MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Har suka isa Kaduna Hajiya sai Maimaita ni Salame zata ma haka..?ni Salame zataci Amana..?sai hawaye suna isowa Hajiya bata jira komai ba ta Fito daga Motar ta fada gidan so take tayi arba da Saraki ta ganin ma idonta Safiya na bayanta sanda suka shigo Falon da magajiya suka ci karo tana ganinta ta Duka tana gaisheta bata amsata ba illah cewa datayi”Ina Saraki..!?
Magajiya kanta na kasa tace”Yana Sama dakin Laila..!
Mamaki take har Safiya takoma Abuja ta dawo ita batayi tunanin tafiya tayi ba,Tare suka Haura sama kai tsaye zuwa Dakin Laila Hajiya ce agaba Safiya na bin bayanta suka Tura Kofar suka shiga Safiyace tayi sallama Hajiya ji take kamar ta Bude ido ta ganta gaban saraki.
Laila tana zaune afalo kan Daya daga Cikin kujerun da sukayima Falon kwanya Kafa daya kan daya tana waya Tana sanye da riga da wando jean da Shirt da suka kamata sosai Gabanta Center table shake da kayan marmari sai marliya dake gefe tana goge goge su hajiya suka fado falon

Laila ta dauka bata gani daidai ba Domin da safe ta sauka kasa ta tambayi Safiya samira suka tabbatar mata da cewa ta wuce Auwali megadi ke fadamata sai alokacin hankalinta ya kwanta Sulaiman na ciki ta Hanashi Fitowa ita ta zo nan ta zauna Tana waya da kawarta da sukayi makaranta tare.

Hajiya har gaban Laila ta isa Idanuwanta sun yi jajir da Sauri wayar hannun laila ta subuce ta Mike Cikin Rawan jiki tana Fadin”Hajiya…Ha..jiya sannu da zuwa..!
“Ina saraki…?
Hajiya ta fada Lokaci Daya tana Tsareta da ido Laila bakinta na rawa tace”Yana daki…!
Hajiya bata tsayaba ta Fara tafiya tana kwala Kiran”Saraki…SULAIMAN…!
Yana zaune daman kamar akan kaya yake jiya Laila ta kasa ta Tsare bai samu satar hanya ya fita wajen sunaima ba,itace aransa tun safe yake so ya Sulale yaje ya ganta Laila taki barinsa kamar ta Fahimcesa yasa ta mai kaahedin kada ya fito ko falo ne
Kamar daga sama yaji kiran Kamar Muryan Hajiya ita uwa ai dabam ce Haka yaji kamar ana jansa sai gashi a Tsakiyar falon agaban Hajiya yana kallonta.
Hajiya kallonsa take yi daga sama Har kasa cikin Tsausayinsa Cikin karaya tace”Saraki nima an saka ka manta dani..Nice fa Hajiyarka mahaifiyarka..!
Sulaiman na kallonta kwarmin idanuwansa sun cika da kwallah Laila ya kalla dake ta Kifta ido alamun ba ta da gaskiya Cikin marairaicewa yace”Lailata in mata mgana..?kinga fa Hajiya ce!
Hajiya ji tayi kamar Duniyan na yawo da ita Safiya tace”Hajiya kin ji kuma kin ga abunda nake fadamiki ko..?ki shaketa sai ta fadi inda suka Binne asirin nan mun hakosa don ubanta..?
Ai Hajiya kamar kububuwa haka ta Dumfari Laila sai dai ina Sulaiman bai bari ba ya shiga Tsakaninsu Hajiya Cikin zubar kwallah tace”Saraki matsa kabani waje..!
Kai ya girgiza yana fadin”A”a Hajiya bazan bari ki daketa ba..!
Ai batasan sanda ta bangajesa ba Safiya na ganin haka ta tayata Damko Lailan data fasa wani gitattacen Ihu Daya Fiddo da Sunaima Daga cikin Daki.
Hajiya ta rika zagmata maruka Sulaiman na riketa yana Fadin”Hajiya Hajiya..!
Fadi take”Saraki ba kai bane..ba haka kake ba Laila ki Fadamin me kikayima D’ana..?
Laila dataji wuya ranta ya kawo wuya tayi kukun kura ta ture hannun Safiya ta kuma bangaje Hajiya da sai da ta Fadi kasa daman bata da karfin Jiki sulaiman na ganin haka yace”Hajiya..!
Jikinsa na rawa Safiya ta kuta tace”Hajiyar kika kada Laila..?
Laila na kokarin daidaita kanta tace”Ita taja..ai ba uwata bace ke kinzo kin Dakeni kin zageni sai na bari itama tazo ta Dakeni D’anki da kike mgana a mijina ne budemai gaba nake yana Shiga kinga kuwa Dole yamin biyayya ke kina budemai gaba ne ballatana ya Fifitani sama Dake..!?
Hajiya data mike idonta ya Rufe da Cin Zarafin Laila ta Daga Hannu ta wanke ta da mari tana Fadin”Ko ban bude gaba ya shiga ba..Don Uwarki salame da bata baki Tarbiya ba na Bude gabana ya fito ta ciki!
Laila ranta ya baci sai Hawaye Tuni ta manta da Sharadin Mallam ta kalli Hajiya da Safiya da suke Huci da Takaici hannunta Dafe da kunci tace”Eh din an mallake shi din..So kike yadda na gama wahala akansa kafin ya aureni bayan mun yi auran kuma na kara wahala..ko kuma na zauna ina jure cin kashin da kuka saba ma matarsa tun tana da Rai..?baki isa ba Kin Haifi Sulaaimam ammh Dole ki kauda ido akansa Mommy ai tafini saninki tasan bazaki barni naji Dadi agidam Mijina ba Shiyasa ta karbomin mganin mallaka yanzu Sorry to say Hajiya ko Dukanki nace Sulaiman yayi zai yi sai dai bana son Ya Tozarta watarana ammh zan iya sakashi ya Koreki..!
Ta juya bangaran Sulaimam bata ma Lura da yanayinsa ba yadda Idonsa ya juye da kuma yadda ya Dafe kansa Cikin bada Umarni tace”Habibi ka koresu in kuma ba haka ba ni zan Tafi na bar maka gidan..!
Tafada Cikin bada Umarni Hajiya datayi mutuwar Tsaye tana Hawaye Safiya ma ta kasa mgana sai kuka Hajiya ta kalli Laila kawai sai tayi Dariyan kuka ta kara Daga hannu ta Zagmata mari tana Fadin”Ba Korata zaki sa yayi ba marin ki zaki saka ya rama miki Mara tarbiya..!
Laila tayi kuta tana Fadin”Habibi kana gani ko..?
Sulaiman na Dafe da kansa Dake juyamai Cikin fitan Hayyacinsa yana jinsa kamar abubuwan da suka Faru acikin mafarki ne.
Ganin ya tsaya yaki motsi yasa ta Daga hannunta da niyyar marin Hajiya tana Fadin”In bai rama min ba zan rama da..!
Bata gama Rufe baki ba Taji an Damke hannunta Lokaci Daya an yarfamata mari Tare da wani Hambarin da sai da ta wuntsila kanta ya Daki kujera sai da ya fashe cikin Fitan Hayyaci ta Dago wadanda tagani suna kallonta Cikin bacin rai da tsana da wani Fushi yasa ta Firgita ta fara ja da baya
SUNAIMA DA SULAIMAN ne cikin Wani irin yanayi sun kare gaban Hajiya dukkansu suna Fitar da Hucin Yadda zuciyarsu ke azalzala.

Ku kara hakuri Dani…

Janafty
MIJIN KANWATA..!
(k’addarata)

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

Barka da zagayowar Ranar Haihuwarku My Sahibatu HAFSAT HAFNAN and u My Jika KAUSAR AGLAN NISSA..Allah ya kara ma Rayuwarku albarka Ameen????

Page 18

Sunaima tana kwance adaki Yau bata da aiki tana Up,duk damuwa ya isheta na rashin ganin Sulaiman taji ihun Laila shine yasa ta fito da gudu Magajiya ke fadamata Zuwan Hajiya da dawowar Safiya sai hankalinta ya kara tashi nan da nan Tunanin Wani abu ne ya faru da sulaiman ya fado mata domin hakanan Hajiya batazo haka bagatatan ba da farko bata so Haurawa saman ba sai dai hankalinta yaki kwanciya gani take yi kamar wani abu ke faruwa shiyasa ta yanke shawaran shigowa.
Tana shigowa daidai Lokacin da Laila ta Daga hannu zata dagi Hajiya Sunaima ta fara tareta idonta ya Rufe saboda alokacin tana Hango Inna ne Matar Ahmad zata mareta uwa ai ta wuce wasa batasan sanda ta tare hannunta ba,Bata idasa kai hannun ba ta Mareta sai dai ba wanda ya ga lokacin da Sulaiman ya kariso sai dai gani sukayi yayi kwallo da ita bayan ya saka kafa ya Tokareta,Ya kasance shi da Sunaima suka Shiga gaban Hajiya suna Jifan Laila da wani kallo na tsana da kyara.
Safiya tana hawaye ta lura da Hajiya ta kusa Faduwa Jiri ya Debeta yasa tayi azaman rikota tana mata Sannu kan kujera ta Zaunar da ita Lokaci Daya ta Zare mata Mayafin Jikinta Saboda ta samu iska.

Laila bata tsorata da ganin Sunaima ba Tafi tsorata da yanayin kallon da Sulaiman ke Binta dashi Cikin Rawan ido Da Faduwar gaba Tuna irin Barambaram datayi sai dai kafin ta samu mafita wata gigitaciyar Tsawa ta Karade falon Cikin muryansa ta Zatinsa ya daga hannu yana nuna ta yana Fadin”Ashe ke dabbace bansani ba Laila..?Hajiya kika Daga hannu zaki mara..?
Ayanayin mganarsa kadai zaka gane ya dawo sulaiman dinsa saboda Alokacin da Laila ke Jan ragamar bai da wannan Zarar Cikin matsancin Bacin rai ya nufeta Hajiya Dake Zaune ta Daga murya tace”Dakata Saraki..Barta kada ka kara tabata..!
Cikin bacin rai ya juyo yana Fadin”Hajiya kefa ta daga hannu zata mara..?Kibarni na Fara sauya mata kamanni tukunnah..!
Mirmishi Farinciki Hajiya tayi sai ga Hawaye Safiyama haka Hajiya afili ta Furta Alhamdulillah ita kuma Sunaima sai ta Furta aranta Saboda Fahimtar datayi alkadarin Laila yau yagama karyewa.
Safiya kuwa Da gudu ta nufesa ta rikesa Cikin matsanancin Farimcikin Tana Fadin”Alhamdulillah Hajiya Ya Saraki ya dawo cikin Hayyacinsa..!
Hannun Safiya ya rike cikin mamaki duk da bai manta wasu abubuwan ba sai dai suna mai kama da mafarki ne har yanzu ya gasa gasgastan abubuwan da suka faru yasa Cikin son Tabbatarwa ya saki hannun Safiya ya karisa gaban Hajiya ya Durkusa Lokaci daya ya riko Hannunta yana Fadin”Hajiyata..Me ya Faru dani ne..?ina ganin abubuwan kamar a mafarki ne..!
Hajiya tayi mirmishi kafin tace”Saraki komai ya wuce..Allah ne kawai abun godiya..!
Safiyace ta shiga Rattafamai abunda ya faru wanda ta sani da wanda ta gani Sulaiman kamar Reveiw din abubuwan take mai domin yana kallon abubuwan Daki daki kamar alokacin abubuwan suka Faru Kafin ta gama idanuwansa sun kada sunyi Jajir jiyoyin kansa sun mike Radau Cikin Fitan Hayyaci ya Zabura ya Mike Cikin Takaichi yace”Hajiya ki yafemin..Wlh bansan abubuwa sun fara haka ba..!
Yafada kamar zai yi kuka Hajiya kai kawai ta kada idanuwanta na kallon Laila tace”Ba laifinka bane Saraki..Laifina ne dana Dage sai kayi aure..Alhalin Auran ba Alheri bane garemu damu dakai..!
Tafada idonta na cikin na Laila wacce ke gefe Hannunta Dafe da kanta Inda ya fashe nadaman abunda ta aikata ya isheta tana Tunanun yadda abubuwa suka kwabe mata me zata ce ma Mommy..?
Sunaima data ga ba wanda ya Lura da ita sai ta kama Hanya zata Fice batasan Sulaiman shi tuni idanuwansa sun dade da gane masa ita ba.
SUNAIMA..!
cak ta tsaya jin ayadda ya kirata Rabon da yayi mata kira Cikin Zatinsa har ta manta da Sauri ta juyo tana kallonsa gabadaya sai alokacin su Hajiya suka tuna da ita duk da sunga Shigowarta dazu..
Kallonta yake da dukkan zuciyarsa Abubuwan da suka faru Tsakaninsu suna dawo mishi Daki daki bai manta komai ba komai yana Cikin kansa ita kuma bazata iya juran kallonsa ba Domin yana kassara mata jiki wanchan kallon na neman mafaka ne dake ce Duniyata yau kuma kallon nasa na dabam ne dake narka mata Zuciya yana bin Sassan Jikinta Data kasa Jurewa sai da ta sadda kanta kasa.
Cikin muryansa mai cike da Sanyi yace”NAGODE…!
Idanuwa ta lumshe kafin ta Bude ta kada kai so take ta fice kada Kwallar datake faman tare su zubomata Dakyar ta Dago kanta ta kalli Hajiya Cikin Ladabi tace”Barka da zuwa Hajiya..!
Ga mamakinta sai taji ta amsa mata ahankali bata jira wani abu ba ta Juya ta fice dukkansu suka bita da kallo Sulaiman hannayensa ya goya akirji ya Dago yana karema Laila kallo wacce ke ta Hawayen nadama da na sani.
Ajiyar rai ya sauke kafin yace”Hajiya kimin izinin na Saki yarinyar nan don Allah..!
Jin haka yasa Hankalin Laila ya tashi ta Duka kan gwiyoyinta tana Fadin”Don Allah kayi hakuri..Wlh Ina sonka ba Laifina bane..Mommy ce tayu komai Wlh Allah ni ban ma sani ba sai bayan an Daura auran..!
Take Fada Tana gunjin kuka ga goshinta Duk jini kallonta yake yana Tuna Ranar daya fara shigowa Dakin nan Tun lokacin dayayi sallama Laila ta Jiyo abubuwa suka rika faruwa dashi ba Daidai ba baya zuwa aiki duk Tsawon Lokacin nan bai kira iyayensa ba Bai nemi kowa ba.
Hajiya ce ta katssmai Tunani da Fadin”Kada ka saketa Tukunnah ba yanzu ba..So nake ta inda aka Hau a sauka ta nan..Gida zaka Tura taje ma da Salame sakona kafin nan so nake Daganan mu wuce Kargi maimartaba ya Zama shaida kan komai..!
Ajiyar zuciya ya Sauke batare da yayi mgana ba ya taka ya fice Daga Dakin zuwa nasa yana jin wani salama da Farinciki a rayuwarsa.
Yana fita Safiya ta kalli Laila Dake Razfan kuka tace”Sai ki tashi ki Tattara kayanki ki san inda kika Fito..Ki je gida ki fadama uwarki Sako Sauran bayanin sai an kiraku Fadar Takawa sai kuyi cikakken bayani..Hajiya tashi muje..!
Daga haka ta kama Hajiya suka Mike sukavFice suna Fita ta Fadi saman Cafet tana ta kuka ganin ba mafita yasa ta mike tana Layi hannu dafe da kanta ta Nemi wayarta Hajiya Salame take Kira ta shiga ammh Kusan Kira Biyar bata Daga ba sai ta Wurgar da wayar ta fara Hada kayanta Domin komai ya kare in ta zauna kila in Sulaiman ya dawo yayi mata Dukan da zata kasa tashi.
Hajiya kunya bai sa ta shiga Dakin Sunaima ba Dakin da aka Sauki Safiya suka shiga salla suka fara gabatarwa kafin magajiya ta Shigo musu da abinci,Suna ciki suna ci suna maida mgana Laila ta Sauko kasa da tarin akwatinta guda Hudu su marliya suka kama mata zuwa Haraban gidan su kansu gabadayansu sun Tsorata da ganin yanayinta Goshi a Fashe Ba Natsuwa ba komai sai kuka take kamar wacce aka ce uwarta ta rasu megadi tasa ya samo mata adaidaita Ta shiga ita da Tarin kayanta zuwa Tasha Duk tambayansu da marliya ke mata bata amsa ko Daya ba to me zatace..?
Ta tabbata mgana takai kunnen maimairtaba Harda da megadin gidan Sulaiman sai ya zama sheda.
Tana zuwa tasamu Motar Direct zuwa Jos karamar Motace tayi shatanta ita kadai tunda suka fara tafiya take kuka Har ga Allah ba taso Abunda Momny ta aikata ba sai dai bata isa taja da Umarninta ba tana son Sulaiman gashi Auransu ko wata Uku bai yi ba komai ya Lalace Tana ganin Kiran Hajiya Salamen bata Dauka ba to me zata ce mata..?ai sai dai ta Jira gani da ido.
Magajiya da Auwalu megadi kamar an Wanke musu zuciya duk da basu sam abunda ya Faru ba suna da Tabbacin komai ya kare su samira ne sai Sanyin Jiki da Zaran ido.
Sunaima kuwa tana komawa Daki tafada kan gado ta fara kuka,kukan ganin Lokacin Rabuwarta da Sulaiman yayi ne ita batasan ma kukan me take ba azatonta kukan Abunda ta Gudurta aranta take yi batasan kukan Rabuwa da sulaiman bane,Ta riga ta gama yanke mata kanta Shawaran da zarar ya Dawo Hayyacinsa zata nemi ya Sauwake mata ita ba saboda komai tayi komai ba sai Saboda wasim da Wafiyya da marigayiya Sunaira yar”uwanta.
Ita ta Kira inna ta Fadamata Allah ya amshi addu”arsu Sulaimam is Back Inna ta Dinga Hamdala haka ma ita ta Kira Saifullahi ta fadamai domin ai masoyin Sulaiman koda yaushe Cikin Kiranta yake yaji ko an samu wani Chanji.
Shima haka yayi ta Murna yana Godema Allah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button