MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Laila na Sharan jinin Dake hancinta tace”Bansan da zuwanta ba..Tana zuwa ta fara dukana tana cewa sai na Fadamata me nayi ma sulaiman..!
Hajiya Zaliha tace”Ina fatan baki fadi komai ba ko..?
Da sauri tace”Eh ban fada ba wlh..nayi ta kiran mommy ban sameta ba..!
Kai ta kada kafin tace”To kada ki kuskura koda wasa kice wani abu..Domin in wani ya sani bayan ni da ke da salame makarin mganim zai karye ne yanzu ni ina ghana Kada ki damu zan kira mamar naki muyi mgana abu daya nake so dake koda wasa kada aji komai abakin ki Sulaiman kuma yana karkashinki ne ayanzu bazai iya yin komai batare da izininki ba..!
Laila ta Sauke ajiyar zuciya tana Fadin”Kina ganin ba mtsala Anty Zaliha..?
Da sauri tace”Kada ki damu bakomai..!
Da haka suka yanke kiran sai lokacin ta samu salama bata so asamu mtsala domin tana jin dadin yadda ta samu mallakan sulaiman acikin sauki.
Toilet ta shige tana kokarin gyara kanta Hanci da baki jini na Zuba Safiya tasan kan mugunta Har kunnenta sai da ya tasa Saboda Zafin hannunta

Safiya kuwa a Zafafe take saukowa saga Stair kamar zata kifa tana saukowa Falon ta samu kujera ta zauna tana Huci cikin Tsawa tace su magajiya su zube agabanta jikinsu na rawa suka Gurfana agabanta suna rawan Jiki ba bata Lokaci tace tana son sanin abunda ke faruwa acikin gidan nan Samira dasu marliya suka yi Tsuru tsuru sun kasa mgana saboda suna tsoron Laila Magajiya ce ta Ssmu dama daman ita take jira ta Fadema Safiya duk abunda ke faruwa tun ranar da Laila ta kwana daya agidan har zuwa yau din nan kafin ta gama Safiya tajike da hawaye harda majina su samira ma ta Daka musu tsawa suma suka yi jawabi abu Daya ya kara Rikita Safiya jin datayi komai na Rayuwar Sulaiman yana Hannun Laila bama ata matarsa wannan Bai damu da ita ba kamar yadda suma Danginsa basu damu da ita ba ya”yansa har dasu Laila ta shafe a kwakwalwar Sulaiman lalle za””ayi Tashin hankali ta inda aka Hau ta nan za”a sauka Dole.
Masaukinta ta koma Tana sharan kwallar Tsausayin dan”uwanta ta rasa wa zata Kira ta fadama Halin da suke Ciki,Tana kuka ta Kira Fadila ta zayyanemata komai itama nan Hankalinta ya tashi cikin Damuwa take Fadin”Yanzu muka gama waya da Hajiya karama Hajiya na kwance ba Lafiya jininta yahau sai da likita yazo ya dubata ya daura mata Drip sai kuka take tana kiran sunan ya Saraki..!
Safiya tace”Kij ji ko..?wlh Bazamu bari akasahemana dan uwa ba..kuma bazamu bari a mallake mana Dan”uwa ba,yanzu irin sakamakon da Inna Salame zatayi ma Hajiyarmu kenan..?ki kalli yadda tayi fadi tashin Taga ya saraki ya auri Laila fa Fadila..?
Fadila tace”Uhm..Dan adam din kenan aikata abunda bakayi tsammani ba..Baiwar Allah nan Marigayiya sunaira muka Dora mata karan Tsana haka take bin mu muna mata wulakanci tazo ta rasu maimartaba ya nema masa yayarta itama muka Dora mata duk da ita bata bimu ba ammh akallah ai basu mallake mana dan”uwan sun raba mua da komai nashi ba..Daman sau tari wani abunda muka so ba Alheri bane kuma na Tabbata hakan daya Faru ishara ne ga Hajiya damu dangin miji masu kin matar dan”uwansu saboda wani Daliki yau ga wacce muke so sanadinta yasa,muna neman rasa Mahaifiyarmu..!
Safiya na Sharan hawaye da jan majina tace”Wlh fadila gaskiya kika Fada sai yanzu nake auna wasu abubuwa..Kai duniya ina zaki Damu?
Fadila tace”Bari kawai..yanzu ta ina zamu fara ko Kargi zaki tafi ki sanarma maimartaba..!?
Safiya tace”A”a ba chan zani ba..Ta inda aka Hau ta nan za”a sauka Gobe tun safe zan koma Abuja yanzu ma saboda Dare yayi ne da wlh ban kara kwana agarin nan ba Hajiya zan je na samu na Fadamata komai itace Tsanin komai so nake taji da kunnenta..!
Fadila tace”Kina ganin ba mtsala..?
Safiya tace”Matsala ai akwaita Fadila kema kin sani ammh gwara mu tari abun da sauri kafin su kara Shiri..!
Fadila tace”Gaskiya ne ina ita Sunaimar ina yaran suke..?
Safiya tace”yaran magajiya tacemin Suna gidansu sunaima chan takai su saboda Zirga zirgan tafiya makaranta ita kuma ni ban ganta ba..Ban kuma Tsaya bi ta kanta ba yanzu mafita muke mema fadila..!
Fadila tace”Shikenan sai goben yadda kukayi da Hajiya ina jiranki..!
Daga haka suka yanke kiran Ranar barci barawwo ne kadai ya Sace Safiya asuban fari ko karyawa batayi ba tayi shirin tafiya dama da kayan kwana Daya tazo bama wanda yasan taafiyanta ta Buga ma megadi tace Direba ya Fito su kama Hanya.
Sunaima itama batayi wani barcin kirki ba domin tun fara shan ruwan adduan nan yau ne rana ta farko da sulaiman yayi fashi bai zo ba ta saba da barci a kirjinsa yau bashi yasa sai dai juye juye sai da ta gaji da Kwanciya tataahi ta Dauro alwala tazo ta kabbarta sallah gabadaya Salolinta da addu”anta kam Allah ya kwato Sulaimam daga hannun Azzaluma irin Laila tayi sauka akan hakan bata san iyaka ba haka Saifullahi duk dare goshinsa akasa yana Rokon Allah ya dawo da Sulaiman yadda yake hakama Abba Tunda ya samu Labari bai kara barci shima Goshinsa na kasa yana kai kukansa ga Allah domin shi kadai ne ke baka yau ya baka gobe bai gaji ba.

Karfe 10am na safe Safiya ta dira agida hajiya karama na shashenta batama san ta shigo ba ko gida bata wuce ba Sadiya ta iske a bedroom din Hajiyar tana gyara shimfidanta tana gaisheta dakyar ta amsa Lokaci Daya tana Kallonta tana Fadin”Ina Hajiyar..?
Sadiya cikin boye mamakin ganinta Tunda hajiyar bata da Lafiya tasama ranta ita tazo gani Cikin Ladabi tace”Yanzu ta shiga Tiolet zatayi wanka..!
Safiya ta karbi gyaran gadon tana Fadin”Barmin na karisa kije zan yi mgana da Hajiya..!
Sadiya batayi gaddama ba ta Fice Dauke da wayarta zuwa Dakinsu ita da Saddiqa yau basu da lecture sadiq ne ke dashi ya tafi tun Safe.
Bata kawo ma ranta komai saboda daman in suzo suna mgana da Hajiya basa zama awajen Saboda Ladabi.

Safiya bata iya karisa gyaran gadon ba, Hajiya ta fito daman tana ciki Tunda taji mganar Safiya ta kasa wanka Cikin natsuwa Safiya na kallon Hajiya duk ta rame ido ya Fada Tsausayinta ya kamata ya zataji in taji Labarin an Mallake mata d’a masu suyowa agareta.
Hajiya zabba”u tabi Safiya da kallo Cikin Dashewar murya tace”Safiya tun da naji muryanki gabana ya Fadi me ya faru ne..?ko yau zaki tafi gidan Sarakin ki gano halin Dayake ciki..!
Safiya ta sauke numfaahi kafin tace”Daga chan nake ma yanzu Hajiya…!
Hajiya ta kwalolo ido Cikin mamaki tace”Bangane ba..!
Hannunta ta kama ta zaunar da ita agefen gado itama ta zauna agefenta tana Fadin”Jiya naje yau kuma da Safe na kamo Hanya ban gayamiki bane nace bari na bari sai na dawo..!
Hajiya Cikin Sauri ta Damke hannun Safiya tana Fadin”Safiya wani hali kika ga Saraki..?nayi mafarkinsa jiya na gansa yana kuka yana kiran sunana Safiya..!
Sai hawaye sharrr..Safiya ta Hadiye miyau kafin tace”Hajiya Allah ne yake nuna miki saboda ke uwace..Da gaske ne Saraki na cikin mayuwacin Hali na neman agaji da taimako..!
Hajiya ta fiddo ido waje tana Fadin”Innalillahi Safiya me ya Faru..?
Safiya tace”Inna salame taci Amanarki Hajiya..ita saka yarta laila ta mallaki Ya Saraki ya manta da kowa da komai Hatta da ku iyayensa da yan’uwansa da ya”yansa Hajiya laila ita ke Da ragamar duka Rayuwar Saraki…!
Hajiya ji tayi kamar mganar tana mata amsa kuwwa cikin Fitar Hayyaci tace”Safiya ban…ban gane ba..!
Nan fa ta shiga warware ma Hajiya komai tunda ga farko kamar yadda taji kuma tagani Kafin ta gama Hajiya ta jike da Hawaye da majina kuka Share Share Kirjinta na Bugawa Fat Fat Cikin Fitan Hayyaci ta Rike hannayen Safiya tana Fadin”Safiya ni Salame zata ma haka..?
Shiyasa ta rage kirana in na kirata ina nata Compain kan rashin samun saraki sai itama tace bata waya da Laila sakamakon da zatamin kenan?
Safiya tace”Wlh Hajiya ya Saraki duk ya susuce baki gani ba nifa har marina yayi akan laila ya koreni abunda tun muna yara ya Saraki bai da Saurin hannu Hajiya…Wlh in bamu mike tsaye ba zamu rasashi gabadaya..!
Hajiya ta fizge hannunta ta mike da Sauri Jiri ya kwasheta sai da Safiya ta Rikota Cikin karaji tace”Lalle Salame ta Tono ma kanta ni zatama haka..?d’an nawa zata saka yarta ta susutashi…?ita na Haifar ma wa..?
Safiya tace”Hajiya taci Amanarki wlh
Daman ance wani abunda muka so ba Alheri bane..!
Hajiya ta wuce wajen wardrope tana Fadin”Nagani Safiya..naga karshen Soyayyah da Amana daga lailar har Salame sai sun gane kuransu zan nuna musu ina nan a zabba”u na ban Chanza ba..Ki tsayamin yanzu zamu juya Kaduna naganin ma idona komai Safiya domin na fahimci ta inda zamu bulloma lamarin..!
Safiya tace”Shikenan Hajiya ammh Abba fa..?ga hajiya karama..!
Hajiya ta Dauki kayanta tana fadin”kada ki damu bazamu sanar dasu ba sai mun je mun dawo..!
Daga Haka ta shige Tiolet ta Sawo kaya doguwar rigar atamfa ta sako Mayafi jakarta Safiya ta rike mata suka fito shashen Hajiya karama suka shiga Safiya ta gaisheta ta amsa Cikin Sakin Fuska ta gaida Hajiya tana kara mata sannu da Hajiya tace zasu fita bata kawo komai ba ta zata wani waje zasu je kuma ita bata da son jin kwakwaf sai bata ce komai ba.
Suna fita Direban Anty Safiya na jira suka fada shi kanshi yaji mamaki da yaji kaduna zasu kara komawa sai dai bai ce komai ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button