MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Sai da ya isa Fridge din ya Bude ya Dauko Ruwa mai sanyi ya Bude ya sha Rabi kafin ya maidashi Inda ya Daukosa,Ya juyo yana Sauke Nunfashi Sama sama Lokaci Daya yana Fadin”To ka iya bakin ka Tun kafin hakan ta Faru dakai..Wlh zan iya marinka lokaci Daya na Hada maka da manyan Ashariya in baka iya bakin ka ba In kana ganin bazan iya ba Just Tary me an see..!
Yafada Lokaci Daya yana zama kan kujeran Ikon Daya tashi Saifullahi ya Jinjina Kai kafin yace”Zaka iya Allah ya Taimaki Saraki..Ammh dai kasan Zagi bai Dace ga jikan Sarkin Kargi ba ko..?
Karamin Tsaki yaja yana Fadin”Sai dai Sarkin Karaye..!
Saifullahi na Dariya yace”Abun har da Zagi ne..?
Sulaiman ya Muskuta Lokaci Daya yana Kokarin Rage Tamkewar Tek tie din Dake Wuyansa yace”D”ansu yaja musu..Ka iya bakin ka in kana son tsira da Mutumcinka..?ya batun Ganawar mu da kamfanin Dasuki Ventures..?
Saifullahi yace”Shigowata fa mganar ta kawani..Sun nemi mu saka musu Ranar da zamu zauna Meeting din..!
Kai Tsaye sulaiman yace”Ka gaya musu Ranar Monday..Zamu Hadu dasu a inda na Fadamaka..!
Saifillahi ya Jinjina kai kafin ya samu Zarafin mgana Wayar Sulaiman Dake gabansa ta Dauki karan neman agaji.
Daga yanayin yadda yayi sanda yaga sunan mai Kiran Saifullahi baya Bukatar wani karin bayani yasa Cikin Dan Tausasawa yace”Hala Hajiya ce..!
Dakai Sulaiman ya amsa mai Yana kokarin Gyara zamansa Kafin ya Daga Wayar Hajiya ai bata Kiran banza Shi fa ba Domin kada yayi Sabo ba Dayace Kiran Hajiyarsu kaf bana Alheri bata Kiranka sai da wani abu babba ko Mutuwa ko kuma ta Kira ta Fadamaka abunda zai hanaka sukuni Hajiya Zabba”u Jarumar macece kamar mijinta a tsaye take kan Mijinta da ya”yanta bata Daukan Reni ko Kadan.
Dakyar ta samu amsa Sallamar Daya Rangadamata yana kokarin Gaisheta ta katse shi Daga chan bangaran.

“Ba gaisuwarka na Kira naji ba Saraki..”

Tafada cikin Kaushinta akoda yaushe Ido ya Runtse kafin ya Bude Cikin Tautausawa yace”Meya faru hajiya..?
Cikin bayyana Bacin ranta tace”Yanzu nayi mgana da Samira ta Fadamin Tunda wannan Tsohuwar guzuman matar taka ta Fita Jiya da Daddare da sunan Zuwa wajen aikin da take Fadi har Yanzu Karfe uku na Rana ta wuce Saraki bata dawo ba kana Sane da hakan..!?
Ta tambayeshi Cikin Kaushin Murya a muryanta sam ba wasa ballatana Sausauuaci.
Miyau ya Hadiye dakyar yana kallon Saifullahi Dashima yake kallonsa Shifa Daman yasan Za”a Rina ba abanza Hajiyarsu ta turo Wanan Munafukar Samarin ba Shifa Daman Tun Sanda ta bashi Umarnin ya Tura Sani Direbansa ya Dauko mata ita Daga Kargi wajen Fulani yasan Za”a Rina C.I.D hajiyar ta sakamai agidansa Saboda ta Rika samun Labaran abubuwan Dake Faruwa ai shi ya Shiga Uku ya Kade har ganyensa gashi Abba baya nan ya Tafi Lagos kan ganawa da wasu kamfonin da suke son saka Hannun Jari da kamfaninsu.
Sumarsa kansa da aka Saisaye ya shafa kafin yace”Bansani ba Hajiya Tun safe ina Office..!
Cikin Fada tacigaba da Fadin”To daman ina zaka sani..?tunda aka Dauki wacce bata dace dakai ba aka likamaka Saraki..Samira ta Fadamin koda yaushe ta Fita aiki sai sanda Taga Dama take dawowa ita ke auran kanta ko kai ke auranta..?ina da list din Duka Shedule din aikin su na asibitin Datake aiki In aikin Safe gareta 2pm na rana suke mika aikin ga masu zuwa yammah in na Rana ne karfe 6pm zata mika aikin ga masu Aikin Dare in kuma aikin Dare gareta Karfe 7am na safe zasu mika aikin Ga Ma”aikatan Safe na Ranar ammh ita sai Ta kai wani Lokacin kafin ta dawo Cikin Gidan Bata wani abu da Zai Nuna tasan Ita Matar aure ce!
Ta karishe Fada Cikin kumfar baki to me zai ce..?Koshi Da yake Mijin nata ai baisan komai game da ita kanta ba. ballatana aikinta ammh Hajiya Har komai ma ta sani Lalle nema.
Bai da tacewa Illah “Hajiya kiyi Hakuri don..!
Bai karisa ba ta katseshi Cikin Tsawa Tana Fadin”kada ka kara cemin nayi Hakuri Saraki..Abaya na Dade ina Cijewa da kalmar Hakurin da Mahaifinka da Maimairtaba suke Jinginamin ammh banda yanzu..In abaya nayi Hakuri ka Zauna da Sunaira Ta Chanchanci hakan ne..Ammh Wlh Tallahi kaji na Rantse maka Saraki wannan karon bazan zuba ido na bari akara Salwarta da Rayuwar D’ana ba.Tunda Iyayenka suka Aura maka wannan Tsohuwar bada izinina da Shawara na ba nayi Shuru bazan ja da mganarsu ba sai dai ka sani wannan karon Mutuwa ce kadai Zata katangeka Daga Auran LAILA..!
Tana gama Fadin haka bata jira cewarsa ba ta Datse kiran Tana Faman Cigaba da kai kawon Datake yi a Tsakar Kayattacen Bedroom din nata Atsaye take domin a kallah Farko in kayi mata zaka Fahimci haka Jin Dadi da Hutawa sun Boye shekarunta sai dai kana ganinta kasan bata da Rauni kuma tana da matukar Jajircewa.
Hajiya Zabba”u Aliyu Kargi kenan Mata ta Farko kuma Uwargidan agidan Alhaji Aliyu Kargi wacce ake kiran da Hajiya Tana da abokiyar Zama mai suna Falmata ita din yar Maiduguri ce Aliyun ya aurota Daga baya wacce kowa da kowa ke kiranta da Hajiya karama.
Har ta Datse kiran bai Dauke Wayar Daga kunnensa ba,Mganar ta gama Shigarsa ita kemai amsa kuwwa acikin kunnuwansa.
Saifullahi ya kallesa Cikin Nazarinsa kafin yace”Me Hajiya tace Kargi..?
Haka suke kiran juna wani Lokacin da sunayen garinsu asalinsu.
Sai Lokacin ya Sauke ajiyar Zuciya Lokaci Daya ya Sauke Wayar daga kunnensa ya kalli Saifullahi yana Fadin”Hajiya tasan komai..Infact ma Wannan yar aikin Data saka aka Daukota Daga Kargi yar Leken asiri ce ita take kira Tana Fadamata Halin da ni da Gidana muke ciki can u juzt Imaging Hajiya tasan Harda Lokutan aikin Yarinyar nan mai Son girma fa..!
Saifullahi ya gyara Zamansa yana Fadin”Ba abun mamaki bane..In Hajiya tasan hakan sai me kuma tace..?saboda nasan ba shikenan ba..!?
Sulaiman ya Furzar da iska Daga bakinsa kafin yace”Tace min in tayi Hakuri a baya Lokacin SUNAIRA yanzu bazata Saurari kowa ba..!
Saifullahi yace”Uhm ina jinka..!
Sulaiman ya Runtse ido kafin yace”,Ta gayamin ta kara gayamin bayan ta Rantsemin..Mutuwa ce kadai Zata gatangeni daga Auran yarinyar nan LAILA..!
Saidullahi ya kuramai ido yana kallonsa na dan wani Lokaci kafin yace”Daman ai kasan haka Zata Faru..Nidai kai mun sani Shurun hajiya baya na nufin ta Hakura bane..Kuma ita kanta Lailan koran manemanta da Rushe auranta da dan Wajen Baba Lawali ai kai take jira..Ta kuma san Kila a wannan gabar Zatayi nasara..Duk da Lokacin Marigayiya Sunaira ta rasa wannan damar..Banda wannan karin Damarmaki ne a abude Sulaiman bama Dama Daya ba..!
Kamar allon magiji haka Sulaiman ke kallomsa Kafin yace”Na sani Saifullahi..Nasan haka zata Faru..!
Saifullahi yace”Ina mafita..?
Sulaiman ya Taresa da Sauri yana Fadin”Babu mafita…Bazan iya auran Laila ba Wlh bantaba kallonta da wani mtsayi face kanwata kamar su Sadiya take..!
Saifullahi yace”Auranta shine mafitanka..Hajiya bazata Tsaya ba..Kuma ina ganin a wannan gabar Ko Abba da mai Mairtaba bazasu iya Tsaidata ba..!
Sulaiman ya Tallafe kumatunsa yana Fadin”Tabbas..Domin Maimartaba ya Fadamun zuwa na karshe wajensa..Na Lallaba Hajiya sun kara mata Laifi akaro na Biyu..na Tabbata wannan karon ko su bazasu bijera ma Bukatarta ba..!
Saifullahi yace”Nima nayi Tunanin haka..Sai dai akwai Hanya guda Daya da zata Kubutar dakai..!
Da Sauri Sulaiman yace”Fadamin ita Saifullahi..kasanni kasan Tsarina Wlh bazan iya Zama da mace Fiye da Daya ba..Tun bayan Rasuwar Noory na Fidda Rai da aure saninka ne nima fa su Maimairtaba ba Shawara dani sukayi ba wajen auramin yarinyar nan ba..Inda sun Fadamin nan take zan Gayamusu bamj dace da juna ba,ba Daya suke da Norry ta ba Hallayarsu ba Daya ba Ta Kowani bangare suna da Bambamci nasan in baka manta ba yarinyar dana bama Shekaru Hudu aduniya Da kunninka da kunnena Ranar da Sunaira ta Cika kwana arba”in aka Daura mana aure Abba ya Mtsa mu shiga mu gaida Inna munji Sanda Take Fadan taya y Kaddara Zata kaita auran wanda Take gogayar Shekaru dashi..!take kallonsa mtsayin kaninta..?ni ne wai Yarinyar nab da son Girma Zata kalla tace kaninta.?
Ya karishe Fada yana nuna kansa Cikin Bacin rai.
Saifullahi yace”Coool Down..Tunda munsan Tana son Girma..mu Barta da Girman kai ka zauna akanin nata mu samo mafita..Ka Daidaita da matarka Sulaiman..Kila Faruwar haka ya Rufe Damar da Hajiya ta samu ayanzu Wajen Tusa maka auran Laila..!
Wani irin kallon kama Rainamin Wayau Sulaiman kemai kafin yace”Ni in zama kaninta..?Bansan kana shan kwaya ba sai yau Saifu..!
Saifullahi yace”Tare muke shan..Kai bakasan abun arziki ba kankantar zai makale maka ne..Kai da in kuka Hada kanku da girman nata da komai Zaka Lamkwasata ta koma kasanka sai yarda kayi da ita Namiji ne fa kai Duk Girman kanta tana da Zatin Ka ne..?ta isa taja da Namiji..!duk kamewarta ai Mutum ce Tana da Kwayoyin Halitar Bukatar Namiji atare da ita..!
Tsaki Sulaiman ya saki kafin yace”Ni da ita?ko ka manta Yayar matatace Sunaira..?
Saifullahi yace”Nasani..!
Sulaiman yace”Kuma kake fadin na je na Nuna mata Girma na..Hala ce maka akayi ni yanzu ma ina da wata Sha”awa ne…Mtseww Tun bayan Rasuwar Noory komai ya Tsayamin kamar tatafi da duka kuzarina ne..!
Saifullahi yayi Dariya yana Fadin”Yanzu Sunaira ta Shude a Rayuwarka Sulaiman..Sunaima itace K’ADDARANKA yanzu..!
In kana son komai ya Daidata sai ka Bude Zuciyarka da Hannayenka ka Rumgumi kaddaranka..!
Sulaimam ya juya kawai kujeraansa na Iko Tana Juyawa dashi Bayason ma ya karajin mganar Saifullahi domin abun bama mai yuyu bane,Yarinyar da ta gama Rainasa wai kaninta..?agidan Ubanta ya zama kaninta tasama ya Kunduma Baba zagi..Shekaru hudu ya bata ammh Tana mai kallon kasa da ita Gata da Girman kai sai abunda Taga Dama take yi ba Tun yau ba yasha Jin Noory tana Complain kam Taurin kan yayar nata Tun Tana da Rai alokacin Tabe baki kawai yake acikin Ransa yana Fadin Duk wanda ya aureta shine za”ayi ma Jaje ashe ashe Alokacin Zanen kaddaransu yana Hade gashi yanzu shine acikin Jajen Tsumutsumu.
Kafin Saifullahi yayi niyar Bude baki yayi mgana Sakariyar Sulaimam Lazifa ta Bude Kofar Office din ta Shigo da sallama Saifullahi kadai ya amsa mata Cikin Ladabi ta Ramkwafa Tana Fadin”Ranka ya Dade..Sani Direba ne yazo yana son ganin Yallanbai..!
Jin haka yasa bai jira cewar Saifullahi ba ya Juyo yana Fadin”Send Him in..!
Kai ta Jinjina kafin ta Fice Tana wani Taku Daya bayan Daya Dukkansu da kallo suka Bita Saifullahi ya Dagamai gira yana Fadin’Ga wata fa..In Laila bataa maka ba,sai ka Raka da Sakariyarka da nasan ka Dade da Fahimtar she is in love with u..!
Sulaiman ya Tattare Fuskarsa kamar yaga kashi kafin yace”Jira nake ta kasa Hakura ta Furta..She wil Fired aranar Wlh..!
Yafada yana Bubbuga kafarsa saman Tattausan Cafet din Dake Office din Dariya Saifullahi yayi daidai Lokacin da Sani amintattacen Direban Sulaiman ya shigo matashi ne mai jini ajika Dukawa yayi yana gaishesu Saifullahi ne kadai ya amsa banda Sulaiman daya katse shi da Fadin”Ina su Wasim..?ina fatan ka kaisu gida ka Damka su hannun Magajiya..?
Yafada yana Duba agogon Hannunsa ganin Har La”asar ta Kusa.
Sani Cikin Sadda kai yace”Yallabai koda naje na Iske Antynsu tazo Daukansu nayi nayi ta bari na kaisu Gida Taki yarda Daga karshe ita ta bani Umarnin dawowa kamfani ita kuma ta Daukesu suka wuce gida..!
Tunda ya Fara mgana Sulaiman ke kallonsa Yana Jin bacin ransa na Karuwa Cikin Dan Sauta Murya yace”A ina ta Dauke su Sani..?
Cikin dan In ina yace”a..Adaidaita Ranka ya Dade..!
Mikewa yayi a Fusace yana Buga Teburin gabansa da karfi sai da wasu Fayels suka Zube a kasa Lokaci Daya Cikin Hargowa yake fadin”Wani irin iskanci ne wannan sani..?kamata a rika Yawo da ya’yana acikin adaidaita duk Tarin arzikin dana mallaka..Kana sane ba iya wannan ma”aikatan ba Ina da Kamfanin Sarrafa Madara na S.A.KARGI YOGHOURT, AND FURA dana gina shi da gumina ace duk tarin arzikin nan nawa ya”ya na suna yawo acikin Adaidata sani kana ganin kamim adalci kenan..?
Ya karishe Fada Cikin bayyana Bacin Ransa Sani Cikin rawan jiki yace”Wlh Yallabai nayinayi da ita ta shiga na karisa dasu gida taki yarda..Tace na dawo kamfani kana Bukata ita zata karisa dasu..!
Sulaiman ya watsamai wani kallo yana Fadin”Wato itace ma mai baka Umarni..?ita ta Dauke ka aiki ne Sani..?nace ita ke Biyanka albashinka Duk wata ko ni..?
Sani da kansa ke kasa Cikin Rawan jiki ganin megidansa nasa cikin Bacin rai yace”Amin afuwa Ranka ya Dade..Naga Antyn suce..Kuma Hajiya fa Matarka shi..!
“To hell with Hajiya..Da Anty su din Gabadaya sani bar gabana kafin Raina ya baci na zageka Wlh..Har kai zaka Fadamin matatace..?kafini sanin haka ne..?
Nace kafini sani ne..?
Yafada cikin Hargowa har yana kokarin baro inda yake zuwa gaban sani Da sauri Saifullahi ya Mike ya kalli SaniDake Durkushe yana Fadin”Allah ya huci zuciyarka Ranka yallabai ayi hakuri..!
Hakurin Dayake basa ji yake kamar yaa Mangaresa Hararansa kadai yake yi ganin haka yasa Saifullahi kallonsa yana Fadin”Sani tashi kaje abunka..Jeka Jirasa a waje..Wannan Fushin ba naka bane..!
Da hanzari sani ya Mike ya Fice yana Sauke Numfashi da Oga Saifullahi ya Kwace sa da yau megidansa nasa ya Zazzagamai na Zazzagawan nasa.
Yana Fita Saifullahi ya juyo kan Sulaiman Dake faman kokuwa da bacin Ransa yana Fadin”Ina Ruwan Sani da zaka rufeshi da Fada..?umarni ta basa kuma yabi..In kana son gaskiya kamar yadda Zaka bama Sani Umarni yabi haka itama Zata bashi..kuma bakaji me yace ba Antynsu ce fa?kaima in da kara ai Antynka ce..!
Yafada yana Danne Dariyansa Sulaiman ya Juyo yana kallonsa aransa yana Daidaita manyan Ashariyan da zai Shimfidama Saifullahin ne.
Saifullahi Daya Fahimci haka sai ya Daga hannu yana Fadin”Nifa kadaina kalloma haka..Tattara wannan Angry din naka ka bari in ka koma Gida Antnynka nachan na Jiranka..!
Sulaiman bai ce komai ba ya wuce zai shiga Tiolet din dake Office din Saifullahi na Dariya yace”Yauwa Kargi don Allah ka siya adaidata Tunda naga Anty naka tafi kwarewa ahaawanta sai ka Daukan mata Direba Shikenan ba damuwa acikin haka..!
Sulaiman kamar bazai Tsaya ba sai kuma ya Dakata ya Juyo Fuskarnan Tamau yana kallon Saifullahi kafin yace'”Baka fahimta ba..Aini ya”yana na Damu dasu..Ba ita ba..Ba adaidaita ba ko bayan a kori kuran awakai zata shiga ko akwalan Dan mutanen Kargi..!
Daga haka ya Tura Kofar Tiolet ya shigo ya bankota da karfi yabar Saifullahi da Dariya shima Ficewar yayi zuwa nashi Office din yana Faman Tunanin yaushe ne Kargin nasa zai Daina Gujema kaddarasa Daga shi har Sunaima din..?
Yana ji ajikinsa Kaddaran Data Hadasu mai karfi ne da bazata Rabasu Cikin Sauki ba..!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button