BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Yaya babba ta taɓe baki ta ce, “Salisu ka fita a idona tun da ba kai nake gayawa ba, Musbahu ko ka ji na ambaci sunansa?” Musbahu ya ce, “A’a Inno.” Dubu da ke gefe ta ce, “Inno idan baya son jin labarin ai mu muna so.” Baba Munkaila ya zuba mata uwar harara, Ita kuwa Yaya babba kamar wacce aka ƙarawa ƙaimi ta ce, “Allah dai ya yi miki albarka Dubu. Kin ga Munkaila ban taɓa sanin ya iya waƙar salawatu ba alƙur’an sai ranar da Kulu take naƙudu. Ranar mun ga abu iri-iri ni da Furaira, daga fara biya mata suratul Khaifi sai ya zarce da salawaitu. Ni kuwa na hau istigifari don ina gudun fushin Ubangiji an haɗa ayarsa da waƙa. Ban tsinke da lamarin Munkaila ba sai da na ga yana kuka wai ta mayar masa cikin jikinsa. Ni kuwa na ce raba kanka da haihuwa Munkaila idan cikin ya dawo jikinka, daga nan har ƙofar dawanau sai an ji ihunka. Yo wa ya gaya masa haihuwa ta maza ce wannan jarumtar sai mata…” Baba Munkaila a hanzarce ya miƙe zai fita daga ɗakin, saboda tun da yake bai taɓa jin kunya irin ta ranar ba, bisa tsautsayi ya yi tuntube jallabiyyar jikinsa ta taɗe shi ji kake kiriiiiif ya zube a ƙasa.

Dubu kuwa ta kwashe da wata irin dariyar ƙeta, don dama ta jima tana dannewa bata samu ta yi dariyar ba sai ta wannan dalilin. Salisu na ganin sirikinsa ya faɗi ya fara faɗin, “Subhanallah Sannu Baffa.” Duk suka yi carko-carko Salisu na son zuwa ya taimakawa Baba Munkaila yana fargabar faɗansa, Musbahu da yake gimtse dariyarsa ya kalli Salisu yana yi masa inkiya da ya je ya taimaka masa. Yaya babba ta riƙe haɓa tana faɗin,

“Ikon Allah wai na kwance ya faɗi. An ya Munkaila baka taɓa yi wa mutanen wurin nan fitsari a tsakiyar kai ba kuwa? Idan ban manta ba wannan ce faɗuwarka ta biyar tun daga haihuwarka. Ta ƙarshen da ka yi kafin wannan idan na tuna tun baka fi shekara goma ba lokacin an yi muku shayi kai da su Ado, ka warto cinyar kaza a hannunsa ya biyo ka ya murɗe ya karɓe; to gashi yanzu ma an kwatanta.” Dubu dariya take har da hawaye dukda ta san wannan dariya da take yi tamkar bashin duka ta ɗauka da hannunta. Salisu ya ƙarasa wurin yana dafa Baba Munkaila ya ce, “Sannu Baffa ko na taimaka maka.” Da sauri Baba Munkaila ya fisge hannunsa ya ce, “Sake ni bana so.” Da hanzari ya miƙe yana ɗingisa ƙafa ya fita daga ɗakin.

Yaya babba ta jinjina kai ta ce, “Allah ya fissheka alheri Salisu don wallahi Munkaila ya ɗau fushi da kai, yo meye za ka ce za ka taimaka masa gazawa ya yi?” Salisu a ɗan fusace ya ce, “Don Allah Inno ki yi mana shiru, ta ya za a yi na fusata shi bayan ke kika ɓata komai kin zauna kina zancen angwancinsa a gabana; wai har da waƙar salawaitu, ba dole ki sashi ya tashi ya fice ba.” Yaya babba ta hamgame baki ta ce, “Don Allah Musbahu me ye laifina a nan don na baku labarin angwancin Munkaila, ba Uba yake a wurinku ba?” Musbahu ya yi murmushi ya ce, “Inno Salisu fa sirinkinsa ne auren Zulfa zai yi kin ga ai hakan da kika faɗa bai kamata ba a gabansa.” A sanyaye Yaya babba ta kalli Salisu ta ce, “Salisu kana ganih Munkaila bai yi fushi ba?”

“Ai idan da abin da ya fi fushi ya ɗauka da ke duk ɗaya makafi sun yi dare.” Salisu ya yi maganar a ƙule. Yaya babba ta russunar da kai ta ce, “Allah ya sani ban iya gaba ba halin ƴan wuta ne, ni kuwa me zai haɗa ni da wuta a na zaune ƙalau? A’a raba ni da Munkaila ya je ya yi ta gabarsa ko a lahira karma ya nuna ya sanni, bare mu ƙulla alaƙa. Musbahu ku shaida ko a lahira za ku tsaya mini shaidu a gaban Allah.”

Da sauri Salisu ya ce, “Ai ko a gidan duniya ba zan tsaya miki shaida ba Inno bare a lahira, kema ki yi ta kanki a wannan ranar da har kike neman wani ya yi miki shaida tsakanin ki da Baffa.” Yaya babba ta yi ƙwafa a fusace ta ce, “An ya kana ƙaunata Salisu kuwa?” Salisu ya wara mata hannu ya ce, “Ba tabbas!” A tsorace Yaya babba ta ce, “Alƙur’an bari su Sule su zo sai sun yi mini iyaka da kai, ko a lahira karka nuna ka taɓa sanina.” Salisu ya miƙe shi da Musbahu sannan ya ce, “Inno a ina ma zan ganki muna can sahun ƴan aljanna.” Yana gama maganar suka fita, ai kuwa Yaya babba ta fashe da kuka tana ƙwalawa Baba Sule kira da sauran ƴaƴanta kira.

Gidan Baba Abubakar.

Hajiya Nafisa ba ta san lokacin da ta lailayo wani ashar ta maka ba, a tsananin fusace ta ce, “Ƴar gidan uban waye da za ka bata ɗana ba tare da shawara ba? Nawa Mahaifinta ya baka da za ka yi abu cikin ƙanƙanin lokaci? Wacece wannan Haliman? Wane muƙami ubanta yake da shi a ƙasarnan?” Ta jero masa tambayoyi wannan na bin wannan kamar tsohuwar ƴar jarida, saboda yanda idonta ya rufe ko sunan Mahaifin Dubu da inkiyarsu ta ƊANGWAURO ba ta yi ba. Murmushin tura haushi ya yi ya ce, “Hala baki lura da bayanan da ke jikin katin ba? Me kike ci na baka na zuba Nafisa? Ai duk gaggawar Unguwar zoma ta bari a haihu. Ki wara ido da kyau ki sake karanta bayanin da ke cikin katin.

Kamar sabuwar makauniya haka ta fara ware idanu tana bi daki-daki, kamar wacce kunama ta ɗanawa harbi lokaci ɗaya ta zabura jikinta har rawa yake. Idonta ya sake ƙanƙancewa, fuskarta murtuk saboda ɓacin rai. Ja da baya ta fara yi tana nuna shi bakinta na rawa ta ce, “Wai kana nufin Dubu za a ɗaura masa? Wallahi ba zai yuwu ba. Na rantse da Allah idan nina haifi Aseem ba zai auri wannan jakar yarinyar mahaukaciya ba.” Murmushin takaici ya yi a karo na biyu fuskarsa ba walwala saboda ɗacin maganganunta, tabbas shi kansa ya san Dubu na da wasu ɗabi’u, da dole tana buƙatar gyara amma kalaman sun yi zafi akanta, duba da irin riƙon da Yaya babba ta yi mata. Kuma duk lalacewarta ƴan ɗan’uwansa ce, ta ya za bari a ci zarafinta a gabansa? Tana shirin sake yin magana ya katse ta da cewa, “Hawainiyarki ta kiyayi ramata Nafisa, karki ƙara furta kalma mara daɗi akan yarinyar nan idan ba haka ba kuma ranki zai yi mummunan ɓaci. Aseem ɗana ne kuma ina da ikon aura masa duk yarinyar da na yi niyya, Alhamdullah biyyyyar da nake wa Mahaifiyata ba ta tashi a banza ba, domin Aseem bai watsa mini ƙasa a ido ba. Tabbas wannan abin ɗaga hannu ne na godewa Ubangiji, saboda ba kowanne matashi mai ji da ƙuruciya za a yi wa wannan auren ba, kuma ya amince.” Sakin baki ta yi tana kallonsa, dukda gwiwoyinta sun fara sanyin da jin kalamansa, hakan bata sa ta bada ƙofar da Baba Abuabakar zai ga lagwanta ba, murya a daƙile ta ce, “Shi da kansa Aseem ya amince da wannan maganar? Tabbas biri ya yi kama da mutum! Amma za mu gauraya da shi wallahi sai dai ya zaɓa ko ni ko auren waccen ballagazar.” Tana gama maganar ta fice daga ɗakin fuuuu kamar guguwar da take tsaka da tashi a tsakiyar sahara. Yana ganin fitarta ta ɗau waya ya kira Aseem tare da sanar masa da ya zauna cikin shiri, don a kowanne lokaci mahaifiyarsa za ta iya kiransa a waya akan wannan maganar.

Lokacin da Aseem ya katse kiran da ya yi wa Dubu, dogon tsaki ya yi yana furzar da iska mai zafi. Nasir da ke gefe ya zura masa ido bayan wani lokaci ya ce, “Aseem!” Bai ɗago ya kalle shi ba sai ma girgiza ƙafarsa da yake yi, don ayyanawa yake yau da yana kusa da Dubu mai hana shi shaƙeta a gidan sai Allah. Nasir bai damu ba ya ci gaba da cewa, “Tun bayan dawowarka na lura kana cikin damuwa, na yi tsammanin ni da kai mun zama ɗaya ashe ba haka ba ne. Ko makaho ya shafa ka ya san kana cikin damuwa, wai mene ne yake damunka?” Aseem ya ɗago da jajayan idanunsa ya ce, “Nasir ba ni kara ɗaya na busa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button