MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Ban yi alkwarin bada Upade kullum ba sai dai zan yi kokarin naga ban baku kunya ba..Nagode..

Shakira..
15/05/2022
MIJIN KANWATA..!
(k’addarata)

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

Page 2

A.S.KARGI ENTERPRISES
03:00PM

Wani katon allo ne kafe da sunan A.S.KARGI ENTERPRISES akan wani katon Bulding mai girma da Fadi mai kama da wata alkarya guda Ginin yana Tsakanin kan Shararan Titin nan ne na Garin Kaduna wanda zai Dauke ke ka Shatalele har zuwa UTC sai dai Ginin Babban Ma”aikatan yana kan Titi ne kafin akai Utc.
A.S.KARGI ENTERPRISES babban Ma”ikata ce datayi suna kuma tayi Fice ma”aikata ne da ake Sarrafa Fata zuwa wani nau”in abun amfani da Bukatar kamar su jaka,Takalmi da sauransu ma”aikatan Tana da Tarin ma”aikata kama Daga yan Gida Nageria zuwa ma”aikatan Kasashen Ketare sannan kayan su kaya ne mai inganci da Nagarta Tunda yawancin Kayan aikin su suna yin Odar su Ne Daga kasashen Ketare,A.s.kargi yayi suna sosai saboda Ingancinsu da Nagartasasu shiyasa kaf kasar Nageria ba wanda baisan da zaman kamfanin ba,Duk da wannan karamin ma”aikatan ne wanda D’a Daya Tilo Wajen ma mallakin Ma”aikantan ke Kula Dashi Shekaru Biyar da suka gabata Babban Ma”aikatan Tana garin Abuja Inda Alhaji Aliyu Sulaiman ke da Alhakin Kula da Ragamar wajen Sboda Jajircewarsa da kuma Saninsa kan abunda ya shafi kasuwanci suna da kyakyawan Hulda da Sauran Kamfanoni Saboda nagartansu da yadda suke Tafiyar da kasuwancinsu kan gaskiya da kwarewarsu kan abunda suka karanta uwa uba ga kyautatama kanana da manyan Ma”aikata.
Acikin babban Office din Dayafi kowani Office girma acikin ma”aikatar koda duba da yanayin yadda aka kawata Office din da komai na More Rayuwa kamar dakin mace kama daga Kujerun karban baki karamin Fridge,Tibin bango,A.c,cafet,harda karamin Tiolet in Bukatar hakan tataso.
Zaune yake Daga chan Karshen Office din kan Kujeransa na Iko Kansa na Duke ne yana Faman Rubuce Rubuce kan Tarin Fayel din Dake gabansa Sanye yake Cikin American Suit Baki da Fari ya Daure Wuyansa da Tek Tik baki,Fuskarsa Tana Duke ne shiyasa bata Fito sosai ba sai dai Sumar kansa Da Masu aski suka gyarata Daga ganin yadda Sumar take zaka Fahimci ma maamallakin Gashin baya son Tara suma in baya Cireta Duk Sati to tabbas yana Sansareta Duk bayan kwana Goma.
Agogon Fatan na kamfani Rado Dake Daure a Tsitsiyan hannunsa na Hagu yakai Duba,Karamin Tsaki yaja batare daya Dago kansa ba ya jawo Wayar Telephone din Dake gabansa ya Dandana Wasu Lambobi ya saka a kunni Jim kadan naji Wata Murya Cikin Zati da Haiba yana Fadin.

“Lazifa ki fadama Sani yaje makarantar su wasim ya Daukesu zuwa Gida….!

Daga haka bai jira abunda za”a cemai ba ya Sauke wayar yana dan kara gyara Zamansa Cigaba yayi da aikin dake gabansa Cikin gaggawa kamar wanda yake cikin sauri ko Hanzari.
Yaji Sanda aka Bude Kofar Office din nashi aka shigo bai batama kansa Lokaci Wajen Dagowa ba sanin kowaye Shi kadai ne ke shigomai Office batare da Sakatariyarsa Ta Kirasa ta Sanar dashi ba shi kadai ne ke Shigomai kai Tsaye ba iya Office ba Harta a Rayuwarsa kai Tsayen yake Shigomai.
SAIFULLAHI KARAYE,Aboki kuma Amini Guda Daya daya ke dashi aduniya shi da Saifullahi ba yan”uwa bane asali ma basu taba sanin juna ba sai baya baya nan sun hadu ne a awata Jami”ar Nottngham lokacin Dayaje Hada Degree dinsa na Biyu kan kasuwanci kamar yadda shima Saifullahi yaje sai dai sabanin shi da Mahaifinsa ya Turasa shi Saifullahi Tallafi ne Daga gwannatin kano saboda Hazakarsa da Baiwarsa yasa Gwannati ta Dauke Nauyin karatunsa Tunda suka Hadu suka Fahimci sudin sun Fito Daga kasa Daya Nageria kuma sun Fahimci gabadayansu Abunda yakai su ne agabansu kuma Dukkansu din ba baya ba kwari ne Wajen Sanin Abunda suke karanta har suka gama Karatunsu kunne Doki suke wajen Kokari da Hazaka.
Kuma bayan sun dawo Gida Shi yayi Sanadiyar Dawo da Saifullahi kusa dashi alokacin da Mahaifinsa ya Damkamai amanar kula da wannan ma”aikatan aransa yaji ba wanda zai Tayasa ko Tallafa masa ya cika Burin Mahaifinsa sai Saifullahi lokacin Da ya kai sa gaban Maimartaba da Mahaifinsa sun yaba dashi tun kafin ma su ga Takardunsa,sun zo ma”aikatan sun Hada hannu da karfi Shi amatsayinshi na Shugaba Saifullahi mataimakinsa Cikin Shekaru Biyar sai gashi sun Zarce Tsara acikin Tsararrakinsu Ma”aikatansu ta samu Cigaba da Riba mai yawan da ba wanda ya Taba Tsammani hakan yasa Saifullahi ya Zama Dan gida kuma dan Dangi acikin Tarin iyalan Maimartaba Sarkin Kargi.
Yana jinsa ya zauna kan Kujeran Dake Fuskartansa ammh bai sa ya Dago Daga abunda yake yi ba Saifullahi ya kallesa sosai yana so ya Fahimci meke Damunsa Saifullahi Dogon Namiji ne mai Zati da haiba daka gansa kaga Bakanon Daya jiku da Wahala da Neman na kansa.
Gyara zamansa yayi kafin yayi gyaran Murya yana Fadin”Agogo baka ji Shigowata bane..?
Kansa na Duke kamar bazai tankasa ba sai chan yace”Naji..Sai yaya..?
Yafada Cikin Dakakkiyar Muryansa mai Cike da Zati da Haibarsa na koda Yaushe.
Saifullahi ya shafa dan gemunsa Daya Tara kamar na Rashin kunya yana Kokarin Danne Dariyansa yace”Yau ma kace Antyn taka ta bata maka Rai kenan kafin ka fito..!?ko aiki ta sakaka ne Dan kaninta..?
Yafada yana kokarin Danne Dariyan Dake neman kwacemai,Bai Dago ba kuma bai yi mgana ba illah Dakatawa da yayi da Rubutun da yake yi saman wani Fayel na dan Lokaci kafim ya cigaba Lokaci Daya yana Taune lebensa na kasa Daga gani mganar ta sosai inda kemai kaikayi.
Ganin yayi banza dashi bai ce komai ba yasa ya kara fadin”To ni dai Allah ya Huci Zuciyarka..Antynmu bata kyauta mana ba Haba don Allah sai ta Rika bata maka rai haka ake Rayuwa Fisabillahi..!?
Yafada yana yar dariya kadan Kamar bazai ce komai ba sai kuma ya Tattara Fayel din gabansa ya Rufe Lokaci Daya Ya Turesu gefe ya Dago da kansa da kyau yana kallon Saifullahi Dake kokarin Danne Dariyan Dake Cinsa..!
Cikin Danne giransa tare da Tattare naman goshinsa yace”Saifu an taba Sharara maka mari..?
Saifullahi ya waro ido yana Fadin”Mari kuma KARGI..?
Yafada yana bayyana Razanansa da mganar wanda aka Kira da Kargi na Kallah daidai Lokacin daya Mike Tsaye ingarman jikinsa na kallah Cikakken Bahaushe kuma Bazazzagi Domin ga Tsawon da Girman nan na asalin Zazzagawam da suka Fito Daga Taatson Kargi ta Fanni Uwa da uba.
Bakin Namiji ne mai cikar kamala kyakyawan ne sosai domin ya Dace da Tsararriyar Fuskarsa mai Dauke da Manyam Idanuwansa da matsakaicin Hancinsa ba bai cika Tsawo ba yana da cikar gashin Gira dana Ido sannan Yana da Manyan idanuwa masu Saka ma Duk wanda ya kalla dasu mazari masu Daukeda wani kyalli acikin su.
Fuskarsa Tana da dan Fadi kadan inda ta Dace da Bakinsa dan karami Tattausa kamar baya tauna abu dasu sai Zagayen Sajensa Daya Zagaye Bakinsa dashi wanda ke karamai Kwarjini da Haiba da kuma Zati Hade da bayyana Natsuwarsa akoda yaushe.
SULAIMAN ALIYU SULAIMAN KARGI wanda aka fi sani S.A KARGI Amtsaayin Managing Daractor na Kamfanin Mahaifin nasa Wato A.S.KARGI ENTERPRISES,shine D”a na Farko Kuma Namiji kwara Daya Tal Cikin Jerin ya”ya goma da Allah ya bama Alhaji Aliyu Sulaiman Kargi Kuma Shime maso soyuwa Wajen Mahaifiyarsa Hajiya Zabba”u kuma Shalele ne sanyin Idaniyan Duka Dangi ne kuma Saraki ne wajen Wanda yaci Sunansa Wato MAIMARTABA SULAIMAN SARKIN KARGI wanda shi ya Haifi Mahaifinsa Alhaji Aliyu Kargi Daya kasance da na Hudu ajerin ya”yan da Allah ya azurtama maimartaba dasu.
Kuma Uba yake ga Tilon ya”yansa WASIM da WAFIYYA da Sanyin Idaniyarsa Masoyiyarsa da har yau har gobe bai Daina Kukan Rashinta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button