LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

LAMARIN KADDARAR AURE NA COMPLETE NOVEL

Yau kwananta biyu a gidan su hakan ya yiwa dady dad’i kasancewar yafi son yaga duk zuri’arsa sun auri mai kud’i , zaune suke da rana kowa da farfesu a gabanshi , Afnan wayace a hanunta , ta gwada number Haisam shiru tak’i shiga , hakan yasata shiga damuwa tace ”wayo Allah , hankalin kowa na parlorn ya dawo kanta , momy ce tace ”to mai yafaru kuma?”sunkuyar da kai Afnan tayi tace ”babu komai , dady ne yace ”yanzu so nakeyi wanan yaron yazo ya baki takardar ki kinga zaki fara sabuwar rayuwa ko , uhm kawai Afnan tace ”kana ta maida hankali ga abinda take ci ta ajiye wayar a gefe , suna kammala ciye ciyensu mai aiki ta kwashe kayan ta kai kitchen , Afnan ce ta mik’e ta nufi d’akinta na da lokacin tana budurwa , fad’awa makeken gadonta tayi wanda fentin jikinsa pink ne ,kifa kanta tayi a fillo tafara rera kuka , tana dana sanin fitowa daga gidan mijinta mai yasa tayi haka ?”anya tayiwa rayuwarta adlaci kuwa? kodai zata gudu ne ?”wata zuciyar ce tace ”inhar kika gudu to zaki janyowa kanki mumunan hukunci gurin dady da Anty Bilki.”

Mama na komawa gida ta fasa asusunta ,kud’i ta k’irga sunkai dubu ashirin ,kuma duk a kud’in da Haisam yake bata ne take tarawa , gud’a ta rangad’a wanda hakan yai sanadiyar juyo da hankalin mata gidan , tanajin alamun tafiya ta danne kud’in a k’asan cinyarta tace ”kowa ya watse ba komai nake ciba , duniyar ce ta yimin dad’i , komawa sukayi dan suna ,tunanin fad’a irinna mama , suna komawa ta janyo kud’in ,ta gyarasu tasa a lalita , ficewa tayi gidan wata dilaliya dake kusa dasu , tana sai da kayan d’aki da bokitaye da sauransu na amfani , sababbi da tsofafi , da sallama mama ta shiga , gidan samun dillaliya tayi a zaune tana k’arga kud’i , cikin fara’a d’ajin sallamar mama yasata , gyara zama tace ”barka da zuwa , ywwa mama tace ”inason kayan sa lalle bokiti ta kofin silba da kwano shima na silba , magajiya ce tace ”angama kud’inki dubu biyar , cikin rawar jiki mama ta mik’awa dilaliya kud’in aka had’a mata , cewa tayi sai zuwa dare zatazo ta d’aika dan munafukai sunyi yawa .”
Tafawa sukayi kana mama ta fice , bayan isha’i mama ta yafo gyale tayi ,hanyar gidan su magajiya , samun kayan tayi a gefe a baranda ta ajiye mata , dajin sallamar mama yasa magajiya fitowa ta nunawa mama kayan , d’auka tayi ta fice kai tsaye gidan su ta nufa , sai da ta lek’a babu kowa a tsakar gidan sanan ta wuce , washe gari ta shiga kasuwa ta siyo kayan buk’ata , tana dawowa baba yake tambayarta ina taje. “

Maganar auran Haisam tayi masa , dayake shima kamar ta gama dashi yasashi yin shiru, wata k’anwarta ta kirawo suka shirya kayansu , number Haisam ta kira , cikin sa’a ya d’aga maza maza kazo mama tace ”masa cikin sauri yace ”ganinan zuwa , ba a d’au lokaci mai tsayi ba Haisam ya k’araso gidan , da sallama ya shiga ganin mahaifiyarsa da k’anwarta yasashi durk’usawa ya gaishe su , amsawa sukayi cikin fara’a , k’anwar mama ce ta dubi Haisam tace ”ya maganar kai sadaki , zaiyi magana mama tace ”wlh mudin kaimin wata maganar da bata shafi na Maimunatu ba sai na sa6a maka , cikin sanyin jiki Haisam yace ”sati mai zuwa zan bada akai nawa sukace ?”mama ce tace ”basu yanke ba amma zan kuma tura manya , okay kawai Haisam yace ”kana ya mik’e ya fita.”

Bayan ya mik’a musu d’ari biyar biyar yayi gaba, albarka suka shiga sanya masa , shiko yayi gaba , tundaga wanan rana Haisam ya zamo bashida walwala , yana tunanin zuwa gidansu Afnan yana tsoro saboda ra’ayinsu ta rik’a k’a , da komawarsa gida yai wanka ya janyo filon Afnan ya rungume yanajin kewar matarshi , cikin sanyin jiki ya janyo wayarsa , yafara lalubar number Afnan , cikin rashin sa’a yaji a kashe , tsaki yayi ya maida kansa ya kwanta yana tunani da ban daban , oh god wai maiyasa Afnan zatayimin haka ?”in anyi magana tace tana sona to wai shin haka so yake?” mik’ewa yayi ya nufi toilet d’in d’akin Afnan d’in , cikin sanyin jiki , alwalah yayi ya tada sallah lokacin anayin isha’i , nafila yayi ya kai kukansa ga rabil izati, ya dawo yakuma gwada number Afnan , cikin sa’a ta shiga , wani sanyi ne ya ziyarci zuciyarsa lokacin da yaji sautin muryar ta ta doki dodon kunensa , lumshe ido yayi , yana saurarar sallamar ta , hak’ik’a yayi kewar matarsa sai dai a halin yanzu yana ganin kamar bazata dawo gareshi ba, jin shiru yasa Afnan cewa my honey kayi shiru kuma lpy ? Haisam ne yace ”inafa lafiya kina gani tunaninki yana neman sani cikin uquba wlh karki d’auki hak’k’ina , kinsan dai ban baki izinin tafiya ba ko?”

A halin yanzu bazan iya jure rashinki ba a kusa dani, walh kin horani , wane laifi nayi miki dahar kike k’ok’arin azbtar dani , kalaman mijinta suna shigarta a hankali , k’ara rungumo filon da take zaune a kujera tayi kana tai rau rau da idanu tace ”zan dawo mijina dan Allah karka yi fushi dani zan dawo, k’ara sa sauta murya Haisam yayi yace ”to yaushe zaki dawo inyi miki tanadi na musamman , murmishin yak’e tayi tace ”zan dawo surprise zan yimaka , okay to Allah ya dawomin dake lafiya , suka ajiye wayar , momy dake tsaye a kanta tace ”keda mara zuciyar nan kuke waya ko ?”to babu maganar komawarki gidansa ,karma in k’araji , wlh zan sa6a miki , sunkuyar da kai Afnan tayi tace ”momy kiyi hak’uri dan Allah bazan sake ba , wucewa momy tayi batare da tabi ta kanta ba , washe gari Haisam ya gyara gida ya wanke ya sa turaren wuta ya gyara gado ya wanke toilet yanata farinciki, komai cikin zumid’i yakeyi , yana gama gyare gyaren , ya shige wanka yana fitowa ya shafe jikinshi da turaruka masu k’amshi ya ciro dakakkiyar shaddar sa mai kalar ruwan toka yasa yakuma feshe jikisa da turaruka, d’aga kansa yayi k’arfe sha d’aya na rana 11am k’ara gwada number Afnan yayi , jin shiru tak’i shiga yasa shi doka tagumi .”


Bayan sati d’aya , Afnan ta rame sosai momy da dady sun kuma matsa mata akan bazata koma gidan Haisam ba , Haisam tayi kira a waya shiru , tun tana shiga ba’a d’agawa har yazo a kashe ,damuwa sosai ya shiga gashi safiyar yau mama ta matsa masa akan kud’in auran da yayi alk’awari, ba shiri ya tattara ragowar kud’insa na bank ya nufi gidan su mama , tana ganinshi tahau washe baki Haisam kansa na sunkuye ya wuce d’akin maman itama shigowa tayi tare da janyo bokiti ta mik’a gabansa ta zauna , Haisam ne yace ”mama wanan kayan fa?”washe hak’ora mama tayi tace ”wato da tsumun mu muke tare , jingina kai Haisam yayi batare da yakuma magana ba , ciro kud’i yayi yana juyasu ya ajiyesu a gaban mama , wani irin farinciki ne ya lulu6e mama , tace ”d’an albarka Allah yasa wanan auran kayi a sa’a , abin mamaki da ya dami Haisam shine mama bata ta6a kiran sunan Afnan kokuma cigiyarta , sai ta batun sabon aure take, maganar da mama tayi ne ya sashi dawowa daga duniyar tunani Haisamu kud’in nawa ne , kansa a sunkuye yace ”dubu d’ari ne farinciki fal zuciyarta tace ”Allah yai maka albarka ,amen Haisam yace ”kana ya mik’e yace ”to mama zan tafi , zaro ido tayi tace ”wato ni yanzu nazamo abokiyar jin kunyarka ko ?”
Ran Haisam babu dad’i yasa kai ya fice .

Anty Aishe ce keta doka sallama a parlorn Alhaji, amsawa yayi tare da cewa “Anty kishigo mana , shigowa tayi tana dad’a k’arewa Alhajin kallo , murmushin mugunta tayi dan tanada labarin Afnan ta dawo gida , shine tazo tayi ziga , Alhaji barka da hutawa ,yawwa Anty kinzo lafiya , lafiya lau Anty tace ” sai kuma naji wai wanan yarinya ta dawo gida?” uhm kedai bari Anty wlh abin yayimin ciwo dan rainin wayo ma aure zai k’ara , to bama batun auran ba ,mai yaci bare ya basu da har zai tattago wa kansa aure ?”nisawa Anty tayi kana tace ”to albishirinka yanzu daga kusada gidansu nake dan in tambayi halin da Afnan d’in take ciki , ashe kusan kullum sai uwar mijin tazo tayi mata duka , kuma tace ”sai ta wanke mata kaya????anty ta shararo k’arya …. cikin tunzura Alhaji yace ”dama wanan wahalar takesha shine ta zauna ?so takeyi ya kasheta ya huta ko.”
Gyara zama Anty tayi tace ”koni ba son auranan nakeyi ba kai ka biyewa dangin uwarta dahar sukaci galaba akanka , ran Alhaji ya 6aci sosai ,yanzu kam ya yards da maganar Anty Aisha tabbas laifin momy ne aikuwa babu ita babu auran Haisam, dama ni ba son yarana sudinga shan wahala nakeyi ba , jeki kiramin Wasila ????dan k’ari tau babu batun cewa momy , Anty Aisha ce ta dubi Alhaji tace ”gaskiya bazanje ba karma ka kirata yanzu dan wlh zataga kamar nice na zugaka ka cimata mutunci , eh hakane .✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button