LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

Ad
_____
Kawar da zancen tayi ta ษauko wayarta , lambar momy ta dannawa kira ring ษaya ta ษauka , sallama Afnan tayi bayan momy ta amsa Afnan tace “ya dady da anty suna lpy momy tace .
“lafiyarki kuwa Afnan?” naji muryar taki tayi kama da ta mai kuka , kuma dai dai ta muryar tayi kana tace ” llah momy wlh ba komai nayi missing ษinku ne inason zuwa , momy ce tace ” to shine zaki ษata ranki ? ki kwantar da hankalinki muna lpy karki dinga tada hankali kinga ba ke kaษai bace , waro ido Afnan tayi kana tace ” momy nikaษai ce man au wai kun ษauka cikine da ni ? eh momy tace ” hmm wlh banida komai , cewar Afnan , momy ce tace ” Allah zai kawo ki kwantar da hanlalinki kinji , to tace ” tayiwa momy sallama , numbar anty ummi ta kira dan tasan tayi laifi yaushe rabon da suyi waya.”
Lokacin taga gidan Haisam tana cin azaba gurin mama batada wata uwa banda anty ummi yanzu kuma da ta auri burin iyayenta shine zata watsa mata ฦasa a ido ina , jin an ษaga wayar ya sata cewa aslamu alaikum , daga ษayan ษangaren anty ummi tace " walaikissalam Afnan kinanan? uhm anty da farko dai ayimin afuwa dan Allah , nasan ban kyauta ba , share zancen anty tayi da cewa karki damu yarinyata ,
nan suka kuma gaisawa kana sukayi sallama , turo ฦofar da Abdallah yayi ne yasata kai dubanta ga inda ya ke , tsaye yake a bakin ฦofa ya zura hannayensa cikin aljihu , ya kallonta.
Zaune suka a wani tsararren palo wanda yaji kayan more rayuwa wannan palo shine zakaji ana yiwa kirari da aljannar duniya , hajiya Maryam ce zaune kusada mai gidan nata wato Alhaji Aliyu mai nera , Alhaji Aliyu mai nera shaharaten mai kuษi ne na ji da gani , sananne ne kowa ya sanshi a babu wanda zaka yiwa kwatancen sunansa yace ” bai sanshi ba , shine uba ga Husna ฦดa ษaya tilo da Allah ya basu ,Husna tayi karatu sosai musamman ma na boko , har yanzu taฦi fito da mijin aure da zarar Alhaji yayi magana mahaifiyarta zatace guda nawa take karya takura mata , akwai wata rana tana cikin tafiya a motar ta , sai motar ta sami matsala , tana tsaye bakin titi motar Abdallah tazo wucewa , bayan ta sa masa hannu alamar ya tsaya ta roฦesa da ya temaka ya rage mata hanya zuwa gidansu,
Suna cikin tafiya tana satar kallonsa dan Abdallah kyakyawane in baku manta ba , suna isowa tace " ya bata lambarsa , baiyi mata musu ba ya bata har ya zamo daga wanan rana tana kiransa suna gaisawa , kwanci tashi asarar mai rai , Husna ta fara nunawa Abdallah tsantsar soyayya tun bai san tanayi ba har yazo ya gane , wata rana yazo gidansu badan yaso ba sai cewa da tayi zasu gaisa da mahaifiyarta , yake gaya mata shikam yanada mata , Husna tayu baฦinciki amma kadancewarta wayayya ta nuna babu komai gashi yac" bai shirya yin aure nan kusa ba , itadai a tata zuciyar ta ฦudiri aniyar auransa ko ta wane hali wanan kenan.
Alhaji ne ya dubi Hajiya Maryam yace ” lokaci yayi da zan fitarwa da Husna mijin aure sbda lokutan da na ษaukar mata sun cika , kukan da Husna ta fara ne yasa su Alhaji juyowa kallonta , kuma bai fasa maganar ba , Hajiya Maryam ce tace “a wanan karon ina goyon bayanka ai tanada samarin ruwan ido ne yasa take rainawa mutane hankali , Husna batada zaษi banda dole ta karษi zaษin iyayenta amma kuka yaci ฦarfinta ,tashi tayi da gudu ta haura samma inada ษakinta yake , ta faษa gado tare da sakin wani sabon kukan , tunanin Abdallah da yayi mata nisa tafara yanzu yazanyi duk wata hanya da zanbi dan haddasa musu fitina na kasa dole nabi abinda su hajiya sukeso , da haka bacci mai nauyi yayi nasarar ษaukarta .”
Abdallah ne ya ฦaraso kusa da Afnan ya ษauketa ya ษora akan cinya kamar ฦaramar yarinya , raษa mata yayi a kunne wai two days mai ya sami baby na ne tadena bani kulawa ?” narkewa Afnan tayi kana tace ” nikam babu ruwana da kai , mekuma nayi ? cewar Abdallah , Afnan ce tace ” dan me bazaka dawo da matarka ba ?” walwalar fuskar Abdallah ce ta gushe ya kalli Afnan yace ” zaki iya zama da miji mazinaci ? zaro ido tayi tana kallon Abdallah da idonsa ya ciko da ฦwallah tare da girgiza kai , to inhar bazaki iya ba karki ฦara yimin zancenta akwai maza a duniya bani kaษai bane autan maza ya kamata kisani babu ni babu momy sadiq!!!!!.
Jin zancen nasa babu daษi takeyi amma babu inda zatayi dole ta kawar da zance dakuma tinanin momy Sadiq ta rungumi mijinta , rungumota yayi yana shafa mata gashin kanta tare da murza ฦดan yatsunta , itama fara yimasa wani salo tayi na daban dama tayi amfani da maganin da momy ta bata , tunda naga Abdallah ya fara harata yasani rufo musu ฦofa nayo waje.
Yau Afnan ta tambayi zuwa gida , daฦyar Abdallah ya barta amma da sharaษin karta daษe, tun safe tayiwa momy waya akan gatanan zuwa , kowa na gidan murna yakeyi dan an daษe ba’a haษu ba , momy tasa an shirya mata abinci kala kala, dady ma yau bai fita ba sbda yanason su gaisa da ฦดarsa ,
Abdallah na fita ta fara shiri tana gyara gado taci karo da kuษi masu yawaa tunani ta fara ko Abdallah ya mance dasu ne , ring ษin wayarta ne ya katse mata tunani , Abdallah me mai kiran amsawa tayi tare da cewa ka isa lpy , lpy lou sweety ina kewarki dariya Afnan tasa tare da cewa " kai mijina daga fitarka ? eh man Afy jinake kamar in dawo , zaro ido tayi kamar yana ganinta tasan inhar sukaci gaba da maganar zai iya dawowa yayi mata haramiyar zuwa gidansu , am sorry Allah ya dawomin dakai lpy mijina akwai tanadin da nayi maka so karkaji komai , nidai fatana karka bari ฦดan mata su kallemin kai , dariya sukasa a tare kowa ya ajiye wayar , dafa ฦirjinta tayi kana tace " my man rigima , tacigaba da shirinta
๐ฆ๐น๐น๐น๐น๐น๐ฆ
๐ ๐ ๐
LAMARIN ฦADDARAR AURE NA!!! .
๐ ๐ ๐
๐ฆ๐น๐น๐น๐น๐น๐ฆ
Story and writing by
ZAINAB HABIB
(mom islam)
My wattpad momislam2020
My telegram link
Zainabhabibu713gmail.com
๐ฆAREWA WRITERS ASSOCIATION๐ฆ
EPISODE 49 & 50
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Biki ya kankama na Haisam da Uwani kasancewar mama tace ” inhar yabarta to yabar mata , badan yaso ba ya amince da abinda takeso tunda bazata fasa ba , fatanshi dai Allah ya sanya musu albarka shikenan , hidindimu akeyi sosai sbda yanzu Haisam kuษi sun zauna masa ba laifi harya siyi mota mai kyau ya kuma sauyawa gidan nasa fenti komai dai yayi masha Allah ,
Dama tunda iyayen Maimunatu suka zo suka kwashe kayanta ya kulle ษakin sai yau da za'ayiwa ษakin fenti ya buษesa , kowa sai sam barka yakeyi amma ana cece kuce akan amarya ,ranar ษaurin aure kowanne na dangin mama da magoya bayanta suna farinciki sosai , da yamma za'a kai Uwani tunda taji alamun zuwan motoci tafara kuka ita bazatabi wancan mugun ba , karyazo yana yimata mugunta , kowadai lallaษata yakeyi tunda Uwani dole sai lallaษo , tun a mota take rafka salati da koke koke kamar wacce za'a kai gidan yanka , ana isowa ฦofar gidan nanma sai da aka ririฦeta tana neman guduwa ,
Mutane sunga tashin hankali , faษa aka yimata mai shiga jiki duk rashin kunyarta sai da jikinta yai sanyi , musamman da aka cemata banda yiwa mijinki musu banda yimasa rashin kunya , kasancewar tana tsoron ace wutar jahannama yasata yin laushi da duk wata masifa tata , haka suka tafi suka barta tana kuka , amma a ฦarฦashin zuciyarta tsoron Haisam ne fal.
misalin ฦarfe goma da rabi kowa ya watse sai raba ido takeyi tana daga zaune a tsakiyar gado taji alamun turo ฦofa, shi kaษai ne sai wata ฦatuwar leda dake hanunsa , gyata zaman ษan mayafin tayi kana ta kalli ledar Allah yasa kazace , Uwani tace ” lokacin da ta haษiyi wani mugun yawu , zama yayi bakin gado tare da cire agogon hanunsa ya miฦe , Uwani tashi muje muyi sallah sai da taษan harareshi kana ta miฦe , kunsan dai mai hali baya fasawa amma a tunaninta ta rage rabi ,
Bakinnan kamar wanda aka ja dan fushi ita ba sallar bace damuwarta cin kazar shine matsalar ta , tana yin alwalalr ta dawo ษaki ta zauna gefen gado , Haisam na shigowa yace ” tashi muyi sallah ko kulashi batayiba ta miฦe sukayi sallahr ya shafa kanta yayi mata adu’oi kana yayi mata ฦดan tambayoyi game da tsarki dakuma wanka da alwalah , ba laifi tayi koฦari ta wanan fanni.
Jira take sai kuma taga ya miฦe ya ษauko plet da wuฦa ya baje kazar gata ฦatuwa , wani yawu takuma haษiya , so takeyi taji yace ” mata sakko kuma badan yau sabuwar kunyarshi takeji ba da babu abinda zai hanata daka wawa, sai da ya tsiyaya mata milk a cup kana yace ” bismillah har sikel na harษeta ta sakko ta zauna ko irin yangar nan babu tafara bawa cikinta tanayi tana lumshe ido mamaki ta bashi, sai ya tuno darensu na farko shida Afnan lokacin da ya shigo ฦin buษe fuska tayi kuma da ฦyar taci kazar bawata mai yawa taci ba amma ita wanan ko na bakinta bata gama ci take ษaukar wani.
Tsayawa yayi kallon ikon Allah bata damu da rashin cinsa ba sai suษe hannu takeyi, da ya gaji da dane dannen wayarsa ya miฦe ya nufi ษakinsa , a gajiye yake hakan yasashi kwanciya ‘a madai daicin gadonsa bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi .
Saida takusa cinye kazar sanan ta ajiye ragowa a kan table taje ta faษa gado tana tsalle ashe haka aure yake tabb shine naketa kuka , yasin danasan kullum haka za adingayi da ban tada hankali ba , naci ta yau saura ta gobe yasin su inna zasu ganni nayi mulmul , dahaka itama bacci ya sureta .
magunguna momy ta haษawa Afnan sbda momy mace ce mai son taga ta mallaki zuciyar miji bata hanyar boka ba , ta hanyar magunguna da turaruka ,da kissa hakan yasa dady yafi sonta itako anty bata ganewa maganin mata kasancewarta bata jituwa da magani shiyasa take masa kallon ko in kula , wasu zafafan turaruka momy ta haษawa Afnan a wata ฦดar leda kana ta ฦara da ce mata kartayi wasa da shan magani dakuma kula da abubuwan da mijinta yakeda buฦata , karkuma ta zamo mai ษaga murya akan ta mijinta ta zamo mai tausayi da iya kallo dakuma iya tafiya , ta ฦara da cewa ” ta yawaita amfani da turaruka masu daษin ฦamshi karta dinga barin kanta yana daษewa batare da ta wankesa da shampo ba .
godiya Afnan tayiwa momyn ta , momy ce tace ” bawai na gama bane , abu na gaba inaso kisan wani sirri shi namiji inda kika juyashi haka zai biki tausayi fara’a iya kallo iya tafiya dadaษan kalami uwa uba kuma ษaukar wanka da iya kissa ,karki zamo kina zama nesa dashi a yayin da kuke tare ki zamo masa tamkar yayayyar yarinya ina fatan duk waษannan abubuwan sun shiga kunnenki ,zuwa gaba zan baki wasu muhimman sirrukan , yanzu miฦomin wancan zumar , miฦewa Afnan tayi ta kawowa momy zumar momy ce ta buษe tare da cewa ki kafa kanki ki shanye ki ษauko madara a store ki fasata itama ki shanye , akwai dabino a wanan kwanon ki ษibo kici shima yana temako sosai basai na fayyace miki komai ba.
Ad
_____