MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Achan Kargi kuwa Fada ta Cika makil Ranar duka Ya”yan maimartaba Mazan dasu akayi sallar jumma”a a masallacin Fada bayan an idar aka Gudar da Daurin auran Sulaiman Aliyu Sulaiman kargi da Amaryansa Laila Isa hamza Kargi akan Sadaki mafi Daraja Tuni maroka da masu algaita da masu Shela suka Fara aikinsu Daga Cikin Gida jakadiya kuwa ita ta Shiga da Labarin Daurin auran Cikin Babban Gidan na Sarkin kargi Tuni Waje ya Kaure da Guda da Kirarin Amaran gidan Sarauta ana Daura auran aka sakama Laila akyabba kamar yadda al”adar Gidan ta gada.
Sauran abubuwan da suka biyo baya an shi ancha anyi Soyaye nama da kilishi da gasassun kaji shanaye akayi ta yankawa aka Gashesu abun sai wanda ya gani Ahmad ai bakinsa har kunne yau gashi acikin Fada yana ganin yadda Suke gudanar da Bikinsu bama wannan ba ba”a ware su ba suna Cikin Fadar Sarki Domin sunji Dadin wannan karan matuka da Baba yayi musu.
Daga Cikin Gida kuma Hajiya Zabba”u Burinta ya Cika suka Rumgume juna da Hajiya Salame suna ma juna Barka Haka ta Rike Laila tana dariya haka su Safiya dasu Raliya kowa kagani baki har Kunne yau Ya Saraki ya Cika Burin Hajiya sauran Shagulgulane suka Biyo baya na al’adun Gidan Sarauta sunyi Kilasa wanda Saraki yaso yaki ki Ashe Hajiyarsu ta Shirya komai Ranar an sha Kilasa Saifullahi ya Hau Doki Amaryama ta Fito ta Sauke Angonta saman Doki ta Fesamai Turare,Sulaiman bai ga Fuskarta ba Domin Hulan alkyabban ta Rufe mata Fuska sai hannunta kadai ake iya gani abunda kowa bai sani ba ba Laila bace saboda Sharadin Mganin da Salame ta kashe makudin kudi akansa bazasu hadu da Sulaiman ba sai agobe an kaita Gidansa kuma gashi An matsa sai anyi Kilasa shiyasa taso ta daujema abun ammh ba Hali ita da kawarta Hajiya Zaliha da suka Shirya komai aka saka Laila ta Cire kayan Jikinta Tabama kawarta da aka Duba yanayinsu kusan Daya ta kuma bata akkayyaba da Takalminta Daman Itana tasha kushi sai ba wanda ya gane ba Laila bace wacce suka Boyeta Chan Cikin wani Daki Dake Shashen Fulami dasu kadai ya”yan Sarki sukasan da Boyayyan Wajen.
Ahmad yasha kallo cijen yatsa yake da yana waya babba dasu inna sun sha Kallo yana Tare da sani Direba Daya zama kamar dan masarauta Har shi sai da Sulaiman yayimai Izini yahau Doki su sani an iya Shishhigi.
Mahaifiyar Saifullahi tazo Kargi Taya Hajiya Zabba”u Murna kuma Hakika Taji Dadi a bangaran na Musamman aka Sauketa ana mata Hidima.
Har Dare masarautar tana Cike da jama”a su Abba dasu baba Sa”idu suna ta shan Furan kamfanin Sulaiman suna sakamai albarka Domin kebaanttacen waje suka samu suka zauna gabadayansu suna Hira ta yan”uwa Baba yaso su koma aranar Sulaiman ya hana shima yana cikin su ko Daya basu ware shi ba Shiyasa yake ganin Kimar wannan babban Masarautar data maida Takala nasu kamar Duka Dayane.
Washegari kuma aka tashi da Shirin Tahowa Kaduna kawo Amarya karfe 10am na safe zasu tafi Tunda aranar kowa zai watse,Hajiya Zabba”u wannan karon bata ita ba,ita da Hajiya Salame Daga Kargi sai gidajensu Dukkansu Wakilai suka Tura ita Hajiya Zabba”u hajiya Falmatace kan gaba sai ya”yansu bangaran Amarya kuma akwai su Hajiya Uwani Hajiya Jamila da Hajiya Bilkisu Ta lagos Dayake tazo su da sauran ya”yan su da Hajiya Zaliha kawar Hajiya Salame da kawayen Laila zasu rakata Gidanta Dagachan Wasu bazasu dawo kargi ba irin su Hajiya karama da Tawagan ya”yansu Abuja zasu wuce hajiya zabba”u kuma sai gobe zasu dawo ita da Abba.
An kai Laila Shashen Fulani ta mata sallama bayan Kilishi tayi mata Daganan aka kaita manya Sassan Gidan tayi sallama dasu Daganan sai Fadar Maimartaba Sarki Sulaiman Kargi.
Kafin akaita Fada sai da Hajiya Zaliha tace abar Uwa da ya suyi sallama sai aka basu Daki guda suka Kule aciki.
Hajiya Salame ta Fito da Wani kullin mgani abakar Leda ta warware agaban Laila wacce take kallonta Cike da mamaki sai da ta gama Kwancewa kana ta Dago abunda ke Ciki wani Kwalli ne a karamin kalba da maciyinsa kadan acikin wata karamar kwalba Bakin abu ne aciki Dis baki sosai yana Daukan iso sai kuma wata karamar Kwalba mai Dauke da Turare Fari kar dashi kamar almiski shima Kadan acikin kwalban ta Zauna Gefen Laila Lokaci Daya tana Fadin”Laila Yaye wannan alkyabbab ki Dago ki kalleni Dakyau da duka Hankalin da Allah ya baki..!
Ba gaddama tayi yadda Uwar tace mata Kyakyawan Farar Fuskarta ta Bayyana Laila ba Doguwar mace bace Gajerace sannan tana da Jiki har asaman Fuskatra Kibaanta ta bayyana irin Jikin Yara yan Hutu da fatarsu ta samu jin Dadi sosai.
Hajiya Salame ta Rike hannunta Guda na Dama ta Damkamata mganin nan Guda Daya mai kama da kwalli Tana kallonta Cikin mamaki Laila tace”Mommah nameye wannan..?
Hajiya Salame tace”Kinga wannan abun da na baki..Kwalli ne kuma Sau Daya Tak zaki amfani dashi..!
Laila ta Cigaba da kallonta da karin Bayani yasa ta gyara Zama Tana Fadin”Eh sau daya ina Nufin in kika Sakashi Sau daya bazaki kara amfani Dashi ba Har Abada amfaninsa ya gama..Zaki Sakashi nebayan an kaiki Gidan Sulaiman an shigar Dake Shashenki..Zaki sakashi ne bayan Kin Tabbarar bazaki hadu da kowa ba sai shi wannan kwallin an yi shine Domin Sulaiman kadai in kika Sanyanshi kika Hada ido da wanda ba”ayi mganin Dominsa ba kin bata komai Laila.!
Laila ta kara kallon yar kwalbar Dake hannunta kafin tace”Duk saboda menene haka Mommah..!?
Kai ta Girgiza tana Fadin”Dadina Dake baki cin Riban zence ki bari zan miki bayanin komai mana..Yanzu rike wannan Turaran shima.!
Hada mata tayi awaje daya ta Karba tana kallo kafin tacigaba da Fadin”Wannan Turaran shima Sau Daya zai miki amfani Laila amfaninsa ki Gogosa a hannunki na Hagu ki kisan yadda zaki yau ba sai gobe ba kin Shafi Tafin Hannun Sulaiman na Hagu da wannan Turaran ina Fatan kin jini kuma kin gane sannan zaki aiwatar da abunda na Umarceki.!
Laila tace”Mommah naji zan yi komai kuma na gane Buh ammh baki gayamin Why zan yi wadanan abubuwan ba Ni da Burina ya gama Cika na Samu Saraki..!
Hajiya salame ta mata wani kallo kafin tace”Ke yarinyan ce baki san komai ba..Waya Fadamiki da kin Auri Sulaiman shikenan ai da Sauran aiki agabanmu..Sulaiman ya aureki ne Domin ba yadda zai yi ammh ke kanki kinsan ba sonkiyake yi ba har yau har gobe..Duk da Uban Wahalan da kikasha akansa!
Laaila tace”and so..ai na zama matarsa komai ya kare Mommah..!
Hajiya salame taja Tsaki kafin tace”Dubeni Dakyau komai bai kare ba..Shiyasa ban zauna ba Laila na Shiga na Fita na Kashe kudade saboda ki Samu yadda kike so agidan Sulaiman bana soWahalan da kika sha Kafin ki auresa kuma bayan kin auresa ki kara Ninka wannan Wahalan..Wannan mganin da na baki Har maradi naje nida Hajiya Zaliha makarin Mganin Mallakan Sulaiman ne da naba kudade masu kauri akayi Miki in kika yi yadda na Fadamiki Wlh Tallahi ko Zabba”u sai kin basa Unarnin ya Daga ido ya Dubeta zai Dubeta Laila zaki Juya Sulaiman Dashi da Duk wanda ke karkarshinsa Indai kikayi wannan yadda na Gayamiki..!
Laila ta Dan Washe baki Tana Fadin”Mommah da gaske..?hajiyarsa ta san da wannan..?
Hajiya Salame tace”Ina mai tabbarar miki..Yau ba sai gobe ba zaki Zama Taurarura a wajen Sulaiman bazai ji ba sai ke kuma bazai ga kowa ba sai ke..kuma kada ki sake ki Fadama wani wannan Labarin Hajiya Zabba”u batsan komai ba ke yata ce..Akwai Sirri Tsakanina Dake kamar yadda ita ma akwai sirri Tsakaninta da Danta bakomai take Fadamin ba.kada ki yadda ki Fadamawa kowa in kika Kuskura wani yaji mganar nan bayan nida ke da Hajiya Zaliha zaki Kara Lalata komai Laila..!
Laila ta Jimke mganin A hannunta Tana Fadin”Wlh bazan Fadama kowa Ba..Mommah kuma i promise u zan Yi yadda kikace ko domin na samu yadda nake so agidan ya Saraki na Rama kwatankwancin yadda Soyayyarsa ta bani Wahala..!
Hajiya Salame dataji Dadi ta rumgume yarta tana Fadin”Yauwa My Dota…!
Laila tayi Mirmishi kafin tace”Mommh matar sa fa..?harda ita zan mallaketa..!
Hajiya salame tace”Ita din banza..ita da banza Daya suke agidan..Kikama Mulki wanda ya ijeta ballatana ita..Ke fa kina da yarintarki har yanzu Laila dashi zaki nuna mata Banbamci Karamin kashi da wanda kashinsa ya Nuna Tun agida..!
Sannan sharadin Mganin na karshe shine awannan lokacin dakika gama amfani da duka sharadin na karshen shine kiyi yadda zakiyi Sulaiman ya kusanceki..Saboda Haduwar Maniyinki da maniyinsa shine makarin mgani na karshe da hakan ta Faru komai ya kamallah sulaiman da gidansa sai yadda kikayi dasu..!
Laila tayi wani Dariya kafin tace”Tanque Mommah..U are d good Mother ever in this World..!
Rumgumr juna suka sake yi kafin Hajiya zaliha ta Leko tace su fito su ake jira Mganin Hajiya Salame ta mayar mata aleda tabata a hannunta ta Jimke kana ta mikata wajen Hajiya Zaliha bayan ta maida Hular alkyabbanta ta fito ita wajen su Hajiya Uwani suka shiga da ita wajen Maimartaba.
Ya Dafa kanta yayi mata addu”a da Saka albarka tare da Nasiha kana aka Fito da ita saman Doki zuwa wajen Mota Saifullahi shi ya Dauki Amarya Saraki yabi sani tun dazu sun koma Kaduna shi da Baba da Ahmd basu da mtsalan Motoci bayan na gidam kowacce ai ta mallaki Mota yawanci da Direbobinsu suke tafe.
Kwambon Motoci ne sun fi ashirin aka Hada ajere zuwa kaduna Karfe 2pm da wani abu na Rana suna Kaduna Saifullahi Mahaifiyarsa tun Safe ta koma kargi bata samu raka Amarya Kaduna ba..
Koda suka iso sun samu Tarban Magajiya da Samira da suka gama komai na Taryansu Dama Maimartaba ya bama Laila kyautar Hadimai guda Biyu da su aka Taho.
Kai Tsaye ba”a sauke Laila ako”ina ba sai kayattacen gadonta Daya ji Shimfidun alfarma Dake Shashenta Bayan an Bude Barayin Ba wanda ya Damu da rashin ganin Sunaima sai Hajiya karama da Magajiya ta shaida mata btanan tana gidansu tun jiya.
Ita ta kira Saraki dake Kamfani tacemai bai kamata azo gida Sunaima batanan ba yace tana Hanya tun dazu ya Tura sani ya Daukota ita da yaran.
To bayan sun gama mganar ne ba Dadewa sai ga Suniman ta Dawo ita da yaran Wlh acikin wajen nan banda Iyayen irin su Hajiya Uwani ba wanda ya amsa mata sallama ballatana gaisuwanta sai Sadiya da Sadiqa da suka Nufi yaran suka Dauke su Raliya kamar sun ga kashi Sauran suna Sama Shashen Amarya sauran kuma suna kasa suna cin abinci yaran kuma sun kannen Ubansu suka Nane musu Sunaima Tana gama gaisawa dasu Hajiya karama ta Shige Dakinta Tana Boye kwallarta Lokaci Daya Tarin Nasihun inna suna Dawo mata Daki Daki.