LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

Follow me and vote on wattpad.

Dalilin k’inyin post d’ina shine kuna karantawa bakwa sharhi????

????????????????????????????
???? ???? ????

LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!

     ????     ????     ????

????????????????????????????

Story and writing by

ZAINAB HABIB
{Mom islam}

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com
https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

My Facebook group
https://www.facebook.com/groups/126215122683287/

Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.

BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM

EPISODE 11 & 12

Anty na shirin mik’ewa tace ” yanzu ma anguwa zan zarce daga nan , ganin Alhaji na laluba aljihunsa yasata murmusawa , dubu uku ya mik’a mata tare da fatan Allah ya tsare , godiya tashiga kwararo masa ta mik’e ta fice , batason su had’u da kowa hakan yasata ficewa a ankare batare da sunyi ido biyu da matan gidan ba , fitarta keda wuya sai ga Anty ta shigo da sallama ,amsa sallamar yayi yana k’are mata kallo , to yau kuma yarintar ce ta motsa ?”matsowa kusa da Alhaji tayi tana mai kai cinyarta kan k’afarsa , tofa ???? Alhaji da zancen yafara sakin layi yace ”tashi muje ciki kinsan gidan baya rabo da bak’i , mik’ewa sukayi tare da turani waje suka rufo k’ofar , dare nayi yau Alhaji zai koma d’akin momyn Afnan , tun k’arfe hud’u na yamma tasa ake yimata gyare gyare , duba agogo tayi k’arfe biyar , toilet ta shige ta had’a ruwan wanka wanda yaji turaruka na musamman , tana fitowa tasa turaren wuta dana tsuguno ,kasancewar ta y’ar mai duguri bata wasa da gyaran jikinta bare ma matan gidan kowace tana k’ok’arin gyara kanta ,tana gamawa ta mulke jikinta da mayuka masu d’aukar hankali , wani mai ta tsiyayo ta shafe gashinta dashi ta zauna kan stool d’in dake gaban dress mirror tafara tsara kwaliya kasancewar lokacin ana kiran magrib tariga tayi alwalah , Afnan ce ta shigo da sanyin jiki ta dubi momy ,ta kawar da kai momy ko kallonta batayi ba ,ta mik’e ta d’auko cup da spoon ta dawo ta zauna magani ta d’auko a leda ta bud’e fridge ta d’auko nono mai sanyi ta dama , ganin zata sha yasa Afnan cewa “momy ina nawa , momy kallonta takeyi cikin tuhuma can kuma tace ”a lokacin da kika auri wanda zuciyata da hankali na sukeso to lokacinne zaki dinga ganin gata iri iri so yanzu kibi umarni na kiji dad’i a rayuwarki, sunkuyar da kai Afnan tayi tace ” momy yanzu duk akan auran Haisam ne dukanku kuka tsaneni ?” no Afnan ba tsanarki mukayi ba somukeyi ki gane ban bancin dake tsakanin talaka dakuma mai kud’i , Allah ya horewa mahaifinki company da dama ga dukiya mai yawa amma ace kin k’are ke y’ata ta cikina kin k’are a talaka futuk wanda in yayi kwana d’aya tak bai fita ba zakushiga damuwa.”

Afnan dai tasaba da irin wanan fad’an yasata jan bakinta tayi shiru ,ta zubawa momy ido wani fitinanen leshi ta ciro a drowa mai kalar pink da adon black stone anyi mata d’inkin riga da zani rigar iya guwaiwa mai breastcot tai kyau sosai kasancewar ta mace mai dirin jiki sbda irin jikinta Afnan tayi , war waro ta sa kana taciro tsadajiyar sark’arta ta sanya ni dai gani nayi momy ta koma kamar yarinya , kamar ba ita ta haifi Salma da Afnan ba ,momy na gama kintsawa takuma feshe jikinta da humra ,itadai Afnan a halin yanzu kewar mijinta takeyi sosai ,sallamar dady ce tasasu kai duban su gareshi da alamun fad’a yashigo amma ganin momy tasha kwaliya yasashi sa sauta murya ya kalli Afnan ganin bashi take kalli ba yas shi kashewa momy ido kana yace ”in kin kammala ina jiranki a d’akina zamuyi magana Afnan ta lura da kallon da dady ya ke aikawa momy hakan yasata mik’ewa tayi bedroom d’in ta ta fad’a gado, tana tuno soyayyarsu da Haisam tabbas ta tafka uban kuskure dahar ta biyewa son zuciyarta yanzu gashinan daga dadyn har momy babu mai damuwa da damuwarta yau satinta biyu , tinda tacewa Haisam washe gari zatazo har yanzu shiru ko shine ya sashi yin fushi oho , miƙewa tayi dan gabatar da sallahar isha’i tana idarwa ta jerowa kanta adu’oi dakuma Haisam ɗinta.”

Mama tasa ankai kuɗin aure , iyayen Maimunatu sun yanke lokaci kasancewar su mama sun roƙa kar asa bikin da nisa ,cikin sa’a kasancewar a shirye suke suka amince yau saura sati biyu biki , Haisam na burin zuwa gidansu Afnan yana tsoro yasan dole zai fuskanci cin mutunci da cin zarafi daga duka ɓan garorin guda biyu , wanan shike sage masa gwaiwa ya kasa zuwa ,ga matsa masa da mama tashiga yi yanzu bashida saƙat kasancewar biki ya kusa tasashi siyo akwati ya kawo ɗakinta ,aikuwa haka akayi dan gudun tashin hankali , akwatuna ukune biyu manya ɗaya ƙarami cikin fara’a mama tadinga sanya masa albarka , yanzu kam Haisam yafara cire rai da samun Afnan saboda dalilai da dama hakan yasa ya haƙura da auran da ake shirin liƙa masa amma badan yana soba ,kwanci tashi asarar mai rai yau biki saura kwana uku sbda Haisam yagama haɗa kayan akwati yasa Mama kwantar da hanlinta ,hidima akeyi sosai baba kam baya kula lamuranta dan zata iya tsigesa ba tsoro bare fargaba , ƴan uwa kowa sai yayi tsegumin wanan aure ,kowa tambayarsa itace to ina matarsa , kaf cikinsu ba suda mai basu amsa yasasu jan baki sukayi shiru.”

Biki yayi biki Haisam bai gaiyyaci kowa ba sai dai ya gayyaci abokansa na anguwa , suma gudun kar suyita yi dashi ne amma da babu wanda zai bawa labarin auran da yazamo tamkar auran dole , bayan an ɗaura aure Maimunatu ta kira Haisam ko akwai wani events da za’ayi ?”cikin baƙar magana Haisam yace “to ni babu wani shirme da za’a kawomin ,
“kuma kidena rawar kai ba sonki nakeyi ba liƙamin ke akayi dan haka karki ƙara koda marmarin kirana kinaji ko?” Maimunatu da jikinta yai sanyi duk azabar masifarta amma takasa mayarwa Haisam martani lallai ko zata rama koba yanzu ba katse wayar yayi tare da jan dogon tsaki, ɗakin Afnan ya shiga ganin komai kamar tana nan Allah sarki masoyoyiyar gaskiya Haisam ya faɗa lokacin da ya kwanta a gadon Afnan ya luluɓe jikinsa da blanket ƙamshin turarenta ne yake masa yawo ,gani yake kamar zai ganta kwance kusa dashi , tabbas Afnan da Allah ya bata aihuwa da babu abinda zai hana ƴa ƴanta su taso cikin irin halinta , duk da Allah yayiwa mahaifinta arziƙi hakan baisa ta ɗauki talaka da ƙyama ba , kwance yake duk wannan tunanin da yakeyi , wasu hawaye ne masu zafi zuka kwaranyo masa agefe idansa ,tunowa yayi ashefa wai shine ango ko ?”kuma yau za’a kawo amarya ,tabb to ni mema zanyi? miƙewa yayi ya fice a ɗakin , yasa takalmi yana shirin fita yaji sallamar Fatima ɗago kai yayi tare da amsa sallamar Fatima ce tace “ina yini Haisam lpy lou y gida bata amsa ba tace “har yanzu Afnan bata dawo ba ?eh Haisam ya bata amsa bata dawo ba nima jiranta nakeyi , ficewa tayi batare da ta ƙara bi ta kansa ba , tana faɗawa gida ta saki kuka mai cin rai , shikenan Afnan ko shawara babu yanzu gashinan ya tafi ta barta takuma sakin kuka.”

Tuno ɗaurin auran Afnan yayi da ya kashe kuɗi sosai wanan kam tamkar za’a sashi a kurkuku yakeji tunda babu mai sa ssauta maganar auran ,ganin Fatima ta fice ya sashi koma wa bedroom ɗinshi ya kwanta , jin kwanciyar babu daɗi yasashi juyi a gadon , jin an rangaɗa sallama yasashi miƙewa jiki babu ƙwari , ganin mata da yawa ga motar kaya a waje ya matsa gefe ba tare da ya kallesu ba kanshi a ƙasa yace “ina yininku sama sama suka amsa ,ganin gidan babu lefi yasa su washe baki suna sanya alkairi , a wane ɗakin za’ayi jeren?” Haisam ne yace”ga ɗaki can ,ɗakin baƙi ne zaku iya yin jeren a ciki , wata daga ciki da alama ƴar uwar Maimunatu ce ta turo ɗaurin ɗankwali gaba tace ” aikuwa sai dai in a fito da kayan ɗakin kishiyarta a jera na Maimunatu , danƙari Haisam yac” lokacin da yake shirin ciro kwaɗon ƙofa a aljihunsa ya kulle ɗakin Afnan sa kai yayi ya fice ,kan uba to wlh Maimunatu zatasha wuya a gidan wanan shu’umin sai ta tashi tsaye ,wata daga gefe da tun shigowarsu batayi magana ba tace “wayasani ko kishiyar tata azabarshi ce ta korata gidansu , haka dai suka dinga tsegumi , ganin hakan bazai fishesu ba yasasu komawa bakin aikin nasu , dole a ɗakin baƙin suka yimata jere ɗakin bawani mai girma bane amma dai kayan sun zauna sunyi kyau amma ko ƙafar na Afnan basu kamo ba, kasancewar iyayen Maimunatu talakawa, suna gamawa suka kullo ƙofar suka fito kowa na tofa albarkacin bakinsa akan Haisam shiko ya fice ya barsu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button