BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Yaya babba ta saki dariya ta ce, “Furaira alƙur’an ni kuma fuskar Nafisa ta ƙi ɓace mini lokacin da muka karɓi haihuwarta ta wannan yaron soja kin tuna lokacin har cewa take wai Inno zo na goyaki. Na ce mata ke Nafisa rabani da zancen goyon nan, rabona da goyo tun shekaru tsububu sai yau da kike nakuɗa za ki goya ni, na turmushe ki Garba ya ɗau gaba da ni.” Inna Furai dariya har da hawaye sannan ta ce, “Yoo kafin ki zo har cewa take Inna karɓi cikin, na ce Nafisa lamari ya lalace ina Uwar Garba na karɓi cikin Garba ai ba kanta sai cewa ta yi har Garban na bar miki gabaɗaya.” Dubu ta kife a wurin ban da dariya babu abin da take yi.
DUBU JIKAR MAI CARBI

        ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.

FREE PAGE 9
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan???????????????????????????????????????? subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

 Sallamar Baba Munkaila ne ya dawo da Dubu cikin hayyacinta, ba shiri ta shiga nutsuwarta ta fara kumbure-kumbure don ta san babu makawa zai samu labarin abin da ya faru tsakaninta da Hansatu. A daidai kan Dubu ya tsaya fuska babu walwala ya ce, "Ke!" Kamar bata ji shi ba ta yi biris, sai da ya sake buga mata tsawa sannan ta amsa. Cikin faɗa ya ci gaba da cewa, "Dubu ki kiyaye ni fa, kullin iskancinki da iya shegenki ƙara gaba yake ko? Ƴar ƙanƙanuwarki da ke har kin isa tarar matar aure ki ce za ki yi dambe da ita. Wallahi a hir ɗinki idan kika shiga hannuna na lahira sai ya fiki jin daɗi." Dubu dama kamar me jira yana dire zancensa ta fashe da kuka tana faɗin, "Dama na san komai ni za a ɗorawa alhalin ita ce bata da gaskiya." Rankwashi ya sakar mata a tsakiyar ka aikuwa ba ƙaramin shigarta ya yi ba, a zabure ta yi gefe ai kuwa Yaya babba dama ta fara cika ta dubi Baba Munkaila cikin faɗa ta ce, "Munkaila nakasa marainiyar Allah za ka yi? Ka duba irin ƙusar da ka sakar mata a tsakiyar ka sai ka huda mata kai, ka cuceni ka cuci Ado. Ko da ya kasance likita ba sai an sayi magunguna da alluran da za a yi mata aiki ba. Gaskiya bana so ka fita rayuwar yarinyar nan shi ya sa ga tana kamar ruwan aski kullin bata kumari." Baba Munkaila bai tankawa Yaya Babba ya dubi Dubu ya ce, "Tashi ki ɗau hijabinki ki wuce makaranta. " Tun bai rufe baki ba Dubu ta suri kayanta ta fita waje tana kurma uban ihu.

Inna Furai ta ja tsaki ta dubi Baba Munkaila ta ce, “Munkaila wai me ya sa ko yaushe burinka ka zazzagewa yarinyar nan albarkar da ke kanta? Yanzu da ka kaɗa ta waje idan ta shiga gari wa ya shiga uku idan ba mu ba.” Yaya babba ta cafe zancen da cewa, “Wallahi idan na rasa Dubu hukuma ce za ta raba ni da Munkaila dama na daɗe ina zargin ba ƙaunarta kake ba.” Baba Munkaila ya yi murmushi sannan ya ce, “Inno yanzu so kuke a zurawa Dubu ido ta taso babu nutsuwa da rashin ilimi? Kuna ganin Fatima yarinyar nan kowa sha’awarta yake, saboda ilimin addininta. Mu kuwa wa yake sha’awar Dubu? Ku shaida ne a rana sai a kawo muku ƙara ta yi sau goma. Amma Inna furai ai bai kamata mu zura mata ido haka har girmanta ba.”

Yaya babba ta yi shiru tana nazari sannan ta ce, “Munkaila ka yi tunani, kuma wallahi ina jin hannu aka sawa Dubu dole na sake nema mata maganin baki don wallahi baki ba ɗan’uwa ba ne.” Baba Munkaila na ganin ya yi wa Tsofaffin iyayen nasa dabara ya tashi ya fice daga gidan.

Dubu na fita ta goge hawayenta ta maƙale jakarta ta ɗauki hanyar islamiyya, sai dai tana saƙa da warwarar abin da za ta yi wa Hansatu don ta fanshewa abin da ta yi mata. Kamar daga sama tana shan kwanar hanyar da za ta sadata da makarantarsu sai ga Ɗan’iya ya fito da tallar wake da shinkafa a kansa, hannunsa na riƙe da bokitin ragadada. Yana ganinta ya yi baya da sauri a tsorace don ya san mai ƙwatarsa a hannun Dubu sai Allah, don haka bai yi wata-wata ba tun Dubu bata tanka masa ba ya fara cewa, “Dubu don Allah ki yi haƙuri wallahi ba zan ƙara ba.” Kamar wani abu bai haɗasu ba, haka Dubu ta basar da Ɗan’iya ta ce, “Da aka yi me?”

Ɗan’iya ya washe baki ya ce, “Faɗanki da Innarmu mana.” Dubu ta zurawa bokitin ragadadar hannunsa ido, take ta ji yawunta ya tsinke, ta kai hannu za ta taɓa ya janye da sauri. Dubu ta riƙe ƙugu tana jinjina kai sannan ta ce, “Ɗan’iya wallahi ko ka bani bokitin nan ko kuma in haɗa gabaɗaya da Shinkafa da waken da shi bokitin ragadadar in kifar da su don wallahi wannan rigimar mun fara ta kenan ni da ku.”

Tun ba ta rufe baki ba Ɗan’iya ya soma hawaye ya ce, “Don Allah ki mun rai wallahi Innarmu duka za ta yi min.” Dubu ta yi dariyar mugunta ta ce, “Idan ka koma gida in ta tambayeka ka ce ta zo gudanmu ta karɓi kuɗinta.” Ɗan’iya ya fara ja da baya Dubu na tsaye ta ce, “Tsaya-tsaya Ɗan’iya gaya mini duka kayan naka na nawa-nawa ne?” Ɗan’iya a tunaninsa rangwame Dubu za ta yi masa idan ta ji tsadar abinci ya taƙarƙare da ƙarfinsa ya ce, “Shinkafa da wake na Dubu biyu ne Ragadadar dubu ɗaya ce.” Dubu ta yamutsa fuska ta ce, “To Allah ya yi belinka saboda wallahi da babu kayan nan sai na jiƙa maka jikinka, amma yanzu dole za ka bani bokitin ragadadar nan wallahi, ko in haɗa da kai da su duka na damalmale ku a cikin ƙasa.” Ɗan’iya ya yi shiru yana nazari don ya san ciniki ko hamsin ne babu a ciki, Innarsu cin ubansa take bare bokitin Ragadada gabaɗaya. Ragadadar da sai sun yi da gaske suke samu Mahaifiyarsu ta ke basu yanka ɗaiɗai yau ita ce zai ɗauka ɗungurungun ya bada bokitinta.

Dubu na ganin haka ta buga tsalle tana ƙoƙarin janyo robar shinkafar, Ɗan’iya na ganin haka ya miƙa mata da sauri don kar ya yi biyu babu. Wani wawan kuka ya saki lokaci ɗaya ya juya zai koma gida Dubu ta sha gabansa ta ce, “Maza wuce wallahi ba za ka koma gida yanzu ba sai ka sayar da abincin nan salan ka min mugunta tun ban gama cinyewa ba ka sa azo gidanmu. Munafiki yana zare idanu kamar shege a rabon gado.” Ta ƙarasa maganar tana ɗake masa ƙeya. Babu yanda ya iya haka ya nufi titi yana share hawayen fargaba da tashin hankali.

Dubu sai da ta saita Ɗan’iya ya bi titi sannan ta bi wani layi bata tsaya ko’ina ba sai cikin wani sabon gini da ba a ƙarasa ba. Zama ta yi dirshan ta kwashi ragadada tana ci tana siɗar romo, kafin wani lokaci tuni ta cinye shi tas, saboda ba ƙaramin daɗi ya yi ba, ya ji farin magi zaƙwai ga ɗan yaji-yaji. Tana gama ci ta sa gefen hijabinta ta goge baki. Ta ɗauki bokitin ta cika shi da yaji ta ɓoye a cikin hijabi ta fice daga cikin kangon.

Dubu bata tsaya ko’ina ba sai ƙofar gidan Hansatu, Hansatu na tsaye a kan ƴarta Mairo da take ta zuba ragadada a ƙananan robobi, ta hango Dubu tsaye a ƙofar gida. Suna haɗa ido Dubu ta ƙarasa ciki kamar mutuniyar kirki ta ce, “A bani ragadada.” Tana maganar tana sakin wani irin murmushi. Hansatu ta hangame baki tana yi wa Dubu kallon mamakin wato rashin kunyar Dubu ta bunƙasa haka. Balabare da ke bakin bishiya yana sharɓar ragadada ya yi zaraf ya ce, “Dubulliya ta nawa za a baki?” A fusace Hansatu ta ce, “Ta nawa za ki siya?” Ba musu Dubu ta miƙa naira ashirin nan fa Balarabe ya fara leƙenta yana kashe mata ido ɗaya. Dubu ta ɗauke kai kamar bata gan shi ba. A fakaice Dubu ta sunkuya tana gyara takalminta ta cikin hijabi ta dire mata bokitin ragadada, ta bayan ƙatuwar tukunyar ragadadar. Ta matsa can gefen bishiyar da Balarabe yake zaune. Hansatu mace ce mai matuƙar son kuɗi don duk abin da zai haɗa ku da ita muddin ka zo siyan abu wurinta bata zuciya. Tana da tsumulmula saboda ko ita bata iya zagewa ta ci ragadada idan ba mijinta Balabare da Allah ya jarrabeta da mutuwar sansa ba. Duk abin da Balarabe ya tambaya ba ta iya hana shi. Don haka a ƙa’ida kullin ta sauke tukunyar ragadada kwanonsa daban yake, kuma ko kara ya ajiye ba za ta iya tsallakawa ba.

Hansatu na ɗauko leda ta shiga wurgawa Dubu harara sanna ta fara zuba mata, za ta ƙulle ledar Balarabe ya ce, “Ke Hansatu ƙara mata ta hamsin.” Ai kuwa kamar ya watsa mata ruwan zafi ta ɗago a zafafe ta ce, “A kan wane dalili za ka siya mata bayan ɗazun nan yarinyar nan ta gama ci mini mutumci…” Nan fa Hansatu ta zayyanewa Balarabe yanda suka yi, kamar ta rufe bakinsa shiru kake ji sai dai sam ba haka ya so ba, Dubu na karɓar ragadadarta ta nufi hanya za ta fita sai ga Ɗan’iya ya shiga gidan yana kwala ihu.

Da kallon mamaki ya bi Dubu har ta fice, Hansatu don sauri zaninta har faɗuwa yake. Ta fara jefo masa tambaya a hargitse, “Ɗan’iya ina bokitin ragadadar?” Tun bata rufe baki ba ya hau nuna ƙofa ya ce, “Dubu ce ta karɓe mini.” Ai kuwa kamar wanda ya ɗanawa wuta haka Hansatu ta zabura tana cewa, “Buhun uban can, kai buɗe baki ka yi mini magana yanda zan fahimta.” Dubu na jin haka ta fara zuba sauri bata tsaya ko’ina ba sai islamiyya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button