MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL


Acikin wani kyakyawan Lambu mai Cike da korayen ganye shar shar dasu Ta Hango wata mata zaune kan wani kututuran Icce gabanta wani karamim Koramana ne tana ta Daukam kananun Fararan Duwatsun Dake wajen tana Jefawa cikin Ruwan Wanda yake Fallasomata har saman Fuskarta Tana Sanye da Fararan kaya Tun daga sama har kasanta ko Tafin Hannunta ba”a gani.
Sunaima ta samu kanta Cikin Lambun Tana Faman waige waige Da kayan Jikinta Ta ga kanta acikin wannan kayattacen Lambu ba gida gaba ba gida baya sai ta fara tafiya Kafarta ba Takalmi tana waigen bayanta da gabanta.
Acikin hakane ta Hango bayan Sunaira Bata iya ganin Fuskarta ba yasa ta fara takawa zuwa Wajenta Daidai tana zuwa Daidai tana Mikewa tajuyo suna Fuskarta juna ido Cikin Ido da wani Rawan baki dana Jiki tace.
“SUNAIRA…!
lokaci daya ta Nufeta zata Rumgumeta da Sauri ta kauce Daga Rikon Cikin mamaki Sunaima ke kallon yar”uwanta kafin tace”Meyasa kika Hanani Rumgumeki yar”uwata..?
Sunaira takalleta da kyalin Idanuwanta cikin Hasken Farin watan Daya mamaye wajen.
Tace cikin amon muryan ta data Sauya”meyasa zan yadda ki Rikeni SUNAIMA..?
Alhalin bayan Barina Duniya baki Rike Amanar yan”uwantakan mu ba..Baki yadda ni din yar”uwanki bace..!
Da sauri Sunaima tace”Meyasa kikace haka..!ina da yar”uwan data wuceki ne Duk Fadin Duniya..?
Sunaira ta yi Kayattacen Mirmishi Kafin tace” In kin Daukeni yar”uwanki ta Jini meyasa kika ki Rumgumar KADDARANKI…?
SULAIMAN ZAHIRINKI ne Sunaima Shine Duniyarki ayanzu…!
Tafada kafin ta juya mata baya tana Fadin”Ya”yan dana Haifa Duka mallakin ki ne Sunaima…Sulaiman Kaddaranki ce ni aronta na karban miki gashi kuma na Dawo miki dashi ammh baki Rikesa Dakyau ba…To ina so ki sani Sulaiman na Cikin Wani Hali kuma ke kadaice Aduniyarsa da zaki iya Fito dashi daga wannan Halin ke kadaice Duniyarsa yanzu..Kece Kaddaransa..Ki karbesa Hannu Bibbiyu ki gyara Duniyarsa in kina so na kara zuwa Har ki kirani yar”uwanki na amsa..!
Tana gama Fadin haka ta bace bat awajen Sunaima ta Fara Waige waige tana Kiran sunan Sunaira Kamar Zautattaciya.

“Sunaira…Sunaira…Sunaira….!


Afirgice ta Farka kamar Wacce Tayi Gudun Famfalaki gabadaya ta Hada Zufa Har Tsiyaya take Dakin Take kallo Ganin haske ya gauraye ko”ina sannan ta koma tana kallon kanta Kayan Jikinta ne da su taga Sunaira Tun sanda ta Fara kukan nane barci ya kwasheta bata sani ba Shine tayi mafarkin Taga Sunaira..
Jikinta na rawa ta mike Jiri ma Take gani Saboda kanta gabadaya ya Daure Zufa ta kara yankomata Ta sama da kasa ta yarfe,kanta ta Dafe tana Fadin”Innalillahi Sunaira…Sunaira..!
Take Fadi tana kokarin Tuna abubuwan da suka wakana acikin Mafarkinta ta kasa ma Dora mganar akan Mizani Jikinta taja ta Shige Tiolet wanka tayo gabadaya kasala ya Rufeta Alwala ta Dauro Saboda barcin kwata kwata ya Fita Daga Idanuwanta.
Darduma ta Shimfida bayan ta Saka wata Doguwar Rigar barci da katon Hijabinta na Sallah ta Fara sallar Nafila Raka”a shida tayi kana ta Zauna ta Fara karatun Qur”ani sai da asuba ta kawo Jiki Sunaima na Zaune tana karatun Qur”ani tana kuka Gabadaya lamarin ya kasa barin Ranta tana Cikin Wani Halin Datake Bukatar matallati Wazata Tunkara Awannan yanayin Datake ciki bata Tuna Kowa ba awannan yanayin ba Sai INNA..!
UWA domin awannan gabar Uwace kadai Zata iya Tsayawa ta Fahimceta har tatayata samun ma kanta Mafita da wannan Gudurin ta Tashi da Safe sai karfe Biyu take da zuwa Wajen aiki bata Sauya zani ba kamar Kullum ba yau ma ita takai su makaranta Yau ma Din lemo ta siya musu da Biscuit Dakyar ta Lallashi Wasim ya Fara Rigiman kwai zai ci to har alokacin Laila bata bada damar Bude Kitchen din da Wuri ba kamar yadda aka saba ba.
Daman da Shirinta ta Fita Daga makarantar su Wasim Gida ta wuce a kofar gidan taci karo da Baba ya Fito da Mashin zai tafi Wajen aiki Ahmad ma ya Shirya zai tafi makaranta yana Jiran Baba ya Daukesa ganinta da Safe haka Fuska duk ta kode yasa Baba ya kalleta kafin yace”Sunaima Lafiya..!?
Tana Duke tace”Lafiyalau Baba…!
Bai matsanta mata da Tambaya ba Ahmad ne ya isheta da Tadinsa bata Biyemai ba ta Shige Cikin Gida.
Yanayin yadda Inna taga Sunaima sai jikinta ya bata ba Lafiya da Sauri ta Saki Sharan Tsakar gidan datake ta Bi bayan Sunaima data Fada Dakinta.
Tana Shiga ta ganta Tsaye ko zama batayi ba Cikin Damuwa Inna Tace”Lafiya Sunaima..!?
Sai kawai Sunaima ta fashe da kuka ta isa ga Inna ta Rumgumeta Tana Fadin”Inna ya zan yi..?
Wannan Kaddaran ta auran Mijin kanwata tamin girman da bazan iya Dauka ba Inna..ki bani Shawara ya zanyi..!
Tafada Cikin kuka Inna batace komai ba illah Bayanta data Dafa Tana Lallashinta Har ta Tsagaita Kafin taja ta zaunar da ita saman Kujera kwara Daya Dake Cikin Dakin Waje ta Fita Taje Madafi ta Dibo mata ruwan Randa mai Sanyi ta koma dakin ta bata Tana Fadin”Cire Hijabin ki sha ki Samu natsuwa…!
Ba musu ta Cire Hijabin Jikinta Riga da Sikat din Atamfar dake jikinta ta bayyana ruwan ta karba ta kafa kai tasha da yawa kafin ta mikama Inna ta karba Tana Fadin”Kin samu natsuwa yanzu..?
Kai ta gyada mata Kafin ta Sauke Numfashi Gefenta Inna ta Zauna Lokaci Daya tana ijiye kofin Hannunta Cikin Tattara natsuwarta ta maida kanta Tace”Meke Faruwa ne Sunaima…?

Janafty
MIJIN KANWATA..!
(k’addarata)

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

AFUWAN..!AFUWAN..!AFUWAN..!

Page 12

Dalla Dallah cikin Natsuwar da Inna ta taimaka Sunaima ta samu ta shiga Zayyanemata duk abunda ya Faru Tundaga washegarin Zuwan Laila Gidan da abunda ya faru jiya da Daddare da mafarkin datayi Sunaima ta kalli Inna Idanuwanta sun cika da kwallah Tace”Inna Sunaira ta nagani acikin Mafarkina sai taki yarda tamin mgana ballatana ta Tsaya ta Saurareni Abu Daya take Fadamin Sulaiman Shine KADDARA TA kuma Duniyata ne ni kadai ce zan iya Fiddosa Daga Halin Daya ke ciki…Sannan ta Fadamin daman chan aro ta Rikemin yanzu Kaddaran tawa tadawo hannuna Gabadaya kaina ya Kulle Inna na rasa madafa da Tunanin wannan Wani irin mafarki ne Shiyasa nace bari nazo na sameki na Fadamiki yanzu nan Daga kai Wasin makaranta nake na Zarto nan..!
Ta karishe Fada Hawayen idonta na Gangarowa saman Fuskarta Inna da tagama Jinta da kunnen Basira ta Sauke Tagwayen Numfashi kafin tace”Inna Lillahi Wa”inna Ilaihirraju”un..Allah gareka muke kuma gareka zamu koma ka iya mana abunda muka gaza ka kuma Taimakemu adukan Lamuran mu Ina Fatan wannann mganar ni kadai kika Fadama ko Sunaima?
Inna ta fada tana kallonta Sunaima ta Gyada kai tana Share kwallarta kafin tace”Kema Inna Kinsan bani da wata kawa da zan iya wata mgana da ita..Sunaira ce kuma bata agidan Duniya sai ke Inna..!
Inna ta jinjina kai kafin tace”Kinsan Abunda ke Faruwa da Rayuwar Sulaiman..!?
Sunaima ta girgirza kai kafin Inna Tace”Ai kinsan Sihiri ko..!to shi aka yi mai kuma shi ke Dawaniya dashi..!
Sunaima ta saki baki Tana kallon Inna Kafin ta maimaita Cikin mamaki”Sihiri kuma Inna..?
Inna Tace”Tabbas..Kuma na Mallaka ne Sunaima..Laila bata shigo Rayuwar Sulaiman ba sai da tayi babban shiri akansa..Shi wannan Sihirin na mallaka da Namiji zai zama kamar bawan mace ne komai tace awajensa Shine Daidai yana mantawa da komai nashi indai tana gabansa bar batun Ya”ya ko mata ko iyaye harta karan Kansa ma yana mantawa dashi..Sannan Sihirin yana Sarrafa mallaka Hatta abunda Mutum ya mallaka yake Tare dashi kamar shi Sulaiman zata Mulki Ma”aikatan Gidan da kowa Dake karkashin sa Ciki Hardake Sunaima..!
Sunaima ta Zaro ido kafin tace”Hardani fa kikace inna..?
Inna Tace”Eh Hardake..Sai dai a bayananki na tabbata da Kin Tsallake wannan Sharrin Allah ya kareki abun bai yi Taziri akanki ba..kuma Gaskiya ne kece kadai Mabudin Rayuwar Sulaiman ayanzu..Ni bana Fassaran mafarki kuma bana Duba sai dai ayyada kika Fadamin wannan mafarkin Raina da Jiki na ya bani Yar”uwanki tazo miki cikin Mafarki ne Domin tasakaki ki Farka Daga Barcin Daya kwasheki Tana Fushi Dake Saboda har yanzu baki karbi Kaddaranki ba Sunaima tana so ne ki Mike Tsaye ki nuna ma Duniya Mijin kanwarki yanzu Shine Kaddaranki Domin Dake Dashi ku Rabauta Har gobe Kiyama..!
Ta karishe Fada Lokaci Daya tana kara Nazarin Sunaima wacce tayi kasake Tana kallon Inna kafin Tace”Ya akayi duk kikasan wadanan Inna..?daman kinsan Sihiri haka..?
Inna tayi Mirmishi kafin tace”Kinsan Kawuna Jafaru na Zuntu..?
Sunaima tace”Sosai ma Inna kawu Jafaru dai naki..!
Inna tace”Yauwa to shi..Ai Sana”arsa kenan karya Sihiri Shima da ayoyin Allah sannan yana da Lakanin Shima wani abokinsa Bafullatani da sukayi zama tare a Lagos ya bashi awajensa duk nasan Sihiri da in aka Fadesa nake iya gane Wani iri ne..!
Sunaima ta Jinjina kai kafin tace”to yanzu ina Mafita Inna..?ko Hajiyarsu zamu fadamawa tazo taga Halin da ake Ciki..!?
Inna ta Dakatar da ita da Sauri tana Fadin”Kul kamar ki Fara..Wannan ba Fadan ki bane..ai Diyar tasu ce Saboda haka ki zura ido ki koma Gefe Fadan nan na Hajiya Zabba”u ne na Tabbata yadda take son D’an nan nata da kuma yadda take a Tsayen nan ko Yar”uwartace Uwa Daya Uba Daya bazata yadda yarta ta asircemata Da ba..Muna nan Dake in komai ya Kwabe zaki ji kansu..Kada ma ki Fara Ahali ne Daya ne su din ke kuma ai barece acikinsu Saboda haka wannan Fadan ba naki bane kada ki kuskura ki Saka bakinki..!
Sunaima tace”Inna to mganar yaranan fa?ina Tsausayinsu gashi wannan Satin mai shiga zan Fara aikin Daree fa hannun wa zan barsu?in abaya ga Magajiya yanzu ita kanta bata da Damar hakan..!?
Inna tace”Kada ki damu Babu abunda Zai gagara..Yanzu mafita Dayace Sunaima kuma Tana Hannunki ne..!
Sunaima ta kalli Inna Cikin Rashim Fahimta kafin tace”Yana Hannuna kuma Inna..?
Inna Ta gyara zama tana Fadin”Eh haka nace kuma haka nake nufi..Mafitan da gyaran komai yana Hannunki ne..!
Sunaima ta kasa mgana Ganin Haka yasa Inna ta Cigaba da Fadin”Kinsan meyasa nace haka..?
Bata bata Zarafin mgana ba ta Cigaba da Fadin”Saboda kece Duniyar Sulaiman ayanzu..Ki kauda mganar Mahaifiyarsa bata son auranku ke baki Fahimci Kaddaranki Auran Sulaiman Tundaga Launin MAhfuz bane..?abaya kin Taba Tunanin Sunaira Zata rasu har watarana ki Auri Mijinta..?
Sunaima ta Girgiza kai kafin Inna ta Cigaba da Fadin”To kamar haka nake so ki Auna hakan aranki. sai ki natsu ki Fahimci Shin Tsarin mune ko kuma Tsarin Allah ne..!
Sunaima ta Bude baki Zatayi mgana Inna ta Dakatar da ita da Cewa”A”a ba yanzu zaki bani amsa ba..So nake kije Gida ki Kulle kanki adaki Sunaima ki Fara Nazarin Rayuwarki Tundaga matakin Yarinta Har zuwa yau ki gani Duka Tsarim Waye..?meyasa tun abaya baki yi aure ba Har kanwarki ta Rigaki..?in har kika yarda kika kuma Gano Duka Tsarin Allah ne kuma Kaddaransa ne kece zaki ci gajiyan Auran Sulaiman in har kin yarda kin Amince Shi din kaddaran ki ne kuma da Allah ya Tsara kin Shirya zaman Gidan Mijinki ki Kwaci auranki Domin Samun Aljannah ki Dawo ki Sameni ki Fadamin Inna na yarda na Kuma Amince komai Tsarin Allah ne Sannan zan Rumgumi Mijin kanwata a mtsayin kaddarata ni kuma nayi Miki alkawarin bazAmu kauce Hanya ba kamar yadda wanchan ta Kauce ba da Izinin Lahi Indai jinin Zazzagawa na yawo acikin Jinina kuma yana yawao acikin Jikinki wlh lokaci kadan ne Sai Labarin nan sai Mu Tuna Sunaima komai zai zama Tarihi..!
Inna ta karishe tana kafe Sunaima da Ido tana kara Fahintar yadda ta ke Saurarenta da yadda mganganunta suka Samu Muhalli a wajenta ta gamsu Domin taga Tsoro da wani Sadaukarwa a idanuwan Sunaiman.
Ganin Haka yasa Inna ta kara gyara Zama Tana Fadin”Kada ki Damu kije kiyi Nazari a tsanake..!
Sunaima ta Runtse ido kafin ta Bude ta kalli Inna tana Fadin”Inna in na yarda da duka mganganunki Tayaya Zamu Fitar da Abban su wasim..Sihiri fa kikace Inna..!?
Inna Tace”Wannan ba mtsala bane..Nasanki baki wasa da addu”a da Karatun Qur”ani shima sun samu sa”anshi ne da kuma Kila yana Da Rauni Wajen azkar da Karatun Qur”ani kema ina kyautata Zaton Shi ya kwaceki Allah zamu gayama Sunaina sannan in kika amince Kece ai zaki Gudanar da komai kamar yadda na Fadamiki Tun Farko..!
Sunaima tayi Shuru ta kasa mgana Tagumi kawai ta Zabga wani Abu na Tsirgamata acikin Jinin Jikinta Gabadaya Tana cikin Tashin Hankalin Halin da Sulaiman yake ciki bata da natsuwa Mutun kamarsa ya Dawo haka akwai Tsausayi sannan Taya zata Fara zaman aure da Mijin kanwarta wanda suka Gudanar da Rayuwar aure harda ya”ya a tsakaninsu..?,gaskiya da kunya da Nauyi bama haka ba Tana ganin In Sunaira ta Chanchanta ai ita bata Chanchanta ba Shekarata Talatin aduniya Sulaiman kamar kaninta Take kallonsa Tataya zata Fara zaman aure na Hakika dashi..?
Wannan Nazarin sune suka Hanata ma kara mgana Inna bata matsa mata ba ta Fice ta barta ta koma Tsakar Gida taciga da Shara acikin Ranta Tana addu”an Allah yasa Sanadin haka Komai ya zama sai Labari Tsakanin Sunaima da Sulaiman.
Sunaima bata san Tsawon Lokacin Data kwashe Tana Tunani ba Har barci ya kwasheta bata sani ba sai Farkawa Tayi ta Duba agogon Wayarta Taga 12na rana ta Kusa ta makara a afirgice ta mike Karfe Daya da Rabi Zata isa Wajen aiki Fitowa tayi a Hanzarce Hijabinta da jaka a Hannu a Madafi ta Samu Inna tana Dafa wake Har ta gama Sharan tayi wanki ta zo ta gyara wake tana Dafawa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button