MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Janafty
MIJIN KANWATA..!
(k’addarata)

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

Page 8

Kwanakin da suka Biyo duk na Shiryen Shiryen Daurin auran ne Hajiya Zabba”u da tawagansu Hajiya karama da ya”yansu gabadaya gidan Tun Ranar Laraba suka sauka a kargi Sadiq kadai suka Bari agida sai Ranar Jumma”a sai Biyo Abba su Taho tare Hatta da wasu Daga cikin Hadimansu Hajiya ta taho da wasu aminttunta domin ita tafi yarda tayi aiki ko Mu”amala da wanda ta aminta dashi.
Uwar Amarya kuwa Hajiya Salame sai da kowa ya gama zuwa kana ta iso Ranar Alhamis da yammah ita da gayyarta ta Fake da cewa Amarya tayi Lonching ita da kawayenta achan Jos alhalin bayan Taron harda Tsaikon Kawarta Dataje Maradi karbo mata sako sai da ta Jirata ta dawo ta bata sakon kana suka Dunguma suka iso Kargi.
Gabadaya Ahalin Maimartaba na Nesa dana kusa sun Hallara Domin wannan Bikin Hajiya Zabba”u yadda taci Buri akansa in ma wani bai zo ba ai sai ta Kullacesa nan da nan aka Bude Store din Masarauta Ana ta fitowa da kayan abinci Nau”i Nau”i dabam dabam Hadiman Bangaran Madafa suna ta aikinsu.
Amarya ashashen Kilishi aka Sauketa ita da kawayenta Guda Biyu da suka Taho Daga jos sai sauran Dangi yan Biki,sauran suna Shashen Fulani da sauran manyan Sassan Gidan na Sarkin Kargi mai Girma da Fadi.
Sulaiman ya Fadama Saifullahi yadda sukayi da Sunaima sai ya nunamai ya Bata Kudi saboda Hakkinsa ne zai kara aure Tunda ita ba”ayi mata kayan akwatin Dannan Kirji kamar na al”ada ko alokacin Tarewarsu Abba ne yayi mata kayan auran Hajiya karama ita ta Hada kayan shiyasa da Saifullahi yace ya bata wani abu ya Ciro Kudi a banki Sabbin yan Dubu Dubu na 50k ya saka mata ambulan ya rike a wajensa da Niyyar Ranar Jumma”a Da Safe zai bata kafin su wuce.
Rana ai daman bata karya sai dai Uwar Diya ta ji kunya Tun karfe 8am na Safe Saifullahi ya iso Gidan Sulaiman yana Jiransa Tare zasu Tafi Zasu Biya Gidan su Sunaima su Dauki Baba,Tunda zai je sai sulaiman yace ya bari su wuce Tare Sani kuma yana Kamfanin Madaran Sulaiman yake karban packages wanda zasu tafi Dashi Chan Kargi saboda Maimartaba da Sauran iyayan Sulaiman din.
Saifullahi yaci Shadda Riga da wando Harda Babban Riga kalan Sararin Samaniya,ya kafa Hularsa Zanna Bukar da Rufaffan takalminsa baki na Fatar damisa.
Yana ta Kiran Sulaiman yace mai gashinan Fitowa shi kuwa alokacin Ya gama Shirya kansa Cikin Wani Rantsntsiyar wangambari mai maiko da yarari akalah zata bama Dubu hamsin baya Kalanta Sky Blue ce,ya saka yar ciki da Babban Riga sai ya Dora Hularsa Zanna mai Zanen kalar Shaddarsa ya saka bakin Takalminsa rufaffe na Fatar damisa sai agogon Hannu baki shima na kamfanin Rado.
Yayi kyau har yagaji da kyau duk da Fuskarsa ba Fara”a sosai yasan ai bai isa ya Zillema wannan Daurin auran ba Tun Jiya Hajiyarsu ke kiransa wai yana Hanya ne..?ya fadamata sai gobe zai Taho bazai bar ma”aikata ba kowa ba wane shi ya kwanta yace bazashi ba yau da garin Allah ya waye baisan adadin Kiranta dana ya”yanta Daya gani ba Harda Kiran Hajiya karama yayi bakam Domin yasan Duk Hajiyace zatace su Dokamai Kira daga yau ai shikeman anyi an gama Sai Hajiya ta barsa ya Huta.
Yana Saukowa Daga Saman Upstair yana amsa Kiran Saifullahi Daya Gwazabamai da Kira ya Daga wayar Cikin Muryansa akoda yaushe yana Fadin”Kafa isheni da kira..Gani nan Saukowa..!
Saifullahi yace”Su Abba fa Tuni sun kusa isa kargi..kai kana Kaduna kana batamana Lokaci..!
Tsaki yaja ya Datse kiran daidai Lokacin yana isowa Falon daya iske Magajiya tana ta gyara Dukawa Tayi ta Gaisheshi ya amsa mata sama sama yana Fadin”Yaran nan sun tashi kuwa Magajiya..?
Kanta na kasa tace”Eh Tun dazu ranka ya Dade..Hajiya ai ta shiryasu itama na ganta ashiryenta ko har dasu zaku Tafi Chan Masauratar Yallabai..?
Kai ya girgiza kafin yace”A”a Gidan su zasu je..Keda da Samira zaku zauna agida in kuma Zata tafi Dake chan Saboda Yara shikenan..!
Bai bata ma Zarafin mgana ba ya Tunkarin Dakin akoda yaushe yana Samun Faduwar gaba indai zai Tun kari Dakin
Ya tura da Niyar shiga yaji Dakin a Garkame,sai ya tsaya yana Knooking Lokacin Tana kokarin sakama Wafiyya Takalminta dan karamin Cover na yara taji Buga Kofar ita Duk azaton to ko Magajiya ce Domin ta Sata Hada musu abinci a lunch Box dinsu da kayan da zata tafi dasu kai Tsaye ta Mike bayan ta gama Sakama Wafiyya Takalmin tana gyara Zaman zanin Leshin Dake Jikinta ta Tunkari kofa kanta Tsaye Wafiyya kuma tabiyo bayanta Digi Digi da Tafiyarta na yara masu jiki.
Bata kawo ma ranta shine ba yasa ta Bude Kofar kanta Tsaye tana Fadin”Sannu magaj….!
Sauran kalamanta sun makale ne sanda Fuskokinsu suka Hadu waje Daya Domin ta bude Kofar ta Tsaya shi kuma bai kawo komai ba ya Tusa kansa zai Shigo goshinsu ya Hade waje Daya sannan Karan Hancinta ya Gogi nashi Dukkansu atare suka Janye Jikinsu Lokaci Daya da wani Bakon Yanayi ya Ziyarce Sunaima Hannunta ya kusa Takore kofar saboda Tayi Saurin janyen jikinta Cikin Zafin Nama Saraki ya Rike hannun nata gam Har sai da yaga ta Tsaya da Kafafunta Idanuwanta Ta lumshe kafun ta Budesa tsab a kansa Shima kallonta yake cikin wani yanayi bai Taba ganin tayi kwalliya irin na yau ba Tunda yake da ita.
Tana Sanye da Daya Daga Cikin Swiss less din Da aka sakamata Cikin akwatin Lefenta,Bata taba saka atamfa ko wani less ba sai dai Takan yi amfani da kayan barci ko Dagayen Riguna sune kayanta bata zuwa Biki bata zuww suna Daga Gida sai wajen aiki Shiyasa amfanin da kayan suka zame mata Wahala bama Haka ba Duk Abunda ya Shafi Sulaiman Kargi Hakuri kawai take tana amfani Dashi Domin babu yadda Zata Gujema Kaddaran data Hadasu zama waje Daya..
Dinkin riga da Zani ne Rigar Fittied ce data amshi Jikinta Matuka Ta Daura Dankwalinta saman Kanta wanda ya Zauna Tsab saman gashin kanta da ta nannadeshi Cikin band,fuskarta ba Kwalliya sai dai ta shafa Hoda da Man Baki mai kalan Ja kalan sai Dankunneye Kunni da wuya sai awarwaro hannunta Tayi kyau matuka kamar ba ita ba ahaka sai ya ganta kamar Sunaira sai dai bambamcin ita Sunaira Tafita jiki da Kiba ayayinda Sunaima take yar Ficika da ita bata da Cikar Jikin Hallita ballatana cikar Dakin Miji.
Ya Shagala da kallonta yasa baisan tana Kokarin zame hannunta ba sai da yaji ta Zame hannun nata kana yadan Basar Cikin Muryansa akoda yaushe yace”Are u ok..?
Kai ta gyadamai Tana kallonsa Ta gefen Ido bata wani Tsaya karemai kallo ba ammh tasan yau kam yasha kyau sosai,Wasim ne da Wafiyya ne suka ga Babansu suka Nufesa suna Kiran Daddy Daddy dukawa yayi ya Tarbesu Dukkansu ya Daukesu Lokaci Daya yana Fadin”Eyye..Kunsha kyau..!
Yake Fada yana kallon Sunaima Data koma Bakin gado ta Dauko bakin Hijabinta ta saka Bata ma juyo ba ballatana ta Fahimci yana kallonta.
Wasim yana Sanye cikin Riga da wando na Shadda,Irin wanda Sulaiman ke Dinkamasa ne,harda Hulansa yayi kyau sosai sai Wafiyya Dake Sanye da Bulawis na yara Iyakarsu gwiwanta mai kalan ja da Fari kanta Sunaima ta saka mata karamar Hula ta Rufe mata kananan Kalaban Datayi mata Jiya da Daddare.
Dukkansu suna sanye da Takalma Rufaffu ne.
Wasim ne mai Surutu fadi yake”Daddy Anty tamana wancha..Ta sakamana sabon kaya zamu je gidan Inna..!
Yake Fada yana Murna Wafiyya ganin Yana Murna sai ita ta fara Washe baki Tana gaurancinsa Shi kuma yana Biye musu Cikin Sha”awa da Burgewa Takawa yafarayi zuwa Cikin Dakin Lokaci Daya ya saka kafa ya maida Kofar ya Rufe har tayidan karan Daya sa Sunaima ta waigo tana kallonsa Bai Taba ganinta da mayafi ba Koda yaushe Cikin irin wadanan Hijaban take masu Daurewa ta saman kai.
Ganin Tana saka wayarta Cikin karamar Jakar Dake hannunta yasa yace”Kuma kun Shirya kenan..!?
Dakai ta amsa mai batace komai ba ganin yaki Sauke yaran yasa ta Dago Tana Fadin”Daka Sauke su..kada su bta maka kaya.!
Mamakinta ya kamasa sai bai ce mata komai ba illah gyara Tsayuwarsa da yayi yana Fadin”Wazai kai ku..?sani na aikesa kuma Dagachan zai wuce Kargi ne..!
Bata Damu ba tace”Daman ai ban saba Shiga Mota ba..Adaidaita Shine Daidai da dan Talaka irina..!
Dakuna Fuska yayi yana kallonta Ita kuma sai ta maida kanta Gefe Cikin Kaushinsa yace”Ko Sau Daya bazaki koyi da Halin yar”uwarki ba..Sunaira ba Haka take ba..Ba haka takemin mgana ba..!
Sai da ya fada sai yaga baikonsa itama sai kalamansa ya bata mamaki ganin ta Tsaya tana Nazarin mganarsa yasa ya Sauke Wasim da wafiyya a kasa ya Saka Hannu a aljihun Wandonsa ya Dauki Farar ambulan din Daya sakamata Kudi ya mika mata Kin karba tayi tana kallonsa Cikin Rashin Sakewarta tace”Name nene..?
Kai Tsaye yace mata”Kudi ne..Ki rike a Hannunki..!
Nokewa Tayi tana Fadin”Bazan karba ba..Nacemaka bana Bukatar komai..!
Bai Tsaya Sauraranta ba jin yadda Wayarsa ke Daukan Agaji yasan Saifullahi ne kan Jakarta Dake gefen gadon ya ijiye mata yana Fadin”Koda baki Bukata ya zama Dole ki karba..Hakkina ne na baki kuma kema Hakki ne ki karba..!
Ku fito mu kaiku daman zamu Biya mu Dauki Baba..!
Yafada yana Kokarin Ficewa Daga Dakin Sunaima Cikin mamaki tace”Baba..?
Juyowa yayi yana Fadin”Eh yayi Laifi Saboda zai je Daurin aurena..!
Baki ta Mele batace komai ba Shi kuma sai ya Duka ya Dauki Wafiyya data Biyosa ya Rike hannun Wasim suka Fice Daga Dakin bata tsayama kallon Kudin ba ta barsa nan saman Madubin Dakin ta Dauki jakarta ta Rataya bayan ta saka wani Takalmi Flat baki ta Fito Daga Dakin haka kurum Taji tana Bukatar Sirri ta Saka Key din Dakin ta kulle aharaban Gidan ta gansu suna jiranta ga Samira ga Magajiya suna Tsaye bayan ya gama Fadamusu su kula da komai.
Magajiya ce tace”Hajiya da Yallabai yace Tare zamu tafi..!?
Sunaima tace”Eh haka yace..Ni nace kiyi Zamanki ai zan iya Kula dasu..Gwara ki Tsaya agida ki kula da komai Domin ba lalle bane wacce aka bari tayi yadda ZAi yi ma su Hajiya Dadi in sun iso ba..!
Tafada kanta Tsaye ta koma kuma ta Tauke bakin kamar bata taba Dariya ba Samira na jinta tasan da ita take Mirmishi tayi batace komai ba Domin Hajiya Laila na zuwa ai yar Dakinta Zata koma alokacin ne Zata gasa ma wannan Tsohuwar gyada ahannunta.
Abayan Booth aka saka karamar Jakar kayan su Wasin da Tarkacen madaransu harda kayan Wasa Sulaima ya shiga gidan gaba Dauke da Wafiyya ita kuma Saifullahi ya Bude mata Gidan baya yana Fadin”Antynmu barka da Safiya..!
Kadahan kadahan ta amsa mai aranta tace in ma Gatse kake ai sunan kenan Daga haka ta Dinke ranta Sulaiman kuwa Nata Hararan Saifullahi ji yake kamar ya Bugesa in yana Fadin Antynmu din nan to Antynshi shi da Uban wa..!
Har suka Fice Daga Gidan su magajiya da Megadi na Binsu da adawo lafiya da Fatan Allah yasa a Daura aure Lafiya.
Tunda suka Dauki Hanya bata ce komai ba sai Wafiyya Datake ta Gaurancinta Wasim kuma na Jikinta yana Wasansa sai Saifullahi ne ke mganar abokan aikinsu da ma”ikatansu suma duk wasu sun wuce chan Kargi,Sulaiman na Jinsa kala dai bai ce ba sai lura yake da Sunaima ta madubin Mota ita batasan ma yanayi ba shi kallonta yake yana so ya gani Da gaske ne ashe basu kama da Sunaira sai ayanzu yake yarda Sunaira Tana da Dan Fadin Fuska yayinda Sunaima keda Doguwar Fuska ga kananun Idanuwa kamar kuma sai dai kama kawai ta Jini.
Cikin Lokaci  sai gasu sun iso anguwar dosa kofar gidan su Sunaima Tun daga nesa suka Hango Ahmad Tsaye Kofar shagon Hamisu yana Tsaye yaci Farar shadda kayan sallansa ne na bara harda Hula Tunda Sunaima ta Hangosa tasam Ahmad yaci Burin shima sai Baba ya tafi Dashi Mirmishi tayi acikin Ranta sanin Halin kanin nata.
Yana ganin Motar ai yasan Motar Sulaiman ya taho da sauri suna gama parking ya Bude ma Sulaiman gaba yana Fadin”Ah yallabai barkan ku da zuwa..Daman mun Shirya ni da Baba kumuke jira..!
Wafiyya na ganinsa ta fara Zillo”anchul..!
Yana Dariya ya mika hannu Sulaiman ya bashi ita yana Fadin”Akwai amana Yar gidan anchul!
Sulaiman yana kallonsa cikin Fara”a yace”Ahmad harda kai za”a je..!?
Yana sosa kansa yace”Ai na Shirya ne kawai..ka tayani Rokon Baba yabari nidai yau naje masarautarku Ranka ya Dade..!
Saifullahi Daya kariso wajen yayi yar Dariya yana Fadin”Mallam Ahmad kada ka damu yau dakai zamu je Kargi da yardan Allah..!
Fadin haka yasa ya washe baki Sunaima Da ke cikin Mota ganin sun manta da ita yasa ta Bude Murfin Mota ta Fito ita da Wasim sai alokacin Ahmad ya ganta yace”Ah..Antynmu…Wai Allah sai da kika ga zan yi tafiya zaki zo..!?
Yafada yana Dariya Wasim ke ta Kiran sunansa yasa ya rike hannunsa Sunaima ta Dungurema Ahmad kai tana Fadin”Ba inda zaka ayaho..Muna Gida Tare dakai da Inna..!
Ahmad ya bata rai yana Fadin”Ah fa nan fa Daya Antynmu..yau kam Fadan Sai dai kijisa ke kadai nida Baba Allah yayi mana Freemode yau..!
Dariya ta kamata har sai da ta Murmusa ta Bugi kafadansa ta Fara Tafiya tana Fadin”Sai na Fadamata..!
Yace”Oh ko kin Fadamata taga bata ganni ba kanki zata Sauke gwarama ki Rufa asiri..!
Hamisu mai shago ne ya kariso yana Gaisheta ta amsa mai Cikin Dan Sakewa Sun nufi hanyar shiga gida ita da Ahmad da yaran wanda ganin Sunaima yasa ma ya manta da su Sulaiman dake binsu da kallo Saifullahi ya karkato Gefensa yana Fadin”Wlh kadai ji kowa Anty yake Kiranta..Anya Kiran sunanta kai Tsaye ba Rashin ta ido bane..!?
Karamin Tsaki yaja zai yi mgana sai ga Baba ya Fito yana gyara Babban Rigansa sun kusa cin karo dasu Sunaima ganinsa yasa ta Tsaya Cikin Fara”a yake fadin”Maraba da Sunaima..Ah maraba da Aliyu da Zabba”u..!.
Yaran suka fara Kiransa Baba baba..Wafiyya ya Dauka Wasim kuma ya Dafa kansa Sunaima Ramkwafawa tayi tana Gaisheshi ya amsa mata Cikin Sakin Fuska Sulaiman su yake Kallo sai yanzu yagano dawa Sunaima Take kama da Babanta ne Domin Harta Tsarin Dariyarsu irin Tashi ce.
Karisowa sukayi suma suka rankwafa suna gaisheshi ya amsa musu Cikin Fara”a yana Fadin”Ai tun dazu na Shirya kada kuzo kuna jirana..!
Da sauri Ahmad yace”Wlh ai tun Safe muka shirya ko Baba..!?
Hararansa yayi yana Fadin”Na gayamaka bazan je dakai ba ko Amadu..?
Baki ya Tura yana Fadin”Plz Baba..!
Sunaima tayi yar Dariya Tana Fadin”Baba kada kaje dashi..!
Ya marairaice yana kallonta yana Fadin”Kai Antynmu..kar muyi haka Dake..!
Saifullahi ne yace”Baba kayi Hakuri muje dashi ai ba komai Duka Dayane..!
Sulaiman dai bai ce komai ba Baba ya kalli Sunaima yana Fadin”Sunaima Dake za”a tafi chan kargi ne..?
Da sauri Sulaiman yace”nan zata kwana ita da yara Baba..ai ba Taro bane sai zuwa gobe sai ta koma in sun kawo Amaryan..!
Sai da kuma ya fadi Amaryan sai ya Dago yana kallon Sunaima ita kuma ta kauda kanta Baba yace shikenan Daganan sunaima taja ya”yanta suka shige cikin Gida Ahmad na Fadin tace na Inna su sun wuce ta shige Tana Dariya Daman Inna taji Hayaniya Daga Zaure.
Tana ganin Sunaima ko bata Fada ba Taji Dadin ganinta saboda akwai mganar datake so suyi da juna Maraba da sannu da zuwa ta fara musu yaran suka Riketa suna mata Oyoyo Inna na Dariya tace”Ai yau Inna Zatasha Kira..!
Sunaima na Cire Hijabinta tace”Inna Har gobe ma..nan zamu kwana..!
Bata gama Rufe baki ba sai ga Ahmad da Tarkacen kayansu ya ije ya Fita da Gudu yana yi musu Bye Inna ta Bisa da kallo Tana fadin”Wannan yaro dai sai Allah ya shirya..!
Sunaima tayi yar Dariya tana Zama kan Tabarman da Inna ta Shinfidamata ita kuma tana Fadin”Kamar da sanyin safiya wajen nan..Ko zaki shiga ciki ne..!
Tace”Bari dai mu zauna nan Inna..Ina kwana..!
Inna tace”Lafiyalau..su baban naku sun wuce ne..?
Kai ta gyada kafin tace”Eh shi ya kawo mu shi da abokinsa sun Dauki su Baba sun wuce..!
Inna ta kada kai Tana Fadin”Allah ya Kiyaye Hanya..Uhm..Allah yasa a Daura aure lafiya..Sai mukaji Aure Daga sama Daman ko baki zo ba Wlh zan kira ki Sunaima na kuma ji Dadin da zaki kwana anan zamu samu Lokacin mgana Sosai..!
Sunaima tabi Inna da kallo batayi mgana ba to me zatace ai tasan Tsatsuniyar gizo ai bata wuce ta Koki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button