancanci istigifari ba?” Dubu ta bushe da dariya ta ce, “Yasin Inno kaɗan ma kika ji.” Inno ta dafe ƙirji a tsorace sannan ta ce:

“Au tana faɗin abin da ya fi haka? Amma dai Zulfa an yi ƴar banzar yarinya, ta yi ta sunne kai ƙasa kamar mumina ashe shakiyya ce.” Dubu ta ɗauko wayar Yaya babba ta ce don Allah Inno ki kira min shi.”

Yaya babba ta ƙanƙance ido tana kallon wayar ta ce, “Kin san dai ba iya nemo lambarsa na yi ba, duba ki kira shi.” Cike da ɗoki Dubu ta fara dubo lambar Aseem sai da, A ɗin kawai ta riƙe amma takamaimai sunan Aseem ba ta san shi ba. Sai da ta kira mutane biyu waɗanda sunansu ya fara daga A, na farko ta kira Baba Adamu da aka sawa Yaya babba sunansa da Ado sai lambar Auwalu. Sai a na uku ta samu ta yi nasarar kiran Aseem.

Cikin wata irin sanyayyiyar murya ta ji ya ɗauka da cewa, “Salamu alaikum.” Lumshe ido ta yi ƙirjinta na bugawa ta yi ta maza ta ce, “Wa’alaikas salam.”

Jin ba muryar Yaya babba bace ya sa ya furta, “Wace?”

“Me lob ni ce na kira ka, Dubu ce i lobiyu.” Dubu ta faɗa cike da ɗoki don ta saba jin waɗannan kalaman a bakin su Zulfa idan suna waya da samarinsu, suna cewa My love da i love you.
[7/1, 10:17 PM] Ameera Adam????: DUBU JIKAR MAI CARBI

        ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

FREE PAGE 11

Aseem kusan sandarewa ya yi da jin kalaman Dubu, don ya fahimci inda maganar tata ta dosa dukda bata faɗa yanda ake furtawa ba. Babban abin da ya fi ba shi mamaki yana yi mata kallon ƙaramar yarinya sakarai marar wayo, ashe shi take yi wa kallon haka? Tun da har ta san ta kira saurayi ta ce masa My Love, ba tare da kunya ko jin nauyi ba. Jin ya yi shiru ya sa Dubu ta saci kallon Yaya babba ta sake cewa:

“Me lob wallahi ina ta kewarka kuma na yi musun ɗinka.” Yaya babba na jin haka ta saki murmushin farinciki, don bata ɗauka Dubu za ta iya nutsuwa lokaci ɗaya ta yi waya da saurayi a haka ba.

Aseem bai gama tunani ba Dubu ta sake jefa shi cikin kogin mamaki, da jin kalaman da idan za a sa mata wuƙa bata san takamaimai abin da suke nufi ba. Dubu ba ta damu da jin shirun da ya yi ba ta ci gaba da jawabi.

“Me lob dama kiran da na yi maka don mu gaisa ne, na san kaima ka yi kewata; kuma ban ji ka ce komai ba…” Tun bata ƙarasa ba ya buga mata tsawar da ta katse ragowar kalamanta da cewar: “Ke! Kina hauka ne?” A tsora ce Dubu ta zame wayar daga kunne, ganin haka ya sa Yaya babba ta kalleta tana faɗin, “Dubu lafiyarki kike razana kamar wacce aka ɗanawa wuta?” Wayar Dubu ta miƙa mata tana faɗin, “Riƙe ki ji abin da yake faɗa Inno.” Da sauri Yaya babba ta karɓi wayar ta sa a kunne tana faɗin, “Sojaaa.” Aseem na jin haka ƙit ya kashe wayar yana huci. Maganganun Dubu sun jima suna yi masa yawo a rai, yana mamakin har yaushe ta ga makwancinsa da za ta kira shi a waya tana ce masa My love.

Yaya babba ta yi zuru tana nazari sannan ta ce, “Dubu me kika yi wa Soja da zafi haka da zai hau yi miki barazana?” Dubu ta kwaɓe fuska ta ce, “Inno kina ji dai a gabanki na yi wayar.” Wayar ta sake miƙawa Dubu ta ce, “Maza lalubo mini lambar Garba, alƙur’an idan shi yake zuge shi a kanki zan ji dalili. Saboda Allah me ya sa Garba ya cika hassada? Dama tun rannan na lura da hassadar da yake yi wa Soja akan aurenki. A’a ba halina ya gada ba bare kuma mahaifinsa, Allah ya sani wannan ɗabi’ar ƴan wuta ce idan kuma Garba ya ɗore a haka na shiga falsafar tashin hankali a ce jinina na da ɗabi’ar ƴan wuta ina na kama.” Dubu ta gama dube-dubenta ta miƙawa Yaya Babba wayar ta ce, “Kin san dai ba iya nemo lambarsa na yi ba Inno kawai ki kira Baba Munkaila, ki sa ya kira shi” Suna cikin haka Salisu ya shiga shi da abokinsa Musbahu, da sauri Yaya babba ta miƙa masa waya ta ce, “Maza kira mini Garba.” Da ido ya tsare Dubu da kallon tuhuma, don ya san ita take juya Yaya babba kamar waina, ya ce, “Me za ki ce masa Inno.”

“Me ye ma ba zan ce masa ba Ɗan nan? Ka kira mini shi idan ba za ka kira ba, wuce ka kira mini ubanka ko Munkaila in sa su kira shi.” Gudun magana irin na Yaya babba ya sa ya karɓa ya kira mata Baba Abubakar, sai dai an yi rashin sa’a wayar a kashe take.

Musbahu abokin Salisu cikin ladabi ya gaishe da Yaya babba ta washe baki ta ce, “Lafiya ƙalau Musbahu ya Uwale?” Ya amsa mata cikin girmamawa, Yaya babba ta ɗora da cewa:

“Ina ma Soja ya samu abokan ƙwarai irin ka Musbahu, don Allah da bai more ba? Don Allah waye ba ya san farantawa, ka duba yarinyar nan Dubu daga kiran Soja zai fara sauke mata falsafar rashin mutumci, ana zaune ƙalau don Allah wannan halin mutumci ne?” Musbahu ya yi murmushi ya ce, “Gaskiya bai kyauta ba Inno, amma ki yi haƙuri.”

“Don Allah rabani da haƙurin nan Musbahu! Kai Salisu ba ina ji rannan Zulfa na ce masa tana kewarka ba. Musbahau don Allah ka ji wata lalata irin ta ƴaƴan zamani. Lokacin da aka ɗaura auren uwar Zulfa, ni kaina da nake uwar miji sai da ta kwana a ɗakina, kwananta biyu tana gudun miji za ta yi na uku na ce, a’a ta rabani da wannan falsafar kar Munkaila ya ɗau gaba da ni ana zaune ƙalau. Munkaila kunya Kulu kunya yooo gadon wa tayo a cikinsu na rashin kunya? Don Allah gane mini hanya Musbahu.” Salisu ya karɓe zancen da cewa, “To ke tsohuwa ina ruwanki da sa ido ne?”

Kafin Yaya babba ta yi magana Baba Munkaila ya shiga ɗakin da sallama, Yaya babba na ganinsa ta saki dariya ta ce: “Ɗan halaka kaƙi ambato!” Baba Munkaila ya yi murmushin jin daɗi don ya ɗauka labarin wata bajintar ta shi Yaya babba take bayarwa, da ta ganshi ta faɗi haka.

Yaya babba sai da ta ga Baba Munkaila ya zaune a gefe kusa da ita, ta ɗaga faifai ta miƙa masa kwaɗon rama ta ci gaba da cewa, “Kun ganshi nan a daren angwancinsa ma kasa shiga ɗakin amarya ya yi, kunya dai a cikin Munkaila har da ta siyarwa. Ashe biyu ce ta haɗu shi kunya Kulu kunya, yoo bayan kwana biyu ba sai amarya ta hau guje-guje ba.”

Kunyar duniya ta kama Baba Munkaila da ke zaune a ɗaki ɗaya, da Ɗansa Salisu kuma saurin babbar ƴar sa Zulfa da ake shirin ɗaura musu aure. Hakan ce ta faru a ɓangaren Salisu ba ƙaramin kunya ya ji ba, daga shi har Musbahu aka rasa mai bakin magana. Dubu na gefe sai sunne kai take tana dariya ƙasa-ƙasa, musamman da ta lura da yadda Baba Munkaila ya yi fiƙi-fiƙi da idanu, ba abin ya tashi ba yaran ɗakin su fahimci abin da ya tashe shi daga ɗakin. Yaya babba kuwa ko a jikinta ta ci gaba da cewa:

“Kai Allah dai ya sawaƙe kuma bayan kwana biyu fa sai ganin ciki muka yi, na yi dariya na ce Allah mai iko ashe dai rabon a kusa yake. Yoo ashe kunyar duk ta banza ce ban sani ba sai ranar da Kulu take naƙuda.” Salisu ya yi karaf ya ce, “To mu dai ba tambayarki muka yi ba.” Saboda kunya Baba Munkaila kasa ɗaukan lomar hannunsa ya kai baki ya yi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button