MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Janafty
MIJIN KANWATA..!
(k’addarata)

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

Page 14

Tun Daga nan ta cire ta kuma Sare da Inna ta Kirata Bata iya ce mata ta kasa ba sai dai ta Fadamata cewa har yanzu Tana iya bakin kokarinta akan Hakan ne alhalin ta Riga ta sare Kwata kwata taji kamar bazata iya Taimakon Sulaiman ba, kamar yadda Inna da Sulaiman suka Dora Duka yakininsu akanta.
Tundaga Ranar ta cire rai da Sulaiman zai zo Gareta ta Fara aiwatar da Taimakon da Nauyinsa ya koma kanta.
Ranar Alhamis da Daddare tana asibiti Sulaiman ya samu Sa”a bayan Sun gama Raya sunnarsu kamar yadda Laila ta maidashi Ibada ita ke Sarrafa Ragaman Domin sulaiman ya bar mata wannan Fanni bayaji baya gani ballatana har ya iya Tantance wani abu
Kamar ko yaushe ta Kamkameshi batare data damu data Tsarkake Jikinta ba,Shi yana kwance ne ammh kazantar Jikinsa ya ishesa ballatana na Jikin Laila gabadaya kyama da kyamkyami ya ishesa Sulaiman bai iya Zama da Najasa ko Lokacin Sunaira komai Dare sai sunyi wanka kuma bai yarda da Hada wanka ba yace kazanta ne Kowacce suna wankanta Dabam sannan Hada wanka yana kawo Cutar Mutuwar gaba da kananun Cututtuka.
Shiyasa yayi kokarin tashi Laila ta Bude Rinanun Idanuwanta da suka Fara Rinewa saboda barci Da Sauri yace mata wanka zai yi kamar tace wani abu sai kuma ta koma ta kwanta Sunaima ce ke ransa laila itace Duniyarsa yana mantawa da kowa da kowa in Tana gabansa ammh wani Ikon Allah baya mantawa da Sunaima Tun Ranar da sukayi mgana tacemai Tana da mganin Mtsalansa yake neman Hanyan Da zai fita yaje Dakinta ammh Laila ta Tare ko”ina Shi kuma baya iya mata gaddama Komai yake yi in ya ganta ko yaji Muryanta kamar an zaremai Komai na Jikinsa ne kamar ita ke da alhakin jan Ragamar Rayuwarsa haka yake ji.
Yana wanka yana Tunanin Mafitarsa Domin in ya kebe kansa shi kadai Haka Kurun yake ji kansa ba Daidai ba..Baida Lafiya akwai abunda ke Damunsa acikin Rayuwarsa bai iya Furtama kowa ammh ya iya Furtama Sunaima yana da Tabbacin tasan mganin Mtasalansa ya zama Dole ya Nemeta Domin ta bashi Abunda zai sa ya Dawo Cikin Hayyacinsa ya Daina Jin kamar bawa yake akan Laila.
Yana Fitowa wanka Jallabiya ya Saka Da Ruwa ma yana Diga Daga Jikinsa Sanda yake ganin Laila tayi barci yana so ya Tabbatar da barcinta yayi nisa yasa ya Taba kafarta ammh bata Motsa ba Ganin haka yasa kamar zai Kifa ya Fice Daga Bedroom a Hankali Lokaci Daya yana Sakayomata Kofar Koda ya Fito Falo wajen 1am na Dare ne Gari yayi shuru kowa yayi barci da wannan Daman ya samu ya Sulale yacFice ya Sauka Falon kasa Inda Allah ya Taimakesu gabadaya an Kashe Hasken Gidan wanda Daman Dokarsa ne gabadaya kwayayan Gidan ake kashesu in Dare yayi Shiyasa yabi Duhu har Dakin Sunaima Gidansa ne ko Daga magagin Barci zai kai kansa Duk inda yake so..!
Sai dai me..?ya taki Rashin Sa”a Kofar Dakin sumaima akulle ta kulle abunta da zata tafi Wajen aiki Kuma aranar ta Fara Rufewa Tundaga Satin Kofar abude take saboda Tana Zaton zuwan Sulaiman yanzu kuma ta Fidda Ranta..
Jin Kofar akulle bai kawo ma Ransa wani Tunani ba ya Fara mata Knooking a hankali Saboda Tunaninsa Tana ciki ta kwanta ne sai dai har yagaji Shuru kuma alokacin Tunaninsa bai basa Tana asibiti ba wannan ya shafe Daga kwakwalwarsa..
Jiki a sanyaye ya koma Sama Inda ya Fito in ka kallesa kamar yayi kuka afalo ya kwanta saman kujera ya Fara Tunanin meke Faruwa dashi ammh Har barci ya Daukesa bai kama Komai ba abunda Allah ya Hanasa ya Tuna da ambaton Allah ballatana ya Kirasa Kila Sanadin haka ya taimakesa komai yazo mai da Sauki Tunda Laila ta samu mallakan Rayuwarsa bai kara maida Hamkali ga Ibada ba baya Salla cikin Jam”i kamar yadda ya Saba baya kuma yinta akan Lokaci Domin wani Lokaci Kirkiri ana Salla in Laila na Wajen bai iya tashi sai da Umarninta da Zarar kuma ya Idar Kwakwalwarsa
Ta riga ta Shafe baya iya Tuna abunda ya Shafesa ballatana ya Tuna da amBaton Allah aljanin Dayayi aiki akansa ya Shafe Tunanin Komai Daga kansa sai na Laila sai dai Allah bai basu ikon Shafe Tunanin Sunaima Daga Duniyarsa ba.
Washegari da Safe da Sunaima ta Dawo Daga wajen bata ga wata alama da zai nuna mata Sulaiman yazo bata nan,Kuma tunda ta dawo bata Leko ko Falo ba Tana ciki tana Fama da kewar su Wasim da kuma Tunanin kasawarta akan komai yasa gabadaya bata da wani kuzari ballatana Karkashi.
Sai Dare ta Fito Lokacin da shirinta na Tafiya wajen aiki,Bata ga magajiya ba Kila Tana cikin Dakinsu yasa ta kama Kanta ta wuce sanin ba wanda ya Damu da Fitarta da dawowarta.
Aranar da Daddare sulaiman ya kara Samun Farar sa”a kamar Jiya Daga wanka Laila ta samu barci mai Nauyi ya kara Sulale wa ya Fice yau Allah ya Tunasar dashi Sunaima indai bata Gida tana Wajen aikinta asibiti.
Yasa Bai tsaya Ko”ina ba sai Haraban Gidan Dakin megadi ya isa Direct Lokaci Dare bai yi ba, wani abu 12 saura ne Allah ya taimakesa har ya Fito bai Hadu da su Samira ba.
Auwal megadi na Cikin Dakinsa yadan Kishingida Daga Jin Radionsa Kofarsa Tana Bude ne saboda Zafi Ballatana Shi baya Rufe kofa saboda ai amanace a Hannunsa Ko yaya yaji Motsi sai ya Fito ya Duba ko”ina sai ya Tabbatar da komai Lafiya Tukunnah.
Sulaiman Daya Leka yaga Auwalu na barci kawai sai ya Nufi Kofa zai Fita sai yajita a kulle yaja Get din ya Jijjjiga nan ma akulle take ko Motsi sai kawai ya Fara jijjiga Get din da karfi Wanda yasa Auwalu ya tashi a Firgice Sandarsa ya Dauko da Addarsa ta gadi da Fitilansa mai Haske ya Fito da Sauri yana Dallare Sulaiman Dake Tsaye yana Jijjiga kofa Saboda alokacin yana ji kamar in bai Fita ba yau zai Rasa Damarsa Dayake da ita.
Cikin Dan Tsoro Auwalu da bai gane Sulaiman ba ya tsaya Daga baya baya yana Fadin”Waye nan?Nace waye anan..?
Yafada yana kara Haskesa da Fitila da Sauri Sulaiman ya Hango Auwalu ya ga Fuskarsa Cikin Tarin mamaki ya kariso yana Fadin”,Allah ya taimaki Mgajin garin kargi..Yallabai kai ne da kanka..?
Sulaiman ya saki Kofan yana Fadin”Auwalu budemin kofa Zan Fita ne..!
Auwalu megadi ya kallesa Cikin mamaki Domin kimamin wajen Sati biyu kenan bai saka yallabai a idonsa ba ammh Kallo Daya yayi mai ya ga kamar yallabai bya Cikin natsuwarsa..!
Cikin mamakinsa yace”Ranka ya Dade fita fa kace zakayi da wannan Daramn..?Allah yasa dai lafiya..?
Sulaiman yace”Ka Bude nace Kana bata min Lokaci.zan samu abun hawa zuwa asbitin Barau dikko Dake cikin gari..?
Auwalu ya karisa ya Ciro Makulli Daga aljihun Rigarsa ya Fara Kiciniyar Cire kwadon Daya garkame get din yana Fadin”Ranka ya Dade..Ko da ranar Allah b”a cika samun Gilmawar masu Adaidaita ba..Saboda anguwace ta masu Hannu da Shunu kowa kagani yana da Motarsa sune kadai ke Kai da kawo atitunan namu in kaga adaidaita to Kila ya kawo wani ne zai Fita..!
Yafada bayan ya gama Bude Get din ya Kuma Bude mai karamar Kofar Sulaiman ya Fice ko Takalmi babu akafarsa Audu daya Fahimci haka ya Biyosa yana Fadin”Ranka ya Dade kafarka ba Takalmi fa..!
Yafada yana kallonsa da mamaki Daga shi sai jallabiya ko Dogon wando babu ajikinsa Sulaiman bai Damu ba sai alokacin ya Tuna da yafada kafarsa ya Kallah kafin yace”Bani naka na saka..!
Auwalu ya fara Tamtama kila yallabai ya Fara zarewa kokuma wani abu ya Faru Cikin Rudewa yace”Nawa kuma Ranka ya Dade..?
Ido ya sakarmai kafin yace”Eh ko bazaka bani bane..!?
Da sauri ya Tube Dan madinan Dake kafarsa Ya mikamasa Duk da ya sha Jiki,ba kyamkyami ba Raini sulaiman ya Saka Takalmin yana Fadin”Yanzu dai bazan samu abun hawa ba kenan..?
Auwalu yace”Gaskiya..To yallabai ka Dauko mota mana Tunda Fitar gaggawace ta Kamaka..Ko ka Kira Sani..!?
Sulaiman yace”Waye Sani.?
Auwalu ya Fara Salati acikin Ransa kafin yace”Sani dai ranka ya Dade…Direbanka wanda ke janka zuwa wajen aiki yake kuma kai su yara makaranta..!
Sai alokacin ma ya Tuna da Sani Cikin Mamaki ya kalli Audu kafin yace”Yauwa kana da lambar sanin..?kirasa kace yazo da Mota ina Jiransa..!
Auwalu da yajaji kamar ya saka kuka yace”Ranka ya Dade kamanta Hajiya Amarya ta karbi key din Motar daga hannun Sani kuma tace kada ya Dawo sai ta Kirasa tun Ranar bai kara Dawowa ba kuma ga Motar nan Ahaaraba yallabai..!
Sulaiman yayi shuru yana Tunani sai yanzu ya Tuna komai gabadaya wayarsa da Keys din Motocinsa suna Hannun Laila ta karbe komai Daga Hannunsa kansa ya Dafe ya rasa mafita bai so ya koma wannan ne kadai Damar Dayake dashi..
Kamar daga Sama yaji Auwalu megadi na Fadin”Ranka ya Dade ko zaka Kira Yallabai Saifullahi ne..?
Jin sunan Daya ambata sai yaji kamar an mai gafara da Sauri ya Dago kansa kafin yace”Yauwa kiramin shi..!
Auwalu ya Kifta ido kafin yace”bani da lambarsa Ranka ya Dade..Sai dai in kana dashi ga wayata nan inaga akwai yan Chanji sai kayi amfani dashi..!
Sulaiman ya fara Nazari da Tunanin Ko ya Haddace lambar Saifullahi yana da ita akansa ammh yana jin tana bacemai Da sauri ya mika hannu yana Fadin”Ban wayar..!
Jiki na Rawa Audu megadi ya Mikamasa Wayarsa Nokia data ji Jiki Duk ta Nade da Salatif da Robali Karba Sulaiman yayi sai yama kasa amfani da ita,Sai dai mikamasa yayi yana Fadin”Zan fado maka Lambobin ka Rika sakawa ina Tunanin ina da Lambar akaina..!
Karban wayarsa yayi Sulaiman ya Runtse ido ya shiga Karantomai Lambar Kamar almara sai gashi ya kawota Duk da yana dan Tantama Auwalu ya gwada kira cikin Sa”a sai ga Lambar ta shiga sai dai har ta gama Ringing ba”a Daga ba Megadi ya kallesa yana Fadin”Ba’a Daga Wayar ba Ranka ya Dade..!
Sulaiman yace”Ka kara kira..ka Kara karar wayar..!
Ba musu ya sake kira bayan ya Sakata a speaker tana gabda yankewa Saifullahi ya Daga Cikin magagin barci Sulaiman najin muryansa Yayi Saurin amsar wayar ya kara a kunne Lokaci Daya yana Fadin”Saifullahi…!
Saifullahi Dake kwance Yana barci yaji kiran waya bai ma Duba lambar ba Ya Daga kiran sai dai jin muryan Sulaiman kamar amafarki ya Mike zaune barcin Idonsa ya Kare Cikin mamaki yace”Sulaiman…!
Yafada cikin mamaki Sulaiman bai Tsaya Biyema Mamakin Saifullahi ba yace”Saifullahi in kana Gida plz kazo da Mota ka Daukeni..Sunaima nake son gani. !
Saifullahi Cikin mamaki yace”Sunaima kuma..?bata gidan ne..?
Sulaiman yace”Eh..Ina jin Tana wajen aik..!
Bai gama mgana ba Kudin Dake Cikin Wayar ya kare sai kawai ya mikama Audi wayar bai ce komai ba Auwalu ya karba yana Fadin”Kudin ne ya kare yallabai..!
Dakai ya amsa bai ce komai ba sai dai ya rike Kugu ya kasa ya Tsare kamar mai jiran wani abu megadi ya kallesa aransa yana ayyana yallabai ba Lafiya kuma Meye ya Faru bai rasa nasaba da Zuwan Amaryan nan acikin Ransa yace Allah ya Fitar dakai yallabai.
Ganin ya Coge yasa shima bai koma Gidan ba ya Tsaya nan bayansa Duk da anguwan Tsit sai Haushin karnuka ammh ko”ina Tar yake da Wutar kwayayan Lantarkin da kowani megida ya Zuba akofar gidansa da suka Taimaka suka Haske anguwan gabadaya..
Jiran Mintina Talatin da wani abu sai ga Hasken Motar Saifullahi Allah ne yasa Sulaiman zai samesa Domin yau din yaso ya Tafi karaye Sai ya Fasa Yammah tayimai sai ya bari sai Gobe asabar da Safe zai tafi.
Tundaga nesa ya Hango Sulaiman yasan ba Lafiya motarsa bata gama Tsayawa ba Sulaiman ya Nufesa Ya Bude Murfin Motar ya shiga Sulaiman ya Taka Birki da sauri har sai da Kansa Sulaiman ya Bugu ammh bai Damu ba Fadi kawai yake”Kaini Asibitin da Sunaima take aiki..!
Saifullahi ya Duba agogon Motarsa yana Fadin”Lafiya me ya faru..?kasan ko karfe nawa yanzu..!
Sulaiman ya jingina bayansa jikin Kujeran Motan yana Fadin”I don”t Care Saifullahi ji nake ina neman Mafita..kuma ita kadai keda Mafitata..Ina so nasan meke Damuna..Tacemin tana da mganin Lalurata ina so na warke na Dawo Sulaiman Dina kai kanka kasan am Not ok..!
Yafada kamar zai yi kuka Saifullahi yaji kamar yayi masa kuka yasa Kawai ya Tada Motar suka fara Tafiya Auwalu ya Bisu da kallo aransa yana Fadin Allah ya kiyaye ahankali ya Juya ya koma ya Rufe get din ya koma Dakinsa ya Zauna baya so ya kwanta barci ya kwashesa Yallabai ya Dawo bai ji ba.
Sun Fita Daga anguwan kenan Saifullahi ya juya ya kalli Sulaiman Dayayi kamar mai barci acikin Ransa yana addu”an da FAtan komai ya Daidaita Daman wannan Zuwan nasa karaye Daganan zaria zai wuce suyi mgana da Baba Sama”ila Raanar Lahadi Daga karaye chan zai wuce in ya gansa zai ya Wuto kaduna.
Kamar ba Daga bakinsa mganar ta Fito ba”Saifullahi ya kamfani..?
Saifullahi ya kallesa kafin yace”Komai na Tafiya Daidai…ammh kasan ban saba aiki baka ba..!
Sulaiman yaji kamar ya Kurma Ihu kafin ya Bude ido yace”Laila…!
Saifullahi yace”Me ya faru da ita..?
Sulaiman yana so yayi mgana sai yaji kamar an kullemai baki sai kuma ya kasa ya koma ya Jingina yana Dafe kansa bai kara mgana ba har suka iso bakin Babban get din asibiti Da Security bayan an yi Cheecking din Motarsu suka shiga ciki sukayi parking a parking space suka Firfito Direct Ciiki suka shiga aganeral Hall din suka Tsaya Saifullahi ya tsaya yana Tambayan wani Security Gabadaya Cikin asibitin kamar Rana Ko”ina Haske sannan ga Mutane da Likitici nata Hada Hada..
Sunaima ya tambayesa yace anan take aiki sai yace gaskiya ma”ikatan suna da yawa su karisa ciki su Tambayi wani likita ko Nurses
To sun shiga kenan Allah ya yanke Musu Wahala sai ga Sister Aneesa ta Fito Daga Labour Roon yau anan Take Sunaima kuma tana Maternity ne ita suka Tsaida Saifullahi ya TambayetacCikin mamaki take kallonsu kafin tace”Sister Sunaima Abdu Datti..?
Da Dauri Saifullahi yace”Eh ita..Don Allah ki taimaka ki mata mgana Is Urgent Mijinta ne yake son ganinta..!
Yafada yana Nuna mata da Sulaiman wanda yake kallon Wani Dogon korido kallonsa baya kansu ammh Hankalinsa na kansu Aneesa ta kalli Sulaiman aranta Tana Jinjinama Sunaima ashe Mijin nata babban goro ne Ita bata ma lura da yanayinsa ba Da Sauri tace”ku jirani bari naje na Fadamata Tana Maternity ne..!
Da sauri Saifullahi yace”Yauwa mungode..!
Da sauri ta wuce tana kara waiwayonsu ganinsu duk ba Daidai ba ko me ya faru..?take tambayan kanta.
Sunaima na maternity tana Duba ma Wacce akayi ma aiki ne Dazu aka kawo nan Dakin bata Farfado ma sai dai karin ruwan da aka saka mata ne ya kare wata yar”uwanta ta Kirata Daman su Biyu ne yau ita da Sister Fatima.
Ta gama Cire mata karin ruwan kenan Aneesa ta shigo tana Kiranta Juyowa tayi tana kallonta Cikin mamakin kiranta yanzu sai ga Aneesan ta kariso kusa da ita Tana Fadin”Sunaima kin yi bako fa..!
Sunaima ta baro inda take ta Riki Aneesa suka matsa gefe kafin tace”Bako..? Bansan wasa ba..kedai Fadamin me kike so na Taimaka miki Domin na Lura da kin samu wannan cikin Laulayinki yayi yawa..!
Aneesa tayi Dariya kafin tace”Yau dai naga Mijinki Sunaima..!
Sunaima ta kalleta Shekesheke kafin tacw”mijina kuma..!?
Aneesa tace”Eh Wlh suna Chan General Ward suna Jiranki..!
Sunaima ta Zaro ido kafin tace”Wai da gaske kike Aneesa..!?
Bata tsayama kara mata mgana ba ta Damki Hannunta kii suka Fice Bata Saketa ba sai da suka Fito kana tace mata”Muje na kaiki ki gani sai ki yarda..!
Tafe tafe sai gasu gaban su Sulaiman Sunaima mamaki ya Kasheta Aneesa ta Saki hannunta Tana Fadin”Gatanan na kawo muku ita..!
Tafada tana kallon Sunaima da mamaki ya gama Sandarar da ita.
Saifullahi yace”Mungode sosai..!
Mirmishi tayi ta wuce tana ma Sunaima Rada”Na kawo miki jakarki ne..?domin nasan daganan sai gida..!
Hararanta Sunaima tayi ita kuma ta Wuce Tana Dariya.
Sunaima ta Dago ido tana kallon Sulaiman Daya kafeta da ido kamar ya wanke makanta sai ta maida kanta kasa Saifullahi ta gaisar ya amsa Yana Shirin mata bayani Sulaiman ya isa gabanta ya Rike Duka Hannuwanta Lokaci Daya yana Fadin”kin ce nazo Dakin ki zaki bani mganin Mtsalata..Jiya nazo bakyanan yau ma haka shiyasa na Biyoki nan..Sunaima Ki Taimakeni ki bani mganin da kikace Sannan ki Fadamin meke Damuna..!
Yafada yana kara Rike hannunta ya kamkame kunya ya kamata ganin Daidaikun Mutane suna kallonsu ga Saifullahi yasa da Sauri Tace”Ka bari na dawo gida da safe..!
Tafada Tana kokarin kwacce Hannunta Sai ma kara Riketa da yayi yana Fadin”Bazaki Taimakamin ba?
Wlh ko nawa kikace zan Biyaki Indai zan Dawo Sulaiman dina..Inajin ajikina am not ok..!
Yafada gabadaya Yardansa na kanta Saifullahi Dake kallonsu yana Fadin”Sunaima plz Ki Dubesa mana..!
Yafada yana Kallonta Cikijnwani yanayi tace”Abun yana gida fa..kuma ina on Duty ne yau..!
Da sauri Saifullahi yace”Na yau kawai ki Dauki Excuse plz..!
Sunaima ta rasa yadda Zatayi Sulaiman na neman ya Rumgumeta ganin haka yasa ta kalli Saifullahi Tana Fadin”Kace mai ya Sakeni..Zan je na Dauko Jakata da Hijabina..!
Saifullahi ya kalli Sulaiman yana Fadin”Saketa Kargi..Bari ta Dauko Jakarta ta dawo sai mu tafi..!
Sulaiman ya kalleta kafin yace”Promise zaki dawo..?
Kai ta gyadamai Ta kasa mgana Gabadaya ya gama kashe mata Jiki sai alokacin ya saketa ta koma Dauko Jakanta Sister Fatima ta ma Sallama tayi Karyan rashin Lafiya daga gida tace an zo Daukanta Daganan Head dinsu na On Duty taje ta Fadamawa kafin ta saka Hannu ta bata izinin Tafiya Tana Fitowa yana Hangota yazo ya Rike mata Hannu kamar Zata Gudu gabadaya ta kasa Kwatan kanta.
Har Mota yana Rike da ita Gidan baya suka shiga Sulaiman gani yake kamar Zata Gudu in ya Saketa Saifullahi na Tuki yana jin kamar yayi kuka Saboda Bayason ganin Sulaiman ahaka..
Wajen 1:30am nadare suka Dawo Saifullahi bai yi Hon ba Daga kofar Gidan ya Tsaya suka Fito ya kalli Sunaima yana Fadin”Kada ki Damu..Wannan Lokacin Allah ne ya bamu aronsa..Don Allah ki yi Kokarin komai yayi Daidai..!
Kai kawai ta Dagamai Kamar zata gudu yana Rike da ita Saifullahi ya Buga get din Auwalu yazo ya Bude Suka Shige bayan Saifullahi yace ma Sunaima tabi a hankali.
Kamar wasu barayi Sadaf Sadaf suka shigo har Dakinta Dakyar ya barta ta Dauko makkuli acikin jakarta ta Bude Dakin suka shiga suna Shiga ya Fara Fadin”Ina mganin..?daukomin mganin don Allah..!
Yanayinsa yasa ta Fahimci baya Cikin Hayyacinsa Jakarta ta ijiye Gefen gado kafin tajasa ta Zaunar dashi Gefen gadon Tana Fadin”Ka samu natsuwa.Zan Dauko maka..!
Hijabin Dake saman kayan aikinta ta Cire gefen Wardrope dinta ta Ijiye Jakar Nan taje ta Dauko da karamim Kofin Tangaran Data Dauko Tun Ranar Datake Tunanin zuwan Sulaiman tazo gabansa ta Durkusa Duk yana Binta da kallo Bude Jakar tayi da Bismillah ta Tsiyayamai cikin Kofi Ta mikamai ya karba da Sauri Zai kafa kai tayi Saurin Rike masa Hannu kallonta ya Tsayayi kafin yace”ki barni nasha..!
Sunaima tace”Kayi bismillah..!
Kace Bismillahi..!
Ba Musu ya maimaita kana ya kafa kai yasha Duka ya Mikamata yana Fadin”Karomin..ko bani Jakarkan na Shanye duka Zan Dawo daidai..?
Mirmishi tayi kafin ta Kulle Jakar Tana Fadin”A”a sai da safe zaka kara sha..Yanzu ka Sauke Numfashi kace Alhamdulillah..!
Kamar yadda tace haka yayi sai kuma yaji Sukuni da kwanciyar hankali ya koma yana Sauke Numfashi Ita kuma sai ta Mike tana Tsaye akansa Tana ta addu”a tana Tofamai bai sani ba.
Har sai da taga yana ta Sauke Numfashi sama sama kafin kuma ya Sulale saman gadin ya kwanta yana Lumshe ido,bata gaji ba Tsaye take akansa tana addu”a Tana Tofamai addu”an da Inna ta kawo mata ne sai Suratul yasin Datake ta Karantamai Har batasan ya samu barci ba sai da Taji Saukan Numfashinsa.
Kana ta Sauke ajiyar zuciya tana Kallonsa maida komai tayi inda ta Daukosa kana ta Shiga wanka Ta Dauro alwala tazo ta Sauya Kaya wata Rigar Barcin Doguwa mai Taushi Darduma ta Shimfida ta Tada Sallah Domin bata jin barci..sai wajen uku da Rabi ta idar da Salla tayi addu”o”inta Ganin Sulaiman ya kusa Fadowa Domin yana gefen gadon yasa ta Cire Hijabin jikinta ta isa kusa dashi a Hankali Tana kokarin Daga kansa ta Dora Saman Filo Cikin Barci ya Juyo kawai sai ya jawota ta Fado gefensa kafin ta samu Damar tashi ya saka Duka Hannuwansa ya Nannadeta kansa na kan Kirjinta Duka hannunsa na bayanta ya Riketa Sunaima Dakyar ta iya Numfashi Jikinta ya Fara rawa Tsoro ya kamata ganinsu kwance waje Daya In Laila tazo ta gansu komai zai Lalace Tun kafin al”amarin yayi nisa tayi kokarin zame kanta sai ma ya kara Riketa Tamau kamar ya sakamata Karfi Duk yadda Jikinta ke rawa haka ta koma ta kai kanta saman Filo tana Sauke Numfashi Jin Numfashinsa Saman wuyanta yasa ta Rikice ta Fara Zufa da Rawan Jiki Gefe Daya wani yanayi na Shigarta Duk yadda taso Takai Asuba idonta Biyu ya gagara Barci ya kwasheta Cikin yanayin da bata so ko Barawo ne ya saceta ba..!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button