MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Magajiya ya kallah da kanta ke kasa yace”Ki Tattaro kanku gabadaya magajiya ina son ganin kowa da kowa afalon nan..!
Magajiya kanta na kasa tace”Ranka ya Dade kowa fa kace..?harda Megadi da Sani Dake Haraba yana Jiran Fitowarka..!?
Laila data fara gajiya da Kankabar Dattijuwan tace”Baki jin Hausa ne..?inace ce miki yayi kowa da kowa..Malama ki tashi ba Megadi ba kowa Dake gidanan yake son gani yanzu agabansa kuma ki kama kanki kafin na Fara Dake bana son mijina na mgana Kina neman ki Rika ja da mganarsa Ki kiyaye..!
Magajiya ta Kara kantar dakai Tana Fadin”Allah ya Huci Ranki..Allah ya baki Hakuri..!
Kanta ta Tabe gefe kafin tace”Ki yi maza ki isar da sakon..bamu da Lokaci Zamu koma Ciki ne ko Habibina..!
Mirmishi ya sakarmata yana Fadin”Yadda kikace haka za”ayi Lailata..!
In yace Laailata Dadi take jin yana Neman kasheta yau ita kam Burinta ya gama Cika ta samu Sulaiman a Hannunta Dari Bisa Dari godiya ga Mommah itace Duniyarta..
Magajiya Jiki na rawa ta je ta Fadama su Samira daganan ta fita waje ta Sanar ma Sani da Megadi data samesu suna shan Fira sani Tun dazu yazo yana Jiran Sulaiman har wayarsa ya Kira bai Daga ba anan ne megadi ke Fadamai yau ko masallaci bai je ba. Dariya yake aransa yana Fadin yallabai ana ta amarci nehaka.
Sai ga mgajiya tace yallabai na son ganinsiu afalo mamaki ya kamasu gashi bata Tsaya ba ta koma abunta ta barsu Tsaye suna kallon juna.
Tana Dawowa ta Zube nan gabansu kusa dasu Samira da suka Bayyana Tun Dazu Shuru shuru ba Megadi ba Sani yasa Laila ta Daga ido Tana kallon Magajiya kafin tace”Ina sauran..?
Magajiya kanta na kasa tace”Megadi da Sani Direba ne na sanar musu suna zuwa.!
Bata samun Zarafin mgana ba suka Shigo Falon da Sallama mamaki ya Cikasu ganun Yallabai zaune kugu da kugu da mace abunda basu Taba gani ba Hannunta Cikin nasa kuma yana Binnta da kallo Cikin Narkankun Idanuwansa ai da gudu suka Sanda kansu kasa suka Zube Daga Chan gefe suna kwasan gaisuwa Wlh sulaiman baima san sunayi ba kallon Laila kawai yake kamar shine aikinsa ne itace ta amsa tana wani cin mgani Tsigau da ita ko mayafi babu abunda ba Tsari Sam
Sai da tagama kare musu kallo kafin ta juya wajensa Tana Fadin”Habibina Banga yayar matarka ba..!?
Cikin Idanuwanta yace”SUNAIMA…!
sai da gabanta ya Fadi ta Mele baki kafin Tace”Oho ban sunanta ba..Komail watake da sunan ban damu ba..Ai itama ya kamata ka gabatar dani awajenta ko..!?
Kai ya gyada yana Fadin”Hakane..magajiya shiga wajen Sunaima kice tazo ina Kiranta..!
Ba Musu magajiya ta Mike ta wuce Dakin Sunaima.
Kwankwasa tayi da Farko taji Shuru sai ta kara kwankwasawa sai ga Sunaima ta bayyana ta Bude Kofar ganin magajiya yasa ta Fara gaisheta Tana Fadin”Hala kin jini shuru. ko motsin su Wasim yau baki ji ba..!
Kan magajiya na kasa ta Rankwafa Tana Fadin”A”a Hajiya..ai tunda najiki Shuru keda su nasan Lafiya..Daman Yallabai ne yace yana son ganinki yanzu afalo..!
Cikin mamaki tace”Yallabai ni kuma..!
Kai ta gyada mata Sunaima tayi jim kafin tace kice gani nan zuwa Daga haka magajiya ta Juya ita kuma ta Koma Cikin Dakin Wasim da Wafiyya sun yi baza baza da kayan wasansu suna Wasa aranta tace Kila su Wasim yake son gani bani ba..
Karamim Hijabinta ta saka kan Doguwar Rigar atamfat Dake Jikinta ganin Zata Fita yasa Wasim da Wafiyya sukace ai basu san wannan ba Dole ta Dauki Wafiya ta Rike ganin Wasim suka Fito Daga Dakin suka Nufi Falon.
Har ga Allah bata kawo ganin Laila ba Ita kanta Tsaye ta Shigo Falon hankalinta na wajen gyarama Wafiya Dankunnenta Daya sarke Cikin Gashin kanta ta shigo Falon Dagowan da Zatayi tayi mummanan ganin da bata tba yi ba Laila ce ta Kwantar da kanta saman kafadan Sulaiman Tana Rike dashi shikuma sai Binta da wani mayen kallo yake gabanta sai da ya amsa Tuni taji akaron Farko Zuciyarta ta Harba Tabbas abunda Ta gani yayi kama da Taga wani abun da bai mata Daidai ba ballatana Tsari.
Ido Cikin Ido suke kallon Juna ita da Laila basai an gabatar musu da juna ba Dukkansu sun Shaida juna Sunaima Cak ta Tsaya ta kasa gaba ta kasa baya yaran ne da suka ga Babansu suka hau Kiran sunansa Wasim ya Kwace hannunsa daga hannunta ya Nufesa yana Fadin
“Daddy…”
Wandaya jawo hankalinsa ya Dago yana kallonsu itakuma ta Duka Zata Sauke Wafiyya Data Fara Zillo Tana Kiran Daddy itama Tana Dagowa Kyakyawan Idanuwansa suka Shige Cikin Nasa sai yaji wani Sanyi ya Shigesa kamar yaga warakansa Kallonta yake kuri kamar ya warke makamta ita sai abun yamata wani iri kanta ta kauda Cikin Takaichi Tana Tunanin da Saninsayake komai ammh ai bai kamata ai ba kansa Farau aure ba yaso gaban yan aikin da Suke Girmamsa yana Biyema Shirmen wata Dikekiyar mata wai da sunan su Amare.
Kanta ta kauda bata kallonsu tana Amsa gaisuwan sani da Megadi taji Sanda Laila Tace”Lala..Habibina Sauke su..Kalli fa zasu bata maka kaya..!
Tadai kallo wajen nan Tana so taji amsan da zai bata sai dai ga mamakinta da sauri kamar Daman Jiran Umarninta yake ya Saukesu Dukkansu har Wafiyya na Turkudewa ta Fadi sai ta saka Kuka Wasim ya Tsaya Sororo yana kallon Uban nasu shima kallomsu yake cikin wani yanayin daya kasa gane ko na Miye,gabadaya ba wanda bai ji wani iri ba wajen hatta da Samira sai da abun ya bata mamaki akwai abunda Sulaiman ke so da kauna bayan Iyayensa ai yayansa ne.
Sunaima ta Saki baki da Hanci tana kallon Ikon Allah,Wasim bai Dandara ba ya kara Komawa Jikin Uban Tsawa Laila ta Dakamai Ta saka hannu ta Sauko dashi Daga jikik Uban ta Dangwarar dashi a kasa Tana Fadin”Matsa chan dallah…ku zauna a kasa yadda kowa ya zauna..!
Tafada tana Budema Wasin ido da Yayi kwal kwal zai yi kuka Laila ta kara Hade rai daman ita Duk Duniya tafi Tsanan ya”yan Sulaiman Fiye da komai Domin Sanadin Uwarsu Sulaiman ya Wulakantata Shiyasa Jin masu mata nasihan ta Rike ya”yansa kamar nata take ji Mommah ta Fadamata Sulaiman take so kuma shi ta aura ba ya”yansa ba tasan yadda Zatayi ta yakicesu daga Jikinsa ta yadda itama Yayar matar tasa bata da wani madafa.
Sunaima Gabadaya Jikinta sai ya Fara rawa zata Dauki komai banda ta mata ya”yan Sunaira,Cikin Fushi ta taka zuwa Inda su Wasin suke taso ta Wankama Laila mari ne sai kuma ta Fasa ai baitace abun mari ba ga na mari nan Sulaiman yana Zaune mace tana Sarrafasa
Takaichin haka yasa ta Duka kawai ta Dauki Wafiyya Dake kuka ta Rumgume ta Riko hannun Wasim ta Mikar dashi Tana Fadin”Taho muje my Boy..Kaji.!
Tafada tana Rikosa yako Lafe ajikinta Sulaiman ta kallah da idanuwanta da Laila kafin ta kada kai ta wuce Laila ta Kalleta Tana Fadin”Ina zaki kuma..?
Baki Tsaya mun gabatar da juna ba..!
Sunaima ta Tsaya kafin ta Juyo Tana kallonta Cikin Dakewa tace”Gabatar dakai..?ai bana Bukatar ki gabatar min da kanki wanda kikayi yanzu ya isa nasan koke wacece..!
Laila tayi Mirmishi ta Mike tana Fadin”Habibina bari mu gaisa da Yar”uwata..!
Kamar gaula haka ya Daga mata kai Sunaima ita mamaki ma ya gama Cikata Laila sai da ta kariso gabanta Cikin wani Taku tana kallon Sunaima Daga sama har kasa kafin ta Mika mata Hannu tana Fadin”Hi am Laila..and u..!
Sunaima taki karban Hannun nata kafin tace”Sunana Sunaima Abdu Datti nasan kinsani neman karin Bayani kike yi..
Laila tace”Sosai nasanki mana Kece yayar matarsa da aka Tusa masa ke..ai na ganeki sosai..!
Sunaima batace komai ba,ai cin Riban abun ka jira Lokaci kawai yasa ta Juya Zata wuce Laila ta Juya tana kallon Sulaiman Lokaci Daya tana Fadin”Habibi zata tafi fa..!
Sai alokacin yayi mgana”Ki Tsaya mana SUNAIMA..!
Yadda ya Kira sunan nata yasa mamaki ya kamata Domin bata taba jin ya Kira sunanta ba sai yau yasa ta Juyo Tana kallonsa Mganar Dayaso ya Fadamata sai yaji ya kasa yasa da Sauri yace”Plz ki Tsaya..!
Aran Laila tace kan Uba Harda Rokonta ita da akace Ita ce kadai Zata bama Sulaiman Umarni yabi ammh Taga alamun wannan Tsohuwar kashin Zata bata mtsala fa
Sunaima taso tayi wucewarta ne sai kuma ta Sauya Tunani ta koma ta Zauna Tana Rumgume Wafiyya akirjinta Lokaci Daya ta na Dora Wasin akan Cinyarta Gabadayansu suka Lafe ajikinta gwanin ban Tsausayi Tana jin yadda Zuciyarsu ke Bugawa haka nata ke Bugawa.
Ta fara Shiga Rudi Daga Lokacin da Sulaiman ya gabatar da kowa sannan Laila tace kowa ya Fadi sunansa da aikinsa acikin gidan tana so ta sani.
Megadi ya fara fadin nashi ta kallesa Daga sama Har kasa kafin tace”Aikin gadi shine aikinka..Kada ka yarda na kama ka da Rashin zama a inda ya Dace Bakin get nan ne Muhallinka kana jina..!
Cikim Rawan jiki yace”Naji Hajiya Insha Allahu bazaki sameni da wani laifi ba..!
Kai ta kada kafin Sani ya gyara Zama Muryansa na rawa yace”Sunana Sani ni Direban yallabai ne..Ina kaisa Wajen aiki ina dawo dashi sannan ina kai su wasim makaranta na Daukosu..!
Laila ta kallesa kai tsaye tace”Karfe nawa kake zuwa aiki da Safe..!?
Sani yace”Ranakun makaranta yara..7:30am muke fita ni da oga mu biya makaranta mu ijiyesu kana mu wuce wajen aiki ranakun Mako kamar yau kuma mukam Fita 10am na Safe..!
Kai Tsaye Laila tace”Daga yau kada ka kara zuwa gidanan sai an kiraka..!
Cikin mamaki ya Dago yana kallomta ganin Sulaiman bai ce komai ba Juyawa tayi tana kallon Sulaiman kafin tace”Kana gani Ma”aikacin ka Dake karkashinka nayi mgana zai yi gaddama dani..Laifinka ne Habibi da baka Fada musu komai nace Dole ayisa yadda nace din ba..!
Da Sauri yace”Yi hakuri Lailata..Sani ka bata Hakuri..Dukkanku ban Dauke ma kowa ba ko bana gidanan wani ya Sabama mganarta Abakin aikinsa..Zata yanke Hukunci kamar yadda zan yake acikin Gidan nan..!
Sunaima ta Fara Fahimtar abubuwa basa Tafiya daidai
Laila ta saki kayattacen Mirmishi tace”Nagode Habibina.!
Sani dai bai ce komai ba ya Duka yana Bada Hakuri hannu ta Dagamai kafin Tace”Ku fice ku bani Wuri..kai bani Key din Motar dake hannunka yau Habibina bazai fita ba in Lokacin Fitan ya kama zan nemeka..!
Yallabai bai taba karban Key Daga hannunsa ba Yasa Jikinsa a sanyaye yaje gabanta ya ijiye kafin ya Mike shida Megadi suka Fice Jikinsu Duk yayi Sanyi key din ta Dauka Tana Fadin”Habibina kula da Fitanka ya koma Hannuna ina Fatan ba Damuwa..!
Mirmishi yayi mata kafin yace”Duk yadda kika yanke daidai ne dani da Duka Abunda na mallaka Duk Bayinki ne..!
Sunaima batasan sadda tace”Azubillahi..!
Azuciyarta ta fada batasan ya Bayyana ba Laila ta Dago Tana kallomta Itama kallonta Take ido na Cikin ido Laila taso tace wani abu ammh Sai taji shakkar kallon da Sunaima take mata yasa ta maida kanta kan mgajiya dake gabatar da kanta.
Sai da ta gama kana ta kalleta Tana Fadin”Daga yau keda Marliya zaku Dinga Kula da bangaran Kitchen..Samira da mariya zasu rika kula da bangaran gyaran Falo da Sama Chan Shashenmu..Bana son Shisshigi bana son saka ido ina son arika jin mganata bana son gaddama in na kafa Doka abita azauna Lafiya in na kama Mutum yana Munafunta ta Wlh zan Dauki mumman mataki akan mutum!
Gabadayansu suka amsa mata kafin Tacigaba da Fadin”Sannan ku nuna ma su marliya tsarin aikin Tunda su baki ne..sannan bazasu haura mana Sama ba in Habibina yana nan in bani na Kira Mutum ba..Sannan baza”a Rika Dafa komai agidanan ba sai da Umarnina sannan Za”a Rufe Kitchen sai sanda na bada Umarnin abude adafa wani abun..haka tsarina yake komai ake so sai amtabayeni kuna jin Mijina ya bani Dukkan Dama ko ba haka ba Habibina..?
Kai ya gyada mata yana Fadin”Duk yadda kikace daidai ne..!
Sunaima ta Fara Fita Daga Tunaninta sam ta Lula wani Tunanin batama san ta sallami su magajiya ba,sai da Taji Mganar Laila asama tana Dago kanta Taga taja Sulaiman sun Haura sama ammh yanayi yana Waigen sunaima Data Bisa da kallo kamar wata gaula.
Har suka bace ganinta ta kasa Daina gasgasta abun Da take gani kuma take ji Tunaninta ma ya Tsaya waje Daya Cak ita dai bazatace tayima Sulaiman sani soaai ba sai dai tasan shi tasan yadda yake son ya”yansa da kuma yadda yake Daraja ma”aikatansa Jajirtattace da bai kamata yau kawai ta gansa haka ba To meke Shirin Faruwa hakane..?
Koma tace ya faru ko alokacin da Sunaira keda rai ita shaidace Sulaiman yana matukar sonta ammh bai bata Daman Sarrafa Rayuwarsa haka ba tasani tama da labarin laila awajen sunaira tun abaya Sulaiman bai taba sonta ba asalima Ita ake so basa ya nuna bayaso ba tana kuma da kyakyawan yakinin Hajiyarsu ne ta Hada wannan auran bai kamata taga komai ya Sauya Daga dare zuwa Safe ba..
Kwakwalwarta na neman Rikitata yasa ta Kwaahi su Wasim suka koma Daki ta kwantar dasu duk sunyi wani iri sai yaran suka bata Tsausayi,gefensu ta zauna tayi Tagumi Tunanin Duniyan nan tayi shi ta rasa gane bakin Zaren tana so ta kama wani mgana sai dai bataso Zarginta ya Tabbata.
Ranar haka ta wuni adaki ita da yaran Daga Bicuit sai tea sukayi ta sha Sai kuma tayi ta jan hankalinsu da Wasa suka saki jikinsu suna ta wasansu Ita kanta bata Cikin natsuwarsa bata taba Kallon Sulaiman da Dubam Mijinta ba ita har Gobe kallom Mijin kanwarta take ma ita kuma Tana Zaman kula da ya”yan yar”uwanta ammh wannan Abunda tagani ya sakar mata da Duka gabban Jikinta
Har garin Allah ya waye bata kara Fitowa da yaran ko Falo ba da Wuri ta Shirya yaran itama ta Shirya kanta Tare zasu fita yau aikin Safe gareta sai dai ko da suka Fito ba Sani Direba kuma ba Luch box din su Wafiyya ita sam ta manta mganar Jiya ta Kira Magajiya tana tambayanta Magajiya kanta na kasa tace”Hajiya kin manta Jiya Hajiya ta ce ba”a sake Dafa komai ba sai da izininta tama karbi key din Kitchen din jiya..Da safe na Shiga wajenta na mata Tunin saboda su Wasim tace na Fita na bata Wuri..!
Magajiya ta Fada Kanta na kasa Sunaima tace”Naji magajiya banzata ta saka yaran Cikin Dokarta ba..Ina shi Abbansu Wasim din kin gayamai..?!
Magajiya ta Dago tana kallon Sunaima Abunda ba Halinta bane tana da kankantar da kanta tace”Agaban sa ne hajiya kuma bai ce komai ba..!
Sunaima ta ji mamaki ya kara kamata ta Dafe haba Tana Fadin”Oh ni Sunaina wai meke Faruwa agidan nan ne..?taya yara zasu tafi makaranta ba abinci Don ma ina da Sauran kayan Tea a daki da sauran Bicuit shi suka karya daSafe..!
Magajiya ta kalleta kafin ta Sadda kanta batace komai ba sai dai tana so ta maganta ai ita ba yarinya bace tasani ta kuma gane Laila bata shigo Gidan nan ba sai ta samu Mallaka da zata iya dafadama Sunaima Sulaiman bazai iya komai ba Domin Shirin mallaka na Dawainiya dashi baya ji kuma baya gani
Aranar sunaima ta kaisu makaranta adaidaita lunch Box dinsu kuwa Tea ta Hada musu a Goransu ta siya musu manyan manyan Bisscuit ta saka musu,Tsausayin yaran ya kamata tarasa yadda zatayi da wannan Sabon Al”amarin ita bata da nata Shashen ballatana tace tana da Kitchen din kanta da Zata siyo ko Indomie da kwai ne ta Dinga ta Dafa musu ammh dai bari ta dawo zata samu Sulaiman din ta Fadamai Tana Tunanin kila baisan Halin da ake Ciki bane.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button