LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

Murmishin yaƙe tahau yimasa dan tana tunanin inhr yaga wanan photon to kashinta ya bushe , Abdallah mutum ne mai lura da ankara ,yana ganin Afnan na wanan yaƙen dariya ce kawai baiyi mata ba amma a zahiri baiyi mata kyau ba kuma ya fara tunanin da akwai abinda yake faruwa da Afnan taƙi gaya masa ne , kasancewar da abinda ya dawo dashi ,ya riƙo hannunta tare da rungumota suka nufi kitchen soyayyen dankalin data soya ɗazu ya zubo musu tana rungume a hanunsa suka dawo parlo a baki ya fara bata tanaci tana zuba shagwaɓa ,amma a ƙasan zuciyarta tana fargabar ranar da sharin wanan budurwa zai hau kanta , kawar da zancen tayi kar Abdallah ya ganota.”

Kwance yake yanata saƙa da warwara shin ko ya amince da maganar mama na auran Uwani ne ? wata zuciyar ce tace ” aikuwa da ka auri ciwon kai , dafe kansa yayi dan yama rasa tunanin me zaiyi wanan wace irin jarabwa ce ? ya tambayi kansa , tashi yayi ya dawo palo kallon palon ya shigayi yaushe rabonsa da shara , tsaki yaja kana ya koma bedroom ɗinsa ya shiga toilet ya watsa ruwa , yana fitowa ya zauna nanma dai tunanin ne ya addabi zuciyarsa , badan yaji ance Afnan tayi aure ba da babu abinda zai hana ya dawo da ita , wasu siraran hawaye ne suka zubo masa , sharewa yayi ya fara shafa mansa mai ƙamshi , bayan ya gyara sumar kansa ya feshe jikinsa da turare , yaje gaban drower buɗewa yayi ya tsaya a gurin yana tunanin kalar kayan da zai sa tuno kalar kayan da Afnan takeso yayi wato farin boyel da farar baƙar hula da takalmi baƙi sai agogo fari , bayan ya sa ne ya dubi kansa a mudubi yai wani murmishi wanda ya ƙara fito da ainihin kyansa can kuma ya dake tare da ɓata rai , to wa nayiwa wanan kwaliyar ? hhhh lol niko nace Uwani …key ɗin mashin ɗinsa ya ɗauka tare da rufo ƙofar ya nufi waje ,Faty da ta fito daga maƙota ganin Haisam ya tuno mata da Afnan hawaye tabb ƙwayar idonta ta shige gida ,Haisam bai lura da abinda ke wakana ba yaja mashin ɗinsa ya nufi gidansu mama , dan yanason zuwa gurin aiki da wuri.

Da isarshi anguwar tasu ya hango Uwani taci ɗamara tana shirin faɗa da wata budurwa wacce a shekaru ta zarce ta amma tana shirin faɗa da ita taɓɓ , Haisam ne ya jinjina kai kana ya tada mashin ɗinsa ya nufi gida , yana shiga ya sami baba a kan kujera ƴar tsugunno yana shan kunu , baba na ganin Haisam ya hau washe baki yana fara’a , durƙusawa Haisam yayi ya gaida baba amsawa baba yayi yace ka shiga ciki a zubo maka kunun naƙoshi Haisam yace ” tare da miƙawa baba dubu biyar , baba zai yi magana Haisam yace” baba kayi shiru kawai ,share hawaye baba yayi kana yace ” Allah yayi maka albarka Allah ya baka mata tagari Allah ya yalwata arziƙinka , dajin wanan adu’ar sai da jikin Haisam yayi sanyi sosai,

Saurin miƙewa yayi dan kar mama ta ritsashi a gurin , kasancewar da tazara kaɗan tsakanin gurin da baba ke zaune dakuma ɗakin mata , yasa Haisam wucewa can kukan Uwani ya jiyo da robar ɗibar ruwa yayi gashi robar a fashe ,dariya ce taso kuɓuce masa sai ya gimtse , Uwani ce ta kalli Haisam da yabata haushi a rayuwarta ta tsani abu ya faru da ita aƙi jajanta mata tace “ɗan yaya ɗan gayu wlh kayiwa wanan yarinyar magana dan ni ba sa’ar wasanta bace tamm,

Kallon inda take magana da girgiza yayi bai ce mata komai ba ya nufi ɗakin mama , shiga yayi ya zauna kasancewar ta shiga wanka , Uwani da baƙin ciki ya isheta kasa zama tayi a ɗakin tayo waje , mama ce ta hangota a zaune bakin ƙofa tana bubuga ƙafa alamun masifa , a ‘ a Uwani me kuma ya faru?” fashewa tayi da kuka tace ” ina cikin ɗibar ruwa a famfo shine wata gardiyar budurwa tazo ta janye bokiti na tasa nata ,shine nikuma na janye nata shine suka yimin taron dangi harda fasamun bokiti , Haisam tun yana dariya a ciki ciki bai sani ba ta yanzu harda ƙya ƙyatawa maganar yarinyar na sashi dariya

????????????????????????????
???? ???? ????

LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!! .

 ????   ????    ????

????????????????????????????

Story and writing by

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

????AREWA WRITERS ASSOCIATION????

EPISODE 45 & 46

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Mama ce ta shigo tace “wato kanaji tana kuka baka fita kaga wacce suke faɗan da ita ba ? sunkuyar da kai yayi tare da cewa mama ai tafi mai faɗan ƙarfi , hakan ya kuma tunzura Uwani tukuma fashewa da kuka ,

 Safiyar Laraba ƙarfe 7:am dai dai Afnan ta shiga wanka sbda zuwa ɗauko Sadiq tunda Abdallah ya lura da harda wanke kai zatayi dan yaga ta ɗauki shampo , ya ɗauki wayarta cikin azama yafara bincike ko ina na wayar gallery ya shiga , mai hankalinsa yayi ga hotunan wayar gana bikinsu gana ƙawayenta , gurin hotunan whtsapp ya shiga cin karo yayi da hoton ta daga ita sai pant da bra innalilahi Abdallah yace " ya cigaba da bincika wayar sai kuma ya ga hotonsu shida husna , kansa ya fara ɗaurewa a ina husna ta san numbar Afnan ? dama sunada alaƙa da ita ne ? komawa whtsapp yayi anan yaci karo da lambar Husana sbda ya haddace ta a kansa ba tun yau suke tare ba, gir giza kansa yayi tareda cije lips ɗinsa , yasan sharrin Husna fitowar Afnan ne ya sanyashi ƙare mata kallo dan ya riga ya ajiye wayar bayason ta fahimci akwai wata matsala , janyota yayi ya kaita gaban drees mirror ya zaunar da ita gaban stool ya shafa mata mai kana ya shafa mata hoda , taƙi sakewa dan tana tunanin yaga pic ɗin , 

Kasancewar yayi nashi wankan bayan ta gama shiryawa suka fito dama driver ya shirya suka ɗauki hanya direct gurin da Sadiq yayi musu kwatance suka tsaya , Abdallah ne ya ƙara kiransa yace ” sun ƙaraso , daga can ɓangaren Sadiq ya ratayo school bag ɗinsa ya fito bayan ya bada keys ɗin ya nufi bakin get , yiwa mai gadi sallama yayi ya buɗe murfin get ɗin , hango motar dadyn yayi ɗan nesa da da get ɗin , ya ɗanyi tafiya mai tsayi kana ya iso , ba tare da yayi magana ba ya buɗe gidan gaba ya zauna yai kicin kicin da rai ,

Afnan ce tace ” ayi mana afuwa , Sadiq dake cika yana batsewa ya dubi side ɗin da dadyn ke zaune yaga bama tashi yakeyi ba , dane danen wayarsa yakeyi hawayen da bai shirya zubowarsu bane suka zubo masa , sharewa yayi ya maida hankalinsa ga kallon titi ,Abdallah ko yana kallon Sadiq duk wani abu da yakeyi yanzu kam ya fiddashi daga cikin jerin ƴaƴansa , tabbas Sadiq baiyi kama da jininsa ba , suna cikin tafiya naji Abdallah yace ” driver juya zuwa wancan titin kaf ɗinsu ba susan ina zasuje ba hakan yasa kowa yai shiru ya zubawa kwalta ido tunda suka shiga layin gabab Sadiq ke faɗuwa , Abdallah ne yace ” is ok bayan driver yayi parking suka fito banda Sadiq da ya zauna bama shida niyar fitowa.”

Wata tsawa Abdallah ya daka masa mai firgitarwa , ba ƙaramin firgita Sadiq yayi ba dan a iya saninsa dadynsa baya ko yimasa kallon banza bare wanan tsawar a tsorace ya fito , shima driver dake gefe lamrin ya matuƙar bashi mamaki dubada irin soyayyar da Abdallah ke yiwa ɗan nasa katse tunanin yayi dan yaga sun shige ciki Sadiq ne a baya kamar wanda aka doka , dan ya firgita matuƙa ,  Gidane dai dai misali bazaka kirashi da gidan talakawa ba ,zadai ace gidan masu rufin asiri gidane mai ɗauke da ɗan madai daicin get sai filin tsakar gidan da yake malale da siminti daga can ɓangare hagu wani kasko ne guda biyu masu flawoyi ,ƙofar da zata sadaka da sashe matar gidan itace ƙofar dake kallon ymma kasancewar ƙofofi biyune kusan a jere , babu sashin da Abdallah bai sani ba dan haka ya shige ƙofar dake ɓangaren dama suma suka rufa masa baya , da sallama a bakinsu suka shige matar gidan na tsakar gida tana wanke wanke ta ga su Abdallah , washe haƙora tayi tare da cewa" lalle marhabun barkanku to kai Sadiq ka shiga dasu man jiki a sanyaye Sadiq yayi musu jagora zuwa babban palon gidan , zaune take a cikin ɗaki a gefen katifa taci kuanta ta godewa Allah musamman da sukayi waya da Sadiq ya faɗa mata a hotel ya kwana ta razana sosai , jiyo muryar mamy na kiran sunan Sadia yasata aiyanawa a ranta cewar ai harda Abdallah ma , 

Miƙewa sadiq yayi yahau bankaɗa labule yana duba islam wato autar mamy , bankaɗo na ɗakin da momynsa ke ciki yayi da sauri ya isa gareta ganin hawayen fuskarta yasa shi fara shre mata hawaye ,

Afnan dake zaune gefen Abdallah da sai yanzu ta sami damar yin mgna tace ” ina mukazo ? gidansu momyn Sadiq ya bata amsa a taƙaice , jan bakinta tayi tai shiru kana ta zubawa sarautar Allah ido , mamy ce ta shigo hannunta ɗauke da jug na ruwa da food flaks na abinci ajiywa tayi a gaban su Sadiq kana ta zauna kujera mai kallon tasu , sauka yayi daga kan kujerar yace ” mamy barka da yamma mamy ywwa barka ya gida ya aiyuka lpy lou Abdallah yace” Afnan ma gaisheta tayi kana shiru ya biyo baya , Abdallah ne yace ” nakawo Sadiq ne , da alamun damuwa mamy ta dubeshi tace ” Abdallah naji duk abinda ke faruwa yanzu dai inason kayi haƙuri dan Allah banda tone tone , sunkuyar da kai Abdallah yayi yace ” mamy momyn Sadiq bata kyauta min ba wlh eh nasani , labarin bashida daɗin sake mai maitawa dan Allah kadubi darajar maraici ka maidata ɗakinta , Afnan sai yanzu ta gano abinda ke faruwa cikin sanyin murya tace “dama bakwa tare da mmn Sadiq? ko kulata bai yi ba shigowar momyn Sadiq da Sadiq ne suka shigo palon .”

 Kallonsa ya kai gareta kana ya sada kansa ƙasa dan jiyakeyi kamar yaharbeta amma bashida mafita , kuma yana tausayawa rayuwar mutanen gidan kasancewar su masu ɗan ƙaramin hali , gashi mamy nason matsa masa oh Allah Abdallah yace " lokacin da yakai dubansa ga Sadiq ya kauda kansa gefe , shikam ya tsani zina kokuma ɗan zina ,sake kai dubansa gurin mamy yayi kana yace " da sharaɗi inhar ta amince bazata jemin da Sadiq gidana ba , wata razananniyar ƙara yasa tare da cewa" to waye mahaifina ki nunamin ."

Muryar Sadiq sukaji Afnan ce ta miƙe tare da riƙo masa hannu , cikin kakausar murya Abdalah yace " karki kuma gigina taɓashi ba jinina bane !!! timmm mamy ta faɗi sumammiya , da sauri Afnan da momyn Sadiq sukayi kanta mai adu'a nayi mai ɗibo ruwa nayi ,duk da haka Abdallah bai dena zazzaga bala'i ba , momyn Sadiq ce tace "inhar kazo kawomin shi ne to , inkuma kazo tayar mana da hankali ne sai ka faɗa , Afnan dai lamarin ya ɗaure mata kai ta rasa wane lamari ne ke shirin faruwa da rayuwarta ?" a zuciyarta take wanan batun , eh duk inda kika ɗauka haka ne , cewar Abdallah dan zan temaka na maidake wlh bacin tausayinki da nakeji babu abinda zai sa na maidake !!!, mamy na farfaɗowa ta tsinkayo maganarshi ta ƙarshe , cikin dauriya dajin zafin kalamin nasa tace " Abdallah abin bai kai ga haka ba mungode basai ka mayarda ita gidanka ba , daganan ta shige ɗaki , dukaninsu suna tsaye Sadiq ko yabi mamy ɗakinta

????????????????????????????
???? ???? ????

LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!! .

 ????   ????    ????

????????????????????????????

Story and writing by

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

????AREWA WRITERS ASSOCIATION????

EPISODE 47 & 48

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Afnan da tun usulinta batason tashin hankali tafara kuka tare da durƙusawa a gaban Abdallah ta riƙo masa hannu , kana tace ” dan darajar iyayenka ka kaida ta , bai yi magana ba sai ficewa da yayi daga ɗakin , momyn Sadiq kasa magana tayi sbda baƙin ciki Afnan ce ta rungimeta suka dinga kuka, bayan fitarsa driver ya shigo a guje tare da cewa hajiya mai gida na mota yana jiranki ,sallama tayi musu kana ta rufawa mai gadi baya , buɗe murfin motar tayi ta shiga suka miƙi titi , babu mai cewa kowa komai , shikam zuciyarsa tafar fasa takeyi kamar garwashi gaskiya da ba zina tayi ba zai iya mai data amma tuna abin ya kasance da haka yana ganin sai dai su haƙura kawai , horn ɗin da driver yayi ne ya tabbatar musu da cewar sun iso gida , buɗe murfin motar tayi da sauri ta fice tana kuka , tana shiga palo ta wuce bedroom ɗinta da gudu ta faɗa gado tana wani irin kuka mai cin rai , ita kam tafi tausayin Sadiq ɗin a kan mahaifiyar tasa , can kuma wata zuciyar tace ” ke meye naki na tausayin sa bayan bakida alaƙa dasu? gaki a cikin matsala ,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button