Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

Ad

_____

Afnan ce ta koma d'aki rik'e da kumatu tana kuka , janyo akwatin ta dake saman durowa tayi tafara loda kaya , sai da ta cikashi tabb sanan ta d'auki hijab d'inta ta fito waje , kulle gidan , ta mik'awa Fatima mukulli Fatima da ganinta tace ”ina zuwa kuma yau , Afnan na kuka tace ”zani gidan iyayena , bazan zauna ba , Fatima cikin tausayawa tace ”karkitafi bada izinin mijinki ba ,girgiza kai Afnan tayi tace ”karkiyimin haka ,iya hak'uri nayi to yau nagaji da zagarmin iyaye da akeyi wlh , babu inda Fatima ta iya ,sabda tasan iya hak'uri Afnan tanayi , an k'ureta ne , haka ta k'ar6i mukullin ta janyo hijab a igiyar shanya tabi bayan Afnan , mashin ta tara ,sai da ta d'ora akwatin sanan ta hau tana d'agawa Fatima hannu ."

Mislin k’arfe goma na dare Haisam ne ya keta bubuga k’ofa amma shiru , cikin mamaki ya nemi guri a kan mashin d’insa yana jira Afnan tazo ta bud’e masa , yasan dai bata bacci sai ya dawo , sallamar da yaji ne ta katse masa tunaninsa , mijin Fatima ne ya mik’a masa hannu .”

Bayan sun gaisa ya mik'a masa mukulli , cikin rashin fahimta Haisam yace ”wanan mukullin kamar na gidana ?"mijin Fatima ne yace ”eh shine mai d'akin naka ce tabawa Fatima tabaka , ran Haisam babu dad'i ya kar6i mukullin ya bud'e gidan , shi ko lura ma baiyi ba gidan da kwad'o sai yanzu ."

 Shiga da mashin d'in yayi ya ciro wayarsa a aljihu , ya danno lambar Afnan , jiyayi ance a kashe take , cikin tashin hankali ya bud'e parlorn ya shige bedroom d'insa , zama yayi a bakin katifar tasa cike da tunani , tun zamansu da Afnan bata ta6a tafiya anguwa bata sanar masa ba , to anya yau lafiya kuwa?" sai sak'e sak'e yakeyi a zuciyar sa , tun a hanya yakejin yunwa ,amma da yashigo yaga gidan babu gimbiyarshi yasashi ,jin komai ya ishe shi , ya had'e kai da gwuwai wa ."

FARKON LABARI
Afnan yarinya ce ga Alhaji Nasir , Alhaji Nasir yanada arzik’i dai dai gwar gwado , zuwa makkan shi sau biyu , yanada mata biyu , da Hajiya Zainab da Hajiya Wasila , Hajiya Zainab tanada yara biyu ,da Afnan da Salma ,Hajiya wasila nada yaro d’aya babba mai suna Usman ,duka yaran nasu sun girma kuma suna gidan aure , Alhaji Nasir yanada zafin rai sosai kuma ba kasafai yakeson ana kawo complain d’in yaransa ba , inhar kunason zaman lafiya dole kaso yaransa koda sunyi abin rashin kyautawa, kowace a cikinsu na k’ok’arin ganin sun kyautatawa y’ay’ansu ,amma baya gani , yanada wata yaya mai suna Anty Aisha , bata k’aunar matanshi ko kad’an ita kuma Allah bai ta6a bata aihuwa ba , ta tsani taga y’ay’an mutane , kuma a hakan tasami shiga , a gurin Alhaji Nasir .”

Kuma shawarar ta tana aiki sosai , acikin y'a y'anshi Afnan ce bata auri mai kud'i ba , kasancewar batada hangen nesa , kuma Allah ne ya had'ata da Haisam , a gurin wani biki da sukaje , shekaru uku da suka wuce , na k'awarta , yanayin kamun kanta yasa Haisam jin yana sonta , sun dad'e suna soyayya , kuma a soyayyarsu sunci karo da mahassada da makusa , kaf cikin dangin ,dadynta da Hajiya Zainab da Hajiya Wasila babu mai son auran , hakan yasa duk wuyar da takesha bata magana ,saboda tasan babu mai temaka mata , wata k'awar mahaifiyarta mai suna anty Ummi 'itace mai zuwa gidanta ta kawo mata abubuwan da zasu amfaneta ,kuma take tambayarta matsalar ta ,itama Rana kai mata ziyara sosai bata d'aukar lokaci mai tsayi bataje ba, Suna shiri da y'ay'an ta sosai kuma ziyartar junansu , wanan kenan ."

 Suna zuwa anguwar su Anty Umma ta sauka , Ciro kud'i a jakarta tayi ta mik'awa mai mashin ,tafara bubuga k'ofar , mai gadi ne ya fito yana washe baki , gaisawa sukayi Afnan ta shige ciki , direct parlorn da zai sadata da , Anty Ummi tayi ,parlor ne tsarare yasha kayan alatu komai na gidan a in burgewa ne , inka shiga parlorn kamar karka fito saboda wani k'amshi da keyiwa mutane sallama , Afnan ganin bataga Anty a parlor ba yasata wucewa bedroom d'inta ,samunta tayi tana waya, janyo akwatin nata tayi ta zauna a bakin gado, saboda bata ban banta Anty Ummi da mahaifiyarta ba , kasancewar bata nuna mata wani abu dazai 6ata mata rai , Anty na gama waya ta zauna a bakin gadon kusada Afnan , idanun Afnan sun ciciko da hawaye ta kifa kanta a cinyar Anty , mamaki ne ya kama anty ganin akwati a gefe kuma ga Afnan na kuka ."

 Anty ce ta d'agowa Afnan kai tare da jero mata tambayoyi , meyafaru mai Haisam d'in yayi miki ?kodai mahaifiyar tasa ce? "babu tambayar da Afnan ta amsa sabida kuka yaci k'arfinta ,cikin tausayawa anty ke kallonta tana girgiza kai , Anty ce ta shiga toilet ta had'a mata ruwan zafi ,ta bud'e mata sabon brush da man goge baki , ta tara mata ruwa a bahon wanka ....✍️.

Idan naga comments zan cigaba ,saboda kune na maidashi free , rashin sharhi zaisa ya zamo na kud’i🤙.
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!

   💍   💍   💍

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

Story and writing by

ZAINAB HABIB
{Mom islam}

MARUBUCIYAR👇
ZAINABU ABU
ZAZZAFAR KISHI
LADIDIN KAUYE
NANCY YAR KARYA
AND NOW👇
LAMARIN K’ADDARAR AURE NA

DOMIN KU YASA NA MAIDA WANNAN LITTAFIN KYAUTA👌RASHIN SHARHI ZAI SA NA MAI DASHI NA KU’DI

WATTPAD momislam2020


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com
https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.

BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM

🅿️EPISODE 3 & 4

Taji dad’in wankan , ta fito d’aure da tawul dakuma wani a kanta, Anty data ciro mata kaya a ‘akwati masu kyau tace ”kshafa mai kiyi kwaliya inkin gama ga abinci can a dining sai muyi magana , to tace ” ta je gaban dress mirror ta shafa mai da powder , ta sanya janbaki da kwali , ta d’auko kayan da Anty ta za6a mata , riga da skirt na atamfa ,dinkin ba k’aramin kyau yayi mata ba , dama itan mai kyauce ,kowane kaya tasa sai ya amshi jikinta , mik’ewa tayi ta fito daga bedroom d’in tabar Anty da sak’a da warwara , dining ta nufa ta bud’e food flaks d’in wani tashin k’amshi tayi a duka kulolin macaroni ,ce da taji kayan lambu sai farfesu a gefe rufe na farfesun tayi ,tafara cin abincin sai da ta k’oshi sanan ta bud’e farfesun tafara ci , tana gamawa tasha lemun kwakwa ta mik’e ta koma parlor , y’ar aiki ce tazo ta kwashe kayan tayi dasu kitchen , anty na bedroom tana zaman jiran Afnan ,batasan Afnan ta koma gaban TV ba , MBC 2 take kallo film d’in yasata nishad’i sosai , hakan yasata mancewa da wata damuwa da take ciki.”

Fuskarta yalwace da murmishi ta gyara zamanta tare da maida hankalinta ga TV , Anty ce ta fito da wayarta daga hand bag d'inta ,ganin a kashe yasata kunnawa , tace ”oh ko menene yasa Afnan fushi harta kashe waya oho , Anty na cikin tunani taji Ring d'in wayar  , ganin sunan my Husband ,na yawo a screen d'in wayar yasata mik'ewa da sauri , ta nufi parlor , ganin Afnan na kallo yasata kuma harda dariya ,yasata tsayawa ,tana kalonta , wayarce ta kuma ruri a karo na biyu , hankalin Afnan ne ya juya ga gurin da tajiyo k'arar wayar ta , kalon kalo sukayi da Anty ta sunkuyar da kanta k'asa , k'arasowa Anty tayi kana ta mik'a mata wayar ,tace ”ki amsa man , d'agawa tayi cikin sanyin murya tace ”Aslamu Alaikum , wa'alaikissalm ,yakike ina kika shiga nazo gida bakya nan ?"shiru Afnan tayi can kuma tace ”gobe zan dawo , ran Haisam in yayi dubu ya 6aci ,Afnan ba k'aramin 6ata masa rai tayi ba , ajiye wayar yayi batare da yakuma magana ba ya fad'a gado zuciyarshi na k'una , da tunani iri iri ."

K’arasowa Anty tayi ta zauna a kujera mai kallon ta Afnan ta d’auki remote ta kashe TV , Afnan maiyasa zaki bar gidan mijinki ba tare da izinin shi ba , kuma ba tare da kinyimin waya ba¿”eh tambayarki nakeyi , Afnan idanunta zun ciko da k’wallah tabawa Anty labarin dalilin tahowarta , Anty ta tausaya mata sosai ,musamman ma akan gorin rashin aihuwa , amma Allah maji rok’on bawansa sekaga Allah ya kawo , Anty ce tace ”to yanzu dai tunda dare yayi mubari zuwa gobe ,in Allah ya kaimu sai in maidaki ,to Afnan tace ”tare da mik’ewa ta nufi wani d’aki da ban na y’ammatan gidan kasancewar sunyi aure, juyi takeyi a gadon rungume da pillow ,da rasa abinda ke yimata dad’i , hawaye ne masu zafi suka kwaranyo mata , tace ”ko ya Haisam zaiji inyazo yasamu bananan sai Allah , tuno Fatima mak’ociyarta tayi , da tace ”Afnan karki tafi batare da sanin mijinki ba , ina idanunta sun rufe, lokacin tana cikin tsananin 6acin rai ,kuma juyawa tayi taji sam kwanciyar babu dad’i ,tasaba dajin d’umin mijinta yanzu kam komai komai ya kwance mata , tarasa washe shawara zataba zuciyarta , tsananta kukan tayi amma ba’a jiyo sautin sa sosai .”

Washe gari tun misalin k'arfe hud'u na asbha ta tashi ,tayi wanka tayi alwalah ,tafara jero nafil fili ,tanata kai kukanta gurin Allah , tana idarwa ,ta koma gaban dress mirror ta janyo stool d'in ta zauna tare da cire d'an kwalin kanta tafara tsara kwaliya , dama gwanace , tana gamawa ta feshe jikinta da turare kasancewar ba bu inda zataje daga nan sai gidanta , batajin ma zata iya yin breakfast ,a gidan Anty saboda kewar mijinta takeyi ,jiyo kiraye kirayen sallah tayi daga masallatai da dama , hakan yasata sanya hijab tabi wani masallaci sallah , suna idarwa ta yi adu'a ta shafa ta cire hijab d'in ta d'aura d'ankwalinta , ta yafa gyale ta fito parlor ,gidan shiru kamar ba mutane , dake Anty ce da y'ar aiki ,kawai a gidan mijinta yatafi k'asar waje , sai kuma drivers da masu bawa flawoyi ruwa , zama tayi a parlor rik'e da hand bag d'inta da wayarta a hannu , jiran fitowar Anty takeyi amma shiru , daurewa tayi ta nufi kitchen ,ta tsiyayo ruwan zafi a flaks  tasa lipton ,da madara da da sugar ta dauki biscuit ,tadawo parlor ,tana sha , harta gama sha Anty shiru , kuma mik'ewa tayi ta nufi bedroom d'in anty tafara nocking , tare da sallama , Anty da tayi sallah yanzu take shirin komawa bacci tace ”daughter lafiya kuwa?".

Lafiya Anty ceawar Afnan , inason komawa gida ne ,murmishi Anty tayi mai cike da maganganu sai kuma naji tace ”to babu damuwa jekiyi breakfast ,yanzu zanyi wanka , nayi cewar Afnan ,to ki jirani ganinan fitowa , to kawai tace ”ba haka taso ji daga bakin Anty ba ta koma parlor tacigaba da zaman jira ,tana kwance a parlor har k’arfe takwas kuma tasan k’arfe goma Haisam yake fita, tana shawarar tashi sai ga Anty nan ta fito sanye da doguwar riga pink color mai adon fararen stone a jiki , kanta tayi rolling d’in d’ankwalin , tayi kyau babu lefi , kasancewarta fara , zama tayi kusada Afnan tace ”daughter ,na d’auka zaki yimin kuwana uku ne , gimtse fuska Afnan tayi batare da tak’ara magana ba , Anty ce tace ”to mik’e mutafi tunda sammako zamuyi , amma biyoni d’aki daganan saiki d’auki akwatinki, rufawa Anty baya tayi suka zauna a bakin gado , Anty ta rik’o hanunta tace “daughter jeki bud’e bed site ki d’aukomin wata leda , mik’ewa Afnan tayi ta bud’e ta ciro ledar ta mik’awa Anty , kar6a Anty tayi ta bud’e ledar , ciro wata gorar Zuma tayi tace ”wanan ke naketa ajiyewa su sauran sun kar6i nasu so wanan karki wasa dashi , cokali biyu zaki dingasha ,safe rana dare , ta ciro wata roba mai dabino da kwakwa da Zuma a manne, tace ”wanan gumba ce karkiyi wasa , nasan ta 6angaren mijinki bakida matsala to karkiyi wasa gurin kyautata masa kuma kirik’e shan magani akan jari gadiya Afnan tayiwa ,Anty suka mik’e suka fice , direct gurin motocin gidan suka nufa , da gudu driver yazo ya durk’usa ya gaida Anty Ummi , da Afnan , Anty ummi ce ta nuna masa motar dazasu hau ,cikin azama ya fito da motar tare da bud’e musu back side, suka shiga.”

Sunyi tafiya sanan suka iso gidan , Anty a duk lokacin da tazo unguwarsu , Afnan sai ta jinjina kai , to yauma kamar kulum girgiza kai tayi ,saboda anguwar talakawa ce sosai , banda so gamon jini mezai kawo Afnan anguwar nan da gatanta ,ga mahaifinta shahararen mai kud'i, kasancewar drivern yasan gidan Afnan d'in yasashi parking ,a k'ofar gidan, farinciki fal zuciyar Afnan zataga rabin ranta , harta mance wulak'ancin da ya sanyata fushi , jin Anty ta bud'e murfin motar yasata yunk'urowa ,Anty na fita itama ta fito suka kulle , motar da isarsu k'ofar gidan suka fara nocking , sbda ko da Afnan take nan bata barin k'ofarta a bud'e , jin ana zare sak'ata ,yasasu gyara tsayuwar su , Haisam ne yafito da fara'arsa , yana musu sannu da zuwa ,Anty ce ta amsa Afnan ta kasa koda had'a ido dashi , kai tsaye cikin gidan suka wuce , ko ina fess babu datti , Haisam ne ya d'auko key ya bud'e k'ofar d'akin Afnan su Anty suka shiga , d'akin natama babu datti ko kad'an sai tashin k'amshi yakeyi , da sallama ya shigo ya durk'usa ya gaida Anty Afnan cikin jin kunya ta gaisheshi , ,ya mik'e ya fita, anty ce ta k'ara yimata tuni akan ladabi da biyayya dakuma iya kalami mai sanyaya zuciya , dakuma iya sarafa miji a lokacin da yake cikin 6acin rai , kowace nasiha ta Anty ta zauna daram a kwakwal war Afnan , anty ce tace ”to inaso yau kisha wanan abin dana baki karkiyi wasa dan Allah , to Afnan tace ”Anty ta ciro kud'i zasuyi 20k tabawa Afnan , sosai Afnan taji dad'i , daganan Anty ta fito , tana shirin sa takalmi saiga Haisam ya shigo da alamu fita yayi da k'atuwar leda bak'a a hanunsa , yana ganin Anty yace ”dan Allah Anty ki koma Ante na dariya ta koma ciki ,ta zauna a parlor , Afnan ce ta fito da hijab tana shirin raka Anty mota , ganin Haisam ya ajiye leda ya fita ,yasata bud'e ledar ta lek'a ,dariya Anty tayi tace ”to sarkin kwad'ayi abin nema ya samu ,Afnan tasa dariya , dawowa yayi da plet a hanunsa ya bud'e ledar ya fitoda kaji manya gasasu da ,lemun gora maltina da viju milk da fanta , kasancewar a ya yanke suke yasashi zubawa a babban plet yace ”anty dan Allah kici , Anty na murmishi ta d'auki yanka d'aya ta jefa a bakinta ta mik'e tace ”Allah yayi muku albarka , Haisam dan Allah aci gaba da hak'uri , Afnan tabi bayanta ."

Sai da motar ,Anty ta 6ace Afnan ta dawo gida da kuka , fad’awa jikin Haisam tayi tana kuka ,Haisam da yana fushi da Afnan ,ganin tana kuka yasashi rungumota , tafara share mata hawaye , ganin tak’i dena kukan ya sa6ata a baya yana yimata wak’a yana cewa “wanene ya ta6amin y’ar baby na ,inkamashi , Afnan ta tuntsire da dariya , tafara yimasa cakul kuli yana zulewa , sauketa yayi , yana dariya , filon kujera ta wurga masa aikuwa suka fara karad’e gidan da dariyaku suna gudu , wanan ya jefi wanan haka dai suka dingayi, suna haka har k’arfe , 11 pm tayi basu sani ba ,jin shugowar mutum sukaji babu sallama , cikin masifa tafara zazzaga ruwan bala’i ,tana cewa ” yanzu Haisam asirin da sukayi maka harya fara tasiri a kanka? ” to bazan yarda ba , tsabar rashin aikinyi shine ka biye mata kuke wasan banza kamar awakai ?to wlh ko kazo ka tafi aiki ko kaci gidanku , parlor mama ta shiga , ganin gasasun kaji baje a faranti yasata zare ido tace ”kai Haisam abinda kukeci kenan?”nashiga uku ni Lauratu , tadama abinda kuka koma ci kena?tabb hmm lallai ashe mallakar tafi haka ?” yana shirin magana ta wanka masa mari , tace ”maza kazo gida ina nemanka , munafuka tun kafin yasami mai gadonsa shine kikeson tatseshi ko dan kinga ke juya ce bakya aihuwa, ko wata tazo kartasami ragowa , kuce ma kundena cin hatsi saimu talakawa , Afnan ce ta rufe baki ta shige bedroom d’inta da gudu tasa key .”

Haisam zai bita mama ta dakatar dashi tare da cewa kana binta walhi sai kayi nadama , lashe maka zuciya tayi ?"kokuwa tsoronta kakeji ?niban isa inyimata fad'aba kenan ? ta jero masa wa'inan tambayoyin , tabbas dayasan ,mama zata shigo a dai _dai wanan lokacin da bai tsaya a gidaba dayayi sammakon fita , mama ce tace ”tattaro min naman da lemon duka ka k'ullemin su a leda , cikin rawar jiki Haisam ya tatara ya k'ulle ya mik'awa mama ,tana k'ar6a ta fice tana kaiwa tsakar gida tace ”saura karka taho mutafi wlh zakaga abinda zai biyo baya, tana tafiya ,Haisam yayi hanyar d'akin Afnan yana bubugawa , yana cewa "dan Allah ki bud'e ki saurareni Afnan , kuka yaci k'arfinta tace ”kaje kiran mama kaje kawai , Haisam tun yana tsaye harya gaji da tsayuwa ya fice, daga gidan zuciyarshi babu dad'i, mashin d'inshi ya tayar ya nufi gidan su , gidane k'ato daga ganin gidan zakasan gidan yawa ne mutane ne a ciki zasuyi biyar kowa da d'akinsa , d'akin mama shine farko sai d'akin kishiyarta da tarasu tabar yara sune y'ammatan da sukayiwa Afnan rashin kunya , mama iya Haisam ne yaronta ,ta d'auki son duniya ta d'ora masa sai dai ba kasafai takeson wani yaci arzikinsa ba , aciki kuwa harda mahaifinsa da matarsa , hakan yasa take taka tsan tsan da komai nashi kuma koda ya kawo yace ”tabawa mahaifinshi zatace to ,yana fita ta 6oye , yanzu kam harya zame mata jiki ,kuma dole mahaifinshi yake hak'uri da Halinshi , kowa na gidan yasan masifarta bata barin kowa , sallama Haisam yayi a k'ofar d'akin maman nashi , ko amsawa batayi ba tace ”inka gama munafurcin naka kashigo , shigowa yayi jiki babu k'wari ya zauna a tsakiyar d'akin da aka shimfid'a tabarma kasancewar babu leda a d'akin , yai shiru , kagama bata hak'urin ?"nace kagama bata hak'urin ?"eyee ? kan Haisam na k'asa bai d'ago ba yace ”kiyi hak'uri mama , dakata cewar mama , banason ban hak'urinka banason duk wata kalma dazata karyamin zuciya tunda kai bakasan zuru ba ,wlh Haisam ka kiyayeni , kokuma nayima!!!, Haisam ne ya matso ya katse mata maganar ta hanyar shafa hanunta a fuskarshi , kawar da kai mama tayi , sbda inta fara sababin fad'anta to batajin gari."

To kiyi hak’uri mama dan Allah ,shiru tayi tana girgiza k’afa tace ”ai na hak’ura tunda har gashi zanyima albishir da sabuwar matar danayi ma , ehee?” waro ido mama tayi tace ”kajimun wulak’anci ni sa’ar wasanka ce ?to aure zakayi budurwa mai aihuwa Allah yasama aihuwar fari ta haifo mana y’an biyu , mama na maganar tana dariya , Haisam da zuciyarshi ke bugawa hankalinshi ya tashi ,ya dubi mama tare da had’e hanuwanshi biyu yace ”dan Allah dan girman Allah mama kiyi hak’uri ki janye maganar nan, shek’ewa da dariya mama tayi tace ”walahi sai kayi aure kaji na rantse ,bazaka zauna da juya ba kana cefane tanaci tana zuwa kashi , yanzu ma iskancin da kuka d’aukarwa kanku ,kundena cin abinci sai naman kaza ,ni gani a nan a bushe kukwa kunyi dumur mur , Haisam zaiyi magana mama ta dakatar dashi da cewa , nasan mezakace ,dan haka inason ayi bikin nanda wata biyu ai nasan jarin shagon yanzu ya bunk’asa da wacan juyar na aihuwa ai da yanzu ka kaini makka….✍️.
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button