MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Laila na Zaune kan Cinyar Sulaiman tana Bashi Ice cream din da suka siya ahanya abaki Daga ita sai wata Shegiyar Rigar atamfa da aka Lalata mata Dimkin duk ta kamata kamar wani gaula Haka yake Bude baki tana Sakamai Safiya Data gaji da Sallama ta Bude kofa ta shigo sai tayi mummunar gani Ido Hudu suka Hada da Sulaiman sanda yake Bude baki Zai karbi Ice cream din da Laila ke basa.
Safiya ta kame Daga Tsaye Cikin mamaki Tace”Yaya daman kana Lafiya shine ake kiranka a waya baka Dauka..?
Tafada tana kallon Laila da mamakin ganin Safiyar ya kamata Sulaiman kuma bakinsa Bude ya kasa wani Katabus Daga inda yake zaune.

Janafty..
MIJIN KANWATA..!
(k’addarata)

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

Page 17

Mikewa Laila tayi daga kan jikin Sulaiman Lokaci daya tana Tattaro kalaman da zatayi amfani dashi Saboda kada safiya ta fahimci wani abu na faruwa in bata manta ba, a koda yaushe sukayi waya da mommy gargadin datake mata kenan kada ta sake ta bari wani daga bangaran Sulaiman yasa ita ke jan Ragamar Rayuwarsa.
Da Mirmishi ta tinkari Safiya ita kuma ba ita take kallo ba Hankalinta na wajen dan”uwanta da taga ya rame kamar ba Saraki ba,Bata damu da Laila ba ta wuceta bata ma sani ba ta karisa gaban Sulaiman cikin karin mamakin ganin ko bai mgana bai mata ba ko bai ganeta bane..?
Haba taya za”ayi ace ya saraki bai ganeta ba sai dai in wani abu ne yake Faruwa..!
Kai tsaye tace”Ya Saraki Hajiya ta Damu da Halin da kake ciki bama Hajiya ba kowa da kowa ashe kai Lafiyarka kalau ayi ta kiranka a waya baka Dauka..!
Tafada Lokaci daya tana kara nazarinsa Dagowa yayi ya zuba mata ido da Rinanun idanuwansa azuciyarsa farimcikin ganinta yake yi yana so yace mata wani abu sai dai bai da wannan ikon Laila na wajen yayi kokarin mikewa idonsa na kallon Laila sai kuma ya koma ya zauna kamar wani Sakarai Gaban Safiya ya Fadi ta kallesa Daga sama har kasa na wani Lokaci Tana nazarinsa kafin ta Juya tana kallon Laila cikin nazarinta wacce ta Kakaro mirmishi lokaci daya tana fadin”Sannu da zuwa Anty Safiya..!
Ko amsa mata batayi ba ta sake maida kallonta kan sulaiman cikin son Cire Shakkunta tace”Ya saraki mgana fa nake yi..?meyasa hajiya ke kiranka baka Dauka..?ai ko baka Saurari kowa ba ita ta chanchanci ka Saurareta..!
Sanda take mganar ji yayi kamar ya tashi ya Rumgumeta ya Fadamata bai sani ba wani bakinciki ya Lullubeshi sai alokacin ya Tuna da Hajiya Hajiya fa itace ta Haifesa har da ita ya manta da ita.
Laila na kokarin mgana kawai kamar an Fizgi bakinsa taji yace”Bansani ba Safiya..bansan Hajiya ta kirani ba ni mantawa nake da kowa da komai komai yana Hannun Lailata harda duka Wayoyina..!
Yafada yana saurin kauda kansa yama ji kamar bashi yayi mganar ba kamar an fizgo mganar daga bakinsa ne Wata uwar Harara Laila ta sakarmai wanda yasa ya marairaice yana Fadin”Don Allah kiyi hakuri Lailata..bansan na fadi haka ba..!
A muryansa kamar zai saki kuka Safiya datayi mutuwar tsaye kanta ya Sara Kirjinta ya bada wani Dam!
Jikintaya fara rawa ta dafe kanta ita ba yarinya bace tsakaninta da Sulaiman shekaru hudu tasan komai a shekarunta yaci ace ta Fahimci wani abu.
Hawaye suka ciko idanuwanta hakoranta suka fara kafkaf kamar wacce zazzabi yakamata Laila kuwa kokarin kare kanta take yi Cikim Muryanta take fadin”Kaji Habibina da wata mgana?saboda kaga Anty Safiya kake bani hakuri..?kinji kyalesa fada fa ya gami mun yanzu shine don ya ganki ya sauya mgana..mganar wayarsa kuma ta Fadi a kasa ne Screen ya Lalace ba”a ganin mai kira tana Hannuna wayar nayi nayi a siya wata yaki yace yafison agyarata to tana wajen gyara mai gyaran wayar ne sakarai ya bar wayar a kunne kuna ta Kira shuru..!
Safiya data gama jin Rainin Hamkalinta cikin wata murya tace”Ke baki da waya ne..?ko ya Saraki ya rasa yadda zai kira iyayensa ne..?sannan nazo gidanan tun Safe bakwanan da kuka dawo na aiko a sanar daku me kikace..?
Bazaku ga kowa ba..Daman haka kuke ma baki in sun zo..?
Laila na shafa girarta tace”Ai bamu san ke bane..na zata!
Bata gama Rufe baki ba Safiya ta kariso gabanta batayi wata wata ba ta Chakumi wuyanta Cikin bacin rai da karaji take fadin”Me kika yi ma Dan”uwana Laila..?Don buraubanki me kika bashi yasha ya koma haka..?
Ayadda take mgana ranta ya gama baci idonta kuma ya rufe Cikin karaji take mgana tana jijjiga Laila Da karfi wacce ta tsorata ta fara rawan murya tana Fadin”Ni…ni..ban yi komai ba..!
Fas..!Fas..!
Safiya ta tsinketa da mari har guda Biyu dama da Hauni da sai da ta nemi ta kife Safiya ta sake Chakumota Cikin Tsawa da karaji take kara fadin”Nace uban me kika basa yasha don Uwarki Salame..?
Sulaiman daya mike da Sauri ya Zaro ido Dashi da Laila wacce ta Fashe da kukan tsoro da makirci tana Fadin”Wayyo Ni me nayi mai..?habibi zata kasheni wuyana..!
Kamar kububuwa haka ya karisa ga Safiya ya rike hannayenta Dake wuyan Laila yana kokarin bambareta safiya da bata gani daman bata Daukan Raini itace sak Hajiya zabba”u a Tsaye take bata daukan Raini ko kadan
Safiya batama tsaya bi ta kansa ba ta kara kwadama Laila mari a wajen kunnenta Daya shigeta Cikin karaji ga Hawayen takaichi sun fara zubo mata ta jijjigata tana Fadin”Zaki fadamin ko sai nayi miki dukan tsiya..?
Laila sai Habo ta baki ta hanci tana Lakato hannunta taga jini sai ta fasa Ihu kamar zai Tsaga gidan tana Fadin”Sulaiman kana gani yar’uwanka zata kasheni ko..?
Kalli ta fitarmin da jini fa na shiga uku..!
Take fada tana kuka da ihu wanda yayi daidai da shigowar Sunaima Falon ta iske su magajiya Tsaye hannu Dafe kan kirji Ita dasu Samira kafin ma ta tambayi ba”asi ta samu amsar tambayanta na jiyo ihu da Hayaniya Daga upstsir Cikin mamaki ta kalli magajiya tana Fadin”Meke faruwa ne..?hayaniyar suwaye nake jiyowa..?
Magajiya tace”Hajiya Safiya ce kanwar Yallabai ta haura sama ba Dadewa sai kuma mukaji ihu da Hayaniya..!
Sunaima tayi jim aranta tace ko sun samu Labari ne..!
Ganin bata da amsa ne yasa taja Jikinta zuwa Dakinta ammh gabadaya Hankalinta na Falo tana son sanin meke Faruwa..?kodai wani abu ne ya samu Sulaiman din..?sai da gabanta ya fadi da tuna da hakan Saboda ayanayin datake ciki bata kaunar wani abu ya samu Sulaiman ko Saboda su wasim.

Sulaiman yayi iya yinsa ya Raba Hannayen Safiya da wuyan Laila ya kasa Cikin bacin rai ya kalleta yana fadin”Sakarta Safiya…!
Ko ta kansa bata bi Laila ta shaka Duk tayi wujiga wujiga,Safiya ta kara kaimata mari sulaiman ya tare yana Fadin”Kada ki karamin dukan min mata Safiya..!
Cikin karaji sai alokacin ta Dago tana kallonsa cikin hawaye tace”Bazan daina Dukanta ba sai ta fadamin me tayi maka..?me ta baka kasha ta mallake ka..?
Ido ya Bude mata yana Fadin”Ni nace miki an mallakeni..?
Safiya na kuka tace”Aini ba yarinya bace nasan komai haka kake..?kalli yadda fa ka koma ya saraki..?
Tafada tana nunasa sai kuma ya koma yana bin kansa da kallo ganin haka yasa tayi kukan kura ta kara danko Laila datayi gefe tana sosa wuyanta Lokaci Daya tana Zare idon Wahala ganin tayo kanta yasa ta fasa ihu da gudu sulaiman ya tare Safiya bai yi wata wata ba ya saka Hannu ya Tsinketa da mari cikin Rashin Hayyaci sai kuma daga baya yazo yana Takaichin kansa yabi hannunsa da kallo.
Safiya tadafe kuncinta cikin kuka tana Binsa da kallo Cikin muryan kuka tace”Saboda wannan abar ka mareni ya saraki.?saboda ina so ta fada da bakinta abunda ta aikata maka..?
Laila daga bayansa ta rikosa tana Fadin”Habibina ka karota..So take ta Kasheni in kuma bazaka iya Koranta ba ni zan tafi in bar maka gidanka..!
Tafada cikin kuka ai jin abunda tace kamar dalma haka yaji da sauri yace”A”a ba inda zaki je sai dai ita ta fita ta barmiki gidanki..Ki kama Hanya,ki Fita tunda ba zaman lafiya ya kawoki ba..!
Safiya sai ta kara Sandarewa hannu Dafe da kunci tana kallon Laila tana kara Tabbatar da zarginta tace”Yanzu Saboda tace ka koreni sai ka koreni ya Saraki..?nice fa yar”uwanka Safiya..!
Kai ya Dauke yana fadin”Umarninta shine nawa..Just go Safiya..Bana so ki fita kina sakawa ina jin kaina kamar bani ba!
Yafada cikin wani yanayi Safiya ta tsaya tana ma laila wani kallo kafin tace”Ki Rubuta ki ijiye Alkadarinki ya karye Laila..Tunda Uwarki taci Amanar zaman Tare da kaunar da ke Tsakaninta da Hajiya to ki sani kema watan tonon asirinku yazo daka ke har Uwarki..!
Daga haka ta Fice tana sharan hawaayenta tana fita Laila ta Bita ta saka ma kofa key ta tadawo Sulaiman na mgana bata sauraresa ta shige Bedroom ta banko kofa duk da taji jiki hannun Safiya bata wannan take ba Wayarta ta Dauko ta fara Neman Hajiya Salame ta fadamata abunda ya Faru sai dai kash ta kasa samunta ta Kira Hajiya Zaliha ita ta sameta cikin Rudewa ta fadamata abunda ya Faru Hajiya zaliha ta dafe kanta tace”Kash meyasa kika bari wani daga ahalin Sulaiman ya Fahimci wani abu..?Saboda sharadin mallam ne..!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button