BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

“Munkaila!” Ta ambaci sunan Baba Munkaila a hankali ya amsa don yana gudun kar a kwatanta ta kwanaki. Yaya babba ta ci gaba da cewa, “Kwarankwatsa dubu ka shawarta da ƴan uwa wallahi auren nan janyo shi za a yi; ku rufa mini asiri ku aurar da yaran nan na daina jin miyagun maganganun da kunnena suke ji, wai ma saura kwana nawa?” Baba Munkaila ya haɗiyi yawo cike da fargaba don har zuwa lokacin bai gama haɗa kuɗin kayan gadon Zulfa ba, shi kuma baya jin zai iya taɓa kiwonsa ko kaza ce ya sayar. A hankali ya ce, “Yau saura kwana goma sha takwas.”

“To a rage kwanakin nan gaskiya, don na gaji da jin falsafar rashin ɗa’a a kunnena. Ina dalili ina zaune ƙalau a janyo mana fushin mala’iku har cikin gida. A’a don Allah ka rabani da faɗawa halaka, me ye haɗina da Jahannama ana zaune ƙalau? A’a wallahi ina daga sahun farkon masoyiya Manzon Allah (S.A.W)” Kowa dai ya yi shiru cikin zuƙutansu da irin wasiƙar da suke karantawa.

Yaya Babba bata damu ba ta ci gaba da cewa, “Ku gane mini shi don Allah wa zai ce Salisu halin yahudu gare shi? Maganganun da ya faɗa rannan a ɗakina alƙur’an da ƙyar bacci ya ɗauke ni.” Baƙin cikin duniya ya cika Salisu, ban da harare-harare babu abin da yake yi.

“Wai har da I musu yu, don Allah ku ji kalmar arnanci kamar me kiran muzuru, ni Soja nake yi wa kallon ɓatacce mai halin Yahudawa ashe ina tare da shi a kusa ban sani ba” Hajiya Nafisa ta cika fam wannan kalmar na ƙona ranta idan ta ji Yaya babba na danganta jininta da yahudawa.

Cike da takaici Inna Furai ta juyo ta ce, “Yaya raba kanki da aibanta mini jika idan ba haka ba alƙur’an babu mai hanani zazzage miki albarka a ka.” Yaya baba ta sakar mata harar mai ɗauke da manufar, ai ba ke kika haifar mini mahaifinsa ba. Sannan ta ɗora da cewa, “Furai wa ya haifar mini Uban Salisu a gidan nan?”

Inna Furai ta taɓe baki ta ce, “Yoo don kin haifi ubansa ni da Malam ya yi mini kyautar ubansa tun yana tsammafa.” Yaya babba ta saki dariyar ta ce, “Yoo wa yake bin wasiyyar matacce, Malam dai ya mutu Allah ya jiƙansa amma ba wanda ya isa ya yi mini iko da jinina.”

Inna Furai ta ɓata fuska har da huccinta, ta kalli Auwalu ta ce, “Auwalu Allah idan baka rakani ofishin human rai (Human right) ba kwarankwatsa mai hanani zazzagewa gidan nan albarka sai Allah. Allah ko ka rakani a bi mini haƙƙina ko ku neme ni ku rasa daga nan nida Indo shari’a har ƙashen duniya.” A tsorace Yaya babba ta dafe ƙirji ta ce, “Furai yau ni kike ambata da Indo gatsal? Wallahi magana dai na yi kai Sha’aban ga ƙarin wata shaidar, kwarankwatsa dubu ko a lahira ka shaida abin da Furai ta yu mini, yoo ƙarya na yi masa ba da kunnena na ji watsewar kalaman yahudawa ba wai I musu yu (I miss you), abin da ko a mafarki ban taɓa ji Soja na faɗa ba dukda shi ma ina kokwanto akan tauhidinsa, yo me ake da aikin Soja na aikin kafirai masu busasshiyar zuciya. Allah ya sani Garba ka cuceni da ka sa mini Jika a harkar ɓata don…”

Sallamar Aseem ce ta katse Yaya babba daga jawabin da take yi.

Zuwansa kenan daga garin Lagos, ya shiga cikin gidan ya ga duk babu kowa don haka ya yanke shawara zuwa sashen su Yaya babba. Yaya babbb na ganinsa ta fashe da dariya tana faɗin, “Kun ga Ɗan’halak. Soja zo nan.” Da mamaki ya fara bin mutanen wurin, yana mamakin abin da ya kawo su suka tattaru wuri ɗaya. Bai ankara ba ya ji muryar Yaya babba raɗau a kunnensa tana ci gaba da cewa.

“Soja ka dubi Allah da Annabi, ka san dai Sule bashi da wuta da aljanna bare idan ya ji ka faɗi gaskiya a kan Ɗansa Salisu ya babbakeka. Ka gaya mini meye I musu yu? Don wallahi ba zan juri zama cikin fushin Ubangiji ba?”

Shafi na biyun ƙarshe????????‍♀️???????? daga shafin gobe an gama free pages ku yi hanzari ku fara biya kar a yi babu ku????????????????????????????????????????
DUBU JIKAR MAI CARBI

        ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

LAST FREE PAGES 13

   Guntun tsaki Aseem ya ja ba tare da kowa ya fahimce shi ba, yana daga wurin da yake ya ce, "Inno lafiya kuwa na ga mutanen gidan sun taru?" Ya yi maganar fuska a tamke don ba ya son ta sake jefa masa wata maganar, saboda gabaɗaya ransa a dagule yake. Bai rufe baki ba idanun mutanen wurin suka sauka a kansa, yadda ka san sun ga sabuwar hallita haka suka zura masa idanu. Dubu kuwa sai kallonsa take tana yashe baki, musamman da ta tuna irin huɗubar da Yaya babba ta yi mata akan kissa da kisisina, wai murmushi ma yana daga cikin abin da yake sace zuciyar namiji.  Don haka Dubu ta zage ta riƙa yashe haƙora tana kallon saitin wurin da Aseem yake, har sake miƙa wuya gaba take don ya fi hangota a kan sauran mutanen wurin.

Yaya Babba na jin kalaman Aseem ta ɗan ɓata fuska ta ce, “Tsiya ta da kai kenan Soja. Don Allah ka ƙaraso ka taya ni jin wannan lamarin ko so kake na ji ni kaɗai?” A hankali ya fara takawa yana saƙale da jakar goyonsa wacce kayan aikinsa suke ciki, sai kuma trollybag wacce ke ɗauke da sauran kayansa suke ciki. Ƙirjin Hafsa ban da lugude babu abin da yake yi, tana jin zuciyarta na wani iri kamar za ta faso ƙirjinta. Soyayyar Aseem na ci gaba da mamaye zuciyarta, a fakaice ta sunkuyar da kai ƙasa ta sharce hawaye ba tare da ta bari wani ya lura ba.

Aseem na ƙarasawa shi ma Yaya babba riƙo hannunsa tana faɗin, “Soja wai saura kwana nawa aurenku don Allah?” Nan take fuskar Aseem ta sake haɗewa ya ɗauke kai gefe ya ce, “Na manta.” Ta yashe baki tana kallon mutanen wurin ta ce, “Kun ji abin da nake faɗa, alƙur’an Soja da ba kallon da bana yi maka don Allah ka gafarceni. Allah ya sani ko Garba ba zai nuna maka kunya ba, don shi ma da kake ganinsa a lokacin samartaka ƴanmatan da ya yi Allah ne kaɗai masani. Allah mai sarauta irin soyayya da Garba ya yi da Kandala da gidan nan na magana da ya shede ni, bana buƙatar shedar Furaira don ko a lahira na yanke zumunci da ita.”

Aseem bakinsa sai motsi yake yana san ya yi magana amma yana gudun ta fito mara daɗi, yana shirin cire hannunsa daga jikin nata ya ji Inna Furai ta ce,

“Me ye naki na ambatar sunana kuma? Wallahi ko a aljannah sai na zazzage miki albarka a tsakar ka.” Yaya babba bata bi ta kan Inna Furai ba ta ci gaba da cewa, “Amma dai har Garba ya auri uwarka wallahi ban taɓa jin kalmar Allah wadai a bakinsa ba, gaskiya ba da ni ba wannan falsafar dole a dakatar da ita, maganar gaskiya Shehu auren nan ranar juma’a mai zuwa za a ɗaura shi. A kai yaran nan ko ma huta; ina dalili laifinsu ya shafe mu, mu riƙa sallah ba a karɓa Mala’iku su yi fushi da mu.” Ta ƙarasa maganar tana kallon wurin Baba Shehu.

Baba Shehu ya kwantar da murya ya fara cewa, “Inno da za a taimaka a bari lokacin nan ya zo, mun riga da mun buga katin gayyata duk mun aikawa mutane idan wani abin yaran nan suka yi bayan taro ya watse sai mu zauna a tattauna.” Yaya Babba ta ƙura masa ido har ya gama sannan ta ce, “Dole ka nuna mini iyakata Shehu, ba sai ka faɗa ba dama ai ba ni na haifa muku su ba.” Yaya babba ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.

Wurin shiru ya ɗauka aka rasa mai bakin magana, Baba Aminu ya ɗago ya dubi mutanen wurin ya sallame su. Ɗaya bayan ɗaya haka suka fara wucewa suna barin wurin, dama Aseem da Salisu kamar a kan ƙaya suke tun Baba Aminu bai rufe baki ba suka wuce gaba.

Shiru wurin ya yi daga Yaya babba sai Inna Furai da sauran iyaye maza kowa yanayinsa ba daɗi. Baba Abubakar ya ƙarasa wurin Yaya babba ya ciro hankicif ɗinsa ya miƙa mata ya ce,

“Inno share hawayenki.”

Yaya babba bata ɗago ta kalle shi ba ta ce, “Ka barni ya yi ta zuba idan ya ƙare na mutu kun huta ai.” Murmushi suka yi don ta so basu dariya, ya juya wurin Inna Furai ya ce, “Inna don Allah ki sa baki ta tsaya mu yi magana.” Inna Furai ta ɗauke gefe tana wurga masa harara ta ce,

“Wacce zazzagar kuke so na yi? Maganar gaskiya abin da Yaya ta faɗa yana hanya, wai me ye a ciki lamarin nan fa na gida ne kuma auren nan ko yau aka ɗaura shi akwai wanda zai ce don me?” Baba Abubakar ya yi shiru don ya lura gabaɗaya a rikice suke, Inna Furai ta ci gaba da cewa, “Ba zan hana Yaya ba saboda Allah ina dalili ana nuna muku Annabi kuna runtse ido.” Yaya babba na jin haka ta sake rushewa da kuka. Sai da ta yi mai isarta ta miƙe za ta bar wurin, da sauri suka dakatar da ita sai da ƙyar suka shawo kan Yaya babba ta zauna. Amma duk yadda suka so a bar biki a lokacin da yake fir ita da Inna Furai suka ƙi amincewa. Babu yadda suka iya haka suka amince akan ɗaurin auren ranar juma’a mai zuwa wanda a lokacin gabaɗaya saura kwanan huɗu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button