BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Wannan jaririn hallitar ya ɗauko mata mai shige da siffar kunkuru ya ce, “Ya zama wajibi ki shayar da wannan domin shi ɗin jininki ne.” Idanunta ne suka firfito waje ta ƙarewa hallitar kallo tana yamutsa fuska, bai saurari abin da za ta faɗa ba ya ci gaba da cewa. “Ya zama wajibi ki yanke alaƙarki da wannan yarinyar Intisar.” A hargitse Raihan ta sake ɗagowa ta yi tana kallonsa don a duniya bata da aminiya sama da Intisar, bata da wacce tasu ta zo ɗaya sama da ita amma lokaci ɗaya ya ce dole ta rabu da ita.

    *********

A haukace Daddy ya yi kan Kabiru ya rufe shi da wani mahaukacin duka, sai da ya gaji don kansa sannan ya janye Jabun Raihan ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya. A cen gafe Kabiru ya faɗi yana sauke ajiyar zuciya yana sauke numfashi cikin wahala, ɗagowa ya yi suka haɗa ido da Jabun Raihan a fakaice ta sakar masa wani malalacin murmushi ta fara motsa baki tana magana ba tare da ta wani ya ji abin da take faɗa ba. Duk maganganun da Jabun Raihan take yi a kannen Kabiru, ransa ne ya sake ɓaci ya dubi Daddy da yake jifansa da mugun kallo, cikin bagwariyar hausarsa  ya ce, "Alhagi shi wannan yaron ba mutumin kirki ba ne, azzalumi ne so yake ya shushe ki." Daddy ya sake dunƙule hannu ya kaiwa Kabiru naushi a baki ya ce, "Don uwarka a gabana kake ce min ƴata ba mutuniyar kirki ba ce, ina maka kallon mai hankalin ashe kaima ɗan iska ne, wallahi a yau ba sai gobe ba sai an rufe min kai na ga gatanka mahaukacin banza mahaukacin wofi." Raihan da ke maƙale da Daddy ta sake langwaɓewa tana ɗangale ƙafa. Alhaji Mustafa Indabawa ne ya dubi Daddy yana faɗin, "Abokina don Allah ka yi haƙuri, yanzu mu ƙarasa wurin da gawar yaron nan take." Kabiru ya yunƙura da kyar bakinsa na ɗigar da jini. Daddy na leƙa cikin ɗakin ya yi tozali da gawar Sulaiman, da sauri Daddy ya ja da baya jikinsa na tsuma don ba ƙaramin tsorata ya yi ba. Alhaji Mustafa shi ma yana leƙawa a zabure ya ja da baya har suna gware da Daddy. Lokaci ɗaya Daddy ya yi zuru-zuru hankali a tashe ya furta, "Wannan tashin hankalin ne ya faru a ɗakin Raihan?" Intisar da ƙarasowarta kenan ta amshe maganar da cewar,  "Daddy tun da nake ban taɓa ganin maciji mai muni irin wannan ba." Daddy da jikinsa ya gama sanyaya ya fara jinjina kai, suna nan tsaye macijin nan ya fara warware kansa daga jikin Sulaima. Ganin haka ya sa mutanen wurin suka fara darewa, Kabiru ne ya dafa ƙofar a hankali ya zura ƙafarsa ɗaya cikin ɗakin.

Kallon-kallo aka fara yi tsakanin kumurcin macijin nan da Kabiru, a hankali Kabiru ya fara karanta duk wata addu’ar tsari da ta zo bakinsa. A zabure macijin ya fara ja da baya Kabiru na sake tunkararsa, wani kofi Kabiru ya hango da ruwa a jarka da sauri ya ɗauka ya zuba ruwa a kofi ya fara karanta ayoyin tsari yana tofawa. Daddy ban da leƙe babu abin da yake yi. Kasancewar Jabun Raihan ta san irin soyayyar da Mahaifin Raihan yake yi mata ya sa ta kwaɓe baki a lokacin da ta ga Kabiru ya tasamman halaka Macijin da ubangidanta ya turo, ta ƙwalla wata ƙara tana faɗin, “Daddy wuyana.” Kabiru ya waiwayo yana kallonta, Daddy ya kai hannu kan wuyanta yana faɗin, “Mu je asibiti a duba ki, wallahi duk abin da ya samu ƴata ka kuka da kanka.” Daddy ya ƙarasa maganar yana watsawa Kabiru mugun kallo. Raihan ta sake langwaɓewa ta ce, “Daddy don Allah a bar korar macijin nan kar wani ya ƙara mutuwa kawai ka kira fire service.” Daddy ya kalli wurin da Kabiru yake ya ce, “Kai maza fito daga ɗakin nan kar kaima ka yi mana mushe.” Intisar ta kalli jabun Raihan ta watsa mata harara, sannan ta mayar da kallonta wurin Daddy ta ce, “Daddy amma naga kamar macijin ya fara ja da baya mai zai hana a bari a ga ƙoƙarinsa…” Alhaji Mustafa ya katse ta da cewar, “Tabbas ni ma haka na gama ayyanawa don yaron nan kamar akwai wani taimako da zai yi mana.” Kabiru bai bi ta kansu ba ya sake tunkarar wurin macijin, lokaci ɗaya ya watsa masa ruwan tofin hannunsa bakinsa na ci gaba da ambaton Allah. Nan take macijin ya faɗi gefe yana wani iri gurnani, zaburowa ya sake yi da niyyar kai wa Kabiru sara da sauri Kabiru ya watsa masa sauran ruwan da ke hannunsa. Wata dariyar farinciki Intisar ta saki don ko ba komai ta san an yi wa Mama Uwani illa, jikinsu Daddy ba ƙaramin sanyi ya yi ba da ganin gwagwarmayar da suka yi tsakanin Kabiru da macijin.

Jabun Raihan ta sake kallon Intisar ta saki ƙwafa a takaice, ta so ace Huzaifa ya bata umarni da tuni ta nunawa Intisar iyakarta. A wahalce Kabiru ya sa hannu ya hanyo macijin, ya fito daga ɗakin fuskarsa ɗauke da gumi lokaci ɗaya Daddy ya ji Kabiru ya birge shi saboda jarumtar da ya nuna, wannan ne karo na farko da ya ji ba zai iya ɗaukan mataki a kan wanda ya taɓa gudan jininsa ba, saboda yana matuƙar son mutum mai dakakkiyar zuciya. Sai dai har lokacin yana jin haushin Kabiru saboda abin da ya yi wa Raihan a idonsa.

Kusan tare suka tarkata suka fito daga sashen, kowa da abin da yake faɗa. Kabiru fita ya yi da macijin can bayan gidan Daddy ya kai ya wurgar da shi, Daddy da kansa ya sa aka rufe sashen Raihan tare da cewar sai ya kira ma’aikata sun yi wa ɗakin feshin magani, a ɓangare ɗaya yana tunanin barinsu daga gidan gabaɗaya.

        *************

Raihan bata da zaɓi don haka ta gyaɗa masa kai tare da faɗin, “Duk abin da kika faɗa na amince don Allah ki mayar da ni.” Huzaifa ya yi murmushi jindaɗi don shi kansa ya lura da yadda Raihan ta gama tsorata da shi. Lokaci ɗaya ya ji ta bashi tausayi, ya sa hannu ya zaro fiƙoƙin bakinsa waɗanda suka tsiro ya wara hannuwansa da niyyar Raihan ta rungume shi amma fir ta ƙi. Ya kalli fuskarta ya ce, “Kina ƙaunata.” Raihan bata da zaɓi duk abin da ya faɗa sai dai ta amsa masa da amincewarsa. Tana tsaka da tunani ta ji ya ce, “Rufe idonki.” Kallon hagu da dama ta fara yi a hankali ta furta, “Don Allah kar ki yi min komai.” Huzaifa ya yi murmushi ya ce, “Kina rufe ido za ki ganki a gida.” Tun bai rufe baki ba Raihan ta rufe idonta da ƙarfi, bata jima da rufewa ba ta ji tashin hayaniya na tashi sama-sama. Tana buɗe ido ta ganta zaune a falon Daddynsu, a hankali ta fara bin wurin da kallo, ta hango Intisar da sauran ƴanmatan da suke tare da su a ɗakinta. Suna haɗa ido da Intisar ta ji gabanta ya faɗi rass musamman da ta tuna irin gargaɗin da Mai siffar Mama Hasiya ta yi mata, a hankali ta miƙe ba tare da furta komai ba. Tana fita ta nufi sashen Mommy a kan step ɗin bene ta ci karo da Mama Uwani, tana ganinta ta washe baki ta ce, “Barka da hutawa uwar ɗakina.” Sama-sama Raihan ta amsa, “Yauwa Mama Uwani ina Mommy take?” Mama Uwani ta nuna ɗakin mommy ta ce, “Tana ciki yanzu na kaiwa baƙi abinci ko na yi miki jagora.” Raihan ta dakatar da ita da cewar, “A’a Mama Uwani ki je kawai.” Mama Uwani ta yi murmushi tana faɗin, “Hutawarki lafiya uwar ɗakina.” Raihan bata amsa ba ta wuce cikin ɗakin. Kafin Mama Uwani ta sauka daga kan bene Intisar ta doshi wurin, kallon-kallo suka fara yi wa junansu don ma mutane na zaune a falon, Mama Uwani ta saki wani malalacin murmushi ta wuce ba tare da ta tanka wa Intisar ba.

Intisar na shiga ta yiwa Mommy sallama don a cewarta za ta tafi gida, amma koda ta yi wa Raihan magana ko ƙurarta bata kalla ba balle ta tanka mata. Tun da ta ga haka ta sha jinin jikinta, don haka tana fita daga gidan ta ɓace daga ƙofar bata tsaya a ko’ina ba sai a tsibirin ƙungiyar asirinsu.

Raihan na zuwa jiki a sanyaye ta zauna, tana son sanarwa da mahaifiyarta cewar Mama Hasiya bata mutu ba amma tana tsoron abin da zai sake faruwa da ita. Tana nan zaune Daddy ya kira wayar Mommy ta waya yake sanar da ita, ɓacewar su Inno da Goggo sannan ta ce ta haɗa duk wani kayan sakawarsu don ya sa a ɗauke su daga gidan da suke zuwa gidansa da ke Unguwar sharaɗa. A cewarsa gidan cike yake da miyagun dabbobi, ba za su ci gaba da zama a ciki ba.

(Abin da bai sani ba duk in da zai je indai yana tare da Raihan tana tare da ZAUJATU JINNUL-ASHIQ???? Idan kuma yana tare da Mama Uwani yana tare da JINNUL-ASHIQ???? Mu je zuwa.????)

Duk yadda Daddy ya so hukunta Kabiru ya ji zuciyarsa ta gagara ɗaukan mataki akansa, sai dai abu ɗaya ya riƙe duk abin da ya samu Raihan sai ya ɗauki mummunan mataki a kansa. A wunin ranar suka tare a sabon gidan Daddy da ke sharaɗa, da sauran ƴan gaisuwa suka tare. Ɗakin da ke jikin gate aka bawa Kabiru, yana shiga ɗakin ya ga akwai komai na buƙata sai dai lokaci guda ɗakin ya rikiɗe masa zuwa tafka-tafkan maciji masu fasalin irin wanda ya kashe a ɗakin Raihan. Yana shirin ja da baya ya ji wani ya faɗ masa a gadon baya lafin ya yi wani yunƙuri, ya fara nannaɗe masa jikinsa.

Intisar na zuwa ta kwashi gaisuwa wurin Hatsabibiya bungulu, bayan ta yi gaisuwa Hatsabibiya ta dubi Intisar ta ce, “Me yake tafe da ke da tsakar rana?”

Fuska ba walwala ta ce, “Hatsabibiya akwai tarin matsaloli domin Huzaifa ya saka ni a gaba, bayan Huzaifa akwai wani bafulatanin maigadinsu da alama zai kawo mana matsala. Amma wanda ya fi kawo mana matsala Huzaifa ne, don haka na ce ba zan yi ƙasa a gwiwa ba sai mun san abin yi don yanzu haka…”

Tun Intisar bata rufe baki ba Hatsabibiya Bungulu ta katseta da cewar, “Duk na ga abin da ya faru har ɗaukan Raihan da ya yi zuwa tsibirinsa.” Intisar ta jinjina kai cikin huci tana cewa, “Da alama ya tsoratar da ita kuma a kowanne lokaci tana gabda bijirewa umarninmu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button