MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Shakira..
MIJIN KANWATA..!
(k’addarata)

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

Page 24

Kadan ta taba abincin Zobon da aka kawo mata tasha sai Fruit ta koma ta kwanta mganinta ta Duba acikin karamar jakarta bata gani ba alhalin tasan Sadda ta sakashi da hannunta Bayan Sulaiman ya bata sai yanzu ta Fahimci wani abu Saraki ya cire mganin Tabbas domin ta gansa da Jakar gabda da zasu sauka kwafa tayi ita kadai aranta tace yayi ta kayan mgani ammh ita bazata nemesa ba ya ida kasheta Likita tace ta samu Ishashen Hutu sosai.
Kwanciya tayi saman makeken gadon Dake daki ba Dadewa barci ya Kwasheta ga gajiyan tafiya ga Gajiyar Sulaiman koda su Safiya suka shigo mata sallama zasu tafi tana barci sai basu Tada ita ba Dukkansu da yammah Abba yace kowa ta koma Gidan Mijinta sun gode da Zumunci.
Sulaimam kuma yana Tare da Abba sai yammah ya isa Shashensa na Baya tun yana Saurayi bayan komawarsa kaduna sai Sadiq ya dawo Shashen,Wanka yayi ya sauya kaya Saboda warware gajiya aransa yana Dariyan keta sanin Sunaima zata nemesa Dolenta kodon mganinta Daya Dauke ajakarta.
Su Wasim kuma suna Tare da Hajiya Daman Tana son su sosai Kaunar Datake yima Saraki shi ya shafesu,Tun Sunaira nada rai koda sun zo tana Kulasu sai dai ita Sunairan ne bata bi ta kanta tun alokacin.
Sai mangariba Hajiya karama ta tada Sunaima Domin tayi sallah sai Lokacin tatashi Wanka ta sake yi ta Kara gasa Jikinta ta sauya kaya zuwa wata Saukakkiyar Doguwar riga Kirar Armani,Tayi sallar mangariba tana Zaune tana Azkar taji muryan Hajiya afalo suna mgana da Hajiya karama Sauri take ta gama Azkar din ta Mike ta Fita ta gaisheta sai gashi ta Shigo Dauketa da Wafiya da aka Sake ma wanka aka sauya mata kaya da Sauri Sunaima ta shafa addu”arta ta Mike tana Fadin”Barka da Fitowa Hajiya..!
Hajiya na Mirmishi ta Zauna gefen gadon tana Fadin”Yauwa..Kin sha barci Dazu da su Safiya zasu tafi suka shigo yi miki sallama kina barci nace su kyaleki gajiyar hanya ne..!
Sunaima kanta na kasa tace”Wlh ban san ma barcin nawa yayi nisa ba haka..Allah sarki duk sun tafi kenan..?
Wafiyya Dake jikin Hajiya ta fara mika mata Hannun tana kiran Anty Hajiya ta mika mata ita tana Fadin”Karbi wannan Rigimammiyar yarki..Daman Amaryar Abbansu ne shi kadai ke iyawa da ita..!
Karbanta Sunaima tayi tana Dariya tace”Hajiya kodai kishi ake da ita..?
Hajiya ta Dunkure ma Wafiyya Kishi Tana Fadin”Wazai yi kishi da wannan..Ai ni nafison Megidana Wasim..Yabi su saraki masallaci ammh wannan karon yana matar dani..!
Dariya sunaima tayi batace komai ba Hajiya ta kalli Sunaima tana Fadin”Munga abun arziki Sunaima..Mungode kwarai Allah ya saka.!
Sunaima tace”Ba yawa Hajiya bai FAdamin tafiyar bane sai jiya da Daddare..!
Hajiya tace”Mai yawan kenan..Ya wajen su innan naki..?in sha Allahu in na shiga Kaduna zan je mu gaisa..!
Sunaima tace”Suna Lafiya Hajiya..To Allah yabada iko..!
Ta amsa da Ameen Abun mamaki sai ga shi suna ta Hira da Hajiya tana gayamata irin yadda Abunda Hajiya Salame tayi mata ya batamata rai sosai ya saka mata rai duk yadda suke da juna ta kalli Sunaima tana Fadin”Ko Fulani da maimartaba basu san Tsakanina da Salame ba Sunaima..Duk abunda kikaga inayi Harda Gudummuwarta ko naso na Saki ita ke kara Zugani Sannan wannan abun dayafaru na Fahimci Rayuwar nan Daga Kafa sai kauri kowa nashi ya sani..Ko yan”uwanta suna jinjina amintanmu sosai kuma suma sun mamakin abunda ta aika kuma sun kirani sun bani Hakuri Hajiya uwa harda kukanta kowa kuma yaji Hukunci maimartaba sai yace hakan Shine Daidai..Jiya ma Hajja Giwa ke Fadamin ta Kira Alhaji Isa yana Fadamata itama Laila yana chan yana hukuntata Domin ya Sallami Duka yan aikin gidan ita ke komai Saboda ta gane Rayuwa ta kuma Girbi abunda ta Shuka Lokaci daya tana Idarta agida..!
Sunaima kanta na kasa batace komai ba Domin Daman ai Haka rayuwa ta gada abunda ya saka Dariya wata Rana shi zai sakaka kuka Hajiya cikin Rainin murya take fadin”Sai gashi Auran da naso hadashi Har acikin Zuciyata da Niyyar alheri ne karshe ya Zamemin Sharri. ke da naki ki Sunaima keda yar”uwarki kune Duniyar Saraki Alherinsa Tunda Saraki ya auri Sunaira yake samun Cigaba har tabar gidan Duniya bata taba Daga kai ta kalleni da duk Abunda nake aikata mata ba..har yau har gobe ina jin nauyin ta koma ga Allah ban nemi gafaranta ba Ina jim wannan Nauyin acikin Kirjina..!
Hajiya ta Karishe Fada Cikin Wani Rauni da nadama da Sauri Sunaima tace”A”,a Hajiya Sunaira ta Fadamin bata taba rike ki ba acikin Ranta ba..Har ta koma ga Allah a mtsayin Uwa take kallonki Sannan har yau har gobe Inna Fadamin take ke din tamkar uwa kike garemu yadda zamu bi da ita haka zamu bi dake shiyasa na Fadamiki Sunaira bata koma ga Allah tana mai jin Haushinki ba..!
Hajiya ta kada kai tana Fadin”Madallah da uwa ta gari..Zan je kaduna Domin nayi mgana da mahaifiyarku na gaida Jarumar uwa kamarta Uwar data Haifi ya”yan Data Lullube rayuwar Saraki da Dimin Alheri..Ina kara neman afuwarki Sunaima don Allah ki yafemin..!
Sai kuka Daman yanzu mgana Daya Hajiya sai kuka Saboda abun yayi bala”in tabata Sunaima ta Kalleta tana Fadin”Ki daina kuka Hajiya..Wlh ban taba kullantaki ba..Na yafemiki Duniya da Lahira nima ki yafemin Domin na Taba maida miki mgana ammh har ga Allah bada sunan Reni ba..!
Hajiya na sharan kwallah tana Fadin”Bakim komai ba in ma kin yi min na yafe miki Duniya da Lahira…Allah yayi muku albarka ya baku Zuru”a nagari..!
Sunaima ta amsa da Ameen ameen Hira suka Cigaba da yi kan aikinta Har Hajiya karama tazo itama ta zauna suna Hiran tare Jefi Jefi Sunaima ke saka mata musu baki in sun Sakota Wafiyya na Jikinta tayi barci sai daaka kira sallar Isha”i suka Fita suka barta tatashi ta kwantar da Wafiyya itama ta tada Sallah
Bayan ta idar Hajiya karama ta Leko tana ce mata”Sunaima ki fito Falo Abbansu yace kema dake yau za”ayi Dinner gabadaya..!
Sunaima ta sunkuyar Dakai tana Fadin”Hajiya a koshe nake wlh..!
Hajiya karama tace”Kiran Abbansu ne fa Sunaima..!
Tafada tana Dariya Dole Sunaima ta Saka Hijabinta Dogo da tazo dashi Wafiyya tayi barci Sai ta kara gyara mata kwanciya ta fita zuwa Babban Falon gidan Cikin jin kunya Domin bata Sakewa ita ko agida haka take bata cika son mutane ba ballatana yanzu datake gidan Surukanta sannan uwa uba ga abunda ya Faru tsakaninta da Saraki ba Domin tasan yadda zata kula da kanta ba da Bazata iya Fitowa cikin mutane ba har yanzu tana jinta wani iri bata gama Dawowa Daidai ba.
Tana Fitowa gabadayansu suka Juyo suna kallonta suna zaune dukkansu a babbar darduma atsakar falon,Abba na gefe Hajiya karama da Hajiya sun sakasa atsakiya sai Wasim Dake jikin Abba Sadiya na kusa da Saddiqa sai Sadiq dake gefenta Saraki na Daga gefensa Shima idanuwanta da suka Zuba mata yasa ta fara Hardewa Daga Tafiya barinma Uban gayyar Daya sakar mata ido kamar zai Lasheta.
Kanta na kasa ta kariso Dakyar Wasim ya wage mata baki yana Fadin”Anty….!
Dagowa tayi tana kallonsa kafin tace”Wasim..!
Abba ya shafa kansa yana fadin”Anty da kayi ma yaji tunda kazo baka nemeta ba ka nane ma matana..!
Dariya aka saka gabadaya Sadiq yace”Abba na kishi..!
Hajiya tace”Kuma muna mijin dashi ba..!
Sunaima Dai tana jinsu Sadiya ta matsa mata kusa da ita tana Fadin”Anty Sunaima zo ki zauna kusa dani plz..!
Da sauri Sulaiman yace”A”a tazo ta zauna anan..!
Yafada yana nuna mata gefensa Hajiya ta kallesa ta Hararesa sai ya Sadda kai yana Shafa keya Abba ne yace”Zauna kusa da kanwarki Sunaima kyale saraki..!
Kusa da Sadiya ta zauna ita da Saddiqa ta saksu a tsakiya Kanta na kasa ta Duka tana gaida Abba ya karba Cikin Sakewa yana Fadin”Naga sako nagode kwarai..!
Kanta na kasa batace komai ba Hajiya karama tace”Aifa mun ga abun arziki Sunaima Allah yayi albarka..!
Saddiq yace”Anty sunaima..Dambun naman nan yayi dadi in zan zo Kaduna irin shi zaki man!
Sadiya ta Harareshi tana Fadin”Iyayan kwadayi..!
Shima Hararanta yayi yana Fadin”Nice ke kin manta ne..!
Saraki Dake Shan Fruitsalat ya kallesu yana Fadin”Ya isa haka Sadiq..!
Saboda yasan Halinsu yanzu sai Fada Abba yace”Ya wajen su Mahaifan naki..?mun kwana biyu bamu gaisa da Mallam Datti ba..!
Sunaima tace”Duk suna lafiya sun ce gaisheku..!
Sadiq yace”Ina Ahmad..yana da Dadin zama akwai barkwanci..!
Sunaima tace”Haka yake shi..yana Gida yace duka agaisheku..!
Abba ya kalleta yana fadin”Ya wajen aiki naki..!ina fatan komai lafiya..?
Sunaima tacr”Eh Abba komai lafiya..Mungode Allah ya kara Girma..!
Aka amsa da Ameen kafin yace afara cin Abinci Sulaiman sai Faman neman ya Hada ido yake da Sunaima ita kuma taki yarda ta kallesa saboda tana ganin yadda yake binta da mayen kallo.!
Ferfesun kaji Sadiya ta saka mata mai Romo taji Dadinsa sosai ganin bata da Sakewa yasa Abba Daya gama ya tashi Shi da su Hajiya ya Kira Saraki suka koma Shashen Hajiya suna hira sai Lokacin ta samu Sakewa taji dadi naman sosai,Sadiya da Saddiga suna da Dadin zama sosai,Sadiq kamar Ahmad yake sai ban Dariya barin ma in suka fara Gaddama da Sadiya bayan sun gama cin abinci Tasha kunin Aya sosai yan aiki suka kwashe komai Zuwa Kitchen nan falo suka zauna suma hira duk da bata saka musu baki Daki take so ta koma ta kira Inna Tunda suka iso bata Kirata ba Wasim na Wajen Sadiq har yayi barci ganin Hirar taki karewa ne yasa tayi musu sallama tace zataje ta kwanta.
Tana shiga Dakin ta iske wayar Inna ta Kirata bata kusa sai ta Kirata sukayi mgana tace mata sun iso tun Dazu su Wasin ta tambaya tace mata sunyi barci tace agaida kowa da kowa suma suna gaisheta.
Daganan sukayi sallama wanka ta Shiga ta gasa jikinta Zazzabin ya Saketa sai kanta ke sara mata kadan kadan bayan ta fito ta shafa mai ta saka Wata Doguwar rigar Barcinta mai Saukin Kauri tana da karamin Hannu ne tana Shirin kwanciya taji Sallaman Hajiya Hularta ta Raruma tasaka tana amsa sallamarta Hajiya karama ta leko Daga bakin kofa tana Fadin”Saraki ne ya kirani yace kizo ki karbi mganinki sai yanzu ya gansu Cikin kayansa..!
Sunaima na jin haka tasan bakin Zaren da Sauri tace”Ya barshi kawai bama zan yi amfani dashi ba..!
Hajiya tace”ah ba yace kina ta fama da Zazzabi ba..sai da kuka Biya ta asibiti ba..?
Sunaima sai ta kasa mgana Saraki ya gama Kasheta,
Kai kawai ta kada saboda kada Hajiya karama taga tana ta mata gaddama Ammh tayi alkawarin ita bazataje wajensa suyi abun kunya ba.
Kwanciyarta tayi aranta tana kunkunin mutum bazai barta ta Huta,Bata ga Wafiyya ba sai ta yi Tunanin kila Hajiya Karama ta Dauketa tana nan kwance sai ga wayarsa ya gaji da jira sai da ta katse bata Daga ba sai da ya kara Kira Sannan ta Dauka bai jira cewarta ba yace”Wlh in baki zo ba..Zan zo har Inda kike kuma in nazo sai nayi abunda ma baki Taba Tunani ba..!
Da Sauri tace”Me zakayi..?
Cikin Dakewarsa yace”Bansani ba..Ki jarabani ki gani..Kin yi alkawari kina so ki sabane..?
Kizo ina jiranki a Shashena..!
Daga haka ya yanke kiran bai jira cewarta ba,Sunaima tayi Sororo ta kasa Motsi aiya Jiya zuwa yau tasan Saraki zai aikata Fiye ma da abunda ya Furta din yasa Dole ta Mike ta Saka Hijabi ta fice ba kowa afalon Hajiya karama ma bata nan tana Shashen Abba ita keda dashi.
Sai da tazo Falon gidan ta rasa ina zata Nufa bata san Shashen nashi ba,Tsoro take ji kada Hajiya ta fito ta ganta tana neman Dakin miji ai da kunya wannan aiki Allah ya taimaketa sai ga Sadiq ya Sauko Daga Upstair batayi ma Tunanin zai iya zama Dakin yana sama ne sanin ko agida Dakinsa yana Upstairs ne.
Yana ganinta yace”Anty Wajen Yaya Saraki zaki je..?
Kunya ya kamata kamar ta Nitse bai jira amsarta ba yace”Da kin hau sama Daki na Farko yana ciki..!
Daga haka ya wuce shashem Hajiya chan suka koma da Hiran nasu Shi da su Sadiya.
Jikinta asanyaye haka ta Haura sama tana Wiki wiki da ido kamar wacce tayi karya daki na Farkon tayi knooking Daga ciki taji muryansa yana Fadim”Come in..!
Daman yasan ai zata zo yasanta da Tsoro kamar farar kuura
Tana Tura kofar ta shiga Dakin ba Haske sai na Dumlight,Sai dai tana Hangensa ta dan Haske yana Zaune gefen gado yana Danna wayarsa Daga bakin Kofar ta tsaya tana Fadin”Bani mganin zan koma kada su hajiya su Fahimnci nazo wajenka..!
Bai mata mgana ba sai da ya taso yazo gabanta ya riko hannunta da Hannu Daya ya maida kofar ya Rufo ya Rumgumota Jikinsa yana Fadin”Suma su Hajiya da kike jin kunya..Yanzu haka Daya ta shirya ta wuce wajen Abba..Sai ni sai ki yi min mugunta Sunaima..!
Yafada yana kokarin Rabata da Hijabin Jikinta Cikin tsoro tace”Saraki Likita tace na samu hutu fa..!
Yana karisa Cire Hijabin yana Fadin”Hutun datake mgana shine zan samar miki..!
Wurgar da Hijabin yayi ya fara kwakumarta Jikinta ya Fara kyarma Kira take saraki zazzabi nake ji shi kuma yana fadin”Muna da mgani Sunaima..!
Tana ji tana gani yajata kan gado yana yadda ya gadama da ita abun yayi mata mauyi agidan Surukai sai ta Fara kuka,Tana fadin”Don AllAh Saraki ka bari..Ina jin nauyi..Kabari in muka koma gidanmu sai kayi Dukkan abunda kake so kayi..!
Tafada Cikin Hawaye Sai jikinsa yayi sanyi yadda take magiya sai ya kyaleta bayan ya gama Dagula Mata Jikinta da kansa ya sakamata Hijabin ya kuma bata mgangunar yana Fadin”Yana iya..?Ammh zan yi hakuri tunda an bani damar in muka koma gida nayi yadda naso..!
Haka yafada yana sosa kansa ita dai bata tsaya bi ta kansa ba ta Fice gudu Gudu sauri sauri take yi bata son ta Hadu da wani har ta Shige shashen Hajiya karama sai ta danganta da Kan gadon kana ta Sauke Numfashin Salama da natsuwa sai da tayi wanka ta kwanta bayan tasha mganin Cikin natsuwa barci yayi awon gaba da ita sai asuba ta iya tashi tana yin wanka taji ta Sakayau ba Zazzabin gajiyan kuma ya saketa bayan tayi sallar asuba sai ta koma barcin mganin na saka barci ne shiyasa Hajiya karama Har lekota tayi taga tana barci sai suka karya su kadai Tunda Saraki yace bata da lafiya.
Koda tatashi Saraki da Wasim da Sadiq basa gida sun fita da Abba zuwa Kamfani Sai da tayi wanka ta karya ta Fita shashen Hajiya ta gaisheta Chan ta Zauna Hajiya sai janta take da Hira Dayake Sunaima bata da Sakewa sai dai Tayi Mirmishi mgana Daya biyu sai da su Sadiya suka shigo ne Hajiya ta shige Ciki ta barsu suma Daganan Shashen Hajiya karama suka koma wai zasu kallo Hajiya batason suna mata kallo suna Hayaniya.
Suna fita ta mike ta Shiga gyarama Hajiya Falon tas Ta shiga Ciki ta iske Hajiya ta shiga wanka sai tayi aamfani da wannan Damar ta gyara mata Dakin tana cikin Shiryamata Goggun kayanta da aka Dawo dashi Daga wajen wanki cikin Wardrope sai ga Hajiya ta fito har acikin Ranta taji Dadi tana ta saka mata albarka.
Ita ta Shirya kayan tsab ta turara Dakunam sannan tayi ma Hajiya Sallama ta koma tayi sallah ta kwanta sai barci sai gabda la”asar tatashi ta Sake wanka ta Sauya kaya sai lokacin Saraki ya Kirata yana tambayanta Jikin tace da sauki yace suna kamfani ammh gasunan zuwa Daganan sukayi sallama.
Bata fita ba tana ciki aka shigo mata da abinci Dambun shinkafa da Zogali taci sosai ta Hada da Zobo,bayan ta gama ta kwashe komai ta fita dashi Zuwa kitchen ta iske hadiman suna wanke wanke suka gaisa Sama sama ta Koma Daki ta kira Aneensa sukayi mgana Gobe aikin Safe gareta bazata Samu zuwa ba sai dai jibi Tunda Sai gobe da Safe zasu Dauki Hanya.
Batasan su Sulaiman sun dawo ba sai da Ya kirata yace ta shirya Direba zai yakaita gidan Safiya da Fadila dasu Radiya su sadiya su karata Hakanan ta shirya Hajiya ce tamai mgana tace ya kamata taje ta ga inda suke tunda gobe zasu koma.
Gidan Safiya suka fara zuwa Sadiya da Saddiqa suka rakata Direban su yakaita Safiya taji Dadi ta rasa ina zata sakasu basu jima ba sukabaro gidanta zuwa gidan Fadila bayan ta bata Turaruka gidan Fadila ma haka Harda kayan barci ta bata gidan Radiya kuwa harda kayan mata ta bata tace a gyara ma yayansu Sunaima tayi Dariya gidan Raliya ne na karshe ita dake maitama suka yada Zango nan sukayi Sallar Isha”i Wasim da wafiya suna makale da babansu basu biyota ba,sai tara na Dare suka Dawo gidan agajiye sun riga sun ci abinci gidan Raliya wanka kadai tayi ta kwanta saboda ta gaji sosai.
Washegari tun safe suka shirya Karfe 8am na safe suka Dauki Hanya bayan su Hajiya sun cikata da abun arziki Hajiya ta bata 20k da turaman atamfa guda Uku ta kaima Inna Hajiya karama kuma ta bada kayan barci da Dogayen riguna da takalmi Abba kuma ya bata 30k kayan arziiki kala kala haka sukayi mata ita da su wasin kamar kada su tafi har da Abba abakin Mota wajen Rakiya su Sadiya suna tacemata suna nan zuwa.
Misalin 12pm na rana suna Kaduna Sulaiman bai tsaya ba, kamfani ya wuce saboda Ana jiransa Saifullahi nata Kiransa ita da yaran kadai suka ijiye agida Sakon Inna Ahmad ta Kira tace yazo ya karban mata Yazo ya karba Dayakaima Inna ta kalla tace mahakurci mawadaci kowa yayi Hakuri watarana zai ji Dadin kaddaransa da Hakurinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button