LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

Ƴan kai amarya ne keta shiri dan mama ta kira Haisam a waya akan ya kawo motoci , dole yakebon umarnin ta haka yaje ya taho da motoci aka rakasu gidan su Maimunatu ,kowa sai kururuwar shiga mota yakeyi ƙanwar maman Maimunatu da basu fito da Amarya ba sunanan suna yimata uɗubar tsiya akan ta koyi tattali mijinta mai yawan cefane , tadinga ɓoye wani abin tana kawowa gidan su komai da aka gaya mata ya shigeta sosai musamman ma maganar tara kuɗi, haka acikin abokan Haisam wai ya shiga gidan su amarya yace “ita suke jira tayi ta fito , luluɓo mata fuska sukayi aka nufi ɓota da ita sunyinyi tafiya mai nisa sanan suka iso gidan ,jin guɗa yayi yawa ya sanya Fatima leƙowa taga ko suwaye , ganin mata nata shiga gidan Afnan yasata riƙe baki tace “angama Haisam ma yayi aure ta sa kuka shikenan Haisam ya saki Afnan wane laifi tayi masa dahar yayi mata haka ?”kasa zaman gidan tayi ta kulle ƙofa ta nufi maƙotansu.”

Maimaicin abinda Haisam yayi musu suka fara Maimunatu buɗe ido tayi tana ƙarewa ɗakin kallo babu laifi yayi kyau sosai ta maida mayafinta ta rufe , faɗa aka shiga yi mata har ƙarfe tara na dare , kowa ya cire ran Haisam bazai kawo mota ba , sunata dai zaune wata a cikinsu ma batada kuɗin komawa horn sukaji lokacin ƙarfe tara da rabi hamdala sukayi ✍️.

Follow me and vote on wattpad
Nayi tafiya ne shiyasa kuka jini shiru

????????????????????????????
???? ???? ????

LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!

     ????     ????     ????

????????????????????????????

Story and writing by

ZAINAB HABIB
{Mom islam}

My wattpad momislam2020

Zainabhabibu713 gmail.com

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

My facbook group
https://www.facebook.com/groups/126215122683287/


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com
https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.

BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM

EPISODE 13 & 14

Kufito mu tafi suka ji ana cewa , da sauri suka miƙe suna yiwa amarya sallama , tun tana saka ran shigowar ango harta fara cire rai agogonta dake manne a jikin bango ta ɗaga kai ta kalla ƙarfe shabiyu na dare to ko bazai zo bane ?"ta faɗa cikin ranta  gyara kwanciyarta tayi ba tare da ta cire kayan jikinta ba , ɓangaren Haisam harya shigo ya kwanta a ɗakinsa duk bata sani ba , da asbha ya miƙe cikin salati yayi alwala ya fito da shirin tafiya masallaci tunowa yayi da ace Afnan ce a gidannan da tuni komai ya gyaru amma amarya guda ta saki baki tana bacci , ficewa yayi yabar gidan ya nufi masallacin kusa dasu ko nafilar ma yau baiyi ba ,ƙarfe takwas Maimunatu tayi miƙa tare da salati ta kalli agogo ganin ƙarfe takwas yasata cewa "kan uba wai na makara ne shiyasa na tashi inajin wata azababiyar yunwa , toilet ta nufa ta yi alwala tazo ta tada sallah ko cikakiyar adu'a batayi ba ta shige kitchen, ganin indomie guda uku manya a jere ya sanyata murna to ina zanga ƙwai?" to me hawa sama ya taka leda ai sai tafiya barin dafa indomin ina gamawa na haɗa shayi mai kauri nasha ko zanji sanyi a raina tunda rabona da abinci tun jiya da yamma , ɗaya da rabi ta dafa ta cika kofi da ruwan lifton kasancewar ta nemi madara ta rasa ,Haisam ne ya fito palo kasancewar dole zasu haɗu tunda a palorn take zaune , ganinta yayi ta mimiƙe ƙafafuwanta tanata loda abinci , Maimunatu ce ta ɗago kai ta ƙarewa Haisam kallo cikin zuciyarta tace "nayi sa'ar gwarzon miji mai jini a jika , ta miƙe tana suɗe hannu tace "barka mijina wai a ina ka kwana ?"a gidan ku , nace "a gidanku meyasa bakice nemana ba ?aida kinsan inda na kwana."

Bata damu da maganganun da ya faɗa mata ba ta ruƙo hanunsa tana shinshina ,to sabon salo sai kace maiyya ? Maimunatu ce ta zaro ido tace “kowane miji yana alfahari da daren farkonsa shida matarsa amma kai kamar bakayi , gyara tsayuwa Haisam yayi yace “daren baƙinciki ko ?”to kishirya zaman ƙunci a gidannan dan walah keda jin daɗi muddin kina gidanan kunyi sallama ,oho dai nariga na sameka mekuma yarage kawai kazo mu buɗe soyayyar mu , wani kallon banza Haisam yai mata kana ya fice , Maimunatu ce tayiwa mamanta waya akan taje gurin malamin da suke zuwa dan sunji daɗinsa tun akan maganar auran gashi yanzu ta sami Haisam sunso ya mance da Afnan amma abin ya gagara ,maman ce tace “to ina magun gunan da na ƙulle miki a baƙar leda , Maimuna ce tace “nayi amfani dasu amma shiru , to ki kwantar da hankalinki insha Allah anjima zani ,duk iskancin sa zai sakko yanzu dai babbar damuwar shine inda za’ayi ya kwanta dake har kisami ciki , daganan kinga sabon gata zai rashi da gurinshi da gurin uwarshi , Maimunatu ce ta nisa kana tace “hmm yaushe ma ya shigo ɗakin nawa to jiyama ban san a gidan ta kwana ba , ɓama ce tace”ke wawiya ce bakida tunani meyasa bazaki san inda zakiyi ba sai kace ba mace ba ?”nifa duk iskancin namiji sai na juyashi naga kamar ke bazakiyi gado naba ko ?mama zan gwada karki damu cewar Maimunatu sukayi sallama , tana gama cin abincin ta miƙe ta nufi bedroom ɗunta ta kawanta , tanata tunanin maganar mahaifiyar tata.”

Tabbas inhar Haisam bai kwanta dani ba bazan sami gata ba dan nasan kaf danginmu babu wacce bata aihuwa , to yazanyi ?” kemis zani in siyo ƙwaya , janyo dogon hijabinta tayi ta sanya ta ciro ɗari biyar acikin jakarta ta fice tare da janyo ƙofar gidan , ganin kemis a kusa da su ba sai tasha wutaba yasa ta shiga ,Allah yasa babu layi , ta ce abata maganin tada sha’awa , ƙare mata kallo likitan yayi yace “baiwar Allah wa zaki bawa wanan maganin?”mijina tabashi amsa a taƙaice , mijinki kuma ba auran soyayya kukayi ba ?” Maimunatu ce ta dakatar dashi tare da cewa “kaga malam idan baka dashi kokuma bazaka bani ba in wuce ,wanan tambayar banga amfaninta ba , mai kemis ne yayi murmishi yace “karki damu indai magani ne zan baki , cikin zuciyarsa yace “wlh sai na shirya miki gadar mugunta da zaki sha wuya , sachet ɗaya ya miƙa mata yace ” kibashi biyu kekuma gobe kisha biyu ,to nawa ne ɗari biyar ,ya bata amsa cikin zumuɗi tace “inkasan wata bakasan wata ba wlh sai kazo da ƙafafuwanka kana haɗani da Allah , zanga ƙarshen taurin kai ,tana tafiya tana maganar shiko mai kemis tana fita ya tuntsure da dariya tana tafa hannu.”

Da fara’a ta shiga gidan kai tsaye ɗakin Haisam ta shige , ganin ruwan gora a gefe ga kuma fanta ta gora ansha ragowar zaiyi rabi yasata dan daƙa maganin ta juye a ciki ta girgiza ta ajiye ta fice , wanka tayi ta wanke kwanukan da taci abinci , shara ce dai Allah bai bata ikon yi ba,

Labari ya isarwa Afnan maganar bikin Haisam , tasawa kanta damuwa sosai momy ta sata a gaba da faɗa akan ta damu da Haisam shiko bai damu da ita ba , tun tana damuwa har tazo ta fara ragewa sbda dena tunanin Haisam zaiyi wuya ,taci kuka har ta haƙura , dady yanzu yafara kula Afnan ya canza mata waya ya bata kuɗi mai yawa tayi siyayya hakan tafara rage mata damuwa , Anty ummi rabonta da gidansu an daɗe , kasancewar tunda anty ta cimata mutunci ta tafi ranta a ɓace , yau tana son zuwa gidan su anty ummi tana tsoron tambaya dan dady ya hanata fita , harta fito da gyle ta maida tama haƙura da fita kwata kwata gashi yanzu batada number kowa ,

Salma ce ta shigo da sallama riƙe da Sudais a hanunta , da sauri Afnan ta fito tana cewa”oyoyo my sister cikin fara’a suka rungumi juna ,Salma ce ta ɗauki Sudais tana yimasa wasa , ƙarasawa Palorn momy sukayi , momy na zaune a kan kujera ta fara yimusu oyoyo , ganin yaran nata reras yasata sakin fara’a , Salma ce tace “momy yaushe Anty Afnan tazo ?”momy ce tace “ai ta kwan biyu takardar ta muke jira yazo ya bata , ashe ma har yayi sabon aure , riƙe haɓa Salma tayi tace “tun farko abinda nake faɗa muku kenan yanzu gashi ya maida anty bazawara , momy ce taja ƙwafa tace “ai yanzu komai ya wuce , baban farinciki na ma shine , batada ciki kina bazatayi wuyar samun miji ba ,✍️.

My fans banfa dawo ba kuyi haƙuri

????????????????????????????
???? ???? ????

LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!

     ????     ????     ????

????????????????????????????

Story and writing by

ZAINAB HABIB
{Mom islam}

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com
https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.

BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM

EPISODE 15 & 16

 Haka dai suka dinga hirarsu Anty ce ta shigo ta samesu a palo cewa tayi" aa saukar yaushe ?"Salma ce tace"Anty ban jima ba , gaisawa sukayi hira ta ɓarke tsakaninsu , wanda duk rabin hurar ta Anty Afnan ce , hakan ya sata ƙin kulasu dan inda abinda ta tsana bai wuce hirar Haisam ba ,sai yamma Salma ta fara shirin tafiya , momy ta bata turaruka da su zuma , kirane ya shigo wayarta , ganin number mijin yasata cewa "to drivern mu ya ƙaraso ,bata samu haɗuwa da dady ba hakan yasata tafiya tace "a gaishe shi, momy ce ta ƙwalawa Afnan  kira kasancewar ta koma ɗakinta , amsawa tayi ta fito , momy ce tace "zo kiyi wanka kiyi kwaliya dan Allah ji tsara kwaliyar  maiya faru momy ?" sai kin tambayeni ko kina ganin zan cutar dake ne ? a'a Afnan tace " ta shige toilet  tafara wanka da sabulun da momy ta bata mai ƙamshi , tana fitowa ta tarar da momy a ɗakinta da kaya a hannu  tana gama kwaliya tace "momy wanan kayan zan sa?"cikin fara'a momy tace "eh man ƴar albarka  karɓa Afnan tayi tasa momy ta miƙo mata sarƙa da ɗankunne da war waro , kana ta miƙa mata turare mai ƙamshi , feshe ko ina na jikinta tayi ta juyo tace "momy nayi kyau?".

“Sosai ma my daughter kinyi kyau , yanzu kinsan abinda nakeso dake? a’a Afnan tace “to baƙo zakiyi daga Kano zai zo nan Abuja so ina san ki tarbeshi da mutunci yaron abokin dadynku ne insha Allah Afnan tace “in ya iso zai kiraki a waya oky momy , jekisa a gyara ɗakin saukar baƙi , ficewa Afnan tayi dan isarda saƙon momy ,turare mai ƙamshi aka sanya a ɗakin , ƙarar wayar Afnan ce ta dawo da ita daga duniyar tunani sbda tana tunanin to shi waye kuma mezai kawoshi , inko soyayya ce hmm , amsa kiran tayi tare da sallama a bakinta , wa/alaikis salam barka taji ance daga ɗayan ɓangaren gimbiyar mata kuma sarauniya , gani gurin parking ɗin mota oky Afnan tace “tana shirin miƙewa , da fitarta ta hango wani kya kyawan saurayi lol to koma dai bazawari ne ,nidai ya yimin kama da saurayi , yana hangota ya haɗiyi wani miyau tare da magana a zuciyarsa , shin wanan bazawara ce ?”anya nifa naga kamar budurwa , ga tsayi ga kyau komai na jikinta mai ɗaukar hankali kai masha Allah ,kona aureta bazan haɗata da matata ba ????wai dama yanada mata ?”fans kuzo muji , sallamar da Afnan tayi ne yasashi daɗa ƙare mata kallo ,yana amsa sallamar yace “gimbiya sarautar mata kuma mata a gurin Abdallah , waro ido Afnan tayi tace “wanan kirari haka ?.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button