LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

Tunowa tayi da lokacin auranta da Haisam dady ko kulata bayayi da aka kawota gabansa lokacin da za’a kaita gidan mijinta cewa yayi bashida abin cewa , amma yau itace yake cewa haka , tashi kuje Allah yayi miki albarka yar albarka , wani sanyi taji ko ba komai zata aurin zaɓin iyayenta a gurinta babu abinda yakai farincikin su a gurinta.”

Ɗakin Anty suka wuce da ita itama fuskarta cike da fara'a tace "madallah naji daɗin ganin wanan rana , anty Ummi dake gefe ta ja Afnan wani ɗaki banji mai sukace ba suka fito suka koma ɗakin momy.

Misalin ƙarfe takwasa kowa yayi sallah ya idar motoci suka fara hallara a harabar gidan , daga ganin motocin ma kasan kaf cikinsu babu na haya duk na ma’aikatane , Allah sarki rabuwa da iyaye sai dole Afnan ta ƙanƙame momy sai kuka takeyi momyn ma sai da ta zubar da hawaye sosai ganin Afnan tanata gursheƙen kuka, kasancewar ba wasu ƙawaye ta ɗiba masu yawa ba suka shige mota Afnan ma da ƙyar suka sanyata tanata kuka , ganin babu kowa a motar daga ita sai Abdallah a gefe , sai ma yanzu ta lura dashi , a gefenta sai direba , da ya maida hankalinshi ga wayar dake hanunshi , waro ido Afnan tayi shima Abdallah maida mata da martanin waro idon yayi ya sanya hanunshi cikin nata suka fice , kasancewar kowa ya fice daga gidan iya motarsu ce kawai, Afnan dai bata yi magana ba kasancewar jinta takeyi kamar zazzaɓi ne zai kamata , tafara haɗe hannayenta biyu tare da rintse idonta dataji yana yimata zafi …..✍️.

Ga masu buƙatar littafin daga farko zaku iya duba wattpad momislam 2020

????????????????????????????
???? ???? ????

LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!

     ????     ????     ????

????????????????????????????

Story and writing by

ZAINAB HABIB
{Mom islam}

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com
https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.

BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM

EPISODE 27 & 28

Ganin idanunta sunyi ja tana ta rawar sanyi yasa Abdallah cewa dreba muje asibiti a dubata kar ka wuce damu gida , to yace “ya juya motarsa basuyi wata tafiya mai tsayi ba sai gasu sun iso asibitin kulawa likita yafara bata , cewa “Abdallah yayi muje office muyi magana , ok Abdallah yace kana ya rufawa likita baya da isarsu kowa ya zauna likita yace “wanan matarka ce ?eh Abdallah yace “to tana buƙatar kulawa , Abdallah ne yace ” menene ainihin abinda ke damunta ?”rashin bacci ne amma bayan shi babu wata matsala shine ya haifar mata da zazzaɓi amma zan haɗa mata magani insha Allah zata war ware , godiya Abdallah yayi masa bayan sun karɓi magani suka ɗauki hanyar da zata sadasu da katafaren gidan amarya , kasancewar hospital ɗin a kan titi yake suna isowa dreba yayi horn mai gadi ya buɗe get ɗin sa kai sukayi cikin gidan , samun mutane sukayi cirko cirko a tsaye kowa da mamaki a fuskarshi , ina ango yakai amarya.”

Buɗe murfin motar kowannen su yayi ,Abdallah ya rungumo Afnan suka fito Anty Aisha ce ta taho zuwa gurinsu tace “me yafaru munata jajanta rashin ganinku , murmishi Abdallah yayi yace “batajin daɗi ne shine muka wuce , asibiti to Allah yabada lafiya , amen Abdallah yace “anty ummi na tsaye tana kallon ikon Allah , haka kowa keta ɗan taɓe baki ko mai yasa oho .”

wata mata dake gefe da alamu itama ƴar uwar momy ce ta karɓi Afnan ta shige da ita ciki , gaskiya faɗin tsaruwar gidan ma ɓata lokaci ne maƙudan kuɗin da Abdallah ya kashe bazasu faɗu ba , part ɗin Afnan ɗin na can nesa sana uwar gida amma da tafiya a tsakaninsu dan kowanne da nisa gidan babba ne , zaunar da ita tayi a tsararen ɗakinta dayaji flawoyi ga wani ƙamshi dake tashi , gaskiya komai na ɗakin abin birgewa ne kasancewar dady ma ya kashe nera,

Iya mutum uku ne ragowa dare yayi sauran sun tafi suma suna gama gyara ta kasancewar batada kafiya ta kwanta sukayi mata sallama suka wuce , misalin ƙarfe sha ɗaya na dare shugaba ya shigo bayan yasa dreba yakai su anty gida , sanye yake da wata baƙar doguwar riga mai hula , sai tashin ƙamshi yakeyi saboda shi ma abocin tsafta ne dakuma son ƙamshi ,

Kasancewar zazzaɓin nata ya sauka yasata yin ƙarfi da jikinta tace "barka da zuwa   , ajiye ledar hanunsa yayi ya cire agogon dake manne a tsin tsiyar hannunsa yakai dubansa gareta suka sakarwa junansu murmushi ywwa Afy ya jikin "da sauƙi tace "tare da rage idanunta ta maidasu ƙanana ,to masha Allah , yanzu dai dare yayi ki tashi mu nuna godiyarmu ga Allah ta hanyar yin sallah , sunkuyar da kai Afnan tayi tace "banayi whattt....!!! mekikace ? mai maita masa tayi da cewar banayi , alamun ɓacin rai sun baiyyana a fuskarsa ƙarara sai taji yace "to zokici abinci karki zauna da yunwa , tunowa tayi rabonta da abinci tun na safe gakuma wata masifafiyar yunwa na addabar ta ."

saukowa tayi ta cire mayafinta ta ajiyeshi a kan gado ,Abdallah ne ya haɗiyi wani yawu kai kace "wanda yaga mai siyarda awara , lol fitowa tsararen falon sukayi a jere tana gaba yana baya yana kallon abinda yake ɗauke masa hankali , zama tayi a ɗaya daga cikin jerun kujerun tare da janyo ledar da ya ajiye a gefe , miƙewa Abdallah yayi ya nufi kitchen, ya wanko plet ya kawo mata da cup, kasancewar a ya yanke take yasata ɗiba ta zuba a plet ɗin tafara ci shiko a  haka dai wayarsa yake dannawa amma inka lura da satar kallon da yake yimata ba wayarce ta ɗauke masa hankali ba , tana gama ci ta tatara sauran takai kitchen bayan ta kora lemu mai sanyi dawowa tayi ta zauna tare da duba wayarta ganin ƙarfe ɗaya saura yasata , zaro ido ta kalli Abdallah da ya kawar da kai,

Dare yayi zan kwanta , Afnan tace “ba tare da ta dubeshi ba ok muje niba baccin nakeji , har tafara gaba Abdallah yace “to jirani takowa yayi zuwa gabanta ya riƙe hanunta suka wuce bedroom , kasa cire kayan jikinta tayi ta maida na bacci abin ya gagara irin kallon da Abdallah yake yimata yasata kwanciya tare da juya baya , shima bin gadon yayi ya kwanta tare da rungumeta ya juyo da fuskarta tana kallon tasa , nunfashin su na cuɗanya dana juna , uhm bacci nakeji Afnan tace “lokacin da taji hanun Abdallah a rigarta , cirin sanyin murya yace “to ai yanzu lokacin hutawa ne , bana sallah , cewar Afnan no karki damu ki yarda dani na matsu pls , cikin tashin hankali Afnan ta dubeshi tace “kadai sani ba ƙarya zanyima ba amma mai yasa zaka saɓawa faɗar Allah , nifa ba komai zan yimiki ba to ai ke mallakina ce , eh nasani amma ka barni nayi bacci , Abdallah ne yayi wani irin murmishi tareda ƙara matseta yace “gurinda Allah ya haramta min ƙasanki ne amma daga saman cibiyarki har komai ma zan iya amfani dashi , wanka ya shiga yayi kana ya dawo ya kwanta , Afnan batasan lokacin da baccci mai nauyi ya yi nasarar ɗaukarta ba , shiko ya daɗe baiyi bacci ba yanata juyi shi kaɗai yasan halin da yake ciki .”

Haisam ya kama sana’arshi baji ba gani kasancewar ya roƙi zaɓin Allah akan wanan Alhajin da yakeson ya zauna masa a shago yaƙi yarda , Abubakar yayi yayi amma yaƙi yarda ,

Mama ce keta rangaɗa sallama lokacin ƙarfe goma na safe Haisam na bacci kasancewar bai fiya fita ranar asabar ba yana hutawa.

Mama ce tace "inata kwaɗa sallama ko babu kowa ne a gidan ? cikin ɗaga murya take maganar , walaikis salam gani waye mai dako min tsawa , Maimunatu ta faɗa.

Mama dake ƙarasowa tace “baiwar Allah kice rabo aka samu ? yatsine fuska Maimunatu tayi kana tace “rabo dai muka samu, mama dake murna tana tafa hannu tace “to masha Allah to mushiga daga ciki man , wa ? wlh babu mai shigarmin ɗaki na gyarashi sai dai in ɗauko miki tabarma mijina yana ciki yana bacci , mama ce ta riƙe baki tana kallon Maimunatu da cikinta ya fito sosai dan ga dukkan alamu zai kai wata takwas dan daƙyar take duƙawa , abinka da mai ciki mama ta tausaya mata ƙwarai da gaske ta yunƙura tare da cewa ƴar albarka mai za’a tayaki dashi ? kai kaice baki maimunatu tayi tace ” nifa ba gaiyyar kowa nakeyi ba dan haka a ƙyaleni✍️.

DOMIN SAMUN LITTAFIN NAN TUNDAGA FARKO ZAKU IYA ZIYARTAR wattpad momislam2020

????????????????????????????
???? ???? ????

LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!

     ????     ????     ????

????????????????????????????

Story and writing by

ZAINAB HABIB
{Mom islam}

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com
https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.

BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM

EPISODE 29 & 30

Zama mama tayi a tabarmar niko nace Allah sarki Afnan wargi ma guri yake samu , Maimunatu datasha ɗaurin ƙirji ta dubi mama daketa ƙare mata kallo ta galla mata harara , abinku da ƴar lelen mata mama ta sakar mata murmishi, Haisam ne ya fito da alamun hayaniyar su ce ta tayar dashi , faɗaɗa fara’arsa yayi kana yace ” ah mama kece a gidan namu ?fuskar mama ɗauke da murmishi tace “wlh nazo duba Maimunatu ne , Hausam ne ya durƙusa tare da gaishe da mama, amsawa tayi amma isanta na kan maimunatu dan cikin jikinta yayi girma da yawa sosai kamar mai aihuwar ƴan uku , itako sai aikawa mama da harara takeyi dan ta tsani mama tunda taga take takenta na bibiyar gidan .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button