BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Bayan fitowar su Intisar a kan idonta Mama Uwani ta sauya Raihan da wata Raihan ɗin, murmushi ta yi don ta fahimci manufarta na yin haka kuma ita ma ta shiga nazartar yadda za ta ɓullo mata. Nan take gida ya ruɗe da maganar macijin da aka gani a ɗakin Raihan, hankulan mutane ba ƙaramin tashi ya yi ba. Lokacin da Mommy ta samu wannan labarin da sauri ta aika aka kira Kabiru (Matashin bafulatani Maigadin gidansu Raihan.) Saboda Kabir bai da tsoro sam, bai fi sati biyu da fara aiki a gidansu Raihan ba. Tsayayyen namiji ne mara tsoro don akwai ranar da aka samun kulɓa a kitchen ɗin Mommy, Kabiru na zuwa ya fitar da shi. Kafin Kabiru ya zo Sulaiman ɗan ƙawar Mommy ya miƙe yana faɗin, “Daga wurin ina yake yanzu na fice da shi, ba wani shege kura ma mun kara da ita mun kaita ƙasa.” Babu wanda ya hana shi don jikinsa na rawa ya nufi cikin gidan, saboda yana mutuwar ƙaunar Raihan don haka yake son ya yi wani abin bajinta ko ya samu ya ƙara samun masauki a zuciyar Raihan.

Yana zuwa duk matan da ke zagaye da ɗakin suka dare, ya tura ɗakin da ƙarfinsa. Yana shiga ya samu macijin a tsakiyar ɗakin ya naɗe wuri ɗaya kamar gammo ya fasa kai, bakinsa yana fitar da feshin wuta, a hankali ya waiga yana faɗin: “Wani ya miƙo min katako.” Har rige-rigen tafiya mutane suke yi babu jimawa aka ɗauko masa wani ƙaton katako, kansa tsaye ya tunkari macijin cikin dakiya ya ɗaga ya buga masa a tsakiyar ka. Tsalle macijin ya yi, Sulaiman ya gantsare duniyar na juya masa. Sannu a hankali macijin ya rarrafo ya fara nannaɗe shi har sai da ya naɗe masa jiki, nan take Sulaiman ya hau kakari ƙwayar idonsa duka biyun ta faɗo ƙasa, jini ya fara zuba ta hancinsa da bakinsa. Tun Sulaiman yana iya kakari har ƙarfinsa ya ƙare, tsokar jikinsa ta fara burtsowa daga jikin fatarsa nan take hallitar Sulaiman ta sauya tamkar ba bil’adam ba. Mutane na ganin haka suka fita da gudu cikin kururuwar neman taimako.

         ************

Raihan ta shi ta yi zaune jikinta ba ƙaramin tsami ya yi mata ba, ta dubi Huzaifa da ke cikin siffar Mama Hasiya ta ce, “Mama Hasiya kece? Dama baki mutu ba?” Huzaifa ya gyaɗa wa Raihan kai yana furta, “Ban mutu ba amma na dawo nan wurin da zama za ki zauna da ni?” Raihan ta yi shiru tana nazartar maganarsa jiki a sanyaye ta ɗago tana cewa, “Gaskiya ban yarda ba ina su Mommy?” Huzaifa ya riƙo hannunta lokaci ɗaya ta ji wani yaarrr a cikin jikinta, tana kiciniyar ƙwacewa sai gani ta yi ta fisgo da ƴan yatsu biyu na jikin hannun Huzaifa, a tsorace ta wurgar da su ta fara ja da baya jikinta na karkarwa. Cikin rawar murya ta ce, “Don Allah ki yi haƙuri karki cutar da ni.” Ganin haka ya sa Huzaifa ya fara ƙyaƙyacewa da wata irin dariya har sai da ta sa hannuwa biyu ta toshe kunnuwanta, kakin yawu ya yi ya tofar nan take ƙasar wurin ta fara rozayewa ya sa ɗan yatsa ya nuna mata wurin yana faɗin, “Ki bar wahalar da kanki domin ba za ki taɓa guje min ba, ki zo ki shiga wurin nan idan ba haka ba za ki dauwama a wurin nan.”

   *********

 Al'ummar da ke zaman makoki kusan rabi da kwata kowa ya cika wandonsa da isa, don ceton rayuwarsa. Hatta Inno da Goggo cikin ayarin ƴan ceton rai suke ba tare da su mommy sun farga ba. Hankalin Daddy ba ƙaramin tashi ya yi ba da ganin abin da ya faru, a hankali Kabiru ya fara takawa cikin gidan dukda yana ta cin karo da mutane masu guduwa hakan bai hana shi sake kutsawa cikin falon gidan da zai sadaka da ɗakin Raihan ba, a bakin wata ƙofa ya ci karo da Intisar da ke tsaye ƙyam babu alamar tsoro a tattare da ita. Suna haɗa ido ya ji kansa ya sara juwa ta fara ɗibansa, sama-sama ya fara jin wata irin hayaniya har sai da ya dafa kansa da hannuwansa, a hankali ya fara karanto addu'o'in tsari yana karantawa duk wacce ta zo bakinsa. Lokaci ɗaya ya ji komai ya ɗauke masa, ya dawo cikin hankalinsa sai dai tuni jikinsa ya jiƙe da gumi sharkaf. Idanu ya kafe Intisar da su har ya gagara sarrafa kansa, ya fara takawa zuwa gabanta cikin hausar da bata gama zama a bakinsa ba ya ce, "Washeshe kai?" Intisar ta saki murmushi ta ƙarasa gaban Kabiru ta ce, "Kai bafulatanin ƙauye, karka shiga abin da babu ruwanka." Yana shirin sake magana Daddy ya ƙaraso wurin hankali a tashe yana faɗin, "Kabiru mu je ka ga abin da yake faruwa meye abin yi?"  Kabiru ya yi gaba yana waiwayen Intisar haɗe da ɗora mata zarge-zarge a kanta.

Da ƙarfin gaske Kabiru ya tura ƙofar ɗakin cikin zuciyarsa yana ci gaba da karanta ayoyin tsari dana kariya, Jabun Raihan ce ta ƙaraso ƙofar ɗakin. Abin da ya ji da farko a lokacin da yake tare da Intisar haka ya ƙara ji a wannan karon a haukace ya juya, ya shaƙi wuyan Raihan cikin wani irin ƙaraji ya furta.

“Washeshe kai? Me kake yi a wurin nan?”

DA ALAMA KABIRU YA YANKI TIKITIN BARIN AIKIN GADIN DA YAKE YI A GIDANSU RAIHAN???? TO WAI SHI MA KO YANA DA ALAƘA DA SU NE???? SHIN DADDY ZAI ZURA IDO YA GA AN MAƘURE GUDAN JININSA? SHIN SU DADDY ZA SU FARGA DA MAMA UWANI BA MUTUM BACE SHI NE AINIHIN ALJANIN DA KE RAYUWA DA ƳAR’SU? KO KUMA HUZAIFA ZAI ƘYALE KABIRU HAR YA TONA MUSU ASIRI????????????

TAFIYAR FA HAR YANZU BA A FARA BA DOMIN LABARIN TAFE YAKE DA SARƘAƘIYA????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️ KARKU MANTA HAR YANZU RAIHAN BATA SAN MAMA UWANI CE TA KAWO WANNAN TSIBIRIN BA, ITA DAI TA BUƊI IDO DA MARIGAYYA MAMA HASIYA. WAI INA LABARIN INNO DA GOGGO NE INA SUKA BAZAMA WAYE ZAI TARO SU? ????????

Share Fisabillah????
[7/12, 10:15 PM] Ameera Adam????: ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

© AMEERA ADAM

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

          FREE PAGE 6

Raihan kallon ramin ta yi da yake ci gaba da rozayewa ƙasar wurin na ruftawa, ya yin da ramin yake ci gaba da ƙara girma yana tunkaro wurin da take. A hankali ta riƙa ja da baya cikin rawar jiki, firgici da tashin hankali. Tuni hawaye ya wanke fuskarta ta ci gaba da yin baya ba tare da ta fahimci wurin da take jefa ƙafarta ba, bata yi aune ba ta ji wani dutse ya tokareta ƙasar da ke zaftarewa ta ƙaraso har wurinta har sai da ya rage bai fi taku ɗaya ba ta dakata bisa bin umarnin Huzaifa da ke cikin surar Mama Hasiya. Cikin kuka Raihan ta dubi shi tana faɗin, “Don Allah ki yi haƙuri karki cutar da ni, ban san abin da na yi miki ba kika kawo ni wurin nan alhalin mommy ta ce mini kin mutu.” Huzaifa ya ƙyaƙyace da wata mahaukaciyar dariya ya fara takowa wurinta yana tafe yana zare sauran ƴan yatsun hannunsa yana zubarwa, kafin ya ƙarasa wurinta tuni ya tsinke yatsun hannunsa sai iya dungulmin kaɗai ya rage, daga guraben ƴan yatsun wasu baƙaƙen farata ne suka fara tsirowa a hankali har sai da suka fito zaƙwa-zaƙwa da su, ta cikin ramin ya shiga kamar ƙiftawar ido ya dira a gabanta cikin wata irin murya mai amsa kuwwa ya sake ce mata. “Ki biyo ni cikin ramin nan idan ba haka ba za ki dauwama a nan.” Raihan ta sake girgiza masa kai tana cewa, “Don Allah ki mayar da ni wurin su Mommy.” Baki ya buɗe zai fara dariya wasu dogayen fiƙoƙi suka fara fitowa, da sauri Raihan ta runtse ido tana ƙwallah wata razananniyar ƙara. Wata iska ta ji mai sanyi na ratsa jikinta a hankali ta buɗe idonta, ga mamakinta sai na yi ta yi wurin ya sauya mata ta ganta wani kogon dutse mai ɗauke da ƙananan bishiyu, a hankali ta fara takawa har zuwa bakin kogon dutsen don ta hango hasken rana daga bakin dutsen. Tana fita daga cikin dutsen ta fara gudu da iya ƙarfinta don ganin ta ceci rayuwarta.

Daga nesa-nesa ta fara jiyo kukan jarirai haɗe da haniniyar doki, a hankali ta fara rage gudunta don yadda ta lura hanyar da take tunkara a nan take jin sautin kukan jaririn na sake karaɗe kunnuwanta. Tana tafe tana waiwaye ta bata yi aune ba ta ji ta yi karo da wata murgujejejiyar hallita, hallitar riƙe take da wasu ƙananan jarirai masu surarta, tsayin hallitarta ya ninka ta sau biyu, tana da ƙiba sosai don kaurin cinyar hallitar ya yi kaurin Raihan sau huɗu. Tana ɗauke ƙafa da hannuwa irin na birrai sai ƙaton kai irin na dorinar ruwa. Bakinta tsayi gare shi idanunta kwala-kwala masu ɗauke da launin ja, Raihan na shirin ja da baya Hallitar ta ƙurawa Raihan Ido tana miƙa mata hannu alamar ta zo gare ta. Da gudu Raihan ta juya don ta koma cikin kogon dutsen, karaf ta ji ta yi karo da Hazaifa da ke ɗauke da surar Mama Hasiya sai dai kammanina sun sake munana.

Ajiyar zuciya ta sauke don ko ba komai ta ji daɗin ganinsa, hankalinta ya fi kawanciya da shi a kan na wannan mummunar hallitar. Hallitar na ganin Huzaifa ya ɗauke Raihan sun koma zuwa kogon dutsen ta juya ta koma daga wurin da ta fita, Huzaifa ya saki malalacin murmushi bayan sun koma ciki ya zaunar da Raihan akan wani faffaɗan dutse, ya zauna a gabanta yana kallonta. Tana shirin yin magana ya katseta da cewar, “Kina son komawa gida?” Da sauri Raihan ta gyaɗa masa kai. Jinjina kai ya yi sannan ya ce, “Zan mayar da ke gida amma da sharaɗin…” Da sauri ta katse shi da cewar, “Na amince da kowanne sharaɗinki indai za ki mayar da ni gida.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button