LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

Zama tayi jugub a kujera tana share gumin da yake karyo mata tare da mai maita innalilahi a zuciyarta .

Abdallah wayarsa ya ciro yafara danne danne amma inka lura dashi sosai hankalinsa a tashe yake ,

Ko kaɗan bata ƙaunar taji yayi mata magana hakan yasata miƙewa ta nufi hanyar da zata sadata da bedroom ɗinta keee!!! taji Abdallah yace ” cikin tsawa juyowa tayi batare da tace “komai ba ,

Kuma maida hankalinsa kan wayar dake hanunsa yayi a zahiri kukan zuci yakeyi dan nafili yaƙi fitowa .

Takai wasu mintuna a tsaye a gurin dan yanzu tsoransa ma takeji kar tayi ƙwaƙwaran motsi ya yanke mata mumunan hukunci,

Tashin hankali gami da rashin ƙaunar maman sadiq ya darsu a zuciyar Abdallah ,mai maicin da zuciyarsa take yimasa shine zina ?zina tayi kenam ba ɗana bane ?” ya ilahi ya riƙe kansa da yake sara masa.”

Ya ɗago kansa ya dubi maman Sadiq yace “naji duk abinda kuke ta taunawa akai dame na rageki ci ko sha ko tufafi kokuma haƙinki ne bana saukewa kiji tsoron Allah ,

Yaci gaba da cewa kin cuceni kin cuci ɗanki dan bazance ɗana ba ,

Momyn Sadiq jira take taji kalamin Abdallah na ƙarshe yace ya yafe mata sai taji akasin hakan yace ” na sakeki saki biyu inkin sami miji kiyi aure kuma ki tafi da ɗanki banida alaƙa dashi…..✍️.

Fans kuyi haƙuri kwana biyu kunjini shiru nayi tafiya ne amma na dawo ganin sharhinku shine zai sa kusami pagin gaba amma in bangani ba sai bayan sallah gaskiya ????.

????????????????????????????
???? ???? ????

LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!! .

 ????   ????    ????

????????????????????????????

Story and writing by

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

WANAN LITTAFI GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA SHUGABA

(ANTY HAUWA MAMAN USWAN)

ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA

????AREWA WRITERS ASSOCIATION????

EPISODE 33 & 34

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Kasa tsayuwa tayi a gurin saboda wani jiri dake ɗibarta ta durƙusa kan guwaiwar ta tana kuka mai tsuma zuciyar mai karatu oh ni ƴa su ina zansa kai na ,rarrafowa gabansa tare da sunkuyar da kanta ƙasa tace “dan darajar iyayenka ka yafemin wlh ba ‘ason…!!! wani wawan mari ya wanketa dashi kana ya miƙe tsaye yace “kar in dawo in samu kina gidannan wlh sai kinyi dana sani , ya fice zuciyarsa na suya , driving yakeyi amma hankalinsa a tashe yake ,ikon Allah ne ya kaishi gida , ko horn baiyi ba ya buɗe murfin motar ya fice tare da buɗe get ɗin , mai gadi dake zaune a wata farar kujera ta roba ganin Abdallah ya shigo a fusace ya miƙe yana cewa Alhji barka dai ywwa kawai yace .”

Bai jira ƙara jin wata maganar ba ya shige ciki , mai gadi ne ya jinjina kai ya ƙwalawa driver kira da sauri ya taho sabda shima ya lura da yanayin Alhajin .”

Wangale get ɗin yayi ya shigo da motar, sukazo suka zauna kafa hirar shigowar uban gidan nasu ,

Bai sameta a palo ba ya nemi guri ya zauna , kashe tv da yaketa ƙararsa shi kaɗai yayi , ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya abubuwan da suka faru tsakaninsa da momyn Sadiq suka fara dawo masa ..

Cikin zuciyarsa yace ” ko kaɗan banyi dana sanin rabuwa dake ba dan bansan ko bada ni kaɗai kike taraiyya ba .

Shigowar Afnan ce ta sanyashi katse tunanin tare da faɗaɗa fara’arsa irin karta gane yana cikin wani hali , takowa takeyi cikin isa da ƙasaita ,
kai kace ƴar wani sarkin ce .”

Zama tayi gefensa tare da ratayo hanunta a kafaɗarsa tace “lafiya mijina ? naga kamar kana cikin damuwa ” a’a Afy kaina ke ciwo yanzu ma so nakeyi na ɗan kwanta ..

Badan ta yarda ba ta ƙyaleshi amma ta fuskanci akwai abinda yake damunsa jikinta a sanyaye tayi bedroom ɗinta ta fashe da kuka ,

jiyo kukan yayi lokacin da zaiyi hanyar bedroom ɗinsa ya dawo zuwa ɗakin nata , dole ya jata gado ya rungume ta yana jijiga ta kamar baby har bacci yai gaba da ita .

Ajiyar zuciya ya sauke can kuma sai wasu zafafan hawaye suka sauko daga idonsa , kallon sa ya kai ga Afnan dake ta bacci hankalinta kwance amma fuskarta duk alamun hawaye gasunan ..

In ya tuna Sadiq ba ɗansa bane sai ya saki wani mahaukacin kuka mai ban tausayi , yana cikin hakan ne yaji ring ɗin wayarsa ..

Kasancewar ya bar wayoyinsa a palo ya miƙe a hankali ya isa gurin wayar da ɗaga warsa, my son yagani sai da yakuma zubar da hawaye sanan ya ɗaga wayar, kafin yayi magana yaji Sadiq yace “dady na koma school fa gashi yanzu banida wasu kuɗi a hanuna , jimm Abdallah yayu can kuma yace “zan tura maka zuwa anjima inna fita , nagode dady Sadiq yace ” lokacin da Abdallah ya jiyo ƙarar tafi da dariyaku ya kashe wayar , kirane yakuma shigowa a karo na biyu Abdallah ya ɗaga a fusace yace “wai lafiya ?am dady wayar momy ce tun jiya a kashe dan Allah in kuna kusa ka bata , bana kusa Abdallah ya bashi amsa a taƙaice ya kashe wayar duka ma.”

Lefin momynsa yana neman shafarsa ko da yake yanata shawara da zuciyarsa akan ya fito ya faɗawa Sadiq ba shine ubansa ba sai kuma ya kawar da tunanin , ya shafe mimtuna a gurin yanata tunani iri iri amma babu wata mafita da yaga ta dace , kwanciya yayi a doguwar kujerar tare da ɗaga kansa sama , yau ɗinnan a tunani ya ƙare , bayan Afnan ta tashi tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga baƙa mai adon faraten dutsina ba ƙaramin kyau tayi ba , samun Abdallah tayi kwance a palo bacci ya ɗaukesa gashi lokacin ƙarfe shida na yamma , kasa tashinsa tayi kwai ta miƙe tayi hanyar kitchen,

Abinci mai sauƙi ta yi doya da miyar ƙwai dan yau tunda taga mai gidan babu walwala take jinta babu daɗi , tana gamawa ta dawo palo ta zauna gefensa tana shafa fuskarsa a hankali , buɗe ido yayi yana salati “ana kiran sallah fa , oky yace “tare da miƙewa ya nufi hanyar toilet , bin bayansa da kallo tayi tana mamakin sayawarsa daga fitarsa zuwa yanzu , kodai wani ya ɓata masa rai ne ? ta tambayi kanta , dawowarsa ce yasata ɗago kai tare da cewa Allah ya tsare amen yace “yasa kai ya fice….✍️.

Babu sharhi ?????.

????????????????????????????
???? ???? ????

LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!! .

 ????   ????    ????

????????????????????????????

Story and writing by

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

WANAN LITTAFI GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA SHUGABA

(ANTY HAUWA MAMAN USWAN)

ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA

????AREWA WRITERS ASSOCIATION????

EPISODE 35 & 36

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Washe gari safiyar litinin (monday) Maimunatu ta tashi da wani matsanancin ciwon mara da baya , jin shiru har ƙarfe takwas bata fito ba yasa mama nufar ɗakin , jiyo nishin Maimunatu yasa hankalinta mugun tashi ta shigo a guje , ganinta tayi durƙushe tanata juyi idanunta sunyi ja , subhannallah mama tace " tare da kamo mai munatu ta gyara mata tsuguno , yau kam babu magana kuma bata yiwa mama musu , ganin abin ya wuce tunani gashi dai alamun aihuwar ce amma har yanzu shiru , sake Maimunatu tayi ta wuce ɗakin Haisam dake bacci ..

Bugun ƙofar takeyi tana ƙwala masa kira , a tsorace ya taso ya buɗe ƙofar yace "lafiya mama?" inafa lafiya maza fito kazo ka ɗauko mashin ɗinka muje asibiti wanan yarinyar inaga aihuwa ce , ai dajin tace aihuwa ce yasashi azamar sauya kaya ya fito da sauri mama ta kwaso kayan yaro , kasancewar ba zaman daɗi sukeyi dashi ba amma yana siyo kayan jarirai , kai tsaye suka nufi asibiti ,da isarsu aka wuce ,da Maimunatu ɗakin aihuwa ..

Mama da Haisam sun zuba tagumi kawai jira suke suji ance ta aihu ,

Ɓangaren Maimunatu likitoci ne zagaye a kanta sunata aiki ,itako batasan inda kanta yake ba ,adu’a sukeyi duk wacce ta faɗo musu amma kaf ɗinsu hankalinsu ya fara tashi , tun ƙarfe tara na safe gashi yanzu ƙarfe biyar na yamma , wata likita ce ta fito fuska babu walwala ganin hakan yasa mama miƙewa da sauri Haisam da bai san ko mai ke faruwa shima ya miƙe , hango likitar yayi ta doso gurin su …

Tun a zuciyarsa yafara mai maita innalilahi haka mama itama , likitar ce tace “waye mijin Maimunatu a nan ko kai ne ? ta nuna Haisam ,cikin tashin hankali yace ” nine ok “kazo office munason ganinka , to Haisam yace “jin ba abinda yake tunani bane yasashi sakin fuskarsa ,

Da sallama ya shiga ya nemi guri ya zauna likitar da tazo ta kirashi ne takuma cewa malam muna mai baka haƙuri akan rashin matarka , a razane Haisam ya miƙe daga zaman da yayi yace " ban gane ba ?".

Kina nufin Maimunatu ce ta rasu ? wani doctor dake gefe tunda Haisam ya shigo bai ce komai ba yace ” abokina kayi haƙuri kulli nafsin za’ikatull maut kayi haƙuri adu’arka take buƙata ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button