BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Kamar wanda aka tasa daga bacci haka fitsari ya farkar da shi, kasancewar ƙafa ta ɗauke ya sa Kabiru ya fito bakinsa ɗauke da addu’a don ya kewaya banɗaki. Bayan ya fito daga can bayan ɗakinsa ya fara jin motsi, har cikin zuciyarsa ya ji kamar ya leƙa ya ga abin da yake motsi amma sai ya yi tunanin dare ne ta yuwu ɓeraye ne suke dabdalarsu. Mommy na jin motsin Kabiru ta riƙa ƙwalla masa kira amma a banza ko kaɗan bai san ana yi ba, sai dai har lokacin bakinta yana ci gaba da karanta ayoyin Ubangiji, da abar bauta ta zo kawo mata cafka sai ta ga mommy ta zille mata kamar tarwaɗa. Kabiru na shiga ɗaki ya koma ya kwanta sai dai fir idanunsa sun bushe bacci ya ƙaurace masa, tashi ya ƙara yi ya fito a ƙofar ɗakinsa ya ɗaura alwala yana shirin shiga ɗaki ya ji ƙusur-ƙusur ɗin ya yi yawa. A hankali ya fara takawa yana haske-haske da ƙaramar fitilarsa, daga can bayan ɗakinsa ya hango Mommy a kwance sai shure-shure take yi tana motsa baki da alama magana take yi. Tsoro ne ya kama shi don ko a mafarki bai taɓa ɗauka mommy bace a wurin, a tsorace ya fara faɗin, “Hajiya lahiya kuwa?” Mommy hannu ta fara miƙa masa tana kiran sunansa, ganin haka ya sa Kabiru ya fara ƙoƙarin miƙa hannu don ya taimaka mata amma tunowa da abubuwan da suka faru da shi ya sa ya ja da baya yana karanto aytulkursiyyu ya fara tofa mata tare da falaƙi da nasi. Kamar wanda aka yi wa wankin kunne raɗau ya ji maganar Mommy a kunnensa saɓanin da; da baya jin abin da take faɗa, tsugunnawa ya yi a wurin yana faɗin, “Hajiya me ya fito da dake a tsakar daren nan?” Mommy da ta ji jikinta ya fara sarara mata ta ce, “Kabiru taimaka min ka kaini ciki kar su halaka ni.” Kabiru ya zaro ido yana dube-dube yana shirin magana mommy ta dafo hannunsa da sauri ya yi baya yana kurma ihu don ya gama tsorata gabaɗaya. Abar bauta da take laɓe ta fara Allah-Allah akan Kabiru ya basu wuri don ta dawo ta ci gaba da abin da take niyyar aiwatarwa, donma ita kanta Mommy ba ƙaramar wahala suka sha akanta ba amma so take ko ta wanne hali ta samu ta lakuci jinin jikinta idan ya so ko da sihiri ne in sun kaiwa ɗakin arziƙi jininta magana ta ƙare. Kabiru har zai shige ɗaki da gudu sai wata zuciyar ta ayyana masa ta yuwu ita ma shaiɗanu sun yi mata abin da suka yi masa ne har suka tsorata ta fito. Bakinsa ɗauke da addu’a ya sake tunkararta Mommy ta dafa kafaɗarsa ta miƙe tsaye tana layi, da ƙyar ta iya tsayawa a kan ƙafarta ta fara takawa da ƙyar kanta na ci gaba da sara mata. Kabiru na raka ta bakin ƙofa zai juya fir mommy ta ƙi yarda don har sa da ta saka Kabiru ya rakata har ƙofar ɗakin Daddy sannan ya koma ɗakinsa, tana shiga ta zube a bakin ƙofa tana ci gana da karanta duk ayar da ta zo bakinta. A lokacin da ta koma ɗakin tuni Daddy ya yi bacci, da rarrafe ta fara rarrafawa zuwa bakin gadon tana kiran sunansa. Sai dai babban abin da ya sake firgitata yadda ta ji yana sauke wani irin munshari mai ban tsoro, ga ƙwan ɗakin da fara ɗaukewa yana kawowa.

Raihan da abar bauta kusan tare suka koma kogon dutsen ƙungiya kowannensu fuska babu walwala, abar bauta ta dubi Raihan rai a ɓace ta ce: “Mahaifiyarki za ta bamu matsala domin tana da riƙo da addini. Sannan wannan Bafulatanin yana ƙoƙarin wargaza shirinmu tabbas za mu ɗau mummunan mataki a kansa, amma fa duk da haka Mahaifiyarki bata sha ba domin za mu ɓullo mata ta sigar da ba za ta taɓa tsammani ba. A yau saura kwana biyar ta fara al’ada don haka zan yi amfani da wannan lokacin, domin alƙawarinta na yi ga ɗakin arziƙi.” Raihan ta jinjina kai cikin girmamawa, abar bauta ta nuna wata ƙaramar ƙorama ta ce,: “Ki ɗebi ruwan wanke zunubi ki yi wanka domin kin karya ƙa’idoji da dokar ƙungiya.” Raihan na yin wanka kamar yadda Abar bauta ta umarceta ta fice daga kogon dutsen.

Intisar ce ta ɓullo daga ƙarƙashin ƙasa ta yi gaisuwa ga abar bauta, kusan cikin haɗin baki suka furta, “Huzaifa zai aika da Raihan ƙasar India don bincike na musamman akan Raihan.” Abar bauta ta yi murmushin takaici ta ce, “Na san da haka shi ya sa na nemo ki yanzu. Zai kaita India ne wurin Kakansa Jibbul-Ƙasi don ya yi mata bincike a kanta, ya ɗora zarge-zarge akanta ciki kuwa har da ke.” Intisar ta jinjina kai sannan ta ce, “Tabbas na san za a yi haka domin na san wanenen Huzaifa da bin didiginsa.” Abar bauta ta miƙe tsaye sai da ta yi zagaye wurin sau uku sannan ta ce, “Ba zai yi nasara a kanmu ba, domin za mu mallakawa Raihan duk wani ƙarfin iko, idan a da bata san wacece ita ba ya zama dole mu sanar da ita ta hanyar sakata a ɗakin arziƙi.” Hankali a tashe Mugaza ta ɗago tana faɗin, “Kina nufin tun yanzu za ta mallaki shuɗaɗɗan ruhi ba sai nan gaba ba ya Abar bauta.” Abar bauta ta ci gaba da tafiya tana jinjina kawunan jikinta ta ce, “Alƙawarin ƙungiya baya tashi, matsawar Huzaifa ya kaita wurin kakansa tabbas sai ya gane shirinmu kuma sai Kakansa ya wargatsa ƙungiyar nan. Idan kuwa muka saka mata shuɗaɗɗan ruhi dole zai zama garkuwa a gare ta, za ta gagari Jabbul-Ƙasi da dukkan wani shirinsa.

WASAN YA FARA ƊAUKAN ZAFI????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️ RAIHAN TA KUSA ZAMA SHUGABA LIKAFA TA CI GABA???????? MENENE ALAƘAR SHUƊAƊƊAN RUHI DA RAIHAN, SHIN DAMA RAIHAN NA DA WANI A ƘUNGIYAR ASIRI NE DA HAR RUHINSA ZAI MAYE GURBINTA KO YAYA? WACCE ALAƘA CE TSAKANIN SHUƊAƊƊAN RUHI DA KAKAN HUZAIFA JUBBUL-ƘASI? CAKWAKIYAR ƘARA GABA TAKE???? MAZA HANZARTA KI BIYA DON JIN YADDA ZA TA KASANCE GARA KI BIYA 300 KI KARANTA AMMA IDAN NA KAMMALASHI SAI KIN SAKA 500 ZA KI SAME SHI???????????? WANNAN SHI NE SHAFIN ƘARSHE WATO SHAFIN ƘAUTA???? MU JE ZUWA ƳAN GROUP ƊIN ZAUJATU PAID A CI GABA DA GASH SUYA SAI RANAR BIKIN NAƊIN ???????? RAIHAN A ƘOGON DUTSEN ƘUNGIYA????????‍♀️????????

SHARE HILIS????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button