DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL
Sai dai har lokacin mafarkin da ta yi bai gama sakin jikinta, wani abin da ya bata mamaki bai wuce zuwan period ɗin ta ba alhalin ba lokacin zuwansa ba ne.
Mama Uwani tana fita bayan Raihan ta shiga toilet wata baƙar mage ce ta ratso daga bangon kusurwar ɗakin, idanunta jawur suke kamar gauta ga ƙarshen jelarta wani tafkeken kan maciji ne ban da sheƙi babu abin da yake yi. Kalle-kalle ta fara yi tana shine-shine sannan ta fara girgiza cikin wani irin yanayi, lokaci ɗaya ta fara rikiɗa zuwa kaloli daban-daban. Sai da ta rikiɗa zuwa kaloli sama da goma sannan ta dawo kalarta ta farko, ta buga tsalle zuwa kan gadon da Raihan ta tashi wanda har ya ɗan fara ɓaci da jini. Tana hawa kai ta fara lasa sai da ta siɗe shi tas sannan ta sauko cikin takun ƙasaita tana kalle-kalle, a hankali ta taka zuwa kan mudubin Raihan da ke cike da kayan shafe-shafe da turarruka kala-kala.
Girgiza ta yi lokaci ɗaya ta rike zuwa wata mummunar hallita mai siffar dorinar ruwa da ranƙwalelen ƙaho a goshinta, a hankali ta fara zuƙe mayuka da tururrukan da ke cikin kwalabe da robobinsu, nan take komai ya zama wayam babu komai a ciki. Wani irin ruwa ta shiga ɗurawa mai yauƙi sai da ta gama cika su sannan ta hura iska suka dawo tamkar mayuka da turarrrukan da ke ciki da farko. Mama Uwani ce ta tunkaro ƙofar da sauri wannan hallitar ta sake rikiɗewa zuwa mage wannan karon jelar rabuwa ta yi gida biyu dukkansu ɗauke da kan maciji. Tana jin alamun buɗe ƙofa da sauri ta ratse ta jikin bango ta ɓace daga ɗakin, sai dai takaicinta ɗaya da bata samu ta ƙarasa cimma abin da yake tafe da ita ba.
Mama Uwani jere kayan abincin Raihan ta fara yi, a daidai lokacin Raihan ta fito ɗaure da towel. Da murmushi Mama Uwani ta riƙo hannunta tana faɗin, “Ƴar gatan Uwani me kike buƙata bayan wannan?” Ɗan yamutsa fuska ta yi ta ce, “Babu.” Mama Uwani cikin wani yanayi ta fara bin ɗakin da kallo, Raihan ta ɗan ja guntun tsaki tana faɗin, “Mama Uwani ki bani wuri bana buƙatar hayaniya.”
Mama Uwani ba don ta so ba ta juya jiki a sanyaye ta fice daga ɗakin tana waige, fitarta ke da wuya Mommy na kawo kai tana ganin Mama Uwani ta ce, “Uwani yarinyar ta tashi kuwa?” Mama Uwani cikin ladabi ta ce, “Ta tashi hajiya yanzu na kai mata abin kari.” Mommy bata tanka mata ba ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, Raihan na gaban mudubi za ta fara shafa mai. Mummy ta kira sunanta tana ci gaba da cewa, “Raihan ba dai yanzu kika ta shi kika yi sallaha ba?” Raihan ta ɓata fuska ta ce, “Haba Mommy wai me kika mayar da ni, ni ba sallah ma zan yi ba period ɗina ya dawo.” Fuska ɗauke da damuwa Mommy ta ce, “Period kuma, ina ce yau ko sati biyu ba ki da gamawa ba.” Cikin rashin damuwa ta gyaɗa kai tana ci gaba da shafa mai, juyawa Mommy ta yi ta fi ce tana faɗin, “Gaskiya idan ya ci gaba da yi miki wasa dole mu je mu ga likita.” Raihan ta tura baki gaba ƙasa-ƙasa da murya tana faɗin, “Kawai don period ɗina ya dawo sai ace sai na je wani Hospital ana zaune ƙalau.” Turo ƙofar da aka yi ne ya sa Raihan waigawa a lokacin ta fesa turare tana saka wata doguwar rigar bacci, Mama Uwani ce ta sake shiga hannu ɗauke da kunun gyaɗa ta ajiye, Raihan na ganin haka ta saki murmushi mai sauti ta ce, “Mama Uwani dama kin yi kunu shi ne baki kawo min ba, ai kuwa da na cika cikina sai kin kwashe min tass kin ɗura min kunun nan.” Ta ƙarasa magana tana zame towel ɗin jikinta don ita Raihan bata kunyar ko a gaban waye ta cire kayanta ko ta sauya wasu.
Mama Uwani na ganin haka ta fice daga ɗakin, Raihan na cikin saka kaya ta ji kanta na sara mara lokaci ɗaya jini ya fara bin ƙafarta ga wani irin raɗaɗi da jikinta yake yi ta ko’ina, nan take ta yanke jiki ta faɗi a wurin. Wani irin hayaƙi ne ya fara zirarowa ta jikin ƙofa har sai da ya zo gaban Raihan da ke kwance jini ya fara malala daga jikinta, lokaci ɗaya hayaƙin ya rikiɗa zuwa siffar mutum. Kallon kan mudubin Raihan ya yi yana girgiza kai cike da baƙin ciki, ɗaya bayan ɗaya ya fara zuƙewa mayuwan ciki da yake ganinsu da kalar ruwan nan mai yauƙi, kusurwa bangon ɗakin ya kalla ya ce, “Tabbas ba aikin kowa ba ne sai naki Mugaza, na lura kin fara wuce makaɗi da rawa amma ranki sai ya yi mummunan ɓaci.” Tun bai rufe baki ba magen nan ta sake ɓullowa ta bango, har sai da ta zo gabansa ta yi girgiza cikin surar wata matashiyar budurwa ta ce, “Ka ga laifina don na nakasta mai shirin tarwatsa farincikina? Ko kana tsammanin zan zura ido ka ɗauko mini kishiya alhalin ka san wannan haramtacciyar al’ada ce a zuri’armu. Wani abin takaici ma ka rasa wacce za ka aura sai bil’adam salon ka ja mini abin kunya cikin ahalina, wallahi ba zan lamunci haka ba kuma wannan somin taɓu ne ka zuba ido ka gani.” Tana gama maganar ta sake rikiɗa zuwa mage ta ɓace daga ɗakin, cike da takaici ya kalli gadon Raihan sai kawai ya fara kiran sunan Hidaya. Sai da ya kira sau uku sannan wata matashiyar budurwa ta ratso ta ƙarƙashin ƙasa mai zubin siffar Raihan babu abin da ya bambamta su har kayan jikinta. Wurin abincin Raihan ya nuna mata ya ce, “Ki maye gurbinta kuma bana buƙatar a samu matsala idan ba haka ba har abada ke da biyan buƙatar ƙudurinki.”
Idanunta ne suka ciko da ƙwallah ta ce, “Wuskarbat min kalsusbima wakfit karmu linkasbu muzrabatu fisgatmuha warmi Jalkisu Mu’az.” (Don Allah karka yi mini haka, ka san duk duniya babu wanda nake ƙauna kamar Yarima Mu’az.)
Ɗaukan Raihan ya yi da ke kwance ya saɓa a kafaɗa sannan ya kalli jabun Raihan da ke tsaye ya ce, “Dole ki ɗauki ɗabi’a irin ta Raihan hatta yare dole ki ci gaba da irin yarenta ba namu da muka saba yi ba. Na gaya miki idan aka samu matsala ke da Yarima Mu’az har abada.” Yana gama maganar ya daki tsakar ɗakin nan take ƙasar wurin ta dare ya faɗa ciki hannunsa ɗauke da Raihan suna shigewa ƙasar wurin ta haɗe ta shafe kamar wani abu bai taɓa faruwa a wurin ba.
SHARE HILIS????
Daga yau za ki iya turo kuɗinki don karki bari ayi babu ke????????♀️????????♀️????????♀️
Ummou Aslam Bint Adam????
[7/9, 9:22 AM] Ameera Adam????: ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
© AMEERA ADAM
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.
FIRST CLASS WRITER’S ASSO…
FREE PAGE 2
A hankali Jabun Raihan ta fara bin ɗakin da kallon, miƙewa ta yi ta fara buɗe drowers ɗin kayan Raihan sai kuma ta bi hotunan ɗakin Raihan da ke maƙale a jikin bango tana kallo ɗaya bayan ɗaya, tana jin motsi ta koma wurin kayan abincin ta zauna. Kallon abincin take don sam bai burgeta ba cikin zuciyarta take mamakin irin abincin bil'adam don ita bata ga abin daɗi a ciki ba. Goggo ce ta turo ƙofar tana faɗin, "Rehanu! Ke Rehanu wai ina kika shiga ne tun jiya ban ji wulgawarki ba, yarinya sai iya shege don kin ga na damu da ke." Turus ta yi tana kallon Jabun Raihan da ke cin abinci tana yamutsa fuska, daƙuwa ta yi mata da hannu tana faɗin, "Kin ci ƙaniyarki Rehanu dama kina jina kika yi shiru to kin wulaƙanta uwarki Abu. Meye wannan ɗin kike ci kina yamutsa fuska kamar abinci?" Jabun Raihan a daƙile ta ce, "Gashi kuwa kin gani."
Goggo ta shiga ɗakin ta yi tsaye a kan Raihan tana faɗin, “Oho dai kowa ya raina uwar wani tashi ya raina, wallahi duk maganar da kika gaya min uwarki da Ubanki kika gayawa.” A fusace ta ɗago tana duban Goggo da ke tsaye tana zazzaga ruwan masifa, farantan gabanta ta kalla tana motsa baki lokaci ɗaya ta cinye abincin ciki sai kwanukan, tana kallon Goggo kamar wacce ta basu umarni sai farantan suka yi tsalle zuwa gaban Goggo, wuƙar da Mama Uwani ta haɗowa Raihan don ta riƙa yankar farfesun ƙafar sa ce ta yi tsaye a daidai fuskar Goggo saitin idonta tana wani juyi, kamar za ta tsokane mata ido. Jabun Raihan ta kalli Goggo fuska ba walwala tana cewa, “Kika sake zagar mini iyaye sai na tsokane idonki, ke da sake gani har abada. Wannan kwanukan kuwa sai na basu umarni su yi ta ranƙwale miki kai har sai sun illataki.” Goggo daskarewa ta yi a wurin, tuni fitsari ya jiƙe mata zani gumi sai yanko mata yake ta ko’ina. Tun Jabun Raihan bata gama magana ba, Goggo ta juya da gudu tana ƙawalawa Mahaifiyar Raihan kira, sai dai yadda ƙafafuwanta suka yi mata nauyi ya sa ta fice da rarrafe zanin jikinta kuwa tuni ya samu mutsuguni a bakin ƙofa.