MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Janafty
MIJIN KANWATA..!
(k’addarata)

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

Wannan Shafin Sadaukarwa ne gareki ANTY NICE…Ina godiya da karamcinki Allah ya saka da alheri Ameen

Page 15

Kiran sallar farko na asuba ya Tasheta Daman ko min barcinta wannan Kiran Sallar ko da bataji ba Asuba nayi take tashi Saboda ta Riga ta Saba.
Tayi mamakin yanayin Data samesu Daga ita har Sulaiman,Gabadaya ya Kanannadeta itama Tana kan Jikinsa ne Barci ya sa ta saki Jiki bata sani ba.
Kunya ya kamata da Sauri tayi kokarin kwatan kanta Saboda Har Hulan Dake kanta ta Sabule Gashin kanta ya bayyana Har ya bazu saman Fuskar Sulaiman wanda gabadaya kansa ke saman Kafadanta zuwa wuyanta.
Hannu ta saka tana Kokarin Cire sa Daga Zagaye Kugunta da yayi,Sai dai Hakan bai samu ba Saboda shima alokacin ya Farka Daga Barcin daya Daukesa Mai natsuwa da kwanciyar Hankali wanda ya Dade bai yi kamarsa ba.
Fes kuwa ya Bude Kyawawan Fararan Idanuwansa akanta Lokacin Datake kokarin Raba Hannayensa da Jikinta Ganin haka yasa da Sauri ta Kauda kanta Daga kallonsa Cikin Sanyin Murya tace’Asuba tayi..Ka tashi ka koma Chan kada laila ta Fahimci baka nan..!
Lumshe ido yayi kafin ya Bude Cikin Shakewar murya yace”Ina so zan yi sallah..!
Yafada yana kokarin Danne abunda yake ji Data ambaci sunan Laila,Da Sauri ta kwace Jikinta ta Mike tana Daukan Hulanta Dake saman gadon Lokaci Daya tace”Zaka yi wanka ne..?
Kai ya gyadamata Kafin yace”Eh..Ina so naje masallaci..!
Bata Tsaya ba ta nufi Jikin Wardrope din Dake Dakin Tana Fadin”Zaka iya zuwa..!
Daga haka ta Dauko Jakar Ruwwn mganinan tazo ta Tsiyayamai ta bashi yayi Bismillah kamar yadda ta Umaecesa Haka yayi yasha Sannan yayi Hamdala Kamar afarko,Kansa ya Dafe yana jin wani natsuwa yana Shigansa Kallonsa tayi acikin Ranta Tana addu”an AllaH ya yanke mai Wahala maida komai tayi muhallinsa tace ya fara shiga wanka shi ya Farayi yana Fitowa ya maida Jallabiyansa ya Kalli Sunaima Data Zurma Hijabi kamar Zatayi Sallah yace”Zan tafi masallaci..!
Mikewa tayi tana Fadin”in kaje kayi ma kanka Addu”a don Allah..!
Ido ya sakarmata Cikin wani yanayi kafin yace”Nagode.!
Kai ta Kada batace komai ba Har yakai Kofar Fita ya Juyo yana Kallomta Kafin yace”Yau ba inda zaki je..?
Kai ta gyadamai kafin tace”Sai Monday..Zan koma Dutyn Safe..!
Kai ya gyada kafin yace”Zan rika zuwa ina shan mganina..I need my Self Soon SUNAIMA…!!!
Yadda ya Fadi sunan nata ne sai da taji Ko”ina ma Jikinta ya amsa yana kallon Cikin Idanuwanta ya Fice Daga Dakin Allah yasa ba wanda ya gansa Daman wani Lokacin Allah na Taimakon bawansa kan al”amarin Da ya sanya Duka yakini akansa.
Megadi yayi mamakin ganin Yallabai ya Fito Sallah yau bai ce komai ba Illah yabi bayansa zuwa masallaci
Ba Shakka ya samu Tarin natsuwar Daya Dade bai samu ba sakamakon sallar Cikin Jam”i,Ya zauna Shuru acikin Ransa ya rasa wata addu”a zai yi sai kawai acikin zuciyansa yake addu”an Duk abunda ya Nannade Rayuwarsa Allah ya warware masa ya Bashi Lafiya sai wajen karfe bakwai ya Dawo Gidan ya Haura sama Har Lokacin Shashashen Lailan bata Farka Daga Barcin asaran ba Gefenta ya samu kwanta ya kurama waje Daya ido Fuskar Sunaima ke Giftamai alokacin Duk ko yadda Laila ta Zama Duniyarsa ayanzu.
Kamar yadda Sulaiman yayi alkawarin zuwa wajen Sunaima Duk Dare Allah yana bashi Sa”a da Laila ta Fara Barcinta kamar Allah na kara Doramata Nauyin barcin ne sai ya Lallaba ya Fice zuwa Dakin Sunaima Ita kuma ko tayi barci zata barmai Kofa abude Daya shigo sai ya Tada ita ta bashi mganin yasha ya koma ya kwanta ita kuma bata barci sai dai ta Cigaba da Salla arana ta Uku ne tace mai shima yazo suyi sallar abunda ta Lura ko Ibadarsa an Raunanata sosai,da sun Fara sai yace mata ya gaji nan gefenta zai kwanta ya Fara Barci ita kuma bata barci sai Gabanin Asuba Ta rasa meyasa ta Damu da Halin da Sulaiman yake ciki Addu”an Duka Salolinta shine aciki Bata son ganinsa ahaka Tana Fatan Sulaiman ya Dawo wanda ta sani Mijin kanwarta.
Kullum da asuba yake Ficewa masallaci Daganan ne yake komawa Wajen Laila kuma bata taba Ganewa ba Ballatana Hadimanta ko sau Daya ba wanda ya Taba ganin Sulaiman ballatana akai mata Labari ba ma wanda zai yi Tunanin haka na Faruwa..
Saifullahi ya Kirata ya sanar da ita yaje Zaria wajen Babansa Sama”ila sunyi mgana Shima dai addu”an yace adage dashi,Shima Daganan barayin zai Dake da addu”a Insha Allahu komai Zai zama Tarihi jin haka yasa Sunaima ta Dake bata barci kwana Take Ssllah tana Rokon ma Sulaiman Waraka Daga wajen Allah
Rana ta Hudu ranar bai Samu Fitowa da Wuri ba Har nannayan barci ya Sace Sunaima Data gaji da Jiransa Shi kuma sai chan Dare yazo ganin ta Fara barci yasa ya Fara jan yatsun kafarta Kamar yana mata Tausa.
Cikin barci taji kamar ana Janta Ta Farka agigice Tana neman ta yanka Ihu Saboda ta Rage hasken Dakin akwai Duhu Daya Fahimci Zatayimai Ihu ne yasa yayi Saurin Riketa ya sa Hannu ya Toshe mata baki ita a Tunaninta Bai bata Sulaiman bane Saboda Barcin nata ya Dauketa ne Bagatatan batare data shirya ba.
Sai ta gantsara mai Cizo a Tafin Hannunsa Daya Rike mata Da Sauri ya Saketa Cikin Jin zafin cizon nata yasa yace”Ochhhhh….!
Yafada yana yarfa Hannu kokarin Tashi take yi Saboda akwai Hijabi ajkinta Datayi sallah dashi ganin bata Cikin natsuwarta yasa batare da wani Tunani ba ya kamata ya Rumgume kam kan kafin ya Dago kanta Batare da wani Tunani ba kamar ana Jansa antsaida Duka Tunaninsa akanta ne yasa ya Dora lebensa saman bakinta ya Fara Controling dinsa Cikin Kwarewa kamar wanda Wani abu ke jansa
Kamar amafarki taji ya Rumgumeta Kamshin Turaran Dake Jikinsa taji ta Gane shine,sai kuma taji Tattausan abu samanta bakinta kafin ta Dawo cikin Hayyacinta taji ya Fara yawo da Lebensa saman lebenta Cikin kwarewa tana Kokarin Bude baki taji Ruf ya Zura Harshensa cikin Bakinta ya Fara bata wani irin Sumba mai karfi da Fitan Hayyaci Lokaci Daya yana Rike da ita Tun Sunaima na ganin abun kamar almara har ta Fara gasgastawa cewa wannan al’amarin acikin Duniyarta yake Faruwa yau gata ajikin Mijin kanwatta yana Sumbatarta kamar Allah ya aikosa cikin Fitan Hayyaci abunda wani bai Taba yimata ba Tunda Take shiyasa Kamta ya Fara Juyawa Jikinta ya Fara rawa Jin yadda yake shafa mata Baya Cikin Tattaussaun Hannayensa.
Kamar yadda ta Fita Daga Hayyacinta Shima haka ya Fita Ya Dade bai ji baki mai kamshi da Taushi irin na Sunaima da Farko yaso ya sata ta natsu ne ammh Daga baya sai ya Fita Shima daga Tunaninsa sumbar da tun akan Sunaira bai jin ya kara yima wata mace ko Laila baya yadda yana Hada baki da ita sai dai ita ta Hada dashi da karfi da yaji Kwata kwata ai kamar Tilas ne ammh bawai don yana jin Dadin yin komai da ita ba..
Dalilim Haka yasa ya Dauki Tsawon Lokaci yana Sumbatartar Sunaima Daman Sulaiman Mayen Kiss ne ita kuma alokacin Sunaira bata Tsawon wannan wanan kamar yadda Sulaiman yake iya kai wani Lokaci yana Romancing din mace bai gaji ba Kamar yadda Sunaima gangar Jikinta ya Tallafi Bukatar Sulaiman hannu Biyu bata Dawo Cikin Hayyacinta ba Sai da taji ya Rabata da Hijabin Jikinta Hannunsa saman Kirjinta yasa taji wani Yam..! Daga saman kanta da Sauri ta kwace bakinta Daman Jikinsa ya Saki sai ya koma ya Lafe saman gado ita kuma ta Rarrafawa tayi ta Sauka kan gadon ta Durkushe Tana maida Numfashi kunyar Duniya Duk ya gama Saukan mata meta aikata..?meke Damunta ne..?
Bata iya Hada ido dashi ba Har ta bashi Ruwan yasha Yau dai ya Tsaya sunyi Sallah sosai sai Wajen 4 na Dare Sunaima taji barci ya sake kamata ta Kalli Sulaiman Dake gefenta ya Daga hannu yana addu”a ammh bakinsa baya Motsi sai ya ayyana acikin Ransa baya iya Bude baki ya Fadi wani abu kirjinsa yayi masa Nauyi sosai.
Abun na bata mamaki bai Taba Tambayan ina su Wasim ba alhalin baya ganinsu yasa tana ganin ya shafa addu”ar ta Kallesa tana Fadin”,Baka Tambayi su Wasim ba..!?
Kallonta yayu sai alokacin suka Fadomai arai shifa yana Tunanin ko Harda Ciwon mantuwa ya kamasa Banda Laila Sunaima ce kadai bai Taba mantawa da ita ba.
Cikin Wani yanayi yace”Suna ina..?
Kanta na kasa tace”Suna wajen Inna…!
Shuru yayi bai kara mgana ba illah Mikewa da yayi yaje ya Hau gado ya kwanta ya Nannade waje Daya kamar wani maraya tana kallonsa idanuwanta suka ciko da kwallah da Sauri ta kauda kai Bataso ta hau gadon ya Riketa kamar yadda ya Zamemai Jiki sai ta Sulale nan samAn Darduma ta kwanta ai da Asuba ajikin Sulaiman ta jita Shima ya Dawo saman Darduman ya matsu da ita kamar wani yaron Dake neman Nono bai samu ba.
Sati Dayan nan kaf sun Cinyeta Tare Ruwan addu”an ma ya kusa kwarewa kuma ba Laifi Sunaima tana ganin Sauyi Sosai sai dai yana yawan barci in yasha mganin sai kuma yawan Shuru da Shiga Tunani,Sai dai yanzu Ta Saba Dashi Saboda Tare suke kwana sai Da Asuba yake tafiya Tun tana Hanasa Tabata tana jin kunya har tazo ta Saba Allah ya Taimaketa wannan Watan bata da aikin Dare sai wata mai kamawa Shiyasa ta samu Cikakken Lokaci Suna waya da Inna ta Fadamata mganin ya kusa kwarewa Tace Zata Kira kawu Jafarun kila Ahmad Zata Tura ya karbo wani.
Har kuma zuwa Lokacin kuma Laila bata Taba Lura da komai ba Ballatana su Samira sai dai magajiya ta taba ganin Sualaiman sau Daya zai shiga Dakin Sunaima ta kuma Taba ganinsa zai Fito da asuba ammh bata taba Fadama kowa ba ita kanta Fata Take da Addu”an Allah ya Kwato Saraki Daga Hannun Muguwa mace irin Laila.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button