MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Kofar Kitchen din ta Tsaya tana Fadin”inna baki tasheni ba..Da na makara zuwa wajen aiki..!
Inna Tace”Na kyaleki ne ki yi barcin ki Samu natsuwa..Saboda Daga ganin yanayinki baki samu Barci Jiya ba..!
Sunaima na Zura Hijabinta Tace”Inna Zan barma Ahmed kudi ki basa inya dawo makaranta yaje ya Dauko su Wasim in lokacin tashin su yayi..Da yammah in na tashi aiki zanbiyo na Daukesu..!
Inna ta kada kai Tana Fadin”Shikenan..Ki bar kudin ki akwai a Hannuna in ya Dawo zan basa ya Dauko su..!
Sunaima bata Saurari Inna ba ta Bude Jakarta ta Dauko Kudi Dayawa ta Kirga ta Mikama Inna tana Fadin”Ki basa ya siyamin Katan din Bobo da Caprison sai Katan din Biscuit mai Madara sai madaran gari duka ya Siyomin in ma da Ciko in nazo Tafiya Dasu zan cika Inna..!.
Inna ta saka Hannu ta karba Tana Fadin”To bari ya shigo din zan basa..!
Daganan sukayi Sallama Sunaima ta Fice Tana Sauri Inna ta Bita da Fatan Nasara Tsausayi Sunaimar ke bata Tunda ta Fara aikin nan kwandala bata ci Daga albashinta ba da an Turo mata Zata Turo ma Babanta Tun Farkon Fara aikinta da Baban ya Nuna A”a kuka ta sakamai tace indai Bazasuyi amfani dashi ba itama bataso da haka suka Hakura Wlh Tun Tana gabansu naira bataci sai dai in Zata wajen aikin Inna ta Rika bata na Mota,yanzu kuma Tana gidam Mijinta bata Sauya Zani ba Duk watan Duniya ne yadda Sunaima Take da Raunin Bangarori Sunaira bata dashi Sabida ita tana kananun Shekaru ta Hadu da Sulaiman ya Nuna mata kauna Sunaima fa..?
Batasan komai a wwnnan Rayuwar ba sai Karatunta da aikinta Shiyasa take mata Fatan Daidatuwar komai yadda itama ZAta Fara Dandanan Zakin Rayuwa da kuma jin Dadin Aure.
Sunaima Tana komawa Wanka kawai Tayi ta saka Uniform dinta Tayi Sallar Azahar Abincin ma da Magajiya ta Shigo mata dashi Daki bataci ba nan ta barsa ta Fice banda Su magajiya ba masu Giftawa afalon Laila da Mijin nata suna Sama yau ko Kasa basu Hauro ba Hatta kayan Breakfast din Haura musu dashi Sama Samira da Mariya sukayi.
Shida Daidai ta baro wajen aiki zuwa Gidansu Goslow ya Riketa sai ana mganriba ta shigo Gidan Sai ta Tsaya Tayi Sallah kan Lokacin Ahmad da Wasim da Baba sun dawo daga masallaci Waffiya an samu Filin Tsakar Gida sai wasanta take sai da mangriba ta kawo Jiki Inna ta kamata ta Goya bayan ta mata wanka.
Saboda Dare da kuma Kayan Siyayyan da Ahmad yayi mata yasa Baba yace Ahmad din ya Rakata gida Tunda ga yara Taji Dadin haka bata bar Gidan ba sai da Taci Tuwon Dawan da Inna Tayi da Miyar karkashi kana suka Tafi Zuwa Lokacin Yaran Duk sunyi Barci sai dai suka sabasu
Tashan Adaidaita sukayi zuwa gidan Ahmad ya Daukan mata Wasim da Ledojin ita kuma ta Dauki Wafiya suna Buga get din megadi ya Leko yana ganinta ya Bude mata yana mata Maraba Ta amsa mai Cikin Sakewa.
Har Cikin Falon Ahmad ya Shiga Har Dakin Sunaima ya kwantar mata da Wasim bayan ya Ijiye mata Sakon ba zauna ba saboda Baba yace kada ya Zauna Dare yayimai Suka Fito Falon Sunaimar tana mai mgana bayan itama ta Sauke Wafiyya Daga hannunta.
Da Samira suka ci karo Bayanta Marliya ne Hannayensu Dauke da Kololi zasu haura sama Kallon kallo sukayi musu Basai sun yi mgana ba daga ganin Ahmad ai kaninta ne gama kama nan na jini,Ita kallo Daya Tayi musu ta Kauda kai Ahmad kuwa ya Dameta sai cewa yake ina Sulaiman yake ta gaji ta kallesa tace”Bai dawo ba yana wajen aiki..Ka wuce kada Dare yayi maka..!
Ahmad yana yar Dariya yace”Kai Antymu haka zuwan Amarya yasa aka Sauya Falon nan gaskiya yayi kyau..Au ina ma Anty tamu take Amaryan gaskiya da bikin nan Antymu an sha Shagali Cha..!
Bata bari ya karisa ba ta Mikamai Dubu Daya Tana Fadin”In ka gama Zuban naka sai da Safe..!
Ta juya abunta bayan ya karbi kudin da Dariya ya Bita kasa kasa yana Fadin”Ko Antynmu ta fara Kishi ne..!
Tana jinsa Karamin Tsaki taja Wani Lokacin Ahmad fa kamar Gidan Haya yake Saboda matsalarsa.
Dakinta ta koma ta Fada Tiolet tayi wanka ta Dauro alwala bata tada Sallar ba sai da ta Cire ma Wasim da Wafiyya kaya ta saka musu na Barci kana ta kabarta Sallah tayi Shafa”i da wuturi kana Tayi Shirin kwanciya.
Gabadaya ta kasa barci mganganun Inna suna mata amsa kuwwa acikin kunni kamar yadda tace ta zauna ta fara Nazarin Rayuwatta Daga Farko Haka din ta Fara ta yarda da mganar Inna ta kuma amimce Mijin kanwarta ai kaddarantace Zatayi yadda Inna tace Saboda Yaran nan su Take Tsausayi ammh ba Domin sulaiman nada wani Matsayi a wajenta ba Ita bata taba kawo ma kanta Rayuwar aure nan kusa ba tafi jin Dadin aikinta Fiye da komai.
Barci barawo ne ya Saceta aranar Washegari bata Sauya zani ba ita ta kaisu makaranta Magajiya ta Fadamata Sani ya Dawo Laila tace ya Tafi sai nan da Wata Daya in Sun gama Cin Amarcinsu sai ya Dawo bata Damu ba Tunda yanzu tana da abun basu Murna sukeyi ma da Biscuit din da Bobo din sai aranar da sukaje Bakin makaranta akwai Shago ta Siya musu kwai Dafaffe.
Ranar ma Ahmad ya Daukosu ya kai ma Inna nan suka Wuni sai da tatashi aiki ta Biya ta Daukosu kwana Uku ana Haka Baba na Lura dasu bai Taba mgana ba Saboda ya Zargi koma Miye ke Faruwa da yardan Inna wannan karom Domin Haka kurum bakinta bazai iya Shuru ba akwai wani abu a kasa bai ce komai ba sai arana ta Hudu da Sunaima tazo Daukansu Goslow ya riketa sai mangariba ta Shigo ya Kalleta yace”Sunaima ni kam Yaran nan ina Direban Sulaiman Dake kaisu makaranta ya Daukosu zuwa Gida ne..?wannan Wahalan tayi yawa kina mace Bai kamata ba kullum baki komawa Gida sai Dare..Wannan karon innan taki naga ta Daure ma wannan Zuwan da kawon naki Gindi ne meke Faruwa ne..!?
Kafin ma Sunaima tace wani abu Inna Tayi Zaraf tace”Direban baya nan ne yaje garinsu Shi kuma Sulaiman din Baya Dawowa gida akan Lokaci Shiyasa..!
Kallonta yayi kafin yace”Gidan ba kowa ne da Dole sai an rika kawo yaran nan Rukayyah..?in har Hakane Ahmad din ya rika kaisu gidansu..Ni Abu Dayane bana so wannan kai da kawon Datake da Daddare Kada ki manta macece bai kamata ba sam..!
Inna tace”Hakane kayi hakuri..!
Kai ya Kada Kafin yace'”in hakane din ne sai dai su rika kwana anan Har Direban nasu yadawo..Ita kuma in tatashi aiki ta Rika wuceqa gidan auranta yafi Mutumci yanzu Zamanin nan ya Lalace wani bai da gadonka ammh yana da Gadon yada karya akanka..Kai Ahmad kaje ka Rakata zuwa Gida..!
Yafada yana kallon Ahmad Dake Alwalan sallar mangariba Dayake Baban ya Idar da nashi.
Ahmad yace”To baba..Nifa ko Dadin Adaidata ya kaini..!
Ba wanda yabi ta kansa har ita Sunaimar da mganganun baba suka kashe mata Jiki sai da Baba ya Fice kana Sunaima ta kalli Kafin Tayi mgana Inna tace”kada ki Damu..Bakomai Daukesu ku tafi..Kedai in kin gama Nazarin mganata kin kuma amince Zamu samu mafita..!
Daga haka bata kara cewa komai ba Ahmad bai tafi masallaci ba ya Tsaya ya Rakata Wafiyyace tayi barci Wasim idonsa Biyu suna zuwa Gidan bai ma Shiga ba Daga bakin get sukayi sallama mai adaidaitan ya Juya da shi

Tana shiga Gidan suka ci karo daga magajiya Nan take fadamata Saifullahi abokin Sulaiman yazo Nemanta sau Biyu yau bata nan Sunaima mamaki ya kamata jin wai yazo nemamta sai dai bata bama abun Muhimmanci ba ta tattara ya”yanta zuwa Cikin Dakinta sai dai yaki barin Ranta me yasa Saifullahi zai zo nemanta Mutumin da ba wata Mu”amalan da ta taba Shiga Tsakaninsu,Sai dai kila Saboda Sulaiman ne ko shima yasan Dalilin Chanzawar Sulaiman din ne Abun yaki barin Ranta har Washegari Jumma”a ta shirya da wuri misalin 11,am na safe Ita takai su wasim makaranta Sulaiman Tundaga Ranar dataje sukayi mgana bata kara ganinsa ba Daga ita har Lailan batasani ba ko suna Fitowa kila bata nan alokacin Kowa agidan Umarnin Laila yake bi In tayi mgana Jiki na Rawa suke aiwatar da Bukatunta.
Sunaima har mamaki take yadda taji Shuru ko Dagachan kargi ko Daga Abuja bata karajin Duriyar kowa ba Batasan Daman ba wanda zai Bibiyesu ba sai Hajiya Salame da Hajiya Zabba”u.
Hajiya Salame na Waya da yarta tana kuma sane da komai Hajiya Zabba”u ce batasan meke Faruwa ba Saboda Tayi ta Kiran Sulaiman ba”a Daga ba sai tace kila suna Amarci ne tana jin Dadin komai ya gama Daidaita Shiyasa bata kara nemansa ba Hankalinta ya kwanta Sulaiman da Laila sun zama ma”aurata Haka ta Kira Hajiya Salame tana Murna ta Biye mata sai da suka gama Waya ta shiga mata Dariya.
Sunaima Tana Fita Gida ta Hau adaidaita Direct Kamfanin su Sulaiman tace yakaita A.S.KARGI Enterprises.
Ba bata Lokaci kuwa aka kaita Daga bakin get aka Sauketa tana Sanye da Uniform dinta da Dogon Hijabinta Bule har kasa sai bakin Takalmi Sawu Ciki Dake kafarta Da Jakarta Dake Sagale agefenta,tasan ba wanda yasanta Kuma ta kosa taji abunda yasa Saifullahi ke nemanta bata da Lambarsa ballatana ta Kirasa To ko Lambar Uban gayyar bata dashi.
Takawa tayi zuwa bakin get din akwai Security Su tayi ma mgana da suka Tambayeta wajen wa tazo tace Office din Saifullahi za”a kaita Wani Daga Cikin Security din ne ya mata Jagora Har Office din Saifullahi Dake hawa na Biyu yayinda na Sulaiman ke hawa na uku.
Security din ya shiga Ya fara gayama Saifullahi Dake Tsakar aiki yayi bakuwa yaji mamaki sosai bai kuma Taba Zaton Sunaima bace sai da ta Shigo da Sallama ya Dago yana kallonta Cikin mamaki ya Mike yana Fadin”Ah..Antymu..Kece..!?
Bata saki Fuska ba illah Tsayawa datayi tana kallonsu kafin tace”in ma gatse ne to ba kayi kuskure ba sunan kenan..!
Mirmishi yayi kafin yace”Bama gatse bane…plz Hv a sit..!
Ya fada yana nuna mata Wajen zama,Zama tayi Shima ya koma ya Zauna yana kallonta kafin yace”Me za”a kawo miki..?
Sunaima tace”Bana bukatar komai..Jiya magajiya ta Fadamin sau Biyy kana zuwa Nemana bana nan..Shiyasa yau kafin na wuce wajen aiki nace bari na Biyo ta wajenka..!
Saifullahi yace”Tabbas naje gidanan yafi Sau hudu bana samun ganinki..Kina Wajen aiki..!
Sunaima ta gyadamai kai Shi Kuma ya Cigaba da Fadin”Sunaima ba saboda komai nake son na ganki ba sai Domin ki Taimaka ki Fadamin abunda kikasani game da Gidanan don Allah meke Faruwa..?sulaiman ya daina zuwa aiki baya Daukan wayata in naje kuma sai ace Laila tace bazai ganni ba na Shiga Rudi akwai tarin ayyuka sosai da suke Bukatar sulaiman ya gansu akwai inda muke Bukatar saka Hannunsa shima Duk ba Dama na kasa ganewa shine nace ko ke kila Kinsan abunda ke Faruwa..!?
Sunaima ta dan Girgiza kai kafin tace”Meyasa sai ni ce zan san abunda ke Faruwa..?
Yana kallon Cikin Idanuwanta yace”Saboda ke Matarsa ce..!
Sunaima tace”Eh kuma Mijin kanwata..ba..!
Saifullahi ya tareta da Fadin”Kuma Shine KADDARANKI BA..!
Sunaima ta kallesa kafin tace”Meyasa kace haka..,?
Saifullahi yace”Kema kin sani..Auranki da Sulaiman Kaddara ce Daga Allah Mutum bai isa ya iya Hadashi ba..!
Sunaima batace komai ba ganin suna kamanceceniya da mganar Inna yasa ta Kalli Saifullahi kafin tace”Abban su Wasim fa Sihiri ke Damunsa..Laila Tayi mai Shirin mallaka yanzu bayajin mganar kowa sai ita..ko kansa ma yana mantawa dashi bama wani Dake kusa dashi ba..!
Saifullahi ya Firgice Cikin kwalalo Ido yace”Sihiri fa kikace..?
Ta gyadamai kai Lokaci Daya ta Fara Basa Labarin komai har mganarta da Inna sai dai bata Fadamai Nazarin da Inna tace taje tayi ba kuma bata Fadamai mafarkinta ba.
Saifullahi ya Cire Hula yana Fifita Duk da Danyin A.c Dake Office din Lokaci Daya yana Fadin”Hasbunallahi Wani”imal Wakeel…!
Yake ta Fada yana Jin Zufa na kara Ketomai Cikin wani Hali yace”Haba No Wonder ni nasan abokina..Allah Sarki Ammh kam Ba”a kyauta ba Naga Daga Laila Har Sulaiman abu Dayane Ya Hajiya zataji in taji wannan abun ita da Ta matsa sai Sulaiman yayi auran nan ashe ashe wannan kaddaran ke Jiran Sulaiman..?lalle kuwa Zama bai ganmu ba..Zan yi yarda Zan yi Domin naga na Fitar da Abokima Cikin wannan Hadarin in ta kama sai na kai kaina Fada na Fadama maimartaba komai Shi kadai zai iya gyara komai..!
Da sauri Sunaima tace”a”a kada kaje..Ka manta Fada bata Amsam mgana sai da Hujja..?kai ina Hujjan naka..?
Saifullahi yayi shuru Sunaima ta Mike Tana Turamai Wayarta Lokaci Daya Tana Fadin”Sakamin lambar wayarka..kabar mgananr a Tsakanimu kada ka Fadama kowa mu Abban su Wasim zamu Fara Taimako Sauran yakin banamu bane..!
Bai mata musu ba ya Dauka ya saka mata ya Mikamata ta karba tana Fadin”Zan Kira ka Zuwa gobe…Kada kamanta kada ka fadama kowa…!
Zan yi wannan Kokarin ne Saboda su Wasim da kuma yar”uwata..Na barka Lafiya..!
Daga haka ta Juya zata Fita ya Daga baki ya Kirata ta Tsaya Cak kafin ta Juyo yace”Ba saboda kanwarki ba dai..Ai ita Tagama nata Yayin a Duniyar Sulaiman yanzu ke ta barma Duka Ragaman Rayuwansa Kiyiwa Allah Sunaima Wannan karon Kada ki jiyama kaddaranki baya Dagake Har Sulaiman ku Fuskanceta ku kuma karbeta Hannu Biyu..!
Bata Juyo ba,ko mgana batayi ba ta Kada kai ta Fice kowa sai yace wai ta Rumgumi Mijin kanwarta..?Ta yarda Zatayi komai saboda su Wasim ba Domin wani abu ba In ya Dawo Cikin Hayyacinsa zata Rokesa ya Sauwake mata in yaran zata Rikesu in ta samu miji Daidai da ita ta aura.
Ta yanke shawaran zuwa Gidan Inna Shiyasa yau takudira Karfe 4 zata Dauki Afuwa Daga wajen aiki Da wannan Tunanin ta Fito Daga Kamfanin ta samu adaidaita zuwa asibitin barrau dikko
Shi kuwa Saifullahi Tunda ta Fita ta barsa ya kasa Cigaba da komai ya Fada Tunanin yadda zai taimaki Amininsa Wayarsa ya Zaro ya Kira wani abokin babansa Dake Zaria Malami ne sosai na addini Shine kamar makafin Mahaifinsa Tunda tare sukayi kasuwanci Saida amfanin gona dashi Malam Sama”ila Shiya Kira bayan sun gaisa yamai bayanin yanayin Sulaaiman kamar yadda Sunaima tace Inna ta Fada haka yace mai sannan yace yazo ya Samesa akwai Ayoyin karya Sihiri Daga Qur”ani mai Girma Insha Allahu in akayi Komai zai zo karshe.
Sun Rabu kan zai kirasa in zai Taho bazai yi gaban kansa ba zai jira Kiran Sunaima Domin wannan yakin kusan nata ne Domin itace Matar Sulaiman yanzu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button