LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

????????????????????????????
???? ???? ????

LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!! .

  ????     ????       ????

????????????????????????????

Story and writing by

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

????AREWA WRITERS ASSOCIATION????

EPISODE 39 & 40

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ring d’aya driver ya d’auka tare da sallama yace ”ranka shi dad’e na dawo d’aukarku nasamu babu mota ? dafe kai yayi tare da cewa “innalilahi yanzu ina Afnan ta shiga oh Allah driver ne ya k’ara magana a karo na biyu yace ” mai gida wani gurin tayi ? shut up your mouth wlh zan sa6a maka , kana yaja wayar ya kashe , budurwar nan mai suna Husna ce ta tako har kusa dashi tace ” hi my man mutafi ko ? juyowa yayi a fusace zai yimata masifa ya kasa , shafa k’eyarsa yayi yace ”mutafi , wani irin murmishi tayi wanda ita kanta tasan ma’anar hakan , motarta suka shiga tana driving shikuma yana gefenta , Afnan na zaune a cikin mota a can gefen titi kasancewar gabas sukayi ba lallai su ganta ba amma ita ta gansu musamman lokacin da Husna ta rik’o hanun Abdallah , runtse ido tayi tare da ambaton Allah.”

 Yau watan Maimunatu   daya da rasuwa  duk da bawani shiri sukeyi da ita ba  amma rasuwarta ta dakeshi sosai , haka yakejin gidan shiru babu hayaniyar kowa , wanka ya shiga bai jima ba ya fito daure da towel a k'ugunsa ya wuce d'aki ya shafa mai ya sanya riga da wando na jeans , yayi kyau ba laifi amma ramarsa ta fito , kulle k'ofar yayi da key kana ya nufi gurin mashin d'insa fita dashi yayi waje ya kulle k'ofar wajen ya tada mashin d'in ya nufi gidansu ,da sallama ya shiga babu kowa a tsakar gidan hakan ya sashi nufar d'akin mahaifiyarsa , samunta yayi a zaune da wata yarinya a gaba  a k'alla zatakai shekara goma sha biyar   suna hira zama yayi a kujera y'ar tsugunno ya gaida mama ' amsawa tayi cikin fara'a tare da cewa ya kasuwa Alhmdulilha Haisam yace " yana duban  yarinyar , wacece wannan mama ?" Uwale ce mama ta bashi amsa , Uwale kuma eh man yarinyar yaya Halilu a k'auyen kano suke zaune ba lallai ka santa ba raboka da garin tun kana yaro , jin jinawa Haisam yayi , mama ce tace " baki iya gaisuwa ba ko ?washe hak'ora tayi tace ” ina wuni "lpy Haisam yace " ya mik'e tare da ajiyewa mama dubu d'aya ya fice Allah yayi albarka tace , to inason yin magana dakai zuwa anjima  to mama , Haisam yace " ya fice ."

Kasancewar ta iya mota yasata tuk’awa a hankali kamar mara jini a jika , ikon Allah ne ya kaita gida , mai gadi najin horn ya mik’e a guje yaje ya wangale get d’in a fusace ta shigo da motar ko gurin parking bata wuce da ita ba tayi cikin gida , tana shiga parlor ta zauna dabas a kan kujera tare da cewa maza !! maza!! daga auranmu harya fara bibiyar wata shegiya , matarshi ma bai taho da ita ba saboda yasan abinda ya shirya dama yaso wulak’anta ni ne , ta saki kuka mai tsuma zuciya , Haisam ne ya fad’o mata ,saurin kawar da tunaninsa tayi gudun fad’awa wata damuwar , dafe kanta daya fara sara mata tayi tana cigaba da kuka ,

tana kunna wayarta da niyar kiran k'awarta sai ga kiran Abdallah nan ya shiga  k'in d'agawa tayi saboda a halin yanzu haushinsa kawai takeji batason jin muryarsa a wanan lokacin , miss call biyar yayi mata amma ko a jikinta sai ma k'ara fashewa da kuka da tayi,  


Zaune suke a gurin shak'atawa Husna na zuba masa shagwa6a san ranta , tunda ta lura da Abdallah damuwarsa yaji muryar Afnan , tafara amfani da salon jan hankali tana kasheshi da zantuka masu sanya farinciki , aikwa nanda nan Abdallah ya ajiye waya sunata zuba soyayya , sunyi hotuna da yawa a gurin, wani  ta dafashi wani kuma suna rik'e hannun juna suna dariya, daga nan suka shiga motar , a k'ofar gidansa ta saukeshi ita kuma ta wuce , da sauri ya fara nocking mai gadi ne yai azamar bud'e masa , yana shiga yace "Afnan ta shigo ?" eh baba mai gadi ne yace tun rana ta dawo amma ...shutt, mai gadi ne yaja baki yayi shiru , Abdallah ya k'arasa ciki zuciyarshi a karye , yana shiga ya tura k'ofar parlor n ganin bai ganta a nan ba yasashi nufar bedroom d'inta bubuga k'ofar yafara amma shiru tak'i bud'ewa, Afy  ya fara k'wala mata kira , Afnan na kwance a kan gado tana duba sak'onni a whtsapp tana kuka kamar dole , wani massage ne yaja hankalinta , bud'ewa tayi tana dubawa , hotuna ne sunkai kala biyar , bata tsaya karasa kalonsu ba takuma sakin azababben kuka ."

Jiya sautin kukan Abdallah yakeyi har cikin dodon kunnensa amma babu inda ya iya ,d’akinsa naga ya nufa ya dawo hanunshi rik’e da extra key ,bud’e k’ofar yayi jikinsa na rawa ya nufeta ganin tana rawar sanyi kuma tana kuka , d’aukarta yayi ya fice da sauri tayi k’ok’arin hanasa amma ta kasa kasancewar jikinta babu k’arfi ko kad’an , bai tsaya kiran driver ba ya nufi motar da ita ko hijab bai d’aukar mata ba sbda a rud’e yake ya nufi hospital , da isarsu doctor ya nuna musu d’aki anan aka kwantar da Afnan , har yanzu hawaye bai dena zarya akan fuskarta ba , Abdallah da yakejin zuciyarsa babu dad’i ya dubi Afnan yace ” ya jikin?”.

“Cikin k’arfin hali tace ” na warke , cikin zuciyarta kuwa cewa tayi kaci darajar doctor dake zaune da badan haka ba babu abinda zai sa na kulaka ta runtse ido , tana buk’atar hutu doctor yace ”tare da duban Abdallah , to mungode doctor bayan an saka mata k’arin ruwa bacci mai nauyi ya d’auketa , tunda tayi bacci ya sauke ajiyar zuciya , wayarsa ce tafara ring sai da ya kalli Afnan sannan ya mik’e dan a tunaninsa yanzu baccin takeyi , yana fita ta bud’e ido dama k’arar wayarsa ce ta tashe ta , hawayen da sukak’i dena zubowa ne suka kuma zubo mata sharewa tayi tana tunanin halin rayuwa, shiko da fitarsa ya kuma bin kiran suka fara magana shida budurwar , banji me yake cewa ba ya katse wayar , komawa ciki yayi ya nemi kujerar daya rashi ya zauna tare da kallon fuskar Afnan ko ta tashi , ganin tanata bacci ya koma ya zauna lolz

????????????????????????????
???? ???? ????

LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!! .

  ????     ????       ????

????????????????????????????

Story and writing by

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

WANAN LITTAFI GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA SHUGABA

(ANTY HAUWA MAMAN USWAN)

ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA

????AREWA WRITERS ASSOCIATION????

EPISODE 41 & 42

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Da yamma bayan sallahar isha  Haisam ya shigo gidansu mama  samun Uwale tana rera wak'a yayi mai kamada ta y'an k'auye , dariya yasa kana ya shige d'akin , kasancewar mama na sallah yasashi neman guri ya zauna yana k'arewa Uwani kalo , fara ce doguwa tanada dogon hanci sai dai idanunta jajaye ne sbda tana fama da ciwon ido kyakyawa ce amma ba kowa zai gane ba sai wanda ya lura da hakan ."

Mama na idar da sallah ta kalli Haisam tace " harka dawo to barka , Uwani mik'a masa tuwo yaci , nak'oshi Haisam yace” naci shinkafa gidan abokina Abubakar , to masha Allah mama tace ”tana gyara zama " dama maganar da nakeson muyi itace  wanan yarinya Uwani nakeson a had'a auranku !!!zaro ido Haisam yayi tare da kuma k'are mata kallo tabb ya fad'a a cikin ransa to ni mezanyi da wanan? bashida mai bashi amsa yasashi yin shiru , mama ta fuskanci zabin bai yi masa ba ,tace ” bawai inason cutar dakai bane sonakeyi ka sami nutsuwa aure na k'ara nutsuwa , Uwani na gefe sai boye fuska takeyi a cikin labulen gado kasancewar gadon mai rumfa ne."

Haisam ne ya dubi mama yace ” ko watnni ba’ayi da rasuwar Maimunatu ba kice nayi aure yanzu ?” sakin bani tayi tana kallonsa kuma tayi mamakin maganar baya yimata gardama akan cikar burinta amma yanzu ya fara kai , nasani mama tace ” tare da wayancewa wanan da kake gani zata maye maka gurbin Maimunatu inkuma kanada wacce kakeso to ka kawota , babu Haisam yace ” a tak’aice , nizantafi to Allah ya bamu alheri mama tace ” tana rik’e baki.

 Yau aka sallami Afnan daga hospital labari ya isa gurinsu momy da Antynta batada lpy hankalinsu ya tashi sosai  , wace suke kira da Anty wato k'anwar dadynsu itace ta kira su momy ta sheda musu cewar Afnan tana asibiti laulayi ya sata gaba , kowanensu na murna sosai haka suka nufi gidan , basu dad'e da dawowa daga hospital ba sai ga su momy da anty sun shigo , da sauri Afnan ta fito daga bedroom d'inta tana fara'a , oyoyo anty , anty ce tace ” y'ar albarka tako a hankali duk a tunaninsu cikinne da ita , zama tayi kusada anty suka fara gaisawa ,

Ya jiki suka yi mata dakuma cewa dadynta na gaisheta ya gwada lambarta a kashe ,ina amsawa Afnan tace ” ina zuwa ta mik’e , momy da anty ne suka fara cewa masha Allah daughter takusa samun baby , jin alamun tafiyar mutum yasasu yin shiru , Abdullah ne ya fito sanye da shadda fara alamun yayi wanka ya sauya kaya da bak’ar hula da agogo mai ruwan golden ba k’aramin kyau yayi ba , samunsu momy yayi a parlor , yaji kunya matuk’a dan bai lura dasu ba , k’arasowa yayi ya durk’usa ya gaishesu kana yace ” a gaida dady , komawa ciki yayi , jin k’amshi yasashi nufar kitchen samunta yayi tana suyar dankali da k’wai ,rungumota yayi ta baya yana cewa haba my baby ashe su momy ne sukazo shine ko ki gayamin , galla masa harara tayi tare da janye hanunsa , tabbas yasan yayi laifi , had’e hanuwansa yayi alamun bada hak’uri , bata tsaya saurarasa ba ta zuba abincin a plet ta barshi a gurin , samunsu tayi a tsaye da mamaki ta kallesu tace ” anty yanaga kun tsaya ? anty ce tace ” zamu tafi ne a’a ku tsaya dan Allah kuci momy ce taja hanun anty suka fice , jiyo fitarsu yasa Abdallah fitowa da gudu dan yaji alamun kukan Afnan 20k ya dank’a mata a hannu.yace ” yi sauri ki mik’a musu nayiwa driver magana zai kaisu , da sauri ta fice har sun isa bakin get tafara k’wala musu kira anty ce ta tsaya tare da cewa ” mai ya kaiki fitowa keda bakida lpy ,

 Rau rau tayi da ido ta mik'awa anty kud'in , k'in karba anty tayi tace ” mai muka kawo miki dahar zaki bamu kud'i haka , anty.Abdallah ne yace ”ma ku tsaya driver ya kaiku, suna cikin magana suka hango drivern su yazo d'aukar su nasiha suka k'ara yimata kana ta mik'a musu kudin ta shige gida idanunta cike da hawaye , tana bud'e get ta shige da gudu bata lura da mutum a parlor ba ta wuce da d'an gudunta , Abdallah yarasa wane laifi yayi mata mai girma haka amma yasha alwashin yau insha Allah zai shawo kan matsalar ."


 Gado ta fad'a ta kifa fuskarta tafara rera kuka inta tuno hoton data kalla sai sabon kishi ya tashi takuma k'ara volume d'in kuka .

Kwanci tashi asarar mai rai yau satin momyn Sadiq uku a gida iyayenta sun yin Allah wadai da tarbiyar da ta za6arwa kanta , sukanyi waya da Sadiq amma bata ta6a gaya masa bata gidan Abdallah ba ,tana tsoron halin da zai shiga inhar yaji wanan zance.

Tun daga ranar in Haisam ya shigo Uwani 6uya takeyi wai kunyarsa takeji , shiko abin haushi yake basa , yaza'ayi ace y'ar wanan ficikar itace zai aura , rabonsa da gidan yau kwana biyu kuma bai ta6a tsallaken rana ba , abin yaba mama mamaki sosai ,ita kanta tana tunanin kamar bata yimasa adalci baYau kowa keta shirye shiryen komawa gida kasancewar sun sami hutu , tunda Sadiq yake had'a kayansa yaji gabansa yayi wani mumunan fad'uwa bai kawo komai a ransa ba yaci gaba da shirye shiryensa , lokaci ya tafi kowa anzo d'aukarsa shikam baiga walk'iyar motar gidansu ba mamaki ne ya ishe shi dan dadynsa baya wasa wataran ma shine yazo da kansa ya d'aukeshi to yau lafiya ? ci gaba yayi da zama har aka kira sallalhr mgrib babu ko alamun wata mota , mai gadin makarantar ne ya dubeshi yace ”yaro ni zan kulle makaranta gashi iyayenka basuzo ba Sadiq kam hawaye ne suka zubo a fuskarsa dan yayita gwada number dadynsa shiru ta mahaifiyarsa ma a kashe   , ficewa yayi ba tare da yasan inda zashi ba , gashi dare ya fara jakar dake goye a bayansa ya bud'e tare da ciro kud'i , zasuyi dubu goma ganin wani alo ansa hotel yasashi sauke jakarsa yana tunanin shiga ciki to Allah yasa kud'in ma su ishe shi , haka ya kuma d'aukar jakar ya nufi bakin get yana k'wank'wasawa ,

Waye? mai gadi yace daga ciki , nine inji Sadiq d’aki nazo kamawa , jinjina kai mai gadi yayi kana yace ”yaro mai ya raboka da gidan iyayenka kazo wani guri kwana ? bayani Sadiq yayi , mai gadi ya tausaya masa , yace ” to zuwa gobe sai ka nemi gidanku ko eh Sadiq yace” ya shige ciki .”

Ya kama d’aki akan 5k

????????????????????????????
???? ???? ????

LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!! .

  ????     ????       ????

????????????????????????????

Story and writing by

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

????AREWA WRITERS ASSOCIATION????

EPISODE 43 & 44

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ɗakine rantsatse mai kyau kasancewar makarantar tasu ba a cikin gari take ba shiyasa kuɗin hotel ɗin yayi sauƙi , bayan yayi wanka ya fitoda ragowar ragowar milk ɗinsa da bredi batare da jiran abin haɗawa ba ya hau sha sbda wata masifaffiyar yunwa dake addabarsa , sai da ya cika cikinsa ya yi salolin da ake binsa sanan tunani ya fara yimasa yawo a kwanyarsa , yana da tambayoyi da dama amma yanzu kam bashida mai amsa masa ,dan tunda yazo duniya harya kai ga shiga makarantu dadynsa bai taɓa bari yayi fushi ba yanzu kam kuka ya fara yana cije lips .

Cikin fara'a ya shigo bedroom ɗinta samunta yayi tana  duba fuskarta a mudubi  kasancewar kanta na kallon abinda ke gabanta ne yasashi shigowa kai tsaye ba tare da yayi magana ba ,kawai ji tayi an rungumo ta a fusace ta juyo da nufin masifa , kwarjinin da yayi mata ne  yasata sunkuyar da kai  , ɗaukarta yayi cak kamar baby ya maye gurin zamanta ya ɗorata a cinyarsa , wayarsa ce ta fara ruri babu ƙaƙƙautawa tsaki yayi ya ɗauka , da can ɓangaren Sadiq yace " dady ka manta tun jiya mukayi hutu ?da yake shima ɗin ɗan duniya ne Abdallan yace " lla am sorry ai na manta  yanzu kana ina ne ?, kuma har ga Allah zuciyarsa bata yimasa daɗi ba tabbas Sadiq zai iya gano komai a dawowarsa hutunnan  , Afnan dake gefe yaron ya bata tausayi ta share hawayenta tace " muje mu ɗaukoshi zuwa gobe , duk da zuciyar Abdallah babu daɗi amma hakan bai kasa sashi jin daɗin kalamin Afnan ba , bayan tayi magrib Abdallah yana masallaci sai da tayi isha'i sanan ta kunna  whtsapp , ganin wanan number da tafi kowacce ɓata mata rai tayi saƙonni nata shigowa , hankalinta ne ya kar karta gurin ganin hotuna ne ,

Wannan karon taga abinda ya matuƙar girgizata hotonta tagani daga ita sai pant da bra innalilahi Afnan tace ” tare da dafe kanta da ya fara sara mata nashiga uku a ina nayi wanan hoton? duba rubutun ƙasan hoton tayi fara karantawa tayi ,
Barka da hutawa matar Alhaji Abdallah kinga wanan hotunan naki ?” to kikayi wasa Abdallah zai gansu da idanunsa garama kibini a hankali Afnan ce ta miƙe ta sakawa ƙofar key kana ta dawo ta zauna taci gaba da ƙarewa hoton kallo tana mamakin har da yaushe ta taɓa wanan shigar , cigaba tayi da karanta saƙon taji budurwar tace ” yanzu dai abinda nakeso shine kisa mijinki ya aureni , Afnan jin zancen tayi kamar saukar aradu ,saurin kashe datar tayi tareda dai’daita nutsuwarta takuma shafa powder a fuskarta , jin alamun shigowar Abdallah tayi hakan ya sata ƙara gyara jikinta,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button