MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Janafty
MIJIN KANWATA..!
(k’addarata)

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

Page 29

Yadda Sulaiman ke murna da Farincikin Samun cikin Sunaima kamar bai taba Haihuwa ba sai akanta Duk wani masoyinsa bawanda bai ji labari ba Tun Sunaima najin kunya har ta sake saboda dai taga Sulaiman bazai Daina kara”in dayayi Niyya ba.
Musamman yasa ta Rubuta Takarda aka aika dashi Board na asibitin su Cewa bata da lafiya an bata Bedrest na Sati biyu,kafin ta koma aiki,bata komai sai dai taci ta kwanta yanzu Barci take yi sosai kasala ke Rufeta da Ciwon gobobi,Kullum Sulaiman ke hanyar zuwa karbo mata Danwake da Tuwo wajen Inna in bai je ba Ahmad ya kawo mata,Sannan shine kullum bakin asibiti siyan Kosan manja da Dankalin Hausa shine cimarta Daddawa da yaji kuwa Sulaiman sai da ya fara Tunanin anya bazai Taba Lafiyarta ba Daya kaima Hajiya korafin tace kada ya Damu babu abunda zai faru.
Sannan har zuwa Lokacin bata son ya Kusanceta da an fara sai amai Sai Kuka abun ya fara Damunsa ya Dauketa sukaje wani private Hospital sukayi ma Likita Bayanin komai Shi yace musu Laulayin Cikin ne yasa taji bata son ya Rabeta da zai samu yadan Daga mata kafa zuwa Cikin ya tashi a Laulayinsa yafara kwari sannan yayi korafin Yajin Datake ciki kuma batacin Abinci sosai sai Danwake kawai Likita yace bakomai Kada ya Damu babu abunda zai mata da Cikin ya Fara kwari Shikenan zata Dinga cin abinci sosai,mganin karin jini kadai ya Rubuta mata suka dawo gida.
Dole Sulaiman ya Daga ma Sunaima kafa sai dai sukan Rumgume juna in zasu yi barci,Sai dai baya Kokarin yin wani abu da ita yanzu sai ta fara Amai Shiyasa saboda Cikin jikinta zai iya Hakura koma Menene indai Domin yaga ya Inganta ne.
Cikin Lokaci Sunaima ta Cinye Sati Biyun da aka bata a asibiti Sulaiman ya Hanata komawa wajen aiki Sai da ta kara Sati Daya Lokacin ta kara Warwarewa sannan ta koma Bakin aikinta.
Sulaiman inda son Ransa za”a bi bazai yarda ta koma aikin ba Shima sai da Hajiya tasaka baki saboda su Hajiya Falmata tazo ta Duba Sunaima ita dasu Sadiya Shine taji mganar aikin Da suka koma suka Fadama Hajiya Shine ta Kira sa tayimai mgana Dole ya barta ta koma Bakin aikinta Sannan ganin taji Sauki Amai da sauran Laulayan ya fara Sauki.
Koda ta koma gabadaya abokan aikinta Susan tana da Ciki sai Tsokanarta sukeyi kunya Sunaima ta rasa ina zata saka kanta Ta gama Borin kunya yanzu ga Ciki ya Bulla acikin Jikinta bata da Sauran mgana Shiyasa take yin Shuru sai dai ta Sunkuyar dakai tana Mirmishi.
Kullum Safiya sai Hajiya ta Kirata taji Lafiyanta sosai hakan ke mata Dadi Sannan kannensa ma suna iya bakin Kokarinsu akanta yadda suke ji da ita abun har mamaki yake bata Ko alokacin da Sunaira take da rai bata samu haka bs Daman Haka Rayuwa take Harta Abba Lokaci bayan Lokaci Yana Kiranta yaji lafiyanta yara kuwa akwai Weekend din da Sulaiman yaje ya Daukosu suna zuwa suka Fada Jikinta Wasim ke fadin”Anty kema zaki sama mana New baby ko..?
Tana jin haka tasan mai bakin Daya Fada Kallonsa tayi da Sauri yace”Kina wani Kallo na…bani na Fada musu ba..!
Yafada yana Daga Hannunsa alamun Sarrander Wasim ta kalla kafin Taja Kumatunsa tana Fadin”Waya fada maka Wasim..!?
Sulaiman ya nuna yana Fadin”Daddy ya fadamana Anty..!
Dagowa tayi tana Hararansa Dariya ya Sakarmata yana Fadin”Nifa bani kadai ne Daddynsa ba..Ki kara tambayansa..!
Wata Hararar ta Wurgamai tana Fadin”Bakin nan naka Saraki..Uhm..!
Gefenta ya zauna kan gado yana Fadin”Sai yasha Dirja ko..?yaushe ne zaki Dirji bakin nawa..Nima sai na yi Shagali na Tunda naga kin fara samuwa..!
Da Sauri Tace”A”a Wlh ban fara samuwa ba..!
Dariya yayi yana fadin”Matsoraciya..to ya mganar Dirzan bakin nawa..?
Yafada yana Tura mata bakin Da Sauri tatashi Domin yaran sun Fice Zuwa Falo Dauke da kayan wasansu Tana gyara Zaman Rigar Jikinta tace”Bakin ka bazai Dirzu ba..Saraki kai sai Allah ya shirya ka banga abunda zai saka bakin ka yayi shuru ba..!
Kai tsaye yace”Akwai..!
Cikin mamakinsa tace”Menene shi..?
Sai da ya Mike kafin yace”Saraki..Saraki..Saraki…Ka bari..Saaraki kabari..!
Ya kareshe Fada yana Kwaikwayan Muryanta Lokaci Daya yana Daga mata Gira Baki ta Rike kafin ta Dafe kai Tana Fadin”Saraki…!
Da Sauri ya Rumgumeta yana Fadin”Na”am Sunaimata..!
Duk yadda taso ta Zille masa bai bari ba sai da yadan Mori wani abu kana ya kyaleta Tana Tura baki Shi kuma yana Dariya yace”Uhm rayuwa Juyi juyi yau ni Saraki ake gudu..Uhmm Zaki zo watarana kina yar Murya. kina Fadin plz Saraki ka sosamin yana kin kaikayi..!
Yafada yana wani mele baki,Sunaima Batasan Sadda ta Ruga Tiolet ba Saboda bazata iya da rashin ta idon Saraki ba tana jinsa yana mata Dariya Tana Daga Cikin Tiolet ta Yi Mirmishi afili Ta Furta”Saraki..Allah ya shirya..!
Haka Rayuwarsu ta Cigaba da Gudana Cikin so da kaunar juna Sulaiman yana iya bakin kokarinsa wajen Kula da Sunaima Sai da Cikinta yayi wata uku taje gida Ta wuni wajem Inna Saboda kunya ne yasa bata je ba Tana jin kunyar Inna ta ganta da Ciki Sai dai Inna bata Nuna mata komai ba Duk da Taga yadda Sunaiman ke Wani Sunne kai Ahmad kuwa zama yayi yana Bada Labarin Rawan da zai yi In Sunamar ta Haihu agaban Baba fa Sai da Ta kwabesa kana yayi Shuru Inna bata nuna ma Sunaima komai ba ko afuska illah Farinciki da jin Dadin Yadda Taga Sunaiman ta karbi Kaddaranta tana zaune da Mijinta Lafiya itama Zata zama Uwa nan da Lokaci kadan.
Sunaima tana ta Damun Sulaiman da yaushe zasu je kargi ta gaida su Fulani sai yace ba yanzu ba Ranar Data ishesa Ya kalleta yace”Bafa yanzu ba..Sai Cikin ki ya Turo gaba kin Fara Takawa Dakyar..!
Baki ta Tura tana Fadin”Aikuwa bazani ba in har na koma haka..!
Yana Dariya yaja karan Hancinta yace”In kin ji zuwama Daya kenan..!
Dariya yake mata tayi mai banza Shi kuma hakan yayi mai yayi ta Tsokanaeta yanzu abun ya Farayin Sauki yakan Rabeta koda Sau Dayane asati,Ammh kam ko bai yi ba tana shan Jagwalgwala Da ta fara,kuka sai ya ja kumatunta yace”Sunaima..!
Sai ta hararesa tana Fadin”Saraki..Saraki..!
Shi kuma hakan yake so yayi ta Tsokanarta Tana kiran Sunansa shi kuma Hakan kemai Dadi yana karamai Nishadi.
Cikinta na Cikin na wata uku da sati Daya Khadija da Saifullahi da yarsu Jidda suka so musu Ziyara Sunaima taji Dadi Sosai jidda ta yi Bulbul da ita ta samu Nono mai kyau Sunaima taji Dadi sun zo mata da Tsaraban Su Taura,tsamiyan Biri,Goriba da Aya Jikskkiya Kamar sun sakata a aljannah Kwana Daya tayi mata anan Sai suka tafi Inda Saifullahi yake da zama Tayi mai sati Daya kafin ta Koma Taje Har Abuja wajensu Hajiya ta gaishesu ta kwana Daya ita da Sunaima sukaje da yara Saani yakaisu Sulaiman da Saifullahi suna Kaduna badasu akaje ba.
Sunaima Taga gata a Zuwanta Abuja Motsi kadan sai ance mata me takeso Har Khadija sai da tayi mgana Tace”Sunaima kin gama samun Duniya..Ga Soyayyar Miji ga Soyayyar Danginsa..!
Itadai batace komai ba Domin bayanin ai yana da Tsawo bata da tacewa Ammh in khadija tasan komai Zata san cewa Allah ne ke ikonsa kan komai.
Sunaima bataso Khadija ta koma ba Taso ta zauna akaduna ta samu kawa Sabooda tana da Dadin zama ga Hankali kuma sannan taso tazo Daya sai da Mama bata bari ba Saifullahin ya dauko matarsa ta dawo kusa Dashi tace ba yanzu ba ita kanta Khadijan tana son Zama kusa da Mijinta ammh babu Wanda zai ja da abunda Mama tace zasu Bita ahankali Zuwa gaba Har ta amince su dawo nan da zama.
Sai da Cikin Sunaima yakai Wata Biyar ta Dawo Daidai Ta fara cin abinci kamar hauka sai dai batacin mangyada sai manja sannan Ruwa sai dai na Gartsi bata shan na Leda an samu Saukin cin yaji da Wasu kayan kwalaman kamar Cikin yana karaminsa Taje an mata Scan ta kuma Fara zuwa awo anan asibitin Datake aiki Sannan Tana Hadawa da addu”o’inta Saboda Wani ciwon bakasan yana Jikij ka ba ammh in kana Kokarin azkar sai Allah ya Tsareka ballatana ita datake da Juna Biyu sai ta Kiyaye wasu abubuwan.
Alokacin Cikin har ya fara Fitowa Kadan Dayake tana da Tsawo sai ya Shanye Cikin nata Tayi kiba Bulbul kamar ba ita ba Ta kara Budewa Ranar Har Sulaiman na mata Tsiyan ta Fara zama Buttuka Harara yake ta sha Bata tankamai saboda tasan Halinsa in ta yi mgana Shi yake so in ya Fara Tsokanarta sai yaga ta kusa kuka kana zai kyaleta.
Mganar zuwa Kargi kuwa ta Daina Damunsa ganin bashi da Niyyar zuwa Kuma shima bai je ba sai dai suna Waya da Maimartaba itama Sunaima Fulani da Kilishi sun kirata suka mata Sannu tasan suma sun ji Labari Harda Takawan yaji Labari Sulaiman ya Fadamai Sunaima nada Juna Biyu Maimartaba na Dariyan jin Dadi yace”Masha Allah..Allah ya inganta..Kenan yanzu ba mganar Rabuwa Takawara na yayi aiki..!
Saraki yayi Dariya Kafin yace”Ta matsa sai nakawota ta gaisheka..Allah ya karama Lafiya ranka ya Dade..nagode kwarai Allah ya kara Girma..!
Maimartaba yace”Ameen Allah yayi muku albarka..!
Da haka sukayi sallama aran Maimartaba yana Hamdala da kuma kara Godema Allah Daman kullum addu”arsa Allah ya Daidaita Tsakaninsu ya sanya Farinciki a Rayuwar Jikar nasa kuma Allah ya amsa mai addu”arsa yaji Dadi kwarai.
Kamar yadda ya”yan maimartaba Matan sukayi alkawarin Haduwa su samu maimartaba su bashi Hakuri kan Salame,basu manta ba suna ganin Lokaci yayi Tunda anyi wattani Bakwai da Faruwan almarin zuwa Lokacin Maimartaba ya fara Hucewa ba kamar baya ba.
Hajiya Zabba”u bata Duba abunda Salame tayi mata tace da ita za”aje gaban Maimartaba Data tambayi Abba bai Hanata ba,Duk da baisan me zai kaita Kargi ba alokacin
Hajiya Balki tazo Daga Lagos Hajiya Giwa Daga kaduna sai Hajiya Indo da Kuma Hajiya Zabba”u,Tunda Fulani Taga zuwansu Lokaci Daya ta Zargi Haka Shima Maimartaba ya Zargi haka Tunda yaji Labarin zuwansu da kuma Sakon suna son ganinsa.
Bai samu Zama dasu ba sai Dare bayan an tashi Zaman Fada ya dawo Falonsa na Cikin gida sai da yaci abinci ya natsa kana ya Nemesu bayan gaisuwa da Tambayan iyalai sukayi Shuru kowa kanta a kasa Shima yana ta Nazarinsu ganin sun bata Lokaci kowacce taki mgana yasa ya Kallesu yana Fadin”Lafiya meke Tafe Daku..?Domin nasan wannan Haduwar taku akwai manufarta..!
Hajiya uwace ta fara mgana bayan ta gyara zama Cikin kaskastar dakai Tace”Ranka ya Dade..Allah ya karama Sarki Lafiya..Muna tafe da wata Bukatace..Musan Sarki adali ne mai karban Koken Takalawa da ya”yansa Musan ka kai din Sarki ne mai karamci Cikin karamcinka Ranka ya Dade muke Fatan ka Dubemu ka amshi rokom mu ka kuma Duba Bukatarmi kayi mana Alfarman da muka zo nema awajenka Allah ya karama Lafiya..!
Ta Karishe Fada kanta na kasa Cikin Kallonsu kai Tsaye yace”Ina Sauraranku..!
Wannan karom Hajiya Giwa ce ta gyara Zaman mayafin kanta tana Fadin”Ranka ya Dade..kan dai mganar Yar”uwamu Salame ne..Gamu tafe da kokon Baranmu muna Rokon mata afuwa wajen adalin Sarki da Fada gabadaya..Wlh Ranka ya Dade Salame ta tuba tayi nadama kuma Tayi Laushi Ataimaka a Dubata a Yantota Daga Shashen Bayi Ranka ya Dade..!
Ta fada itama kanta na kasa Maimartaba yayi Shuru yana nazarinsu kafin ya Tsaida kallonsa kan Zabba”u yana Fadin”Zabba”u harda ke kina Goyon bayan Fada ta yanto Salame duk da abunda ta aikata Miki..?
Hajiya ta Dago kanta ta kalli Maimartaba kafin ta sadda kanta Tana Fadin”Ranka ya Dade..Salame yar”uwatace da muka taso tare tun muna kanana..Bazan so yau tana cikin Wani hali na kasa rama Alherinta gareni ba..nasan Ta batamin sannan ruguza amintar Dake Tsakanimmu ammh hakan baisa na Kullaceta ba Har ga Allah na yafe mata..Kuma bani da wasu iyaye bayan kai da Fulani Ranka ya Dade..ko ina akaje Salame yar”uwatace bani da wata kamarta Uban ya”yana yaya yake gareta bani Da kamarsa Salame ta zama Dole ne Bai kamata don Shedan ya shiga Tsakanimi na koma Gefe ba Na tabbata yanzu tayi nadama abubuwan data aikata Ranka ya Dade a Duba wannan mganar Fada tayi afuwa ga yar”uwata!
Tunda ta fara mgana yake kallonta Farinciki da alfahari sun Lullubesa Ko bayan bashi Kan ya”yansa bazai Rabu ba Yana kaunar Zabba”u macece mai Tsananin kawaici da Sanin ya kamata Salamatu yarsace shima yana Damuwa Da Halin Datake Ciki sai da ya Ture Rokom kowa ne saboda Tayi Hankali da hukunci Fada ga Bama Dan Sarki ba Talaka yana Sane ko Fulani Damuwar Dake Damunta kenan su waziri ma duk sun gaji da Magiyan yayi musu bakan ammh yanzu Lokaci yayi da zai mata afuwa..!
Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin yace”Allah yayi miki albarka Zabba”u..Allah ya shirya miki Zuru”a..!
Suka amsa da Ameen kafin ya koma ya kallesu Daya bayan Daya ya fara mgana..”‘Daman bani Salame ta batawa ba..Zabba”u ce kuma tayi afuwa gareta..Zan yi afuwa ga Salamatu za”a yantota Daga Shashen Bayi sai da Sharadin bazan Tursasama Isa ya maidata Dakinta ba In yaji ya gani zai iya mata afuwa naji Dadin haka in bai ji ba to Salame ta Nemi wani mijin na Sake Daura mata Aure Domin bazam lamunci ta Cigaba da Zama ahaka ba..!
Wannan karom Hajiya Indo ce tayi mgana Cikin Girmamawa tace”Mungode Ranka ya Dade..Allah ya karama Sarki lafiya..Allah ya kara Girma..!
Dukkansu suka Zube suna mai Godiya ya amsa yana saka musu albarka kafin ya kallesu yace”Ku tashi kuje..Zuwa Gobe Fada zata yanto Salamatu..!
Da haka suka tashi suna Zubamai Godiya bayan Fitarsu ya Dade yana Nazari da Tunani acikin Ransa yaji Sanyi Daman Zabba”u yake ji kada Taga kamar yayi son kai Domin Salame yarsace shiyasa ya rufe ido ya Hukuntata Daidai da Laifinta.
Koda suka koma Cikin Gida ko Fulani basu Fadama komai ba sai Dai Hajiya Uwa tayi mganar da Kilishi Taji Dadi sosai Ta nuna Farincikinta.
Kamar yadda Maimartaba yace haka ta Faru ya bada Umarnin a Fito da Salame zuwa cikin gida da yan”uwanta suka ganta sai da suka mata kuka,Hajiya Zabba”u Taga yadda Salame kawarta Aminiyarta ta koma ta Rame ta lalace tayi baki Saboda Wahala Tana Hawaye Tace”Salame kece haka?
Hajiya Salame sai Kuka ta Zube gaban Hajiya Zabba”u Ta kama kafarta tana Fadin”Zabba”u nice haka..Kinga yadda som zuciya da Rudin Shedan suka kaini ko..?ki yafemin Zabba”u ban Rike anintarmu ba..!
Take Fada tana kuka Zabba”u ta Duka ta Dago ta suka Mike Tare kawai sai ta Rumgumeta Suka kamkame juna sai kuka Hajiya Zabba”u Fadi take”Na yafe miki Salame..Har ga Allah na yafe miki..!
Kowa Dake shashen Fulani Sai da yayi Hawaye Kilishi ce ta ja Salame zuwa Shashenta Domin tayi wanka ta Sauya kaya koda Fulani batayi mgana Har aranta taji Dadi kwarai Tayi ta ma Hajiya Zabba”u Godiya itakuma Tana Mirmishi tace”Bakomai Fulani Nida Salame duka Dayane..!
Salame tasha Dirzan Jikinta Saboda Daula bata taba Zaton zata samu yanci nan kusa ba,Tayi nadama tayi kuka batsan iyaka ba in ta Tuna Ita yanzu ba matar aure bace bazawarace abunda tayi yanzu ba Riba Tunda agabanta maimartaba yasa Sulaiman ya saki Laila in ta Tuna Haka sau ta fara kuka tana Tsinema Hajiya Zaliha Domin ita takaita ga Wannan Nadamar Datake Ciki ayau din nan

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button