NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

       *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

     _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

    *Talla*

          *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa ta Orange money(ba chap chap ba yan uwa, orange money dan karka tura ta chap chap) akan wannan lambar 91-71-28-22 ko kuma wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura ta naira 300 wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

        1锔忊儯

A hankali ya shiga shafa lallausan gashin kanta dake d’aure cikin hular bacci, kallon siririyar fuskarta yake mai d’auke da k’aramin baki da dogon hanci, nutsuwa ce sosai a tattare da ita, babu damuwa ko k’unci a cikin rayuwarta, ta tashi cikin gata da kulawarshi, yayi abubuwa da dama dan ci gaban rayuwarta, ya rabu da abubuwa dayawa saboda ita kad’ai, daga cikin abubuwan daya rabu dasu kuwa har da mahaifiyarta, yana sonta so na hak’ik’a yanda baya son ganin wani ya rab’eta, har yanzu ya kasa bata damar da zata kula saurayi, duk wanda zai kulata saiya raba ta dashi saboda baya son sab’ani ya shiga tsakaninsu.

Sai dai lokaci ya kusa zuwa da zai rabu da ita rabuwa ta har abada, bai tab’a sanin cewa gangaci yayi wa kansa ba sai yanzu, bai tab’a tsammanin lokacin zai zo ba, farkon al’amarin ya d’auki abun da wasa, ya d’auka zai iya zillewa ta wata hanyar, ashe ba haka bane abinda yayi tunani, yanzu gashi girmanta ya zo kuma shekarar ta k’arato ita ma.

Wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyin gaske kafin ya sunkuyar da kansa ya sumbaci goshinta, gyara mata rufa yayi tare da kashe mata wuta ya fita a d’aki.

D’aki biyu ya wuce kafin ya bud’a wata k’ofa da wani makulli k’waya d’aya na k’arfe mai kama da silba ya shiga, fitilar daya kunna yasa d’akin gaurayewa da haske, babu komai a d’akin sai wata k’ofar shiga, rufewa yayi ya sake bud’a d’aya k’ofar da makullin ya shiga, zaka rance douche (toilet) ce amma nan d’in ma babu komai, haka kawai d’akin yake ko tsinke babu, nan ma rufewa yayi ya kalli wani bango, a hankali ya d’ora hannunshi kan bangon yana d’an motsa bakinshi alamar wani abu yake fad’a.

Abun al’ajabi sai ga bangon yayi wata k’ofa kawai ya shiga ta ciki, tsaf ya samu kanshi a cikin mutanen da kusan kullum ma sai sun had’u, dukansu babu mai riga sai jan yadi da suka lakaya suka fitar da hannu d’aya, wurin duhu ne sosai sai wutacen dake kunne, kana ganin wurin kaga wajen matsafa. Haka ya samu wuri ya durk’usa kamar sauran shima suna kallon babbansu dake kan kujera shigarshi tafi ta kowa muni.

Duk kwana uku su kan had’u dan shan jinin jinjirin da aka haifa a ranar wanda aiki ne da ake ba wa kowa daga cikinsu, yanzun ma wanda aka ba wa aiki ya kawo, haka aka bisu da d’aya d’aya a cikin tangaran mai kyau wanda bai da maraba dana gold ana basu suna sha. Ko da aka idar babban daga kan kujerarshi ya kalli wani dake kusa dashi yace ” Kabeer, jini na gaba kaine zaka bamu shi.”

Sunkuyawa yayi yace “An gama.”

Na kusa dashi ya kalla yace ” Ka ci gaba da shirye shirye Shakoor, lokacin sadaukarwarka ya kusa, nan da kowane lokaci Nga zata iya nemanka.”

Sak’e yayi alamar baya k’aunar zancen nan, can kuma sai ya d’an rusuna alamar to amma bai ce komai ba, da wannan maganar babban na su yayi sama ko k’asa daga kan kujera, haka suma duk suka b’ace a wurin.

A hankali gadon k’irar Apple ya d’an jijjigata, hakan ne yayi sanadiyar tashinta daga bacci, fita tayi daga zanin rufar ta sauka daga kan gadon…

Kuna son labarin???
13/04/2021 脿 03:54 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

       *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

     _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

    *Talla*

          *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa ta Orange money(ba chap chap ba yan uwa, orange money dan karka tura ta chap chap amma zaka iya tura kati) akan wannan lambar 91-71-28-22 ko kuma wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

        2锔忊儯

Tsaf ta shirya cikin suit na riga da siket bak’ak’e, sai dai rigar tana da d’an shatin siraren ratsin fari, siket d’in dogo ne har k’asa mai k’aramar tsaga a baya, daga saman rigar kana iya ganin wata farar riga mai kyau, jakar hannu ta d’auka bak’a ta saka dogayen takalmi masu tsinin gaske, hanyar fita daga d’akin ta nufa, a kan wata gajerar kwabat ta d’auki kofin tangaren d’in da aka aje mata mai d’auke da black coffee, bud’a d’akin tayi ta fita tana kurb’a hankali kwance.

Tafiya ce mai tsayi daga d’akinta zuwa wajen cikin abinci, bata takun da yafi uku zuwa hud’u bata had’u da cikin ma’aikatan gidan ba, kowane da girmamawa yake gaishe da ita har ta k’arasa.

Zaune ta same shi ita kad’ai yake jira ya tangale hab’arshi da duka bayan hannayenshi, yana ganinta ya saki murmushi ya d’auke hannayenshi, ita ma da murmushin ta k’araso tana fad’in “Good morning Abhi.”

Da murmushi sosai cikin farin ciki ya amsa da “Morning princess, how are u?”

Saida d’aya daga cikin biyun dake tsaye kan dinning d’in ta ja mata kujera ta zauna tana fad’in “Fine Abhi.”

Masu servind d’in nasu ce ta shiga zuba mata abinda tasan tana so, saida ta ida ta d’an matsa baya, kallonta tayi tace “Thank u Veronica.”

Sunkuyawa tayi cikin sakin fuska kafin suka juya suka basu wuri, tamgamemen dinning ne dake d’auke da kujera goma sha biyu, ya k’ayatu sosai ga kuma abinci na cin mutum sama da sha biyar, saida suka fara cin abincin mahaifin ya kalleta yace “Yau ce ranar k’arshe ta jarabawarku, akwai abinda kika shirya ma hakan ne?”

Kallonshi tayi da murmushi tace “Yeah Abhi, party.”

Da d’an mamaki ya kalleta yace “Party? Why?”

Da mirmushi akan kyakyawar fuskarta tace “Ina so muyi farin ciki na k’arshe.”

Kallonta yayi yace “Daga can zaki wuce office ne?”

Saida tasa loma a bakinta tace “Yes Abhi.”

Daga haka basu k’ara magana ba har ta ida ta mik’e, saida ta matsa kusanshi ta sunkuya ta sumbaci kumcinshi tace “Ok Abhi, sai na dawo.”

Rik’e hannunta yayi yana kallon fuskarta yace “Prend soin de toi angel.”

Murmushi ta masa ta fita, a daidai k’ofar fitarta ta samu mota a parke tana jiran fitowarta, mota ce gama hawa k’irar Hyundai bak’a sai d’aukar ido take, da sauri mutumin dake sanye da bak’ak’en kaya ya bud’e mata ta shiga ya zagaya da sauri ya tayar, saida sukayi nisa a hanya ta juya bayanta dan ganin ko yau ma mahaifinta ya had’ota da wasu motocin na tsaro, ganin babu kowa yasa ta sauke ajiyar zuciya ta kalli gabanta.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles