LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

“uhm Haisam dama cewa nayi naga kamar Maimunatu bata iya aiki sosai to inba damuwa mezai hana in dawo gidannan indinga temakon ta tunda yanzu naga Allah ya buɗa maka sosai kuma ba ƴar aiki ka ɗauko mata ba ?, Haisam ne yace “to ai mama gara a ɗauko ƴar aikin kamarki ki zo gidannan kina aiki , mama ce tayiwa Haisam daƙuwa tace “kaci gidanku Maimunatu ai ƴata ce inda zan riƙeka haka zan riƙeta dan haka ka ƙyaleni in zauna kawai zan kwaso kayana zuwa su wanki da shara ai kaga su sunfiya sa tsuguno taji da wanke wanke da gyaran ɗaki , Maimunatu dake gefe ta taɓe baki tace “taɓɓ wlh nikam anaso a takuramin ne yo banda takura meye nawani zuwa ace za’adinga yimin aiki dacan wa yake yimin?cikin zafin nama Haisam ya miƙe zai wanka mata mari dakatar dashi mama tayi da cewa kull ba’a taɓa mai ciki koda gaba karkayi kuskuren sake kwatanta hakan , sunkuyar da kansa yayi yace “to mama , kidawo da kayanki kawai tunda ankwashe kayan ɗakin can , cikin murna mama tadinga sa musu albarka , miƙewa tayi tana duban Maimunatu tace “to barin tafi sai nadawo ko kallonta Maimunatu batayi ba ta ɗauke kai gefe .”
Washe gari tun da safe Afnan ta samu tayi wankan tsarki tayi sallahr asbah , dawowar Abdallah daga masallaci kenan ya tarar da ita tana sallah , farinciki fal zuciyarshi zama yayi gefe gado yana ƙarewa kyakyawar fuskarta kallo tare da lumshe ido , ƙarar wayarsa ce ta fargar dashi aga kalon Afnan , aslm yace "cikin firgici naji yace "ganinan zuwa kuyi dashi asibiti , Afnan dake gefe gabanta na faɗuwa tunda taji ance asibiti tasan ba lafiya ba, juyawa tayi bayan ta shafa adu'ar tace "barka da safiya mijina , ywwa barka Abdallah yace dan hankalinshi na gurin masu zuwa asibiti ƙara kai dubanta tayi gareshi tace "waye babu lafiya ?"Sadiq ne Abdallah yabata amsa a taƙaice , waye Sadiq ? yarona ne Abdallah yace ,nizan fita zan dubasu , in da wata matsalar ki kirani a waya ,to Afnan tace jikinta a sanyaye taƙara da cewa"Allah ya bashi lafiya mai ɗorewa.
Da isarshi asibitin ya samu anba Sadiq gado , Sadiq yaro ne da a ƙalla zai kai shekara goma sha takwas mahaifiyarshi wato mata agun Abdallah sunanta Shamsiya ,gaishe da Abdallahn tayi yace “mata ya mai jikin da sauƙi tace “to ya amarya washe baki Abdallah yayi tare da cewa amarya tana lafiya tana gaisheki idanun sa na kan Sadiq dake bacci ta galla masa harara tace “ina amsawa , duba agogon dake ɗaure a hanunsa yayi yace “yanzu ƙarfe ɗaya saura zanje zuwa anjima zan dawo , miƙewa tsaye tayi tasha gabansa tace “ciwo ya kori komai maiyasa bazaka bawa ɗanka kulawa ba ? Abdallah ne yace ” kiyi haƙuri zan dawo anjima, ƙwafa tayi batare da ta ko lallesa ba ta koma ta zauna zuciyarta babu daɗi, kai tsaye motarsa ya nufa tuƙi yakeyi hankalinsa na gurin Afnan cikin zuciyarsa yana cewa “inda nayiwa wanan rana buri bazan bari yauma nakuma rasa farinciki ba , gudu yake yi a titi ikon Allah ne ya kaishi gida , ƙarar horn ɗin da mai gadi yaji ne yasashi tashi buɗe ƙofar da azama , Abdallah ya shige dan baima lura da gaisuwar da baba mai gadi yake yimasa ba.
Zaune take a katafaren falonta mai sanye da kayan more rayuwa faɗin tsaruwar falon ma ɓata lokaci ne dan koni tsayawa nayi ina ƙare masa kallo , hangota nayi kwance a ɗaya daga cikin kujerun da alama waya takeyi ,
Jinayi tace ” momy nasami tsarki kuma nayi amfani da magun gunan tun ɗazu , daga can ɓangaren momy tace “yawwa ƴar albarka dan haka nake sonki kinsan su masu matan nan wlh sai da gyara jiki kuma insha Allah nasa a tahomin da wani haɗaɗen magani da turare insha Allah zakisha mamaki .”
Dariya Afnan tayi tace "momy na kenan Allah ya barmu tare gaskiya sai yanzu na tabbatar aurena da Haisam ba alkairi bane , kinga breakfast ɗina na yau dakuma ranar danazo hmm momy ba'a magana , kwashewa da dariya momy tayi kana tace "ai ba tun yanzu nake nusar dake dai dai ba kinƙi fahimta kice yanzu kin dawo hanya ?gaskiya kam momy ,daganan sukayi sallama ,
Jin sallamar Abdallah yasata miƙewa tare da kashe masa ido , kallon shugar jikinta yayi , can kuma ya faɗaɗa fara’arsa ya buɗe hannayensa duka da sauri ta faɗa jikinsa tare da rungumeshi ta zaunar dashi a palo , oh Allah na gaji , Abdallah yace “lokacin da yake shafo dogon gashin kan Afnan da yasha gyara.”
Ƙara narkewa Afnan tayi tace "baby ka gaji ko ? uhm Abdallah yace" dan wanan shagwaɓar tata tana rikitashi wani lokacin , Afnan ce tace "tashi muje inyima tausa , abin nema ya samu aikuwa cikin azama gogan ya miƙe tare da ɗaukar Afnan kamar jaririya ya kaita bedroom ɗin ɗakinsa ...
Cire mata ɗankune yayi da warwaro ya kwanta gefe tare da rungumota sunajin nunfashin juna , am sorry baby kiyi haƙuri dani pls ni mabuƙaci ne !!!…wata azababiyar faɗuwar gaba ne ya ɗarsu a zuciyar Afnan , kasancewarta wayayiyar mace ƴar boko yasa bata nuna masa alamun damuwa ba amma gaskiya a ƙarƙashin zuciyarta tsorone ya dirar mata , idanunsa a lumshe yafara hura mata iska ta kunne yana shafa gashin kanta hakan yasa ta mance da komai tafara maida masa , daganan salo ya sauya zuwa cire …..am sorry nafito kasancewar naga gidan Haisam ana drama .
Da sallama mama ta shigo kasancewar Haisam bai fita ba shine ya amsa sallamar , kayane ta ɗibosu zasuyi kala ashirin ta ajiyesu a tsakar gida , Haisam ne yace “mama zo in nuna miki ɗakin da zaki zauna cikin rawar jiki mama ta miƙe ta bi bayan Haisam , Maimunatu na ɗaki baƙin ciki ya isheta….✍️.
Uzururuka sunyimin yawa bawai ina yimuku wula ƙanci bane kuyi haƙuri kunkusa samun post kullum afuwan my fans .
Ga mai buƙatar karanta littafinnan tundaga na ɗaya zai iya samunsa ta wattpad momislam2020
????????????????????????????
???? ???? ????
LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!! .
???? ???? ????
????????????????????????????
Story and writing by
ZAINAB HABIB
(mom islam)
My wattpad momislam2020
My telegram link
Zainabhabibu713gmail.com
????AREWA WRITERS ASSOCIATION????
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
EPISODE 31 & 32
Ganin rana tayi kuma Maimunatu bata fito ba yasa mama miƙewa ta nufi kitchen ta kunna risho kasancewar bata iya kunna gas ba , ruwa ta dora da wake a haɗe dan da alama shinkafa da wake zata girka , fitowar Maimunatu daga ɗaki kenan ta leƙa ɗakin Haisam taga babu kowa ya fita , kitchen ta nufa hango mama tana gyaran shinkafa yasata cewa sannu , washe baki mama tayi cikin rawar jiki tace “sannu ƴar albarka.”
sai da Abdallah ya sami nutsuwa da Afnan sanan ya shafo fuskarta tare da manna mata kiss a goshi , Allah yayi miki albarka duk da wani ya rigani amma dole nayi alfahari da wanan rana gaskiya Afy kin shayar dani zuma , Afnan dake kwance tana kallonshi yana sumbatu ta rungumeshi tare da raɗa masa a kunne tace “karka damu mijina koda wane lokaci ina tare dakai , wanan maganar ta Afnan tasa shi jin daɗi sosai ya miƙe ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwa , wankan tsarki ta fara kana yayi na sabulu ,Afnan miƙewa tayi ta ciro masa boyel mai laushi baƙi da farar hula da farin takalmi kasamcewar akwai wasu kayan nasa a ɗakinta ..
Yana fitowa ta shige itama wanka tayi tare da na tsarki ta fito kanta ɗaure da towel na tsane ruwa ,
Samunsa tayi har ya shirya sai zuba ƙamshi yakeyi ga wani sihirtaccen kyau da yayi mata ..
Kamo hanunta yayi tare da ɗorata kan cinyarsa yace “gaskiya zanje in dawo ki kularmin da kanki ,
Ƙara marai rai cewa tayi ta ce “gaskiya nagaji da fitarnan inace hutun two weeks ka ɗauka ,
Buɗe baki Abdallah yayi yace “wane ni yazanyi da jama’ar da suke jirana in dawo ?”
Uhm to yanzu ina zaka ?"zanje duba Sadiq ne wai sun dawo gida ..
Kishi ne ya tasowa Afnan amma dole ta danne dan tanason samun fada a zuciyar Abdallah ,ka gaishe shi shida momyn ‘nashi oky Abdallah yace “yana ɗaura agogo a hanunsa,
Shafa fuskarta ya ƙarayi kana yace “natafi Allah ya tsare Afnan tace “fuskarta ɗauke da murmishi .”
da isarshi gidan takalma ya gani a ƙofar ɗakin zasukai na mutum huɗu ,nazari ya kamayi dan lokacin magrib ta farayi , jiyo surutun su yayi suna cewa ai wlh hajiya ki kaɗa ƴar banza …
Kina zaune da mijin zata fara kawo miki cikas nifa dama bason aurannan da yayi nakeba duk da bani ke zama dashi ba …
Momyn Sadiq ce tace “uhm ni yanzu ma kullum sai nayi kuka sbda ya sabarmin da komai nasa , wata daga gefe tace “uhm nidai banida ta cewa tunda tun farko baki ɗauki shawarar mu ba ….
Akwai wani hatsabibin malami wanda yataɓa yimiki aiki har kika samu cikin Sadiq .
Tagumi ta zuba alamar tunani , momyn Sadiq ce tace “wlh wanan karon bazan aikata zina ba inaji ina gani ,
Nice ban jira lokaci ba ai likitoci sunce akwai lokaci dagani har mijina muna aihuwa ,
taɓe baki sukayi tare da miƙewa sukace to kizauna ta kasheki karkuma ki neme mu , fashewa tayi da matsanancin kuka ta miƙe tsaye tana takowa gabansu tace …
To ni mezan sa boka yayi mata ?” sallamar da sukaji ne yai sanadiya faɗuwar gaban momyn Sadiq ta dafe ƙirji suko sauran ko a jikinsu sukayi waje kowacce na kallon Abdallah .”