MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL


Abuja…
9:30am

Gabadayansu suna saman Dining din Dake babban Falon su inda suke Haduwa suna cin abinci Lokaci Bayan Lokaci,Jiya Hajiya Falmata ta Dawo Daga maiduguri,ita da Alhaji Aliyu kakarta wacce ta Haifi mahaifiyarta ce ta rasu Hajiya zabba”u taje gaisuwan ita da yara sun kwama Daya suka dawo ita kuma Hajiya karama tana chan Sai da akayi bakwai Abba yaje suka taho da ita.
Dukkansu suna bada Hankalinsu wajen cin abincin Harda yaran Hajiya Zabba”u Cokali ke hannunta tana wasa dashi ta kasa cin abinci yana lura da ita,ganin gabadaya kamar Hankalinta baya wajen ta shiga wani Tunani,Yasa ya Ijiye Cokalin hannunsa yana kallonta kafin yace”Zabba”u…!!
Bata jisa ba Tayi nisa Cikin Tunaninta Gabadaya Hankalinsu sai ya koma kanta Sadiya ce ke kusa da ita ta Dafa Kafadarta Tana Fadin”Hajiya..Hajiya..!
Kamar daga sama taji Kira Firgigir ta Dawo Cikin Hayyacinta Tana kallon Sadiya ita kuma Cikin yar Damuwa tace”Abba ke mgana fa..!
Sai alokacin ta Dago tana kallonsa kafib tace”Abbansu me kake cewa ne..?
Tafada tana Dafe kanta Hajiya Karama ta kalleta kafin ta kalli Abba ta kasa mgana itama Tun jiya Da suka Dawo Taga Hajiyar kamar tana Cikin Damuwa saninta macece mai kazar kazar da Tsayawa kan kafafunta Abu ne mai Wahala ke sata tayi Rauni.
Cikin Damuwa ya kalleta kafin yace”Meke Damunki Zabba”u..?
Ajiyar zuciya ta Sauke kafin tace”Me ka gani..?
Da sauri yace”Abubuwa dayawa..Ina Lura Dake Cikin kwanakin nan kamar bakya Cikin Hayyacinki..Wani abu na Damumki.yawan Tunani sannan Duk kin zama wata so Cool dake… ana mgana sai ki yi Lose bkya Tare damu kwatakwata..!
Hajiya karama ta kada kai kafin tace”Koni na lura kamar wani abu na Damunta Tun jiya da muka Dawo..!
Sadiya ma tace”Abba ita kadai fa adaki Hajiya kayi ta mgana bata jika ba..!
Saddiqa tace”Ta rage Hira da Fara”a kamar ba Hajiyarmu ba..!
Sadiq ya ijiye mug din Tea dake hannunsa yana Fadin”Jiya ma Danaje Gidan Anty Safiya sai da ta Tambayeni Hajiya…Tace tana Kiranta bata Dauka..Sannan ranar ta Dauka Duk taji ta wani iri..Hajiyarmu meke Damunki Allah duk kin Sauya..,!
Hajiya karama tace”Su Raliya ma haka sukayi ta fada a maiduguri sun ce Hajiya ta zama so Cool..!
Itadai Duk tana jinsu batace komai ba Kanta na kasa Abba ya kalleta kafin yace”Kin ji mganar yar”uwanki da ya”yanki..Ni kaina ai ba yau na Sanki ba zabba’u tabbas wani abu na Damunki..ba abu kadan ke saka Zabba”un Fulani tayi Laushi ba..!
Hajiya ta Dago Daga Dafe kan Datayi kafin tace”Yaushe Rabon da kayi mgana da Saraki?
Gabadaya Tsam yayi yana kallonta haka yaran suma kowa yana Jin abun aransa Daman mgana ne bai samu ba.
Abba yace”Bamu yi waya dashi ba kwana biyu..!
Da Sauri tace”Tun Da kuka Rabu a kargi baku kara mgana ba ko..?
Shuru yayi kafin yace”Eh..Me ya faru..?Shine Damuwar ai shuru lafiyace sannan ga aiki ga kuma Amarya Kila bai gama cin amarcin bane..!
Yafada Cikin Zolaya yana so ya kauda mganar ammh Shi kanshi ya Fara Tunanin wani abu Tunda yake da Saraki bai taba Kwana Biyu bai kira wayarsa sun gaisa ba ammh kimanin Sati Hudu ba wayarsa ba Sakonsa Sai dai sukan yi mgana da Saifullahi da Farko yayi Tunanin Auran da yayi yanzu Da aka kwarari Lokacin nan Jikinsa ya basa wani abu na Faruwa ammh Wannan Halin bana Saraki bane
Duk ko wani Karshen wata yana Hanyar Abuja yazo ya gaishesu waya kuwa Koda yaushe cikin Kiransu yake yi.
Hajiya karama Dake gefe ta kada kai Tace”Ni kaina Hajiya ina so nayi mgana..Wai Saraki Lafiya kuwa..?ni kaina Tun Rabuwar mu daga Kargi bamu kara mgana ba yaron da Bayan kwana Daya sai ya Kirani mun gaisa..Ni Ranar ma na kirasa bai Dauka ba..Ko Rasuwar nan Abbansu ban jiman ya Jita da Har Maiduguri na Tabbata sai Saraki ya Taka..!
Da Sauri Sadiya tace”Wlh Hajiya baya Daukan wayarmu..ni da Saddiqa kan mganar Chanzamana Mota mun Kirasa har mun gaji ba”a Daga ba..!
Sadiq ma yace ya kirasa baisan adadi bai Daga Kiran ba.
Hajiya Zabba”u taji kamar ta Dora Hannu akai ta Kurma Ihu ita kanta ai bata Samunsa a waya ko ta Kira Baya Dauka,ko Ranar da akayi Rasuwarsa ta Kirasa bai Dauka ba ta Kira Saifullahi yace yana Meeting ne ya Samu Zillema Kiran nata.
Saraki ba Haka yake ba Lafiya Lafiya bazatajisa Shuru haka ba Ta kira Samira ko zataji wata mgana bataji komai ba Ta Kira Laila sai ta Rika ce mata baya nan yana wajen aiki in ta Kirata da Daddare bata Dauka Sai da Safe ta Kirata tana Fadin bata ga Kiran ba.
Abun ya Fara Damunta Har ta Fadama Hajiya Salame sai ita ma ta ce mata ita kanta sai tayi Sati batayi waya da Laila ba, ta Dan Kwantar mata da Hankalin cewa su godema Allah Laila da Sulaiman sun hada kansu alokacin Hankalinta ya kwanta ammh yanzu Taji bai kwanta ba Ko Sulaimam baya kusa ta Kirasa in yazo yaga Kiranta zai Biyo ba ita kuwa batasan adadin Kira nawa tayi mai ba bai Nemeta ba.
Ko jiya da sukayi waya da su Fulani suna ta Jajensa suna mai Tsiyan Tunda yayi amarya suka Daina Jinsa bata Tsinke da ba Lafiya ba sai da Sukayi waya da maimartaba da kansa yake Tambayanta Ina Saraki..?yayi Amarya ya manta dashi Daganan tasan ba Lafiya Domin ta Tabbata Rashin Lafiya me ko Ciwo mai Tsanani zai saka Saraki ya manta dasu iyayensa da mainartaba.
Abba ne Dayake ta Nazarinta yace”Bakina waya da ita yar wajen Salamatun ba..?
Kai ta gyada kafin tace”Eh in na Kirata sai tace min yana wajen aiki..!
Bayaso ya Nuna mata ya Damu shima Shiyasa yace mata”Lafiya ke sa Shuru zabba”u kada ki Damu Saraki yana Lafiya da yardan Allah..kawai in kinji Zuciyarki bata natsu ba Juz kiyimai addu”a..!
Kamar zatayi kuka tace”Kasan Kira nawa nayimai bai Dauka ba..?Abbansu Saraki bai taba kwana ya Wuni Cikin Lafiya ba bai Kirani ba. kodai baida lafiya ne..?
Tafada sai ga Hawaye Hajiya karama Tace”Koni da ban Haifesa ba bai Taba kwana Ya wuni bai kirani ba..Mganar Hajiya abar Dubawa ce..!
Abba yace”Kada ku damu yana Lafiya ko Jiya mun yi mgana da Saifullahi..kuma da akwai wani abu Daya Fadamin..!
Hajiya Zabba”u ta Girgiza kanta Tana Fadin”Ni ban yarda ba..Ni uwace naji ajikina ba Lafiya Nidai gobe zan Shirya naje chan Kadunan nagani..!
Abba ya kalleta Kafin yace”A”a bazaki jeba..Ai baki Fimu son Sarakin ba..Ki bari dai mu gani in mukaji Shurin nan da Sati mai zuwa ko Hajiya karama da Sadiya sai suje su gani..!
Bata da yadda zatayi ta kara Cewa wani abu Domin kuka ne zatayi Sai kawai ta tashi ta Fice tana Sharan Kwallah Hajiya karama tace”Abbansu kayi wani abu..Nima inajin ba Lafiya..!
Abba yayi ajiyar zuciya kafin yace”Kuyimai addu”a..!
Daga haka shima bai kara cewa komai ba ammh iya Tunaninsa yasan shima wani abu na Faruwa sai dai bayaso ya karya musu zuciya zai Binciki SaifullHi yaji ko lafiya ya Tabbata Koma akwai wani abu to yana da masaniya.
Haka Cin abincin ya tashi ran kowa ba Dadi Harta yaran Kowanne Jiki a sanyaye
Hajiya Zabba”u Daki ta koma sai kuka Saraki shine mafi soyuwa cikin ya”yanta Batason wani abu ya Faru dashi ita Ranta ya gama bata ko Hatsari yayi ake boyemusu koma ya Rasu ne..?Tunanin haka ya kusa wa Tayi Hauka Zuciyarta ta Buga.
Tana cikin wannan Halin Safiya ta Kirata ta waya Sai da ta yanke ta kara Kira Kana ta Dauka Daga yanayin Muryan Hajiya tasan tasan ba Lafiya Cikin Damuwa tace”Hajiyarmu Lafiya..?
Jin haka yasa Hajiya ta Fashe da kuka Safiya Hankalinta ya tashi ta Fara Fadin”Hajiyarmu lafiya Abba ne wani abu ya Faru dashi..?ko Hajiya karama..!
Hajiya na kuka ta cigaba da Fadama Safiya Damuwarta ta Kare da cewa”Safiya Wlh na Fara Mugayen mafarkai kan Saraki yana cikin wani Duhu mai Tsanani yana Kiran sunana yana Mikomin hannu..Bantaba irin wannan mafarkin ba Safiya jikina yana bani Saraki ba Lafiyansa ba..!
Safiya tace”Nima Kiran dana nayi miki kenan..Abbnsu Hidiya yaje Kaduna Jiya Hajiya har Office din ya Saraki yaje Sakariyarsa tace bayanan yama zata ya Fita ne yace zai Zauna ya Jirasa sai take gayamai yafi Sati Uku bai zo aiki ba..!
Ido Hajiya ta Zaro kafin ta Dafe Kirji Tana Fadin”Innalillahi Wa”inna ilaihirraju”un..!
Safiya tace”Wlh Hajiya..Daman ya Biya su gaisa shima Workshop suka je yi na kwana Biyu jiya suka gama shine yaje su gaisa.yacemin yaga Saifullahi sai dai shima sai kame kame yake yimai Daga gani wani abu na Faruwa..!
Hajiya Zabba”u ta mike Tana Fadin”Yama Faruwa Safiya..bazan zauna ba ko Abbanku ya yarda ko bai yarda ba..Ni zan je kaduna yau naga Halin da ake ciki..!
Da Sauri Safiya tace”A”a Hajiya baza”ayi haka ba..Ki barmin komai a Hannuna zan matsama Abban Hidaya ya kaini kadunan zan je Har Gidan naga Abunda ke Faruwa nayi miki wannan alkawarin..!
Hajiya tace”ki kokarta Safiya..Ina Cikin Tashin hankali..!
Safiya ta tabbatar mata Zataje taga ko Lafiya da haka suka yanke kiran.
Hajiya Zabba”u tana kuka Tana fatan kada wani mummunan abu ya Samu Danta.
Taso ta Kira Hajiya Salame ta Fadamata tace ko zatazo su je su gani ne sai ta Kirata bata Dauka ba Daganan sai bata kara Kiranta ba da Hajiya salamen tazo ta kirata daga baya kuma sai taji kuma ta kasa gayamata wannan wani abu ne Daya Shafi abunda ta Haifa ita Lailar ana Jinta Saraki ne kanar batan Dabo aka Daina Jinsa Da ganinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button